← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 218

Sashe 141

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

".... _Sultaan_ !...ya sake furtawa saman la66an sa a karo biyu, tunani ya cigaba da yi a kansa, Sultan ya gama 'kure shi..ya gama kaishi ma'kura, Sultan ya riga ya kaishi gejin da sam ba zai iya rintse idanu ya cigaba da barin sa ba, ba zai iya cigaba da barin Sultan yana da'kusar masa da duk wata walwalar sa...ya ishe sa haka nan.

Bai san mai Sultan ke shirin zama a dunia ba sam, bai san ina ya cusa ilimi da tsoran Allahn sa ba, a yanzu ya riga ya kaishi ga6ar da bazai iya barin sa ba, ba zai barin sa sake cin nasara akan sa ba sam sam....

Da fitowar Anty Madeena ta tarar da Zaitoon da Mufee rungume da juna...kallon.su ta dan yi na 'yan sakanni tana ayyana wani abu cikin ranta.
Ba komai ke mata yawo aka ba kusan ko wani lkc face tasan yadda akayi Zaitoon ta samu Mufeeda, musamman idan ta dubi yarinyar taga yadda kusan kullun kamar ta ke 'kara bayyana 'karara sai taji ta sake 'kaguwa da son sanin mafari da tsushen komai...amma ta lura Rayyan kamar har yanzu bai bawa lamarin muhimmanci ba.

A hankali ta dawo da kallon ta ga Rayyan dake dafe da kansa.

Yanayin sa sai yafi 'daukan hankalin ta dan haka wajen sa ta nufa tana zama gefen sa take tambayar sa" ya akayi ne Rayyan...?"

Bude jajayen idanun sa yayi ya sau'ke bisa fuskar Antyn tasa, sai dai madadin ya amsa ta kawai sai ya mi'ke tsaye sannan yace..." Bakomai Anty, bari muje kawai za muyi magana daga baya, akwai abinda ke gaba na yanzu wannan fitinanniyar ta rikita min hankali akan Mufeeda...".

Duban inda suke Anty Madeena tayi sai tayi 'yar murmushi.." Ina laifin me son naka Rayyan...?"

" Hmm"..kawai yace batare da ya 'kara wata kalma ba yayi gaba.
" in kin gama koken sai ku taso mu wuce..."
Yace da Zaitoon batare da ya dube ta ba sannan ya fita.

Kallon Anty tayi tana girgiza kai tace "Anty kice ya barmu anan dan Allah...".
" Kiyi hakuri ki bishi Zaitoon, baki ganin tashin hankalin da yake ciki ne, dole kinsan zai bu'kaci ganin ku kusa da shi ai..tashi kinji yi ha'kuri....".

Tayi maganar tana mai tasowa ta 'dago Mufeeda daga jikin ta dole Zaitoon ta mike tana zum6ura baki.
Cikin ranta take jin babu dadi, meyasa kowa son kansa ya fiye masa yawa ne, taya baza su fahimce ta ba sai kansu? Mutumin da da kunnuwan ta taji ya za6i akashe mata yarinya shine za'a ce zai bukaci ganin su toh suyi masa me kuma..?

Gida Rayyan ya mayar da su sannan ya sake ficewa batare da ko cikin gidan ya 'karasa ba.

Zaitoon wannan karan 'dakin ta dake can 6angaren Ammi ta koma tayi zaman ta.

'Bangaren Rayyan kuma dama ya jima da fara zargin Sultan tun bayan haihuwar Arfan ya fara dasa ayar tambaya akan sa, a hankali yake binciken sa kwanciyar sa jinya ya dakatar da komai, sai dai bayan hakan a yanzu ya gano abubuwa da dama da suka faru wanda Sultan ne da kansa ya jagoranta, ya gano da sa hannun Sultan bisa abubuwa masu dama kuma marasa da'di da suke faruwa a company da ma cikin gidan su gaba 'daya, sai dai he can't directly point a finger on each incidenced.

