← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 218

Sashe 191

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Duk yadda yake jin damuwa gami da 'kaguwa da son jin abinda zai fito bakin Goggon nasa karo 'daya duk yaji wata fitinanniyar bugun zucia daya kore komai sakamakon tsinkayan sautin muryar da tayi sallama...amsa kuwwa sallamar ta rika yi masa a ka.
Dukkanin su juyawa suka yi suka mayar da hankali wajen mashigar gidan..sa6anin Goggo da dama nan take fuskanta.

Inka 'dauke goggo da tayi mutuwan tsaye cikin su bb wanda bai zaro idanu da bu'de baki da ganin ta ba.
Atare Hafiz da Adam suka furta sunan" Zaitoona...!"
Wanda hakan shi ya sanya Goggon Adam mayar da idanun ta garesu cike da tsantsan mamaki.

Ita kanta a 6angaren ta ma haka abin yake.
Cike da tsananin mamakin ganin sa tare da mahaifiyar ta tace" Yah Adam...!"
Tana toshe baki da duk hannuwa biyu.

Kasa amsawa yy kawai ya cigaba da duban ta..ji yk tamkar mafarki, ji yk tamkar idan ya motsa za ace masa ba gaskia bane abinda idanun sa ke gane masa illusion ne kawai da ya saba gani nata.

Amma duk ganin da yake mata cikin mafarkai, hasashe da tunanukan sa bai ta6a kwatanta cikin wannan ni nimtaccen yanayin ba sai dai in zai gansa tare da ita.
Shiga ta kamala, tsabta da kwanciyar hankali 'karara suka bayyana.

Hafiz ne ya sake yin 'karfin halin furta " sunan ta akaro na biyu.
Itama tace " Yah Hafiz"!
Yaushe Zaitoonan sa ta waye? Yaushe ta samu rayuwar mai ingancin da shi ya kasa bata...?
" Yayah Adam...Kai ne...?"
Ta sake tambaya cike da tsananin mamakin ganin sa anan...hakan shi ya yanke masa 'dan guntun tunanin da ya fada.

Wani 'kwarin gwiwa ne yaji ya zo masa nan take bayan tabbatar da cewa ita din ce dai.

Kai ya sosa yana mai 'ka'kalo murmushi yace" Zaitoon Nine..bayan tsawon lkc sai gashi yau ga ni ga kuma ke..."!
" Wa ya nuna maka gidan Inna ta...?"
Ta tasake tambayar sa dan har a lkcn mamakin bai sake ta ba.

Yace
" Baiwa ta ta kawo ni.."!

" Wace ita haka..?"
" Da kaina nazo Zaitoon bayan kin guje ni...?"
Tana shirin magana sai ta hango hadda Innani tayi mutuwar tsaye tana duban ta...fasa maganar tayi ta nufi Inna da gudu tana shirin rungume ta Inanni ta ja baya ka'dan ranta a matukar 6ace ta yadda ko fuskar ta bai 6oye hakan ba.

" Innani ni ce fa...".
Zaitoon ta fa'da da wata karyayyar zucia tana sake duban Innar tata.
Wani lafiyayyen mari Innanu ta sauke mata saman kuncin ta, kafin Shaheed yy wani yun'kuri sai ga Innani ta sake sau'ke mata wani marin.

Da duk hannuwa biyu Zaitoon ta dafe kuncin ta idanuwan ta na zubar da hawaye take duban Innani.
Duk yadda Adam ya shiga tsakanin su hakan bai hana Innani son sake kai mata wani bugun ba..duk da baki 'dayan su hkr suke bata amma Innani tamkar bata sauraren su, ita kuka Zaitoon kuka, Innani fa'di take ta fita ta bar min gida kafin tayi mata mugun duka.

Yadda Innani da Zaitoon ke kuka yasa hatta su Ammi dake waje suna jiran iso daga wajen Zaitoon din kawai suka nufo cikin gidan a tsorace.
Nan suka tarar da hayaniyar.

