Sashe 91
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Kin mance kwana nawa zakiyi ne...?"
" Ban mance ba...amma kasan abu da ikon Allah ne..".
Kicin- kicin yayi da fuska " me kike nufi..?"
" Kai Yalla6ai...toh in haihuwa ta kamani acan kuma fa..ba dole a bu'kaci wasu kayayyakin ba shiyasa kawai na 'diba zan tafi da kayana..."
" Kar kisa in soke tafiyar nan Allah, har hakama zaki ce kenan baki da niyyan dawiwa ma yanzu tunda nasan dai a lissafi haihuwa ma da sauran lokaci..."
Ido ta dan fitar..." Haba dai rufa min asiri kar afasa dan Allah, ni wasa nake maka ma, abin bai kai nan ba fa..Kayayyakin ma wasu zan bada ne akwai masu bukata acan shiyasa na 'diba...".
" Yanzu na ji zanje...".
Yace yana gyara tsayuwa.
Yanzu dai kiyi sallah barin je masallaci in dawo sai muje ki yiwa Ammin sallama ko.?"
" aha..adawo lpy..".
Ta fa'di hakan ne tana 'ko'karin mi'kewa.
Daga gidan Ammin Shoprite suka wuce ya sake yi mata siyayyan kayan amfani nata na kanta da ya san cewa zata bu'kata sannan suka dawo gida.
Da kansa ya 'karasa ha'da mata sauran kayan ta hadda shirgin handbag da zata ri'ke a hannun ta, ya kuma zuba mata ku'di cikin jakar da bama tasan nawa bane.
Yana shirin jefa mata IDCard 'din ta wajen aiki tace" Wannan kam amfanin me ma zai min acan bar min shi agida kawai yafi.."
" Gani nayi kin kwashi su handgloves da sauran su na sani ne ko wani sabon asbiti zaki bu'de acan shiyasa zan saka mk Card 'din naki ai may be ki iya bu'katar sa..."
Ya bata amsa yana 'yar dariya.
Murmushi tayi itama..." Toh ban da abinka dear sabon asbiti ai sai da sabon IDcard..wa zai bu'kaci tsoho kuma..."
" Haka ma zaki ce ko...toh sai ince an fasa tafiyar..."
" Waiyo Allah na, yalla6ai aimin afuwa ni wallahi wasa nake fa...".
" Tashi toh mu wuce ko inzo in 'daga ki..?"
" Zan iya da kaina ma..."
Ta fa'di hakan tana 'ko'karin mi'kewa dan tasan ka'dan ga aikin Rayyan ne idan yaga kamar sai da taimakon sa ta mi'ke yace ya fasa tafiyar.
Har sun fara tafia tana bin bayan sa, sai kuma ta juyo, takaddar last scan da akai mata dake ninke cikin drawer ta dauko ta jefa cikin jaka, bataso ya gani ko da bayam tafiyar ta ne dan duk sauran ta 6oye su shine na 'karshen bata kai ga 6oye shi ba shiyasa ta dauke abinta.
Waigowa yayi..." Ya akayi kuma..?"
" Mantuwa nayi kuma na 'dauka ma..".
" Hmm.."
Yace sannan suka cigaba da tafiya.
Sai da suka je ta yiwa Amrah sallama kafin suka fito, koka'dan babu wata sha'kuwa tsakanin ta da Amrah amma kuma babu raini tsakanin su sam, dan sosai Nadia ke kama girman ta bata bar kowacce kafa da Amrah zata ga lagon ta har ta raina ta akai ba.
Jirgin yamma Nadia ta bi zuwa Maiduguri yayin da Rayyan ya kasa barin filin jirgin har bayan da jirgin da Nadia ta hau ya riga ya tashi.
Haka kawai sai yake jin tamkar ta tafi masa ne da wani 6ari na farin cikin sa.
Bai bar filin jirgin ba har sai da yaji wayar sa na ringing sannan ya saki nannauyan ajiyan zuciya, ko duba mai 'kiran nasa bai yi ba kawai ya tada mota ya dawo gida.
