Sashe 115
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga kan kujerar kawai gani suka yi Rayyan ya zame ya bi kasan tiles basu fahimci abinda yake shirin yi ba sai da suka ga ya sada goshin sa da 'kasan tiles suka fahimci sujudush shukr yayi.....
Anty Madeena kallon sa take yi amma sam hankali da tunanin ta basu a wurin kwata kwata.
Hakika dole a godewa Baiwa, buwaya da kuma cikan ikon ubangiji, bayaga shi wa zai iya wannan abin....Ita kanta 'kwalla take sharewa lkc zuwa lkc.
Bata san kuma me ya rage mata a yanzu da zata yi cikin asbitin ba...hakan yasa ta mi'kewa rungume da Mufeeda suka fita.
Can inda babu kowa ta ke6e ta zauna tana tunani gami da wassafa yadda abubuwan suka kasance...amma still idanuwan ta sun kasa daina tsiyaya.
Rayyan ya da'de yana addu'a gami da nuna tsantsar godiyar sa kafin ya 'dago.
Fawwaz da har lokacin yake tsaye kusa da shi ya rungume yana fa'din thank u so much Fawwaz...
Bai jira cewar komai daga Fawwaz ba kawai yayi gaba.
Parking lot yaje sai dai baiga Anty Madeena ba, dube dube ya fara da jajayen idanuwan sa sai can ya hango ta zaune ta rungume yarinyar sosai.
Anty Madeena ba 'karamin 'kaunar sa take yi ba shi kansa shaida ne ba sai an fa'da masa ba, haka kuma 'kauna da soyayyar ta bata rage kan koda 'ya'yan da suka haifa ba, da kai tsaye za'a iya 'kiran su jikoki agare ta ba.
Hankali ya daga 'kafafu ya taka zuwa inda suke..Anty bata san da tahowar sa ba har sai da ya dur'kusa gefe da ita ganin yanda hawayen ta ke gudu daya bayan daya...duk sai yaji jikin sa ya 'kara yin sanyi.
" Anty Kema kuka kike...?"
Da sauri ta dube shi tana 'ko'karin share fuskar ta.
Tsaye ta mi'ke batare da ta tanka shi ba kawai tayi gaba ya biyo bayan ta.
Ko da suka isa gidan ta bai yadda ya shiga ba,
duk yadda Anty taso ya shigan ko dan yaci abinci ma Rayyan dan tasan mawuyaci ne idan yaci abu yinin ranar kaf amma sam kin shiga Rayyan yayi yace zai je ya dawo.
Tace nasan da kyar ne ka dawo a yau Rayyan, dan haka gargadi zan baka, akan yarinyar nan dan Allah bana so kowa yaji batun nan for now, let it be safe har zuwa wani lokaci kaji? ina tsoron wani abu ne Rayyan sai yanzu nake ji a zuciya ta kamar akwai wasu abubuwa da ba dai- dai suke tafiya ba, ko kuma ince muna tafiya ne da su amma su bayan mu suke hange, dole sai munyi taka tsantsan.. gani nake kamar idan an bayyana ta za'a iya salwantar mana ita da ita, kuma har yanzu bamu san ta ina makiyan mu suke ba balle musan shirin su, baya ga haka ma har yanzu akwai sauran binciken da ba'a kammala ba ka sani..."
" Erh Anty kuma Insha Allah zanyi iya kokari na naga na binciko komai hatta ita Zaitunan, da kaina zan bincike ta..."
" Yauwa hakan yayi, dama dole ne a bincike amma kuma ka tabbatar baka yi shi azafafe ba dan na san halin ka, ko bakomai kuma Zaitun abar jinjina ce agare mu baki 'daya, sannan kayi komai cikin sirri, har ila ban ce kasa Ammi ciki ba tukunna...nafi so a lkcn da labari zai iske ta ya kasance cewa komai ya tabbata ne babu wani sauran kokonto..."
" Insha Allahu Anty.."
" Shikenan...take care.."
Daga hak yaja motar ya sake fita.
Direct gidan sa ya wuce, bai yada zango a ko'ina ba sai 'dakin Nadia, banda kayan gado babu komai, ya riga yasan hakan, dan da sanin sa Ammi ta tattare komai da ya shafi personal life din Nadia.
Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su yana duban gaban mirrorn ta, inda a kullum take zama bayan ta fito wanka" She has already gone far, very far...da yasan bazai ta6a sake ganin ta ba.."
Da 'kyar yake iya 'daga 'kafafuwan sa sbdo nawi da suka yi masa.
Idan har akace wannan 'diyar Nadia ce ya akayi kuma ya ganta da wani jinjiri a wancan hoton da ya samu wajen kundin mutuwar ta...?
Me hakan ke nufi?
Tun 'dazu abinda ke masa yawo aka kenan ya kuma rasa mai bashi amsa.
Kar dai canza masa 'ya akayi aka sace yarinyar aka ajiye mata wanda aka tabbatar baya da rai bayan ansan ta riga da ta koma ga mahalllici?
Wa kenan yayi wannan aika aikan...?"
" Zaitoon!
Wata zuciyar sa ta amsashi.
Da sauri ya motsa kansa..." Ohh noo...bazata iya aikata hkn ba.."
" Then who is behind all these?"
Ko kuma dama karya ake a wancan lokacin ba dagaske bane 'diyar shi tana raye suka ce bata da rai, har suka yi mata hoto da Nadia cikin jini.
Toh indai har hakan ya iya faruwa zai iya zargin matar sa ma tana raye kenan duk da kuwa cewa yasan mutuwa ya kuma san daga Allah ne, amma a zahiri zai iya cewa tana raye duba da wannan kwakkwarar hujja da ta bayyana, babu mmk itama 6atar masa da ita akayi kawai da 'karyar ta mutu.
