Sashe 54
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muphy ta koma ta 'dauko a inda take zaune gefen da tayi sallah tabi bayan Hajja Ladi zuwa wani sashe mai girma...ashe wancan parloun da ta gani ba komai ba ne wannan shine asalin jindadin rayuwa...Hajia ce zaune ta hakimce gefen ta kuma wani ne da bata ta6a gani ba sai dai yanayin jini da ya bayyana kamanni tsakanin sa da Ammi yasa ta fahimci yana da ala'ka da ita.
Zama tayi ta 'dora Muphy saman cinyar ta tana fuskantar gefeyayin da Zaitun ke fuskar su Ammi ta fara gaisar wa cike da murnar ganin ta, ta kuwa amsa cike da fara'ar da nuna kulawar ta gare su.
Su uku ne zaune a parlorn dan haka shima na da ke zaune gafen Ammin ta gaida shi..
A takaice ya amsa mata tamkar mai ciwon baki yana duba tsadadden agogo dake 'daure a tsintsiyar hannun sa...bata iya ta sake kallon inda yake ba duk da tana jin zuciyar ta na muradin.m sake duban fuskar sa, badan komai ba sai dan kawai son tantance tsakanin shi da Ammi shin wayafi wani kyau ne, amma masifaffen kwarjini ne da shi da ya hana ta sake duban nasa, gaba 'daya ji take kamar ya cika ilahirin 'dakin shi ka'dai.
Kallon sa Ammi tayi tana murmushi tace" Saurin me kake haka ne naga kana wani duba agogo..?"
'Yar murmsuhi yy batare da ya bata amsa ba.
Ammi bata damu da amsar tashi ba sai ta dawo da duban ta ga Zaitun tace" Hajja Ladi ta gaya min abinda ya faru, tace tun tafia ta baki fito kin sha iska ba, meyasa kika za6i killace kanki cikin 'daki bacin na fa'da miki ki saki jikin ki a gidan nan..?"
Shiru Zaitun tayi tana wasa da igiyar rigar Muphy dake kan cinyar ta.
" Ganin hakan yasa Ammi gyara zama ta tana mai cigaba da fa'din" Shikenan..wannan ya wuce, in dai bazaki takura ba duk 'daya ai, amma ina so dan Allah in dai babu wata matsala ki bani labarin ki wala Allah ko akwai taimakon da zamu iya yi miki matsayin mu na 'yan uwanki musulmai."
Shiru Zaitun tayi kawai ta sunkuyar da kanta tana kallon 'kafar muphy gami da wasa da yatsun ta.
" Ina jin ki kinyi shiru Zaitun..?"
'Yar 'karamar tsaki Rayyan yaja yana kawar da kansa gefe haushin ma yarinyar yake ji sosai taya zata wani ringa bata musu lokaci angaya mata su din kamar ita ne da bata bawa lokutan ta muhimmanci ba.
Ammi ce ta banka masa harara sannan ta cigaba da tambayar Zaitun.." ina fatan ba wulaqancin namiji bane ya sa kk baro gida da yarinya?"
A hankali ta 'dago kai ta kalli Ammi sai kuma ta girgiza kanta...alamar a a tana mai saukar da idanu.
Iya zaman ta a gidan ta fahimci kowa Ammi yake kiranta dan haka itama da wannan sunan tayi amfani " Ammi ni bansan me zance mk game da labari na ba..iya abinda na sani shine ni bani da kowa bani da gida sannan bani da iyaye ko yan uwa anan kusa, mun kasance ne tamkar marayu, Mufeedah ka'dai ce yan uwa na ita ka'dai nake da shi a yanzu, lokacin da Allah ya bani mufeedah kusan kowa baya son ta, kowa gudun ta yake yi harda ni ma, kalilan ke nuna mana kauna..amma mafi yawa sunce bazasu iya zama da ni da Mufeedah ba ni kuma ina son 'yata...dalilin haka yasa yanzu.bamu da kowa, nayi 'yan sana'o'i a baya wanda da shine ya taimaka mana babu tagaiyara ba har zuwa lokacin da abubuwa suka gagara muka koma bara a bakin titi...nan ta cigaba da bata labari a ta'kaice na yanda abubuwa suka kasance mta har zuwa ranar da suka hadu a kotu da Ammin.
Ajiyar zuciya hajia ta sauqe gami da furta
" Allah sarki…gaskiya kin sha wahalar rayuwa, kuma banga laifin ki ba da kk matukar son 'diyar ki har kika sadaukar da dukkanin farin cikin ki saboda ita…'ya 'ya Rahama ne kuma ga wanda Allah yaso ka'dai yake bada su...muma da kika ganmu babu abinda muka fi so da kishirwa irin muga yara agidan nan amma Allah cikin ikon sa bai nufe mu da samu ba so ni banga laifin ki ba.
"...Ammi.."!
Rayyan ya kira sunan ta cike da kufula jin kamar Ammi na son ta tona mata sirrin ahalin su ne bacin bama gama sanin takamman wace ita tayi ba.
Tun farkon fara labarin nata matsayin sa na mai shari'a ya fahimci ta 6oye abubuwa da dama bai kuma san manufar ta kan hakan ba, toh meyasa ita zata ji nasu.
Hararan sa Ammi tayi saying.." I know what I'm doing.."
A yadda tayi maganar ba lallai Zaitun ta fahimci warning ta bashi ba tamkar sako ta isar haka tayi maganar, musamman da ta cigaba da fa'din" Allah ya raya mk ita yasa mata albarka ya baki ikon tarbiyantar da ita..."
'Kasa- 'kasa ta amsa da " Amin ngd Ammi..."
