Sashe 62
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aikuwa ana yin sallah da kwana biyu ta shirya mata biki a harabar gidan Ammi, Zaitun sai da ta zubda 'kwalla ganin yadda Marwa ke nunawa 'diyar ta zallar 'kauna...
Yadda aka gyara Mufee kai kace 'diyar wani hamsha'kin ne ba 'diyar Zaitun ba.
Ta sani ba 'kananun kudade Marwa ta kashe wajen wannan hidimar ba, haka aka ra'kashe aka yanka cake, Marwa ta sanyawa Mufee a baki ita kuwa Mufeeda data yanko kawai ta nufi bakin Zaitoon da shi tana washe ha'kora, sosai abin ya kayatar da kowa.
Aka sanya shewa ana jinjina kauna irin ta uwa da 'diya, Marwa ma daria take tace" ji ja'ira wato dai har kin san muhimmancin Mamin ki fiye da kowa ko..?"
Lokacin da aka sanya wa'kar Sarkin waka na cikin shirin labari na Marwa tashi tayi tana takawa cikin wani salo mai birgewa ta kama hannun Mufee duk biyu cikin nata suna takawa tana bin bakin wakar a hankali Mufee kanta daria ta ringa 'kyalkyalewa sbd abin ya birge ta.
Bikin ya kayatar da Zaitun sosai, wuri na musamman ta ware ta sanya Marwa har take jin ta tamkar wata 'yar uwarta ce ta jini.
Kyaututuka kuwa Mufee ta shasu na ban mamaki dan Marwa kaf 'kawayen ta sai da ta gayyato, gift 'din Marwa na musamman ne, dan kayan sawa ta siyawa Mufee har kal goma cif kaya kuma da suka amsa sunan su kaya wandanda tasan sun fi karfin sawarc 'diyar ta sai dai dayake na Allah baya karewa kuma ya kan iya azurta ka da abinda baka ta6a zato ba a duk lokacin da yaso.
A ganinta in bama irin su Marwan ba a ina Mufee zata samu irin kayayyakin nan..tasan har abada abu mawuyaci a garesu.
Kamar ha'din baki Ammi ma kayan sawan ta bata sai sauran gifts din da suka hada hadda ku'da'de takalma da sauran tarkace hadda abubuwan wasan yara.
Zaitun tunda aka fara taron kuka take, duk wata kwalliyar da Marwa tasa musamman aka zo har gida akai musu duk ta lalata shi da kukan farin ciki.
Ana tsaka da shagali Rayyan yazo ya tarwatsa komai yana masifar an maida musu gida kamar gidan 'koroso.
Hatta Ammi bata iya dakatar da shi ba sbd dokin zuciya daya hau, dole yasa aka tashi haka nan cike da kyaututtuka na ban mamaki.
Dama tasan ba kaunar su yake ba, dan ko gaiduwar ta ba amsawa yake ba duk ranar da suka ha'du a 6angaren Ammi, haka ma Mufee baya kulata, sai dai tasha kama sa yana bin Mufeedan da kallo bata kuma san ma'anar kallon ba.
Ta kance aniyar ka ta bika inma maye ne kai.
Ita ma yarinyar kamar tasan baya son su haka kawai itama tsoron sa take ji shiyasa take gudun sa. Ko inda yake bata yadda taje.
Shi da kansa yasan ba 'dabi'ar sa bace yawan kallo amma akan yarinyar nan dabi'ar da shi kansa ya yiwa kansa shaidar ta na neman canzawa, bai san mai yake kallo game da yarinyar ba haka kawai tsintan kansa yake da son ganin fuskar ta, ji yake tamkar ganin yarinyar na 'debe masa kewar abubuwa da dama bai kuma san dalili ba.
Sai daga baya da yaga abin na neman fin 'karfin dakiyar sa ya sanya shi yakice lamarin 'karfi da yaji wajen 'dorawa zuciyar sa mummunan tsana, da zarar ya tuno wani abu game da su sai yayi kokarin tuno wani abu mummuna kuma daya 'darsawa ransa game da su musamman ma a yadda ya fahimci labarin su da yaji take baiwa Ammi farkon zuwan su.
