← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 218

Sashe 137

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefe ta karya wuyan ta tana jin babu dadi, kukan take itama cike da tausayin 'diyar ta, rikon da yayi mata kadai abin a tausaya ne, domin tamkar wani sa'an sa ko kuma wani abin cutar wa ya damko haka yayi, hala ya mance ne cewar 'yar yarinya Mufeeda ce a hannun sa ba wani daban ba.

Tasan sarai yana sane tunda ba makaho bane shi ba kuma hauka yake ba cikin hankalin sa yake komai.

Wannan wace iriyar rashin imani ne haka wai...?"

Magana akayi masa cikin wata 'yar abin magana dake ma'kale jikin kunnen sa, hakan yasa ya ajiye mata 'diyar ta da ya fizgo ya fita.

Tamkar jira take ta janyo yarinyar jikin ta ta rungume sosai suna sakin wani sabon kuka atare...Mufeeda na fadin..." Mammi..." Zaitoon na fadin Mufee na...Allah yana gani, kuma nasan zai saka mana tunda ba komai muka yi musu ba.."

Can gida kuwa hankula duk sun tashi an rasa Zaitoon da 'diyar ta ba 'a san inda suka yi ba, 6at babu su sama ko 'kasa ba'a gansu ba.

Babu wanda hankalin sa bai tashi ba kowa kuma tunanin da zuciyar sa ta basa daban, kowa tunanin 6acewar Zaitoon 'din fassara ya bashi na daban in ka 'dauke Ammi ka'dai da sam zuciyar ta ya kasa bata takamamman dalili guda da zai sa arasa su gaba 'daya.

Kar ma ka tona zuciyar Rayyan da Anty Madeena da masu ra'ayin fassarar ya bambanta da na kowa, banda luguden gudu gami da fargaban abinda ke shirin tunkaro su da yai tsaya musu karan tsaye a 'kirji tamkar suyi bindiga haka suke ji cikin zuciyar su... _wannan shine ta leko ta koma._

Marwa kam kuka take sosai, bata ta6a sanin sha'kuwar su ta kai har hakan ba sai yanzun da aka rasa su.

Gida yayi zugum gaba 'daya, hatta Raihana da sauran 'yan uwa tuni labari ya iske su, domin da yawan su sun san Zaitoon musamman lokacin rashin lafitar Rayyan da suka zo dubiya a wannan lkcn da yawan su suka santa...yanzu kuwa da akace babu ita babu wanda bai jimanta ba illa 'kalilan da suka kasance mahassada daga cikin su.

Wani bin Ammi har na mamakin yadda damuwar Anty Madeena ya kasa 6oye kansa, bata san dalili ba amma yanayin damuwar ta ta sosai ya sa Ammi dasa ayar tambaya akan sa, ba zallan sha'kuwa take ganin alamun tasirantuwar sa akan fuskar Anty Madeena ba, zallan damuwa ce dake tasowa tun daga 'kasan zuciya, bata iya dannewa damuwar ta dai- dai da 'kwayar zarra ba, dan ko Marwa bata kai ta shiga tashin hankali a zahiri ba.

Kamar dai yadda ta kasa gane kan Rayyan kwata- kwata, 'kunci ne ko damuwa ko kuwa fargabar rashi na har abada ya sa shi fita hayyacin sa bata sani ba, abu guda da ya bambanta yanayin su shine kawai kasamcewar sa 'da namiji, hakan kuma ya bashi damar dauko jarumta ya sanya wa zuciyar sa da in ba sanin kwaf kai masa ba bazaka ta6a fahimtar halin da yake ciki ba, ita ma 'din sanin sosai tai masa shiyasa tayi saurin fahimtar sa, abinda ta kasa fahimta daga gare shine, shin damuwar 6acewan matar sa ne ya dame shi ko kuwa damuwar sa dan sun 6ace ne 'karkashin inuwar su...?
Ta kasa tantance makomar damuwar Rayyan sam kuma yaki bada 'kofar da za'a fahimta cikin sauki.

