← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 218

Sashe 198

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ba dai hannu zaka sa cikin wankin nan ba..?"
Tayi tambayar cike da mamaki.
Yace" yanzu kuwa..."
" Dan Allah ka bari ai ma saura ka'dan in kammala.."
" Ba'kin ciki kk min kar nima in samu tagomashin lada kenan...?"
" Yah Adam..dan Allah.."!

Ki bari idan mun kammala sai ki fa'da min cewa ban kyauta ba dan na yiwa 'diya ta wanki.."

Shiru tayi ganin har ya tsoma hannu cikin wanda Mufee ke wasa da shi.

Shiru ya 'dan biyo baya.
Ahankali tace.." Yah Adam kasan idan Hajiyar ka taji labari bazata ji da'di ba.."!
" Saboda wani dalili..?"
Tace" Saboda kafi 'karfin yin hakan ga koma waye balle kuma ni Zaitoona...".

Bai ce da ita 'kala ba kawai yayi 'yar daria.
" Ki bini bashin wannan tambayar taki zan baki ita zuwa gaba...amma kafin nan zamu yi wata 'yar gasa...shara'din sa kuma shine in har kika fa'di gasar nan toh sai kin bani kyautar wani abu gagarumi kin amince..?"

Shiru tayi tana 'dan rarraba idanu da tunanin abun kamar me zai iya kasancewa.
Hannu ta 'daga da sauri tana daria tace" Gaskia a a..Yah Adam.."

Gira ya 'dage yana duban ta..." ban amince ba..wlh".
" Sbd mene..?".
" Toh Yah Adam in kuma ya kasance bani da wannan abin fa..?"
" Ina tabbatar mk da cewa kina da shi kuma sau'kin bayar wa gare shi...".

" Fa'da min toh menene...?"
" Ai baki amince ba tukunna."
" Taya zan amince bacin bansan menene ba..."
" Sannu mai rai sarkin tsoro..."!

Ya fa'da yana daria gami da mi'kewa tsaye ya fara shanya kayan da ya gama wankewa..itama dariyar take yi...ta sunkuyar da kai ta cigaba da wankin dake gaban ta cike da annuri.

Adam dake tsaye yana shanya shine ya fara hango mutun tsaye fuskar sa tamkar ba'kin hadari sbd yadda ya ha'de ta.

Babu alamun yama ta6a daria a rayuwar sa.
Gira Adam ya 'dage yana duban sa da mamaki yace" Malam lafia...?"
Dan sam bai gane waye ba.

Maganar Adam ita tasa Zaitoon 'dagowa da sauri ta dube shi ganin inda hankalin sa yake itama sai ta dubi wajen.

Wani tsinkewa da zuciyar ta yayi har sai da taji tamkar bazata iya tsayuwa da 'kafafun ta ba amma ta dake.

Tsaye ta mi'ke da sauri tana gyara zaman hular kanta.

Sosai yake duban ta duba mai cike da takaici, bai sake kallon inda Adam yake tsaye ba...Mufee kam bata ma ankara da shi ba sam.

Ganin sa ya matu'kar bawa Zaitoon mamaki, kuma sam ba zata iya ce ga tsayin lokacin da ya shafe tsaye a wajen ba.

'Kasa tayi da idanun ta yayin da shi kuma ya juya ya fita da hanzari sai jin tashin motar sa tayi da 'karfi ya fizge ta yayi gaba.

Wani ajiyar numfashi ta sau'ke mai tsananin 'dumi tana duban Mufee....

Adam barin abin da yake yayi ya taho wajen ta shi kansa neman natsuwar sa yayi ya rasa ta da ganin sa.." Waye shi...?"
Ya tambaye ta shima 'din fuskar sa babu alamun fara'ah tamkar ba shine ya gama daria yanzun ba.

Tana zama bisa bencin da ta tashi ta amsa shi da fa'din" Abban Mufeeda ne "!

" Ban fahimta ba?"
Kai ta 'daga ta dube shi ido cikin ido sannan ta bashi amsa" Mahaifin Mufeeda ne.."!