Sai da yayi parking kafin ya 'dago wayar tasa ya duba nan ya tarar da missedcalls har biyar, sai yaga ashe ma Amrah ce ke 'kiran nasa sai Sultan da kuma wani abokin sa Fawwaz amma duk bai bi bayan 'kiran kowa cikin su ba sai na Sultan.
" Big bro barka da yamma...ina ta 'kira ne inji ko Anty Nadia ta wuce wlh na shiga gari ne wasu uzururruka shiyasa banzo munyi sallama ba..."
" Bakomai Sultan kar ka damu, ta wuce already yanzu ma nake dawowa daga airport 'din.."
" Masha Allah...Allah ya dawo da ita lafiya..."
Yana 'yar daria yace" Shine ta wuce bata ko yi cigiya ta ba ko dan ma kar na rakata in gano sirrin Kanurai....".
Shima Rayyan murmushi yayi sannan ya fara fa'din" Toh 'dan nema, ka mance Ammin ka ma kanurin ce...kaje wajen ta duk wani sirri da kake nema zaka samu a wajen ta ai...".
Hannu Sultan ya toshe bakin sa yana daria 'kasa 'kasa..." Yace ai Ammi na ta musamman ce ta riga ta sanar da ni wanda ta sani sauran Anty Nadia aka barwa"
Shima Rayyan dariya kawai yayi daga 'karshe cewa yayi..." Indai Nadia ce ai zata 'kira ka indai ta sau'ka.."
Daga haka ya yanke wayar yana 'ko'karin fitowa cikin motar.
Sultan dake kwance a wani tsadajjan 'dakin hotel tun bayan fitar Amrah da ya sallame ta bai iya ya tashi ya shirya ba ma balle yayi niyyar barin hotel 'din.
Duk tunanin sa ya tattara ne izuwa ga Nadia da abinda zata haifa, sosai yake marmarin ganin ya salwantar da koma menene..ko bayan da suka yi waya da Rayyan cikin zuciyar sa fata yake ace jirgin nasu ya 'kone a sama, inama gobe da sassafe yana bu'de Television cikin kanun labarai ya tsinci cewa anyi plain crash daga Kano zuwa Maiduguri.
Mi'ka yayi sosai akan bed 'din hotel 'din, a hankali tuno moments din su da Amrah sai yasa shi sakin murmushi, ya tabbatar zuwa yanzu ta isa gida, sosai yake enjoying kasancewa da ita badan komai ba sai dan kawai yaji aransa cewa ta wannan 6angaren Rayyan bai zarta shi ba.
Inda yake tutiya da alfaharin yan shiga shima tuni ya ratsa shi, Nadia ce ka'dai ya kasa samun wannan damar daga gare ta bai ma ga fuska ta wannan 6angaren ba.
Sannan ya riga yayi maganin matsalar sa ta 6angaren ta dan yasan abu ne mawuyaci Amrah ta samu ciki inma ta samu 'din zai yi wahala ace har cikin ya bayyana batare da ya sani ba.
Abu 'kalilan suka rage masa a yanzu da suka hana shi cimma burikan sa sai dai sun kasance ne kuma sune tsani mafi girma da ha'dari a gare sa, kuskure ka'dan zai yi ya tona asirin kansa shiyasa yake bi a hankali.
Dole zai auri Marwa ta kasance 'kar'kashin ikon sa, inda hali wajen haihuwa yake son Nadia ko abinda zata haifa daya ya tafi abin zai fi zuwa masa da sauki bayan wani 'dan lokaci sai ya sa 'dayan ma yabi bayan 'dan uwan sa, in ma Nadian ce ko kuma abinda zata haifa shikenan labarin su ya shu'de.
Wannan duk mai sauki ne a ganin sa, domin yana da hanyoyin da zai bi kuma yana da ku'din da zai iya sawa duk shirin sa su tafi bisa tsari kamar yadda ya shirya.