Amma yasan ba yadda za'ayi ace Nadia na raye tsawon shekaru biyu amma ace bata dawo gareshi ba.
Kansa ya shafo a hankali yana jin 'kirjin sa na yi masa zafi sosai...sam ya mance ma ashe tun safe bai sa komai a cikin sa ba.
Gaban drawern ta yaje ya bu'de yana tuno ranar da zata tafi, ranar da ya kasabce musu rana ta 'karshen ganawar su, kaita airport da yayi shine bankwana na 'karshe da yayi wa ganin ta...har sun fita ta dawo ta bu'de wannan drawer ta 'dauki wani Paper ninkakke ta jefa cikin jakar ta amma bai san ko takaddar menene ba.
Da ya san haka zai faru da tun a lokacin yayi mata wayo yaga takaddar amma Allah bai nufe shi da yin hkn ba, kuma ya tabbata mai muhimmanci ce tunda har Nadia ta bata muhummanci.
Janyo drawer yayi ya bu'de babu komai a ciki, haka na 'kasan sa ma ba komai, 'dayan ma bakomai.
Wasa wasa sai ga Rayyan yabi duk drawers dake cikin bedroom din ya wangale su hatta saman sip 'din ta sai da ya hau abu ya duba amma babu komai da ya gani.
Bai ga komai da ya danganci Nadia cikin gidan ba.
Yasan Aikin Ammi ne, yasan ita ta tattare komai bai kuma san inda ta zuba su ba.
Zama yayi yana maida numfashi.
Shawaran da zuciyar sa ta bashi yabi dan haka ya ciro wayar sa ya kira Ammi.
Tambayan ta yayi ina ta saka kayan Nadia ne yana so zai duba wani abu aciki, Ammi tace ya taho suna nan gida wajen ta.
Dole badan yaso ba ya tashi ya fita zuwa gidan...Ammi kuwa hanyan haduwa da shi take nema dama, yace mata zai shigo tun 'dazun amma bata ga alamun yana da niyya ba, sai kuwa fa'duwa tazo dai- dai da zama.
Kallo biyu bai yiwa 6angaren sa ba ya nufi baban sashen da yake na Ammi...Can saman ta ya same ta..Ammi duba 'daya tayi masa ta fahimci 'yar ramar da yayi"...Rayyan wai lafiyan ka kuwa...?
Ka dubi yadda kake purnishing kanka abanza wai duk menene hakan wai? wani abin ke damun ka da har zai saka cikin wani hali batare da ni nasani ba Rayyan...?"
" Ammi bakomai fa, ki kwantar da hankalin ki dan Allah...."
Ya bata amsa yana zama gefen ta.
" Idan da kasan yadda nake ganin ka bazaka budi baki kace in kwantar da hankali na ba, kar kace min har yanzu batun Nadia bai bar zuciyar ka ba, shin baka san 'kaddara bane kome kake so ka tabbatar min...?"
" Dan Allah Ammi kiyi hakuri, ni duk ba wannan ne damuwa ta ba, taya bazan san 'kaddara ba bacin nima nasan zan mutu yanzu ko anjima..bani da damuwar komai..Nadia kuma da na miki magana abu ne ya taso min da zan duba cikin kayab ta dole...".
" Naji...toh sai ka fa'da min at first place meyasa ka tafi ka bar matar ka da yaron ka tun jiya baka waiwaye su ba? baka san halin da suke ciki ba? ba ka kuma 'kira waya ba...kasan damuwar da ka sanya zu'katan mu a ciki kuwa Rayyan daga jiyan nan zuwa yau...?"
" Ammi dan girman Allah kiyi hkr ku yafe min, abubuwa ne suka taso min da dole sai na gujewa hayaniya kafin zan samu natsuwar aiwatarwa...."
Yayi maganar da rauni sosai ganin halin da yaso jefa mahaifiyar sa ciki.
Ajiyar numfashi Ammi ta sau'ke bata sake magana ba.
Shiru ne ya dan biyo sai ta gyara zaman ta tana jin sanyi cikin ranta.
" Babu ma alamun ka sanya wa cikin ka abu tun safia.."
" Erh Ammi hakane...zan ci abinci amma please bari in gama duba abinda zan duba sannan inyi zaman cin abincin..."
" Wannan ne kuma bk isa ba...".
Zaitoon Ammi ta fara kwallawa kira da gama fadin hkn, da yake nan saman nata take batasha wahalar kiran ba ta kuwa taho da saurin ta izuwa ga Ammin.
Tun 6ullowar ta Rayyan ya kawar da kansa gefe, yana so yaga fuskar ta amma idan ya tuno Mufeeda sai yaji ya tsani komai, tunanin sa yadda ta samu yarinyar shi kadai ne damuwar sa a yanzu.
Ya kuma san abu mai sauki ne gareta yanzu tace zata tambayi 'diyarta da ganin san shiyasa ya kawar da kansa karma taga fuska...
" Barka da Yamma...Yah Rayyan..."
Tace tana mai sunkuyar da kai ta kuma ce " Gani Ammi."
Rayyan bai tanka ba, itama bata damu ba dama tasan hakan ne.
" Ha'do masa abinci kinji ki ha'do da tea mai dan zafi ya fara sha tukunna koda kadan ne ma..."
" Toh Ammi..."
Ta fa'da tana mi'kewa.
Ambatan abinci da Ammi tayi yaji duk shi fa ina bama zai iya cin wani abinci ba...
har ta kusa isa bakin bene da zai sada ta da downstairs yace.." Kinga...!".
A waigo..." idan akwai fruits kawai ki ha'do min ki bar abincin nan..."
Kai ta 'daga masa sannan tayi gaba.