Ka'dan da ka'dan tsanar tayi tasiri ya rinjayi komai aransa, dan yafi bawa tsanar muhimmanci fiye da sakewa yarinyar.
Da zarar yazo 6angaren Ammin sai ya wani hade rai abu ka'dan ke tunzura shi laifi kadan zaka yi ya maidasa babba...
Baya sakewa Mufee fuska sam, kar Zaitun ma taji labari dan duk 'din su baya son harkar da zata hada sa dasu, ko a kuskure Mufee ta ta6a jikin sa tsawa yake daka mata batare da tunanin 'karamar yarinya bace, duk yadda Ammi taso saita masa tunani akan su abin ya faskara.
Yanda yake hantara da rashin fara'a ga Mufy yasa da zarar ta gansa sai ta 6oye fuskar ta ko kuma ta tsanyara kuka ta nemi wajen shiga.
Idan hakan ya faru da sauri zaki ga Zaitun ta zo ta 'dauki abinta ta rungume dan sam bata son kukan ta ko da wasa karya mata zuciya yake.
Dalili kenan da ya sanya har yau 'din nan bata damun kanta da yiwa Mufy kitso dan yarinyar bata so da an ta6a kanta take sakin kuka.
Sau tari sai dai in taga lallai lallai kannata na bukatar kitson sai ta hana idanun ta bacci cikin dare lokacin da ta tabbatar baccin yarinyar yayi nisa sannan zata dinga yi mata da 'daya da 'daya kuma a hankali sama- sama dan kar yayi mata zafi gashi yarinyar akwai suma sosai akanta wani lokacin har mamaki take yi dan ko ita bazata nuna mata 'kyan gashi ba...sai dai ta nuna mata tsawo da cika amma gashin Mufee mai kyau ne kuma gashi bakikirin amma duk da tarin baiwar nan da Allah yai mata bazaka ta6a ganin kitso mai kyau akanta bacsai dai in Marwa na nan, tun na ranar da akai mata birthday kuwa bata sake yadda an mata kitso ba sbd kukan da take sha wajen yin kitson.
Zaitun bata barin Mufee zama a duk inda tasan zasu hadu da duk wanda bai sake mata ma balle ganin sa ya sanya ta kuka, kullum yarinyar ta na rungume da ita a goye ne ko kuma a hannun ta basu cika rabuwa ba.
Ta 'kwammaci ta goye abinta suyi aikin a haka da ta barta wani banza na firgita mata ita a cewar ta hakan ya fi mata...bazata ta6a gajiya da rainon abinta ba ...a yanzu Feefy ce farin cikin ta itace ka'dai abinda zata gani taji farin ciki ya lullu6e ta tasan cewa itama tana da wani nata kusa da ita...a kullum fuskar mahifiyar ta take gani yake sake bayyana kan fuskar yarinyar, hasken su ma 'daya ne da ita...tasan ba dan wancan 'kaddarar ba da yanzu tana nan cikin dangin ta da 'yan uwanta tana walwala kamar kowa...amma Allah ya 'kaddaro musu wancan 'kaddarar ya za6e ta ya dam'ka mata amanar sa da ya kasanceckaddarar rayuwa ta ne, ta kuma kar6i 'kaddarar ta da hannu bibbiyu kuma tayi al'kawarin bata tarbiya, kulawa da komai da ya shafe ta muddin ranta.
Mufee ka'dai ta ishe ta rayuwa, koda ace zata rayu babu aure babu 'dan kanta matu'kar zata kasance da Mufee a ganin ta bata da damuwar komai, 'kaunar Mufee acikin jinin ta take jinsa, tasan abu ne me wahala ta iya raba zuciyar ta da 'kaunar yarinyar, sun shaqu irin shaquwar da ko wace uwa take iya yiwa abinda ta haifa.
