Sashe 36
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu kam bashi kuma da wani buri a rayuwar sa illah kawai yaga ya kar6i hikuncin sa daidai da abinda ya aikata.
Ranar zaman kotun da ya kasance na karshe, kuma shari'ah ta karshe da za'a gabatar a ranar, a kuma ranar Dr Rasheed ya tabbatarwa kotun cewa Zaitun da Hameeda basu da hannu kuma basu san komai da ke faruwa kan lamarin ba, sai dai duk yadda kotu ta so bincike da gano sauran abokan harkar tasa Dr Rasheed bai bar kofa ba.
Haka dole badan kotu taso ba ta yanke musu hukunci shi da 'Dan Malliki bisa tsari na na dokar kasa.
Kafin atashi a zaman kotun ma aka sanar da dakatar da aikin asbiti da aka yiwa Dr Rasheed shima bisa tsatstsauran dokar takaddun sa bazasu sake yin aiki karkashin kowace ma'aikata ba daga ta gwabnati har wadda ma ba gwabnatin ba.
Wannan shar'iar ta matukar daukar hankalin dubban mutane kowa na mamaki kan yadda zuciyoyi ya gur6ace kan tara dukiya kadai, inda Allah ya taimaki Dr Rasheed ma bai ta6a 'daukan ran kowa ba duk wasu furuci da yk yi duk burga ce kawai sbd ya tsoratar amma ba wai dan ya ta6a yin kisan ba, wannan dalilin ne ya sa kotu ta yanke masa shekaru ashirin gidan yari batare da aikin wahala ba dan bai wahal da shari'a ba, yayin da shi jagaban aka yanke masa shekaru ashirin da biyar.
Daga 'karshe kotu ta sallami Zaitun da Hameeda ta kuma wanke su kan cewa basu da laifin komai, Dr Basheer ne ya nemi iznin kotu inda yayi amfani da wannan damar ya nemi yafiyar Zaitun da Hameeda bisa wahalhalun da suka sha sanadin sa ba tare da hakkin su ba.
Sai a lokacin Zaitun taji wani 6angare na damuwar dake cikin zuciyar ta ya zagwanye...tsabar farin ciki ma sulalewa tayi a wajen kawai tana sakin kukan farin ciki me ta6a zuciya, bata da kowa, bata da wani da zai zo ya rungume ta kamar yadda taga an baibaye Hameeda ana ta koke koke da farin cikin wanke ta da kotu ta yi.
Sosai take jin kewa na shigan ta ta kowani 6angare , tasan ba ahali ta rasa ba, ba masu kaunar ta ta rasa ba, ba kuma wa'danda zasu koka da al'amuran ta ta rasa ba, amma yau 'din sai take jin daban, haka kawai take so itama ta samu majingina, tana so taga me taya ta farin ciki da wannan rana.
Yah Bukar!
Tasan ya mata nisa.
Mahaifiyar ta ma haka.
Mahaifin ta tasan yafi karfin shirmen ta tun asali.
Adam Shaheed...shine ya fado mata amma tasan bazai zo ba, bazai ta6a zuwa ya tayata farin ciki ba alhali ana kokarin kulle mahaifin sa a magar'kama.
Comment
Vote
Share
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...25*
.....A hankali ya sau'ke labilen windon 'dakin nasa yana sakin 'karamar ajiyan numfashi wacce zahiri a hakan zaka iya kiran ta amma a badini shi ka'dai ya san zafin da hakan yake masa a kirji da cikin zuciya, rabon da yayi farin ciki da wahala tun rabuwar sa da Zaitun na farko, raban da aga cikakkiyar fara'a kan fuskar sa koda ta ya'ke ce tun ranar da yaji sunan wanda mahaifi yake gareshi a kotu matsayin shugaba kuma mai 'daukan nauyin ta'addanci, duk da yake ba wata kwakkwarar ala'ka ko shakuwa ke tsakanin su ba amma sosai abin ya dame sa ya kuma tsaye masa a zucia..wannan kalma ta iyaye mahaifi da mahaifiya ba 'karamin tasiri suke da shi azuciyar kowani halitta ba, duk yadda yakai ga tsanar halayyar mahaifin nasa amma deep down yana jin kauna da kewar rashin shakuwa dake tsakanin su, sai dai munanan halayen mahaifin nasa su suka han komai yin tasiri game da shi.