Tuni Zaitoon na dur'kushe bisa gwiwoyin ta tana kuka ta ha'de hannuwa da alamar ro'kon gafarar Innani.

Ammi ce tayi saurin shiga tsakani tace " Haba haba Innan mu...mene hakan wai, sai kace wacce ta aikata wani gagarumin laifi..?"

" Ta fita ta bar min gida nace!...bana son ganin ta, taje ta koma inda ta fito ta cigaba da rayuwar ta, mun riga mun cire ta a ran mu..mun ha'kura da ita..."
Sai ma ta kasa 'karasa abinda tayi niyyar fa'di kuka ne sosai ya ci 'karfin ta.
Nan ta koma ta zauna kukan takaici da bakin ciki na sake fizgar ta.

Bazata ce bata yi farin ciki can 'kasan zuciyar ta da ganin Zaitoon ba, amma idan ta tuna wata sabuwar Zaitoonan ce tazo mata, ba tata ta asali ba, sai taji sam bata da wani 'kwarin gwiwa kuma.

Tsoro take ji kar 'diyar ta yawon duniya taje da yasa tayi kyau haka ta dawo tamkar ba haihuwar jeji girman Ala raya irin Zaitunan ta ba.

Shaheed ne yazo gaban ta ya dur'kusa bisa gwiwoyin sa a hankali ya 'kira sunan ta bata amsa.

Sai da yaja gauran numfashi kafin ya sake cewa" Goggo!"
Bai tsaya ba ya 'dora da fa'din" Kika ce ta tafi? Ta koma inda ta fito? Goggo kika ce kun cire ta a ranku, bacin mintina 'kalilan baya kafin isowarta idanuwan ki jike suke da ruwan kewa da rashin ta, meyasa bazaki bata dama ba Goggo? meyasa bazaki tsaya ki saurare ta ko da sau daya bane, na tabbata tunda kikaga ta dawo rana tsaka da kanta toh tuni tayi nadaman abinda ta aikata...Goggo Zaitoon din ki cefa! Har kin manta? Goggo Zaitoon 'dinki kamammiya ce a duk sanin da nayi mata, kuma har yau bana tunanin zata banzatar da kanta sbd wani abu Goggo, sai dai in kaddarar ta ce tazo da hakan...idan kin amince ni nan Goggo sai in baki labarin waye Zaitoon daga lokacin da ta bar gaban ki har zuwa iya abinda na sani....".
Da sauri Innani ta dago kanta ta dube shi, kai ya jinjina mata alamun tabbatar wa, sannan ya cigaba, " 'Kwarai kuwa Goggo, kuma na fadi hakan ne da dukkan gaskiya ta ba wai dan in kare ta ko kuma dan wani abu ba..."

Kallon sa kawai ta tsaya yi sai ma a lokacin ta tuna da batun yarinyar, nan ta fara dan kalle- kallen jikin Zaitoon bata ga alamun yarinyar ba.

Hasalima yarinya guda ta hango can hannun wani kyakykyawan mutum, sai dai wannan kallo 'daya zakayi musu ka tabbatar cewa jinin sa ce..zuciyar ta ne ya tsinke da karfi...cikin ranta ta ayyana ina Zaitoona ta kai yarinyar mutane? "

" Yarinyar tana nan tare da ita Goggo" Amsar da Shaheed ya bata ne ya sa ta fahimci a fili tayi maganar ba a zuci ba.
Ya akayi ka sani...? Ya akayi kasan haka Adamu? "
Sai yace
" Na ganta a hannun wanda suka zo tare" shima yayi maganar yana mai waigawa inda suke tsaye.

" Kana nufin wancan yarinyar?" Goggo ta fada tana nuna wanda ta hango tsaye da yarinya tana mai yatsine fuska.

Da kai ya amsa ta, tana shirin sake yin magana ya mike tsaye dan baiwa ba'kin nasu wajen zama.