Wani turus yayi yana duban ta..bata san meyasa ba haka nan kawai sai taji gaba 'daya bata da sukuni, ji tayi ta takura baki 'daya.

Yayin da Adam yama rasa abinda zai sake fa'di.
Cikin ransa yake ta tunani.
Mahaifin Mufeeda kamar Yaya? Taya kuma wannan zai kasance mahaifin ta?

Shin dama yana raye ya bar su sukai irin wannan rayuwar ta alla wadai..? Yana raye ya bar su sukayi rayuwa tamkar almajirai?"

Takaicin sa ma 'daya yadda lokaci guda ya fahimci canjin yanayi daga Zaitoon tun bayan ganin sa da sukayi.
" Zaitoon...!"
Ya 'kirayi sunan ta cikin yanayi marar misaltuwa.
Kai ta 'dago ta dube shi.
" Me yakawo shi a halin yanzu?"
" 'Diyar sa yazo gani.."!
Ta bashi amsa Kai tsaye.
" Dama can yana zuwa ne..?"
Shiru tayi bata bashi amsa ba dan bata ma san me kuma zata sake ce da shi ba.

Salmerh😘
[23/01, 6:53 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...103*

........Sallamar Inna shi ya dakatar da tattaunar da suke yi...Dukkan su sun amsa sallamar amma ciki- ciki.

Inna kam bata ma lura da yanayin su ba fuskar ta yalwace da fara'ah take masa lale marhaban da zuwa.

Ganin haka yasa shima ya danne damuwar sa ya 'ka'kalo fara'a kawai sbd Goggon sa.
Sai dai ya kasa jin zuciyar sa cikin natsuwa, gashi bayi da isashshen lokaci ayau 'din hakan yasa bai da'de ba yayi wa Inna sallama ya tafi..da al'kawarin zai dawo bada jimawa ba...dan Inna tace da shi akwai maganar da take so suyi da shi muhimmiya.

Ko ci kanka Zaitoon bata 'kara ce da shi ba sai da zai wuce sannan tai masa fatan sau'ka lpy shima 'din bai amsa ba yy gaba...Adam a fili ya fara fahimtar wani abu da zuciyar sa ke raya masa game da Zaitoon da Abban Mufeeda yana kuma tsoron kasancewar sa gaskia.

Ko bayan fitar sa Zaitoon bata sake sakin fuskar ta ba, dama ba wata doguwar hira suke yi da Innar tata ba hakan yasa itama Inna bata wani damu da canjin yanayin ta da ta gani ba...a tunanin ta rashin sabo ne ko wani abin daban.

Kwata- kwata Zaitoon bata samu natsuwar zucia ba tun bayan tafiyar sa, haka nan kawai take jin ranta cikin damuwa, ba kuma zata iya tantance mene asalin damuwar tata ba.

'Bangaren Rayyan kuwa har wani duhu- duhu yake gani sbd takaicin aabinda idanun sa suka gane masa, wai wannan yarinyar da ke da igiyar auren ssa akanta ce take irin wannan fara'ar ga wwani 'kato can da ko da wasa shi bata ta6a yi masa irin fara'ar ba.
Ba 'karamin sosa masa zucia abin yayi ba.

Yana isa direct gidan sa ya wuce ya zube kan kujera, jijiyoyin kansa duk na nunawa.
Sam ya kasa tantance abinda ya gani, babban damuwar sa sanin ala'kar dake tsakanin su da har ya kawo wannan sha'kuwar.

Babu wanda yasan ya dawo har dare, kuma duk 'kiran da ake yi masa ko damuwa ya duba masu 'kiran ma bai yi ba balle ya damu da 'dagawa.

Fawwaz ne ma daya tashi a aiki bayan maghrib da ya 'kirayi layin nasa yy sa'a ya 'daga, cewa yy kana ina.
Amma Rayyan ya'ki ce da shi komai kawai ya kashe wayar sa.

Sai washegari da yamma yahe gida amma kana ganin fuskar sa ka san ba dai- dai yake ba.