_Ni kam a gani na 6angaren Zaitun ta zake da yawa ma fa.._ 😂
Domin akan Mufee ta sadaukar da duk wani farin cikin ta, ta sadaukar da dangin ta domin ko a lokacin da suka nuna 'kyama ga abin bai mata dadi ba, aganinta kaddara tana kan kowa kuma tana iya samun duk wanda Allah yaso cikin kowacce irin siga.
Amma sun kasa fahimtar ta.
Ba wai dan ta kisu bane tayi musu nisa sai dan bawa kowa dama da kuma hucewar zuciya.
Dan haka ba taga wani 'kato da sama taka zai zo ya ringa firgita mata yarinya abanza ta bari ba, tun daga lokacin ta 'dauri aniyar yin fito na fito da duk wani wanda zai ta6a musu farin cikin su...duk me 'kaunar Mufeeda itama tana son shi ma'kiyin Mufee kuwa matsayin babban ma'kiyi itama yake a wurin ta.
Bata nemi taimakon kowa wurin kula da yarinyar ta ba, balle wataran ai mata gorin hkn, tayi kuma alwashin zata yi kowani irin aiki ne dan ganin kawai yarinyar ta ta samu rayuwa mai kyau kuma Alhamdulillah ta wannan 6angaren yanzu bata da matsalar komai.
Tun lokacin da Allah ya ha'da ta da Ammi kaso mafi yawa daga cikin damuwar ta ya kau...domin Ammi 'yar halak ce, Ammi mutun ce har mutun, ta kula da ita ta kuma bata 'kwarin gwiwa wurin kulawa da yarinyar ta.
Bata ta6a nuna 'kyamar ta ga yarinyar ba hakan kuwa shine sanadin da ya ja mata babban matsayi a zuciyar Zaitun har ya sata sakin ranta da zummar yin aiki karkashin ta har zuwa lokacin data 'dibar ma ranta.
Ammi ta wadata Mufee da sutura mafi tsada da 'daukan hankali, sutura mafi birgewa daga cikin duk suturun da ta ta6a sanyawa yarinyar tsawon rayuwar su, ta wadata da duk wani abu na more rayuwa wanda tasan ko cikin 'yan gayu 'diyar ta ta shiga zata 6ace acikin su 6at.
Zaitun sam bata damu da kanta ba, burin ta taga Feefy na dariya tana wasa tana walwala hakan kawai shine farin cikin rayuwar ta, sai ta zauna ta zuba mata idanu tana murmushi tana tuno abubuwa da dama, atimes kuma in hakan ya kasance sai kaga tana share 'kwalla.
Shekaran Feefy 'daya ne da wasu watanni amma saboda kyakkyawar rayuwa da ta samu idan ka ganta sam bazaka yi zaton ta gaza 2yrs ba, abinda ta jima tana buri bata samu hakan ba sai gashi a gidan Ammi ta same shi.
Ta jima tana burin ganin Mufeen ta ta yi kiba ta murmure amma haka ya kasa samuwa mata sai gashi a yanzu ta samu wannan cikar burin, sai yanzu ma asalin kyan yarinyar da hasken ta suka sake bayyana a fili.
Wani lokacin idan Rayyan na magana zuba masa idanu take yi har sai taji murmushi ya kubce mata, cikin zuciyar ta sai ta ayyana" ka tsani 'yata sai kuma gashi bakin ku ya juye ya koma sak iri 'daya, bakin 'dan cukul mai kyau zagaye da bakin layi da ya kasance dishi dishi sai ya 'kara gyara musu bakin ya koma mai 'daukan hankali.
Zaitun ta kance duk zaman mu baki 'dauki komai nawa ba sai na wannan masifaffen da ko kallon arzki bai ta6a yi mk ba..haba 'yan matana...wannan rashin adalci har ne gaskia.
Ta 'karashe da jan kumatun Mufee tana murmushi.