'Dakin nan da aka sauke su ya shiga da kansa da hanzari, ya 'dauko babbar tabarma ya shimfida musu yana kakka6e hannu yace musu bismillah ga wurin zama.

Innar Zaitoon duk rikice take domin ko tambayoyin da take jerawa Shaheed a rude take yin su, dan ba halayyar ta bane.
Tsoron abinda kunnuwan ta zasu jiye mata na daga rayuwar da Zaitoon tayi shi yafi rikita mata kwanya.

Shaheed ne ya zauna yana fuskantar Goggo ya fara bata labarin duk abinda ya sani ata'kaice, 'karshe yace " Zaitoon ta rayu gaba na tsawon lkc ita da 'diyar ta Goggo, kuma har ta rabu da mu ban ta6a cin karo da wani abin zagi tattare da ita ba...Bata bar gida dan ta banzatar da kanta ba, ta bar gida ne kawai sbd 'diyar ta..kyakkyawar 'dabi'ar da take da shi ko a wancan lkcn shine ya kwa'daita min son auren ta sai dai ban yi nasarar cika buri na ba mukayi rabuwar bazata...haduwar mu ta 'karshe a kotu ne kamar yadda na fadi Goggo...kuma kafin inyi wani yun'kurin tunkaro inda take tuni ta sake min 6atan dabo, nayi matu'kar ba'kin ciki da rasa wannan damar a wancan ranar.

Da yake ko nima a lkcn rikice nk sbd mahaifi na ga kuma ita Zaitoon...da 'kyar zuciya ta ta saba da rashin wa'dannan bayin Allah biyu..kuma har yau har gobe muna nan da kewar su cikin ran mu da fatan sake ganin su, ba ni kadai ba hatta da makwabtan ta suna kewar ta sosai Goggo musamman sbd zaman da tayi da su da zuciar 'daya...rayuwar Zaitoon abin koyi ce ga kowacce 'diya mace Goggo, rayuwa ce abin kwadaituwa ga iyaye bisa 'ya'yan su....."

Maganar da Hafiz yazo yy masa cikin kunne shine ya sanya shi dakatawa da maganar da yake take ya mi'ke tsaye yana jero inna lillahi cikin ransa.

Jikin mahaifin Hafiz ne ya tashi kuma har an dangana ma da asbiti tun tuni mahaifiyar sa da kanta ta sanar da shi.

" I have to go Adam..bcuz i'm needed there..u pls stay with ur family Insha Allahu komai zai zo da sau'ki..."
" Bazaka wuce kai kadai ba ai Hafiz...!"
Shaheed ya furta yana mai sanya kafafun sa cikin takalman sa.
" a a ai baza ai haka ba...kaga...."
Da sauri Adam ya dakatar da shi da hannun sa, sannan yayi wa Goggo bayani amma da al'kawarin zai dawo gobe ko jibi ne da yardar Allahu...nan ya yiwa baki sallama idanun sa akan Rayyan da sam gayen ya tsaya masa a zuci tunda ya gansa...har suka tafi kalma guda bata ha'da shi da Rayyan ba.

Duk ba haka yaso ba yaso yaji meke tafe da bakin nan amma Allah bai yi ba, shi kuma bazai iya banzatar da lamarin da ya shafi Hafiz ya fifita na kansa ba sbd Hafiz cikin ko wani irin yanayi ne yana nan tare da shi bai ta6a gudun sa dai- dai da rana ba.

Hatta Bello a hanya suka so barin sa, ya kuma ciro ku'di mai tsoka ya mika masa dan ya koma gida kafin su dawo amma Bello yace sam shima 'kafar sa kafar su.

Ammi da kanta ta bawa Innani kaf labarin da ta sani daga bakin Zaitoon dama wanda ya faru a gaban idanun ta, bata 6oye mata komai ba.
Chapter 191 · 0% Book details