Sashe 39
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Kalilan daga cikin farin cikin ta ne ya 'karu duk da kuwa nauyin da take ji akan kirjin ta sosai ya ragu tunda kotu ta wanke ta, zama a iya cewa bakin cikin ta ya kau gaba daya, amma kasancewar ta da wannan dattijuwar matar ne bata san dalilin sa ba, bata kuma san me yake nufi ba bata san makamar ta balle tasan karshen ta, ba tasan kuma inda za'a jefa ta ba, musamman da taga sai tafiya ake bb kakkautawa, abinda ya tsaye mata kenan a zuci sai kuma wani tabo daya kasance cikin zuciyar ta da har abada bata jin zata iya mancewa da shi.
Azaman cell da prison din nan idanun ta sunga abubuwa da dama...taga abubuwan da 'karamar kwakwalwar ta bazata iya mancewa da su cikin sauki ba, ta kuma koyi wasu abubuwan da kila su taimake ta ne a rayuwar ta ta nan gaba, ta koyi hakuri ta kuma koyi rashin sa, ta koyi kawar da kai sai dai ba akan komai ba.
" Ina so ne in raba ki da yawon barar da kk ce shi kk yi shiyasa na dawo zan kuma nesanta ki da garin Bauchi ta yadda babu wanda zai kara tunawa da kema balle a tuna yawon bara kike uwa uba a tuna cewa an ta6a shari'a a kotu da me irin kama da ke, nafi son koda zaki dawo Bauchi ki dawo cikin wani yanayi na daban, ban dauke ki dan cutar da ke ba sai dan in tallafawa rayuwar ki sanadiyyan tausayin ki da ya shige ni tun a zaman kotu na farko, nima 'din Lauya ce ta kasa kuma ina aiki da kungiyar tallafawa mata gajiyayyu da kananun yara...fatan zaki bani goyon baya ki saki jikin ki dani...?"
Shiru kawai Zaitun tayi tana mamakin furucin Matar nan, ita aganin ta ai wannan shishshigi ne ba komai ba, bayaga hk ina ruwan ta da su da wata rayuwar su..bata fa bukatar taimakon kowa ma a yanzu ita.
Bakin ciki ma sai ya hanata furta komai kwata- kwata, inda taimakon zata yi mata ma dagaske da kudi ta bata ta nemi haya ta kama inyaso sai ta nemi wata sana'ar tayi...Kamar dai yadda tayi abaya farkon zuwan ta.
Duk da tasan wancan lkcn da kuma yanzu da banbanci, a yanzu mawuyaci ne ma jama'ar garin su kar6e ta cikin sauki, ko abaya ma tasha wahala kafin a kar6e ta balle yanzu da ta kasance tana da mugun tabo a goshin ta.
Duk da hakan batayi 'kasa a gwiwa ba ta bayyanawa Hajiyar ra'ayin ta...sai kawai tayi murmushi.." Kar ki damu can 'din ma in kinaso zakiyi aikin...ita kuma wannan fa...?"
Hajiyar ta 'kare da tambaya tana nuna Mufeeda.
Kallon Mufeedan tayi dake lumshe ido alamar son yin bacci a hnkl ta bata amsa da fa'din.." 'YATA CE".
Jinjina kai tayi tace
" Masha Allah, amma meyasa ban ta6a ganin wani naki ba a duk zaman kotun da ake yi...har yau 'din nan da ya kamata ace 'yan uwan ki na nan tare dake saboda murnar saukan hukuncin kotu akanki banga kowa tare dake ba..meyasa...?"
Baki ta 'dan tura gaba tayi 'kasa da kanta sbd ba shine cikakkiyar maganar da taso ji daga bakin Hajiyan ba...tana so ne taji ina zata kaisu.
" Sbd bamu da kowa ne Hajiya...".
Amsar da ta bata kenan kawai tana gyara zaman Mufeeda a jikin ta.
" Wa'danda naga sun kawo mk yarinyar nan 'dazu a..."
Bata ma jira jin karshen tambayar Hajiyan ba tayi saurin bata amsa da fa'din..." Mahaifiyar Dr Rasheed ce da 'kannan sa, ta rike min ita ne tun lkcn da aka shigar da mu cell tun a farko..."
Hajiyar kam sai ta jinjina kai tana 'dan murmushi jin yadda Zaitun ta bata ansa a fizge tana sake duban ta tace..." Ta kyauta gaskia ta kuma yi abinda ya dace, toh amma ina mijin ki fa, I mean mahaifin 'diyar taki...?"
Zaitun bata ma san lkcn da ta zaro idanu tana kallon fuskar Hajiyan ba, dagaske wai amsa take jiran ji daga bakin ta? shiru motar ta 'dauka kamar bazata yi magana ba sai kawai taji 'kwalla na zubo mata, kenan kowa sai ya tambayi mahaifin yarinyar ne, kaddai itama Mufeeda watarana tayi mata wannan tambayar me zata ce da ita kenan?...cikin sanyi can ciki ta tsinci bakin ta da furta.." Marainiya ce....".
Sosai Hajiyan ta tausaya mata inda tayi mata addu'a cike da alhini gami da tunanin mahaifin Mufeedan ne ya rasu...daga nan bata sake yi mata tambaya ba har suka tsinci kansu cikin garin Kano.