Ko da Ammi ta tambaye shi lafia nuna mata yy babu komai sai bata damu ba..tace kai ka sani ai tunda kai ba yaro bane.

Haduwar su da Fawwaz kuwa har sai da ya 'kwammaci dama bai yadda anyi ta ba, dan ba 'karamin ssha'kar da shi yayi ba da dariyar mugunta.

Be ma san meyasa ya labarta masa ba.
Sai da ya gama dariyar kafin yace" In baka.shawara mutumi na?..ka tattaro kayan ka su dawo kusa da kai hankalin ka zai fi kwanciya..."

Shiru yy bai tanka masa ba, tunani yake dama hakan zai faru da sai yafi kowa farin ciki, amma taya zai yi hakan toh bacin mahaifan ta basu amince ba har yanzu.

Tashi kawai yayi ya bar Fawwaz anan yy gaba.
Yaji da'din shawarar da ya bashin koba komai yy masa nuni ne izuwa mafitar 6ullewa.
Kuma ya tabbatar in ba hakan yy ba bazai yi maganin Yarinyar nan ba.

Bayan kwanaki biyu da faruwar lamarin sannan Shaheed ya dawo, shi kansa tun tafiyar tasa bai samu natsuwa ba, bai kuma yi kauran baki baba, dan ya labartawa Hajiyar sa komai, ya kuma zanta da Hafiz kan haka...Hajiyar sa dai tace ya cigaba da addu'ah yayin da Hafeez ya bashi shawarar fara tuntun6ar Goggon sa tukunna...ya kuma 'kara masa 'kwarin gwiwar da Iznin Allahu zaitun bazata kubce masa a wannan karon ba.

Dalili ma kenan da ya sanya shi zuwa yau din, dan Hafeez yace masa da zafi- zafi ake dukan 'karfe, shi kansa badan jikin mahaifin sa ba da tare zasu kamo hanya..amma babu komai addu'ar su na nan tare da shi.

Sosai Innah tayi farin cikin ganin sa dan dama abokin shawara take nema tsayin kwanakin nan.

Abinda ta fara tambayar sa shine..." lafiya kam...kayi ciwo ne...naga duk kayi sanyi..?"
Yace ba komai Goggo...rayuwa ce kawai sai a hankali.."
Tace " Allah ya rufa asiri..".

Sun tattauna sosai da shi da Innani akan batun Zaitoon.
Adam yaji bb da'di jikin sa yy sanyi sosai, amma sam bai bari Innani ta fahimci komai daga 6angaren sa ba, bai kuma nuna son kansa ba, abu ne da ya riga ya faru, ya dace ya kuma cancanta, matu'kar aka auna sa a mizanin fahimta...toh akwai dacewa sai dai yana gudun a wula'kanta masa 'yar uwa watan wata rana.

Akwai dacewa, akwai mutuntaka, sannan girmamawa da daraja, babban kuma shine 'kaddara daga indallahi.
Haka Allah ya riga ya tsara su basu isa suja da yin Allah ba.

Gefe guda yana jin zuciyar sa nayi masa zafi, lokuta da dama ya kan cire huci mai zafi da shi kadai ya san yyanayin da yake jin ransa.

Domin sam sam bai zaci abin.hhar ya kai hk ba, bai yi tunanin kasantuwar hkn da wuri ba sam, amma meyasa bata sanar da shi ba da bakin ta.?

Meyasa ta barshi ya sake famo tsohon mi'kin da ke binne cikin ransa bacin tasan babu ranar warkewar sa, meyasa ta barshi ya sake saka ransa ga samun daman mallakar ta..?"

Adam bai ta6a tunanin Zaitoon tafi 'karfin sa ba ahalin yanzu, domin aure yasha gaban komai, bai san cewa akwai wannan irin 'ka'kkarafar katangan a tsakanin su ba...ya 'dauka ganin Zaitoon tamkar yayewar wani 6arin ba'kin ciki cikin rayuwar sa ashe yy kuskure, ashe wata sabuwar ba'kin 'kaddarar ke sake tunkaro shi akaro na biyu.
Chapter 198 · 0% Book details