← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 218

Sashe 206

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudun kar ya dawo ya samo ta tsaye a wajen da 'yar guntuwar riga ya sata komawa da sauri ta sake na'de jikin ta da mayafin ta koma ta kwanta.

Wani bacci ma take ji na fizgan idanun ta a lkcn.

Shi kuwa ko da ya fito bai sake bi takanta ba yayi waje abinsa.

Bazai iya sa 'kafa ya bar gidan ba a halin yanzu duk da yasan bacci zatayi mai nauyi Amma yasan ko ya fita ma hankalin sa zai Zama a rave ne, hakan yasa shi yada zango anan palorn sa ya baje duk wasu kayan amfanin sa yana duba sakonni.
Da wa'danda ya jima ma bai duba ba da kuma na kwanaki biyun nan.

Ya amsa waya ya kuma 'kira wasu numbobin ma da kansa yayi magana da su duk kuma akan kasuwanci ne.

Yana shirin ajiye waya 'kiran Fawwaz ya shigo.
" Kace zaka shigo kuma naji shiru...?"
" Na fasa ne.."
Ya bashi amsa kai tsaye.
" Saboda me ..?"
Fawwaz ya tambaye sa.
" Yarinyar nan bata da lafia Fawwaz...bana son barin gidan ne ba kowa...but may be zuwa yamma zan le'ko in naga yanayin jikin nata...".

" Shegen kaya..mai ka aikata Rayyan...?"
Da sannu ya waro idanu...Sai a lkcn ma ya fahimci maganar Fawwaz din.
Da sauri yace " Fawwaz kai munfiki ne..? Me kake tunanin zan aikata...?"
Ya fa'da yana yar daria.
" Ka fini sani ai..."
" Ni an fada maka irin kane wai..?"
" Daga baya kenan".
" Zaka yi bayani ne idan mun hadu".
Daga hk ya kashe wayar dan baya so maganar tayi nisa.
Ya riga yasan koma menene ahalin yanzu Zaitoon sirrin sa ce...bai kamata abinda yayi ko rashin yinsa ya zamto yy exposing ga koma waye ba.

Kafin ya ajiye wayan ya kira Ammi..suka gaisa..tace masa ai ba'ki na nan zuwa gidan...yace ayau?"
Ammi tace" erh..
Ba'ki ne kasan wucewa zasu yi. "
Yace" Ammi da sun bari zuwa gobe zai fi.."
" Tace sbd me...?"
" Yace haka nan kawai Ammi..".
Tace toh shikenan. Ina 'diyata?"
Tana nan lafia.
Agaida min ita.
" Yace toh Ammi ".

Ya za6i yace da Ammi hakanne sbd gudun sa6anin fahimta sam baya so tayi tunani irin wanda Fawwaz yayi.

Bashi ya tashi a wajen ba har sai da yaji 'kiran sallahn azahar sannan ya mi'ke ya d'auro alwala ya nufi masallaci.

Yadda ya barta tana bacci hakanan ya dawo ya tadda ta, bambancin kawai a yanzu fuskar ta na waje ne ba kamar yadda ta rude shi da farko ba.
Tayi fayau da ita tana bacci abinta cikin natsuwa.
Bai isa inda take ba kawai ya sa Kai ya wuce masallacin sa.

Sai da yaje ya dawo kafin ya koma dan sake duba jikin nata.

Goshin ta ya ta6a yaji bb zazza6in ya sau'ka dan har zufa ya goge mata saman kanta.

Hannu ya kai cikin mayafin ya ta6o wuyan ta nan yaji baki 'daya bb zazza6in yanzu.

Wani ajiyan zucia ya sau'ke cike da jinda'di...haka nan shima yaji sha'awar yin bacci ya kamashi, ko Dan ya samawa zuciyar sa hutu Koda Babu yawa ma.