Raihana ba damuwar sa bace balle 'dan ta 'kwaya 'daya tilo da take da shi wato Bassam, domi ko da ace ya bar ta a raye yasan ba ta da iko da kuma sani akan wasu abubuwan na gidan su da dukiyar su kamar sa.
'Dan ta kuwa da gidan uban sa zai yi tutiya ba gidan mahaifan uwar sa ba.
Babban abin harin nasa dama Rayyan ne, amma dole sai yabi komai a hankali.
*****
Nadia sosai taji dadin zuwan ta gida dan ta tarar da Umman ta lafia 'kalau, mahaifin ta ne ma yake 'dan fama da hawan jini amma bai kwantar da shi ba.
Akwai wata kanwar Umman ta dake aure acan Damaturun jihar yobe kuma tana fama da ciwon Cancer tsawon watanni ko da Umman ta ke bata labari cewa tayi zata je ta duba ta kafin ta wuce.
Umman ta taso hanata musamman sbd yanayin da take ciki Nadia 'kin amincewa tayi, tace" Umma ai babu dadi taji cewa nazo kuma banje na gaishe ta ba, ba wani abu ai Umma, shi nauyin jiki kam ai ba sabon abu bane, na taso tun daga Kano ma balle nan Damaturu mintina nawa ne naje na dawo..".
Kai Umma ta ka'da" Toh shikenan Nadia amma ki fara sanar da shi mai gidan naki tukunna idan ya amince sai a samu driver ya kaiki a motar Abban ku a abiyashi tunda ba da mota kika zo ba..."
" Bari dai in yi magana da shi tukunna Ummah ka'dan ga aikin sa ne ma yace bai yadda ba...".
Ta fa'di hakan tana barin 'dakin ta nufi masau'kin ta.
Ringing biyu Rayyan ya 'daga..." Mrs Rayyan ya akayi..? Mantuwa aka yi ne da ba'a fada 'dazun ba sai yanzu...?"
" Kamar ka sani..."
Ta bashi amsa tana gyara zaman ta dan irin wannan magana ga Rayyan sai ta nutsu sosai sbd sanin halin sa da tayi.
" Uhum inaji Mrs Rayyan bani labari..".
Murmushi tayi..." Kasan Aunty na na Damaturun nan ko, ina nufin 'kanwar Umma ta...?"
" Yes..Anty Yakura...".
" Yauwa Dear, dan Allah inaso inje in gaishe ta ne, wallahi wai bata da lafiya serious kuma babu da'di ace nazo har nan na koma ban duba ta ba..kuma kaga bansan ramar dawowa ta....pls my dear...".
Zaune yake saman kujerar sa na office amma da jin furucin Nadia sai da mi'ke tsaye ya isa wajen window ya tsaya, tun ma kafin ta kai aya sai ma ya kasa cewa da ita komai har ta dasa aya.
Jikin sa rawa yake tsabar takaici.
Shin manta yanayin da take ciki tayi ne ko kuwa.
A hankali ya 'kira sunan ta..." Nadia...."!
Abinda ta da'de rabon da taji ya fito bakin sa kenan. Sosai taji bakin ta ma ya mutu da 'kyar la66an ta suka iya motsawa ta amsa da na'am Hubby...".
" Don't pls..don't Hubby me..."
Ya fa'da har yana 'daga hannu kai kace tsaye take gaban sa yana duban ta.
" Dan kin samu kin tafi shine zaki tsiro min da wani abu ko...?"
" I'm sorry..in baka amince ba shikenan..".
" Yes ban amince ba nd ki shirya gobe da sassafe ki dawo Kano.."
" Ok..."
Ta tace tana yanke wayar.
Basu sake magana ba.
Ita kanta Umman ta da taji shiru bata 'kara bi takan ta ba dan tana da ya'kinin bata samu damar tafiyan ba shiyasa taji ta shiru bata fito 'dakin ba.