Gaba 'daya sai ma ya kuma ji mutumin ya sake fice masa aka, musamman da ya kasance dalilin damuwar halayyar sa yasa ya sake rasa damar ganawa da Zaitun a karo na biyu, meyasa a ko wani lokaci da gi6i yake barin zuciyar sa ne? meyasa koda wani lokaci rashin nasara ke gilmawa tsakanin sa da mahaifin nasa? meyasa son zuciya da son kansa sukai masa yawa? meyasa sam bashi da tausayi cikin zuciyar sa? meyasa, meyasa abubuwa da dama?
Idanu ya lumshe fahimtar da yayi cewa hawaye ke bin fuskar sa, aikin kenan, abinda a mafi yawan lokuta ke faruwa matukar haduwa ta hada shi da mahaifin nasa shine zubda kwalla, kusan a kaf 'din rayuwar sa mahaifin nasa shine mutun na farko da ya kasance me sashi zubar da kwalla, in dai kaga Adam na hawaye toh yaci karo ne da takaicin 'daya daga cikin halayyar mahaifin sa dalili kenan da ya sa a mafi yawan lokuta yake kalubalantar ha'duwa da shi.
Akan mutun me irin wannan 'dabi'a shine Hajiya zata yi iya bu'dan baki har tayi tutiya da alfahari dan sun kasance makusantan sa?, shin mancewa Hajiya tayi ne da wuri haka?
Xuciyar sa ke zayyano masa wannan tambayar yana dafe da kansa.
Mutun irin wannan shine Hajiya take kafa hujja dashi cike da ya'kini ta shiga tsakanin sa da Zaitun a wani dalili...?
Sam bai san ma miye ya canza Hajiyar tasa har haka ba, ba mamaki kwata- kwata ta mance ne da waye asalin Jibrin 'Dan Maliki a gareta, may be ta mance ba'kin cikin da ya dasawa zuciyar ta abaya.
Da bayan yatsar hannun sa manuniya ya 'dauke 'kwallan da ke bin idanun sa yana me zama bakin gadon sa ha'de da lumshe idanu...tunanin rayuwar sa ta baya ya fara dawo masa cikin kwakwalwa.
~~~~Cikakken sunan sa shine _Adam Shaheed Jibrin 'Dan- Maliki_ , ya kasance 'da kwara 'daya tilo ga mahaifin sa da ake kira 'Dan Maliki tun zamanin kuruciya, shi kadai kuma ya mallaka a fa'din duniya baki 'daya, duk da yake bai taso gaban mahaifiyar sa ba amma bai ta6a kokawa saboda rashin gata ko kan wani abin ba, hasalima bai taso yaga mahaifiyar sa ba sai dai a photo, bai ta6a jin sautin muryar ta ba sanadiyyan rasuwa da tayi tun bayan da ta haife shi duniya tace ga garinku nan.
Yana taso ne gaban makwafi agare ta, domin bayan dangataka ta jini akwai tarin kama 'kak'karfa tsakanin mahaifiyar sa da Hajiya Talatu.
Hafsat macece mai tarin ilimi, hakuri, natsuwa da nagarta, ta kasance 'kanwa ga Hajiya Talatu wanda su biyu kacal iyayen su suka haifa kafin su bar dunia, sun kuma koma ga mahaliccin su sanadiyyar ambaliyar ruwa da ya afka da su a wasu shekaru can baya wanda a lokacin Hafsat da yayar ta sunje hutu wajen wani Baffan su ne wato 'kanin mahaifin su kafin dawowar su ne lamarin ya auku.