Hkan yasa ya kwanta agefen ta yana duban fuskar ta yana tunanin rayuwa har baccin yayi gaba da shi.
Basu suka tashi ba har sai da akayi la'asar.

Zaitoon ce ta fara tashi ganin sa kusa da ita yasa ta saurin matsawa.
A hankali ta sau'ka daga 'daya 6angaren da san'da ta nufi 'kofa cikin sa'a bu'de ta same shi.

'Bangaren da aka saka ta jiya ta nufa har wani ajiyan numfashi ta sau'ke ganin ta samu fita daga 6angaren nasa.

Bata ta6a jin ta cikin matsananciyar takura kamar yau din ba.
Rayyan kuwa tunda ta tashi yake kallon ta har ta fice ...sam baya son takura ta, baya son matsa mata akan abinda yasan ba ra'ayinta bane..shiyasa Bai tanka ba.

Duk abinda take ganin ya mata aranta shi bazai hanata ba..indai yana kan hanya.

Juyawa yy ya kwanta bisa cikin sa ya saki wani nauyayyen ajiyan numfashi.

Ya shafe akalla kimanin mintina biyar ahakan shi kansa bazai ce ga tunanin da yake ba bazai ce ga ainahin inda zuciyar sa ta nufa ba .
Wannan lkcn agida ya sallaci la'asar 'din sa dan jam'i ya riga ya wuce sa.

Ko da ya idar fita yy da key din mota dan yi musu take away din abinci tunda ya hana akawo daga gida ya kuma san dole zasu bukaci abincin.

Koda ya dawo gidan sai da ya fara shiga 6angaren sa ya 'dauko maganin ta kafin ya nufi nata 6angaren wanda ada yake 6angaren Amrah ne kafin ya tattara su ya bar gidan, duk da yake a halin yanzu ba 'karamin gyara aka yiwa gidan ba amma duk da haka bazai gaza gane part part na gidan ba, da sallamar sa ya isa gami da tura kofa.

Sallah ya same ta take yi bayan ta shirya cikin doguwar rigar atampa da alamu dai wanka tayi.

Bai zauna ba kamar yadda bai ajiye abin hannun nasa ba.
A wannan tsayuwar tasa ne kuma ya samu cikakken damar karewa 'dakin kallo tass fiye da yadda ya kalla da safe.

Sosai ya yabawa kokarin yayyen nata, hakika sun nuna bajinta sosai, duk da ba hakan aka so ba shi kansa bai so ace Zaitoon tazo gidan sa matsayin matar sa da ko tsinke ba but yayyen ta sun nuna su sam sai sunyi nasu kokarin shiyasa aka Basu dama, hatta Ammi ba haka taso ba amma da yake sun matsa shiyasa aka bari sukayi.
Sosai kuwa ya yabawa kokarin su, dan sai ma ya ga kamar nashi 6angaren bakomai bane akan nata.
Kyau da tsaruwa kam 6angaren Zaitoon ya sha shi har ya gaji.

Yana nan tsaye har ta sallame sallar...sai ta dube shi ta dauke kai tamkar bata San da wanzuwar sa ba.
Shima din bai ce da ita komai ba.
Sai da tayi addu'a ta shafa sannan ta sake duban sa tayi kasa da kai.
" Ina yini Yaya?"
Kallon fuskar ta yayi yadda tayi fayau da ita sai yaji babu dadi...ciwon ne ko yunwa bai san takamamme meke damin ta ba.

Kamar kuma be kyautu ace tana karkashin inuwar sa wannan matsala ta same ta ba, Zaitoon ko ba ta tare da shi sai inda karfin sa ya kare wajen ganin ya kyautata Mata, ko da zai karar da dukiyar sa ba zai Yi kasa a gwiwa wajen ganin ya wadata ta da komai da take da bukata ba balle kuma hannun sa take.

