Sashe 74
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido Zaitun ta zaro tana duban Ammi...
Itama kallon ta tayi suka ha'da idanu take sai ta yi kasa da idanun ta kan fuskar Moopy ta sau'ke idanun, take taji wani tausayi, 'kauna da kuma soyayyar ta ya 'kara kama ta.
A nutse ta sake duban Ammi ta 'dan shafa goshin ta sannan ta bu'di baki tace" Ammi kuka fa take yi sosai idan an kaita, bazata ta6a yadda ba wancan ma da kyar aka yishi, kuma, kuma..ni..."
Sai tayi shiru tayi 'kasa da kanta.
Duk abinda take yi Ammin na kallon ta kuma tsab ta karanci yanayin da take ciki, ganin ta kasa furta abinda ke ranta ne yasa ta 'karasar mata da fadin" ....ke kuma bazaki iya juran ganin kukan ta ba ko?"
Murmushi tayi tayi kasa sosai da kanta tana sake rungumar Moopy a jiki.
Ammi ma murmushin tayi tace" gashi tun ba'ayi nisa ba ai na kama ki".
Nasan ai wannan dalilin yasa tun farko baki saba mata da kitson ba dan bata so kema sai baki bada hankali wajen yi mata ba".
'Yar dariya tayi me birgewa wanda take jimawa kafin tayi irin sa, sai ma in taga farin cikin Moopy kafin kaga tayi irin wannan dariyar, Ammi kanta sai da tayi murumushi ganin dariyar Zaitoon din.
Tana dariyar tace " yau dai Ammi nima zan daure raina ai mata kitson nan Allah yasa kar yayi mata zafi.."
Insha Allah ba zai mata ba Zaitoon".
"Amma Ammi ai ba yau ba kam ko...kinga yau akayi wannan..." kar ki damu sai nextweek idan an ware wannan za ai mata..." " shikenan Ammi Allah ya nuna mana".
Dama tun bayan tafiyar su Marwa ba' a sake yi mata kitso me kyau ba.
Da yammacin ranar Rayyan ya shigo 6angaren Ammi, kasantuwar ya 'kira wayar ta baya tafiya sai da ya 'kira ta landline dake Bedroom 'dinta kafin ya same ta nan ta sanar da shi dama tana so suyi magana yazo ya tana jiran sa.
Shima yace yunwa tace ba matsala yazo yanzu ma ake ha'da abincin.
Ko da ya shigo bai tarar da kowa palorn saman Ammin ba, dan haka sai ya koma ya mi'ke kan 3sitter yasan Ammin zata fito yunwa da gajiya duk bi sun kashe masa jiki duk yau bai samu lokaci yasa komai a cikin sa ba.
Sabo da yiwa Zaitun kitso da Moopy tayi ne yasa da ta ga mutum kwance kuma gashin sa luf luf kawai ta nufi wajen sa, hannun ta ta cusa cikin gashin kansa shima tana jagwalgwalawa tamkar dai yadda take yiwa Zaitun da sunan kitso.
Cikin 'dan baccin da ya fara daukan sa yaji ana masa 'kaikaiyi akansa, bai bu'de ido ba ya tsaya idanun sa a lumshe yana sauraran abinda ake yi masa, sosai yake jin natsuwa na shigan sa duk da bai san gwanin da ke yi masa hakan ba zuciyar sa fal da mamaki, a hankali ya bu'de lumsassun idanun sa batare da ya waigo ba, domin tun kafin ya waigo din ya fahimci hannun waye akan nasa haka kawai sai yayi murmushi.
_He wish 'diyar sa ce wannan halittar_
Karo na farko cikin rayuwar sa da wannan tunanin ya 'darsu masa a zuci.
'Dan waigowa yayi ka'dan ya sauke idanun sa akan fuskar Moopy kamar dai yadda yayi zato ita 'din ce.
Wani bugu zuciyar sa tayi da ganin fuskar yarinyar, ido ya tsura mata yana jin zuciyar sa na tsananin bugu da 'karfi, bai san me yasa shi bugun zuciyar ba kuma bai kuma san matakin dauka kan hakan ba.
Moopy kam da hankalin ta ya 'dauku ga kitson bama tasan yana kallon ta ba bata kuma san kan waye take wasa da shi 'din ba har a lokacin.
Sai da ya gama 'karewa fuskar ta kallo sannan ya sake juuawa da kyau ya koma rub da ciki, fuskar sa ya tallafe cikin tafukan hannun sa sai ya kasance gaba daya hankali da idanuwan sa na gareta ne.
Kallon kallo suka tsaya yi da Moopy, tamkar masu karantan juna.
Lokaci guda kuma ta 'dan ja baya tamkar wacce ta tuno wani abu, da sauri take matsawa baya sbd tuno waye shi, tsoron shi take ji sosai, kwana biyu da bata ganin sa yasa ta 'dan mance shi kadan, da sauri ta fara yin baya baya, hakan sam be yi mata ba dan gani take kamar zai kamata ta bayan ta hakan ya sanya kawai ta sanya kuka tana nufar hanyar da tasan ta baro Zaitoon.