" Bakomai Zaitun...sai dai kuma ina da shawara da zan iya baki idan zaki amince, dan agani na shi yafi dacewa akan zaman ki haka nan, duba da irin ha'darurrukan da kika tsallake a baya, gudun faruwar makamanciyar su da ba'a san da wacce siga zasu iya zuwa ba, me zai hana ki koma ga iyayen ki ki basu hakuri ko zasu amince su kar6e ki da yarinyar taki..."
'Dago idanu tayi ta na duban Ammin idanun ta fal tsoro wanda yake har zuciyar ta.
" Kar kiji nace haka kiyi tunanin koran ki nake so nayi daga gida na, sam ba nufi na kenan ba, fatana in kwadaita miki hanyar tsira ne, duk yadda kike tunanin iyaye sun wuce nan Zaitun..kuma dolen mu muyi musu biyayya har mu.rabu da su lafia, kema wannan nake kwadaita mk, kuma kar ki damu ni nan zan miki jagora zuwa garesu insha Allahu kuma ba zasu ki amincewa da zaman ki tare da su ba".
Kai Zaitun take girgizawa a hankali sosai maganar Ammi ta shige ta, wasu sanyayyun.hawaue suka kwaranyo mata...inama inama, inama zata iya hakan, ita oanta bata burin da ya wuce ta ganta cikin halin ta kamar baya amma wani dalili yai mata cikas da hakan.
Abu guda ne zae taka mata birki shine tsoro, a hankali Zaitun tayi 'kasa da idanun ta da suke cike tafi da kwallan da ke sauko mata tace.." Ammi zan koma, ni kaina zan fi son hakan amma dole ba yanzu ba, kiyi hakuri Ammi kar kice na bijirewa shawarar ki, hakika maganar ki ta faranta raina, na kuma gode sosai Ammi, kece mutun ta farko da kika bu'de min zuciyar ki har haka, kece kadai kika nuna zaki iya min jagora zuwa ga iyaye na, amma a yanzu bani da damar hakan Ammi, ko da nace zanyi, rayuwa ta ne da ta Mufeeda zasu iya shiga garari ba mamaki ma mu iya rasa ran mu har ma da wanda zai mana jagoran, bazan so kuma wani abu ya faru dake ba Ammi ta dalili na..kuma kona koma gida a yanzu babu wanda zai fahimce ni babu inda zan samu sauki balle muhallin da zan zauna da yarinyar nan sun riga sun 'kalubalance mu, zasu gani kuma kamar na 'kisu ne saboda yarinyar zasu ga na za6i yarinyar sama da su dan haka tsanar da akai mata bazai ragu ba sai dai ya karu amma na tabbata akwai lokacin da su da kansu zasu fahimce ni, a lokacin da na tabbatar ko da na koma gare su takuran da zasu yiwa Mufeeda bazai iya tasiri ba dan zata iya 'dauka, Ammi nafi so sai shekarun Mufeeda sun kai wani matsayi kafin zan koma, a lokacin da na tabbatar da ita kanta zata iya bawa kanta kulawa, koda bata tare dani, amma a yanzu ni.kadai ta sani, ni kadai ta budi ido ta sani, mufeeda bata saba da kowa ba sai ni zuciya ta bazata iya 'daukan rabuwa da ita ba".
" Shikenan Zaitun, bazan takuraki ba..duk shawara da kika yanke.bi mai goye mk baya ce, fatana kawai shine ki.kasance yarinya mai.biyayya ga mahaifan.ki, kar ki kuskura wasu abubuwa dake cikin.duniyar su ra'de ki ga barinvhanyar tsira..."
" Insha Allah Ammi...".
Ajiyar zuciya Ammi ta saki tana mai fadin.
" Allah ubangiji yayi mana jagora..."
"Ameen ".
Zaitun tace yayin da Rayyan kamar ba shi cikin 'dakin, banda danna wayar sa babu abinda yake yi..kokadan bai sake duban daya cikin su ba amma duk tattaunar sun akan kunnen sa ne, haushi ji yake tamkar zuciyar sa zata yi bindiga.
Meyasa Ammi.ta kasa fuskanta, yarinya karama ta zauna sai ninke take a baibai, dama taya ma za'ayi ta koma ga iyayen ta tasan ta tafka abun kunya in tama da kunya ai dole ta nisance su.
Zaitun kam sake rungume Mufee tayi tana jin ninkin 'kaunar yarinyar cikin zuciyar ta, wani irin so take wa yarinyar, wani irin zazzafan kauna da soyayya, a yanzun ne ma take jin zuciyar ta na sake 'daura sabuwar aniyar bata kulawa.
Tun daga ranar kuma ta fara aiki da sauran ma'aikatan gidan, kullun tare suke aiki a kitchen 'din da su Hajja Ladi duk da ba wani sakin fuska take samu daga wurin ta ba amma da yake akwai Raleeya sai bata damuwa sosai.
Amma ko aiki take yi a kitchen ba ta nutsuwa ta ringa raba hnkl kenan musamman idan tasan ta bar Mufee na bacci a 'daki ta ringa zarya kenan tana zuwa duba ta tana dawowa, wai dan kar ta tashi taga bata nan tayi kuka, a ba'dini kuwa ba manufar ta ka'dai kenan ba, tsabar rashin yadda ne, dan har alokacin zuciyar ta bai sake a gidan ba, gani take kamar zasu cutar mata da yarinyar watarana.
Raleeya na shan mata dariya, wani bin kuma kawai goye abinta take abaya tayi aikin da ita a haka amma sai in tana bacci, in ba haka ba matukar idanun Mufee biyu bata yadda da goyo ta ringa 'kananun kuka kenan har sai ta sau'ke ta.