Kuma shi har Anty Madeena har lkcn sun kasa fitar da abinda ke ransu, dan lkcn fa'dan ba shine mai muhimmanci ba a ganin su, samun su shine kan gaba a halin yanzu.

Hatta baccin dare kuwa 'kalilan cikin gidan ne suke samun yin sa...sbd tsantsar damuwa.

Rayyan abin yafi 'kona masa zuciya sosai, domin tunanin sake rasa 'diyar sa akaro na biyun nan bazai iya dauka ba gefe guda kuma ga auren sa, sai dai bai damu da auren nasa sosai kamar yadda diyar sa ta tsaye masa ba, abaubuwa da dama da yake shirin kammalawa game da ita bai samu yayi ba, karashen binciken tushen lamarin duk bai yi ba, a tunanin sa Zaitoon ta gudu masa da 'diya hakan yasa natsuwa tai masa nisan zango, burin sa kawai ta dawo masa da 'diyar sa ne.

Fa'di yake cikin ransa" lallai wannan yarinya ta gama raina ni, wallahi sai na bata mamaki, sai na nuna mata asalin waye ni, dani take zancen.

Tun dawowar sa daga fitar da yayi da ya shigo bai tarar da dasu a gida ba, da farko ya 'dauka suna can 6angaren Ammi ne shiyasa bai damu ba, yazo yayi tunanin ko sun 'dan fita ne amma still sshiru bayan lkc yaja sosai y fara binciken gateman nan ya samu labarin cewa tun fitar safe da da ta mika Mufeeda skul basu dawo ba.
abin kamar wasa amma sai gashi wankin.hula na nemen.kai su izuwa dare.

Wasa wasa ana neman cike kwanaki biyu cikin na uku babu su babu dalilin su.

Rayyan sai da aka Ammi ta dage kafin yake 'dan samu ya sanyawa cikin sa wani abu, har ya fara komawa 'yar gidan jiya bayan murmurewar da ya samu yayi cikin kwana kin da suka gabata...

Ganin fa dagaske lamarin ke shirin tabbata yasa fargaba da tashin hankalin sa 'kara hauhawa zuwa wani matsayi, har takai ta kawo motsa jikin sa bai isa yayi ba sbd tsantsan ciwon kai da 'dan hawa da jinin sa yayi ya haddasa masa.

Kullum tunanin sa ta ina zai fara nemo inda Zaitoon ta shiga masa da yarinya ne.

Sai a kwana na ukun kafin ya samu wani 'kira da wata numbern da bai da ita ma sam cikin wayar sa.

Bai ta6a zaton wai sace su Zaitoon akayi ba hakan yasa ko bi takan wayar bai yi ba ba, aganin sa damuwar da yake ciki ta zarta zaman amsa wayar da zai yi da koma wanene a halin yanzu.

Rayyan ko tuna cewa baya da isashshsen lpy bai yi, shaf ya mance da halin ciwon da yake ciki...ko da lkcn komawar sa asbiti yayi ma bisa ga ranar da aka basa bai tuna ba balle ya samu damar komawa.

Tuni ya mi'ka cikiya kafafen sadarwa both gidan talabijin da redio stations ya kuma sake musu makudan ku'da'den da yasa suka isar masa da sakon sa da zafi zafi, haka kawai yake ji aransa cewar duk inda Zaitoon ta shiga masa da yarinya bai wuce nan cikin Kano ba, hakan yasa ya cigaba da gudanar da binciken sa ta gefe guda.

A dai- dai lkcn ne kuma wata 'kira ta sake shigo masa...akaro na adadin da bazai iya kiyastawa ba.

Wannan karon a zuciye ya kai hannu ya janyo wayar da niyyar masife mai 'kiran...