Sun yi kuka sun kuma shiga damuwa gami da tsananin alhini saboda rashin mahaifan nasu amma daga baya duk suka dangana suka fawwalawa Allah komai, haka suka cigaba da rayuwa cikin maraicin uwa da uba, sun ga kalubale da dama wajen dangin su saboda mahaifin su asali ba wadata bane dashi sosai amma akwai cikakkiyar wadatar zuci, basu gaji komai daga mahaifin nasu ba sai gona guda 'daya sai dai tana da girma ba laifi.
Basu tashi sanin basu da cikakkiyar gata ba sai da suka rasa mahaifan nasu aka kuma rasa cikakken wanda zai kar6e su da hannu bibbiyu ya rike su ya kuma basu gata da kulawa, 'karshe karatu ma gagarar su tayi saboda rashin wanda ze biya musu kudin makarantar, haka kuma batun gonar mahaifin su ma basu samu cikakken bayani akan ta ba.
Lokacin da Hajiya Talatu tayi auren ta na farko tare da Hafsat ta fara zama domin a cewar ta hankalin ta zai fi kwanciya ne idan tana ganin Hafsat din tare da ita, ta bayyana hkn ne kawai amma ita ka'dai cikin zuciyar ta tasan dalilin ta, irin dabdalar da akayi wajen aurar da itan kadai yafi tsaya mata a zuciya, wadanda suke gani sune jigo agaresun da kyar suka hada suka sama mata kayan dakin da suka aurar da ita bayan an sha gwagwarmaya da kai kawo, har da su fa'dace fa'dace sbd rarrabuwar kai da aka samu, a lokacin wata zuciyar har na zuga ta kan kawai ta fasa auren ma gaba 'daya, Hafsat ce ta ringa tausan ta da ban baki har aka kammala komai aka mi'ka ta da'kin ta komai sai a hankali, a fili zaka fahimci cewa maraici da rashin gata na tattare da rayuwar ta karara, cikin sa'a kuma sai Allah ya bata miji me kaunar ta da fahimta bashi da tashin hankali.
Wannan dalilin yasa taji sam bazata iya barin 'yar uwar ta cigaba da zama tare dasu ba zata rike ta gaban ta har zuwa lkcn da itama Allah zai bata mijin aure domin tozarcin da akayi mata ma ka'dai ya isa, bazata juri ganin na 'yar uwarta a nan gaba ba.
Allah cikin ikon sa sai ba'a jima ba itama Hafsat batun auren ta ya taso dan already dama ta zama budurwa matashiya, ko lokacin auren kuwa Hajiya Talatu taso ta nuna kin amincewar ta sakamakon shaidar rashin halin kwarai da aka yiwa manemin nata Jibrin 'dan Maliki, amma Hafsat ta nuna tirjiya da zallar kaunar da take yi masa ga yayar tata, a lokacin kwata- kwata shekarun ta basu fi goma sha shida zuwa sha bakwai ba, amma hakan be sa ta zama me ragaggen tunani ba, ba tsananin so ba ne ba kuma kauna kakkarfa ba, ba wai ta 'kagu tayi aure bane, ba kuma gajiya tayi da zama da 'yar uwarta tata ba, kawai gani take kamar tsarin zaman nasu be mata ba, so take ta basu fili su sarara suma a gidan auren su, musamman ma shi mijin 'yar uwar ta ta, mutun ne mai tsananin sanyin halayya hakuri da kawaici, bai fiye nuna gajiyawar sa kan abu a zahiri ba, wannan dalili ya sanya take gani kamar koda tana takurashi bazai nuna ba, koda tana hana shi sakewa cikin gidan sa bazai ta6a nunawa ba, dan duk abinda 'yar uwar tan ke so shima mara mata baya yake, sosai yake tsananin tausayawa maraicin su so bata so su kure shi.