Duk da yake wannan shine karo na farko kuma farkon zaman su tare, bazai ce dagangan yayi haka ba, amma duk da haka yafi ala'kanta faruwar hakan da laifin sa, duk da yafi ala'kantawa da gajiya da kuma rashin samun natsuwa lkcn taron bikin shine ya haddasa mata wannan ciwon.

" Ina ke mk ciwo yanzu ?"
Da kai ta amsa shi alamun babu komai
Yace" Ban jiba..."!
Sai da ta 'dan cuno baki sannan tace" Bako ina".
" Kan naki fa?"
" Yana ciwo ka'dan".
" Kince bako ina kuma..?"
" Ai da sauki sosai.."
" Ok".
Yace yana matsowa kusa da ita.
Ledan ya ajiye mata sannan maganin, yace" kici abinci kisha magani zanje in dawo ki kuma tabbatar kinsha magani if not kuma...hmm".
Ya fada yana dage gira.

Bata ce da shi komai ba haka shima bai 'kara ba yayi gaba abinsa yama fice daga gidan zuwa gidan Anty.

Salmerh😍
[03/02, 11:59 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...105*

........Kamar yadda yace haka tayi, abincin ta caccakula sannan ta ta kora maganin tana yatsine fuskar ta.

Yamma ta riga tayi sosai dan haka bata so ta sake kwanciya musamman ma sbd ganin maghrib ta gabato, hakan yasa kawai ta yanke shawarar zagawa cikin gidan, amma sam sai taji zuciyar ta bai yi na'am da hakan ba, tsoro ma taji ya tsirga mata lokaci guda.

Nan ta zauna tana tunani bata ankara ba sai jin 'kiran sallar maghrib tayi...bata 6ata lokaci ba ta mike ta gabatar da sallan ta har tayi isha'i kuwa bata jin motsin kowa ba...nan tsoro ya sake shigan ta sosai.

Tashi tayi taje ta rufe 'kofan ta da makulli, windows ma duk ta rufe su ta gyara curtains 'din ma tsaf sannan tayi shirin bacci.

Duk kuwa abinda take yi cikin sanyin jiki take yin sa dan ko motsin kirki bata iyawa balle ta6a abinda tasan zai bada sauti a zahiri sbd tsananin tsoro...wani turare ma da ta 'dakko zata fesa jin yana bada sautin 'yar 'kara da sauri ta ajiye sa ta 'dauki wanda tasan bai fidda sautin komai illah kamshi tayi amfani da shi...domin ta jima da koyon son 'kamshi wajen Marwa.

Tana gamawa tayi kwanciyar ta ta rufe har kanta cikin duvet sannan ta fara karanto azhkar cikin ranta.

Tana 'kewar Innar ta, Mufee, da su Marwa amma ba halin magana da su.
Sam bata san amfanin kawo wannan gidan ba, haka nan kawai an tsamo ta cikin 'yan uwanta aka jefo cikin wannan gida da baida maraba da kurkuku...gidan da hatta Mufeedan ta ma shamaki yy mata da ita.

Lokaci guda sai tunannin ta ya koma baya, can baya lokacin da aka ta6a sace su ita da Mufee...yanayin halin da suka shiga da yanayin mutanen, a hankali tunanin ta ya gangaro kan Sultan.

Wani sabon firgici da tsoro ne ya diran mata lokaci guda da ko dan yatsanta bata 'kaunar motsawa balle jikin ta, illah addu'a da take iya yi shima a zuci.

Haka nan kawai sai taji wasu zafafan hawaye na sakko mata.
" Banda ba'kin hali ina ma laifin akaita gidan Ammi, da yanzu suna can tare da Mufee da Marwan ta".
Ta sake ayyana hakan cikin ranta.

Haka ta dauki tsawon lokaci cikin wannan yanayin, bayan ta gaji da kukan bacci 6arawo ya sace ta.

Bata san lokacin da ya shigo gidan ba dan haka ko motsin sa bata ji ba.
Chapter 206 · 0% Book details