Vote
Share
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...25*
.....A hankali ya sau'ke labilen windon 'dakin nasa yana sakin 'karamar ajiyan numfashi wacce zahiri a hakan zaka iya kiran ta amma a badini shi ka'dai ya san zafin da hakan yake masa a kirji da cikin zuciya, rabon da yayi farin ciki da wahala tun rabuwar sa da Zaitun na farko, raban da aga cikakkiyar fara'a kan fuskar sa koda ta ya'ke ce tun ranar da yaji sunan wanda mahaifi yake gareshi a kotu matsayin shugaba kuma mai 'daukan nauyin ta'addanci, duk da yake ba wata kwakkwarar ala'ka ko shakuwa ke tsakanin su ba amma sosai abin ya dame sa ya kuma tsaye masa a zucia..wannan kalma ta iyaye mahaifi da mahaifiya ba 'karamin tasiri suke da shi azuciyar kowani halitta ba, duk yadda yakai ga tsanar halayyar mahaifin nasa amma deep down yana jin kauna da kewar rashin shakuwa dake tsakanin su, sai dai munanan halayen mahaifin nasa su suka han komai yin tasiri game da shi.
Gaba 'daya sai ma ya kuma ji mutumin ya sake fice masa aka, musamman da ya kasance dalilin damuwar halayyar sa yasa ya sake rasa damar ganawa da Zaitun a karo na biyu, meyasa a ko wani lokaci da gi6i yake barin zuciyar sa ne? meyasa koda wani lokaci rashin nasara ke gilmawa tsakanin sa da mahaifin nasa? meyasa son zuciya da son kansa sukai masa yawa? meyasa sam bashi da tausayi cikin zuciyar sa? meyasa, meyasa abubuwa da dama?
Idanu ya lumshe fahimtar da yayi cewa hawaye ke bin fuskar sa, aikin kenan, abinda a mafi yawan lokuta ke faruwa matukar haduwa ta hada shi da mahaifin nasa shine zubda kwalla, kusan a kaf 'din rayuwar sa mahaifin nasa shine mutun na farko da ya kasance me sashi zubar da kwalla, in dai kaga Adam na hawaye toh yaci karo ne da takaicin 'daya daga cikin halayyar mahaifin sa dalili kenan da ya sa a mafi yawan lokuta yake kalubalantar ha'duwa da shi.
Akan mutun me irin wannan 'dabi'a shine Hajiya zata yi iya bu'dan baki har tayi tutiya da alfahari dan sun kasance makusantan sa?, shin mancewa Hajiya tayi ne da wuri haka?
Xuciyar sa ke zayyano masa wannan tambayar yana dafe da kansa.
Mutun irin wannan shine Hajiya take kafa hujja dashi cike da ya'kini ta shiga tsakanin sa da Zaitun a wani dalili...?
Sam bai san ma miye ya canza Hajiyar tasa har haka ba, ba mamaki kwata- kwata ta mance ne da waye asalin Jibrin 'Dan Maliki a gareta, may be ta mance ba'kin cikin da ya dasawa zuciyar ta abaya.
Da bayan yatsar hannun sa manuniya ya 'dauke 'kwallan da ke bin idanun sa yana me zama bakin gadon sa ha'de da lumshe idanu...tunanin rayuwar sa ta baya ya fara dawo masa cikin kwakwalwa.
~~~~Cikakken sunan sa shine _Adam Shaheed Jibrin 'Dan- Maliki_ , ya kasance 'da kwara 'daya tilo ga mahaifin sa da ake kira 'Dan Maliki tun zamanin kuruciya, shi kadai kuma ya mallaka a fa'din duniya baki 'daya, duk da yake bai taso gaban mahaifiyar sa ba amma bai ta6a kokawa saboda rashin gata ko kan wani abin ba, hasalima bai taso yaga mahaifiyar sa ba sai dai a photo, bai ta6a jin sautin muryar ta ba sanadiyyan rasuwa da tayi tun bayan da ta haife shi duniya tace ga garinku nan.
Yana taso ne gaban makwafi agare ta, domin bayan dangataka ta jini akwai tarin kama 'kak'karfa tsakanin mahaifiyar sa da Hajiya Talatu.
Hafsat macece mai tarin ilimi, hakuri, natsuwa da nagarta, ta kasance 'kanwa ga Hajiya Talatu wanda su biyu kacal iyayen su suka haifa kafin su bar dunia, sun kuma koma ga mahaliccin su sanadiyyar ambaliyar ruwa da ya afka da su a wasu shekaru can baya wanda a lokacin Hafsat da yayar ta sunje hutu wajen wani Baffan su ne wato 'kanin mahaifin su kafin dawowar su ne lamarin ya auku.
Sun yi kuka sun kuma shiga damuwa gami da tsananin alhini saboda rashin mahaifan nasu amma daga baya duk suka dangana suka fawwalawa Allah komai, haka suka cigaba da rayuwa cikin maraicin uwa da uba, sun ga kalubale da dama wajen dangin su saboda mahaifin su asali ba wadata bane dashi sosai amma akwai cikakkiyar wadatar zuci, basu gaji komai daga mahaifin nasu ba sai gona guda 'daya sai dai tana da girma ba laifi.
Basu tashi sanin basu da cikakkiyar gata ba sai da suka rasa mahaifan nasu aka kuma rasa cikakken wanda zai kar6e su da hannu bibbiyu ya rike su ya kuma basu gata da kulawa, 'karshe karatu ma gagarar su tayi saboda rashin wanda ze biya musu kudin makarantar, haka kuma batun gonar mahaifin su ma basu samu cikakken bayani akan ta ba.