Sai dai tun lkcn da sautin muryar mai 'kiran ya doki kunnen sa yaji komai ya kwance masa...tsaye ya mike yana takawa a hankali yana dawowa 'karshe zama ya koma yayi yana mai jin kansa na sarawa.

Batare da wani 6ata lokaci ba suka sanar da shi cewa Zaitoon da Mufeeda na hannun su ne.

Ya shiga firgici da tashin hankali fiye da zaton mai karatu domin bai ta6a kawowa cikin ransa cewar hakan ne zai faru ba kwatsam sai gashi sigar da abin ya koma, ya kuma rasa kalmar da zai fada musu su fahimce shi.

Taya akayi haka? ya akayi suka san Zaitoon har suka 'dauke ta, ya akayi suka san da cewa akwai dangantaka tsakanin mu, a ina suka ganta? yarinyar da bama fita take agida ba, kuma waye ya basu family number 'din sa da har suka samu daman 'kiran sa da shi.

Abinda ya tsaya tunani kenan bai samu damar basu amsar tambayar da sukai masa ba, infact bai ma ji 'karashen bayanan nasu ba balle ya amsa su.

Ji kawai yayi wayar ta yanke, kuma ya bi 'kiran atake bayan furzar da numfashi da yayi amma sam baya tafia.

Bayan kamar mintina talatin wani 'kiran ya sake shigo masa.

Sai dai wannan karan 'kiran daga Anty Madeena ne, sun yi magana da ita ya kuma sanar mata bayanin da akai masa, ita ma mamakin ne ya kamata.

Duk yadda Rayyan ya so bibiyar layin abin ya faskara domin sun toshe duk wata kafa da zai iya bayyana su, amfani 'daya suke da layi shikenan ya tashi a aiki, duk yadda kaso bibiya kuma bazaka ta6a tarar da abinda kk da buri ba, hakika ba 'karamin sani suka yiwa na'ura ba domin alamu sun nuna hakan 'karara, shikan sa Rayyan ya tabbatar da haka.

Kusan za'ace babu wanda hankalin sa bai sake tashi akan na baya ba da jin cewa garkuwa da su akayi.

Basu sake kiran sa ba har sai washegari bayan an fito sallar maghrib.

Da sauri ya 'daga domin dama 'kage yake da son sake magantuwa da su duk da yake ba wancan numbern bane amma cikin lkcn tsammanin kiran su yake a kowani irin time dan yasan dole zasu sake 'kiran sa...ya riga ya gama yankewa cikin ransa cewar ko nawa suke da bu'kata a shirye yake ya basu matukar dukiyar sa zata kai indai zasu sako masa su.

Sai dai ga mamakin sa a yadda ya tsammaci lamarin ba a hakan ya zo masa ba. Maganganun da sukai masa ba 'karamin tashin hankali suka sake sanya shi ba, gaba 'daya ma sai ji yayi 'kwa'kwalwar sa na neman tsayawa da aiki.

Dagaske wa'dannan ba kidnappers bane ma'kiyan sa ne...cikin kalaman su ya fahimci hakan..ya kuma tabbatar tabbas ba hakanan kawai bane..dole akwai ha'din gwiwa ciki.

Domin basu nemi ku'di ba kamar yadda ya tsammata, za6i kawai suka bashi na wanda za'a kashe acikin Zaitoon da Mufeeda ya za6i guda...a kuma kashe guda.

Wannan batun ba 'karamin ta'azzara tunanin sa yayi ba, gaba 'daya komai ya kwance masa, babu abinda ke kaiwa da kawowa a jikin sa sai da yaji komai ya tsaya masa cak.

Bai san lokacin da ma ya nemi waje ya zauna ba..." A wani dalili kenan...?"
Ya jefa musu tambayar yana mai baiwa kansa 'kwarin gwiwa.
" Umarni ne...na wa cikawa..."!
Aka bashi amsar da ba ita yake da burin ji ba.
Chapter 137 · 0% Book details