Amma kidnapping Zaitoon da Mufeeda da akayi ya kuma revealing masa komai, domin ba 'karamin tsaurara bincike yayi kan lamarin ba tun bayan fahimtar da yayi cewa a 'daya daga cikin guest house din Abban su aka 6oye su.

Wannan gidan ya kasance mallakin mahaifin su ne wato Sa'ad Auta...kuma su ka'dai ahalin gidan ke amfani da shi suma 'din banda matan cikin su, a atakaice yanzu kuwa daga shi ne sai Sultan araye kawai ke amfani da wannan gidan...kusan ma Sultan ya fishi dan shi ba kasafai yake zuwa ba sauran gidajen Abban nasu ba.

Yaso yayi jayayya da zuciyar sa akan saurin sau'kar da zargin ta bisa kan Sultan duk da kuwa yana da hujjoji 'kwarara but hkan bai yi tasiri cikin ransa ba..dole ya tabbatar da shi 'din ne dai, babu wanda ke da access da wancan gidan bayan su, kuma basu bada hayar sa balle aro dole shine ko Sultan, in ba shine da kansa ba kuwa sai dai Sultan...da 'kyar ya harha'de Puzzle din, amma har gobe ya kasa gano manufar Sultan kan haka, kenan dai Sultan ne ya kidnapping 'din su ko kuma yasa ayi domin yasan baya 'kasar a halin yanzu, ya kuma razana shi akan kisan 'daya 'daga cikin su alhali bai kashe ko guda ba, me hakan ke nufi kenan...?"
Sultan ya kar6i ku'di a hannun sa masu yawan gaske da sunan ku'din fansan ran Zaitoon bayan acewar sa ya sa an sanar da shi cewar an kashe Mufeeda....Sultan! Sultaan!! Sultaan!!!..what's the meaning of all these...wai duk wannan shirin Sultan din sa ne ya yisu...?".
Ya tambayi kansa.

Tuni ya sa an kamo wasu dake aiki da Sultan din ciki kuwa hadda su Yusee da su Huzaifa anan kuma ya 'kara samun cikakken bayani kan komai...ya kuma tabbatar da zargin sa.

Cikin firgici yake tariyo 'kazamin aikin da Sultan ya aikata musu batare da sun san shi bane, batare da sun san kwana suke su tashi da makiyin su ba, Sultan ne ya kashe masa mahaifi da 'kanin mahaifin sa, Sultan ne ya kashe masa 'dan uwan sa da duk ahalin sa mata da 'diyar sa bayan ya tabbatar da cewar ya fara zargin makircin sa, Sultan ya kashe masa 'yar uwa duk a bakin yaran sa ya samu cikakkun bayanan da be ji kokonto akan su ba dai dai da kwayar zarra.
Sultan ya gama 'kure shi gaba 'daya, bayan duk wannan kuma shine yake fita da matar sa Amrah ya ke kuma bata maganin hana haihuwa dan kar ta haifa masa 'dan da zai gaje shi...'karshe kuma shi ta haifawa 'dan suka kuma waske kamar 'dan Rayyan ne batare da sun san ya gano su ba.
Sultan ya kan dauki Amrah suyi duk tafiyar da suka ga dama tamkar ba auran sa ne akan ta ba, tamkar ba zaman 'dan uwa Sultan yake a wajen sa ba.
Hakika Sultan bai kasance 'dan uwa abin alfahari ba, Sultan ya nuna masa bambanci tsakanin jini da ruwa, hakika kaurin jini ya rinjayi ruwa nesa ba kusa ba, Sultan yayi masa gi6in da har karshen rayuwar sa bazai ta6a mantawa ba.

Kallon 'dan uwa yake wa Sultan ta yadda koka'dan bai ta6a zargin sa kan komai ba, har gidan soja ya kaishi bisa neman cika masa burin sa na 'karya, erh mana na 'karya tunda burin shaho ne ba na gaskia bane tunda 'karshe Sultan ajiye aikin yayi duk fadi tashin da yayi kafin ya sama masa.

Ta6a masa ahali a halin yanzu bazai iya jurewa ba, domin jin su yake tamkar ransa...duk ya fahimci shirin Sultan aka sacen sun da sa ayi, unfortunately kuma da aka 'kira aka bashi za6i sai ya za6i Zaitoon yace inma kisan ne su kashe yarinyar.

Ba dan komai yy hkn ba kuma face dan rama khairan da khairan.
Bai yiwa Zaitoon adalci ba aganin sa idan ya za6i 'diyar sa akanta bayan duk wahalhalun da tayi tayi su ne sbd Mufeedan yasani.

Hakan kuma da yayi shi ya bawa Sultan tabbacin cewa basu da ala'ka da yarinyar, dalili kenan da yasa duk wani shiri nasa da hasashe ya korar da su...ya kar6i makudan ku'dade a hannun sa...ku'daden sa na halak da ya tara su da gumin sa amma Sultan yake can yana kashe su ta hanyar banza, da dukiyar sa Sultan yake amfani wajen ci masa dunduniya, da dukiyar sa yk amfani wajen yin duk shashancin da yaga dama ciki kuwa hadda matar sa ta sunna.

Bazai ta6a iya barin Sultan yasha haka nan kawai ba...idan yabar shi yasan bazai ta6a barin sa yin abun kansa ba.
Dole ne sai ya 'dauki tsatstsauran mataki a akan sa.

Tun kafin Sultan ya dawo Rayyan yasa aka tsaida komai nasa, an dakatar da share da ake basa na company an kuma rufe account din ma gaba 'daya.

Rayyan ya gama duk shirin sa ya tattatara hujjoji da bayanan sa gamsassu dawowar Sultan 'kasar kawai yake jira a yanzu sai kuma a lkcn yaji hankalin sa ya kwanta.

'Bangaren Sultan kuwa hankalin sa tashi yayi bayan fahimtar da yayi cewa asusun bankin sa duk an dakatar da su, ya tuntu6i bankuna kuma sun nemi da dole sai yazo ya ciccike wasu forms kafin komai ya daidaita, cikin rashin sani sai yi dogon nazari ba, sanin na'urar sa ya kasa yi mai amfani kan hkn.

Sannan ko ya 'kira yaran sa da yake aiki da su baya samun su a waya.

Yayi magana da Amrah kuma tace masa babu mamaki shirye- shiryen 'karshen shekara ne ya biyo takan asusun nasa.

Dole ya fara shirye shiryen dawowa gida.

Rayyan kam ciwon sa ne ya kusan sake kwantar da shi bayan da ya gama binciken sbd stress da yai masa yawa, domin tsananin damuwa da rashin sukuni ya dan sa jinin sa haurawa, sai da yasha treatment aka bashi hutu sosai kafin ya 'dan samu nutsuwa, sai kuma a lkcn ne Zaitoon ta je duba shi domin tun bayan dawowan su gida da Mufee bata 'kara yadda ta je inda yake ba bata sake sanyashi a idanu ba domin bata fita ko'ina koda yaushe tana dakin ta, hatta Marwa ita ke biyo ta 'dakin suyi hira gaishe da Ammi ka'dai ke fidda ta shima 'din ba kullum ba.

Haka ma Mufeeda bata sake zuwa makaranta ba...shi kansa yana sane da hakn amma yana so sai ya gama shirin sa tukunnna.
Tuni ma yaje yayi magana da makarantar akan yarinyar.

Ko rashin lafiyar tasa a abakin Marwa taji, ta kuma ga yadda duk suke rawan jiki kan hkn...hakan yasa ta yanke shawarar zuwa gaida shi.

Salmerh😘
[9/12/2022, 4:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...80*
Chapter 141 · 0% Book details