Zaitun na tsaka da gugan kayan Ammi kawai taji muryar gudan jinin ta na 'kiran _Mammy_ cikin kuka ai da sauri ta ajiye iron 'din ta fito da hanzari tama mance da cewar kan mayafi tabar iron 'din...tana isowa bakin kofar taci karo da ita duk ta rikice, sama da 'daga ta idanun ta na kan sa da yake Zaune dafe da kansa sbd hayaniyan kukan Moopy da ya cika masa kunne yake neman rabashi da nutsuwar sa.
Wani kallo na mugun tsana, haushi da takaici Zaitun ke binsa da shi tana kwantar da kan Moopyn kan 'kirjin ta.
Sam ta kasa dauke idanun ta akansa, ga kuma takaicin rashin sanin abinda yayi ma yarinyar da ya addabi zuciyar ta.
Tana jin da ace tana da dama da babu abinda zai hana ta ramawa Moopy duk muguntar da yk yi mata.
Dadin da'dawa ma ga yarinyar ta kasa yin shiru, dama 'dan banzan zuciya gareta da idan ta riga ta fara kuka to lallashin ta da kyar take iya yi.
Tana tsaye a wurin Ammi ta fito jin 'karan kukan Moopyn, da zuwan ta kuwa kallo 'daya tayi musu ta fahimci me yake faruwa dan kuwa har a lokacin idanun Zaitun na kansa ne tana yi masa mugun kallo yayin da shi kuma ke dafe da kansa da duk hannuwan sa biyu be masan da zuwan Ammi wurin ba.
'Karamin tsaki ya ja ya mi'ke ya nufi hanyar barin palorn, ganin hakan yasa Ammi saurin dakatar da shi da tambayar" Me ka yiwa yarinyar nan Muhammad?"
Cak ya tsaya da jin furucin Ammin amma bai waigo ba.
" Me Ammi take tunanin.zan mata..?"
Ya tambayi zuciyar sa.
Sai da Ammi ta sake maimaita tambayar tata da alamun 6acin rai sosai cikin muryar ta wanda ya bayyana har kan fuskar ta kafin ya waigo, kan zaitun ya fara sau'ke idanun sa kana yayi hanzarin maida su kan fuskar Ammi, sosai yayi kici- kicin da fuska, shi kansa ransa 6ace yake yanzu ganin yarinya 'karama na neman ha'da sa da mahaifiyar sa, kan abinda ko hauka yake bazai iya aikatawa ba...
ya riga yasan duk zargin sa suke da dukan yarinyar while shi ko da wasa be ga abin bugu a wajen ta ba me ma tayi masa da har zai 'daga hannu yi buge ta...ko wancan ma daya ta6a faruwa bisa kuskure ne amma ba niyyar sa ya bige ta ba.
Ha'da idanu da suka yi da Ammin ya fahimci tsananin bacin rai da ta shiga.
A hankali ya lumshe idanun sa sannan ya 'daga 'kafafu ya yi waje be ko sake kallon inda suke ba.
Zuwa lokacin ma Moopy tayi shiru jikin Zaitun sai ajiyan zuciya da take saukewa.
Ammi ma sassautawa ranta tayi tunda ta ha'da idanu da Rayyan din...domin kuwa ita tasan abinda ta haifa, tasan duk rashin hankalin Rayyan ba zai iya 'daga hannu ya bigi Mufeeda ba.
Hakan yasa ta juya ga Zaitun tace ba mamaki tsorata tayi da ganin sa shiyasa take kuka kinsan ba wani sabo ne tsakanin su ba...mi'ka min ita ki duba aikin da kike yi, ina jiyo 'kauri."
Ammi ta 'karashe maganar da mika hannuwa dan kar6ar Zaitun 'din.
Mi'ka mata yarinyar Zaitun tayi tare da komawa 'dakin nan taga 6arnar da tafka, ashe bata tsaida iron din ba kan mayafin Ammi ta barshi gashi ya kwashe mayafin ya kone sa.
Cike da firgici take kallon wajen tana mamakin yadda ma akayi ta manta.
Ami dake bayan ta ma kallon mayafin tayi sai kuma ta dubi Moopy dake hannun na tana murmushi irin nasu na manya.
Juyawa tayi da niyyar fita bata yi niyyan tankawa ba.
Jin motsin ta ne yasa ta waigo da wuri ganin.Ammi yasa ta mikewa da hanzari.
Tasan ta riga ta gani.
" Ammi..."
Tace sai kuma ta kasa 'karasawa, tasan bata kyauta mata ba.
" Ammi dan Allah kiyi hakuri..."
Wannan karan tayi kokarin furtawa
" Kar ki damu..."
Ammi ta bata amsa batare da ta waigo ba, ta kuma cigaba da tafiya har ta bar 'dakin.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Zaitoon ta sauke, ganin alamun Ammi bata damu ba duk da yake tsaddaden mayafi ta kone mata, shiyasa har kullum darajar Ammin kara hauhawa yake mata a zuciyar ta.
Gaba 'daya laifin kacokam ta tattara sa akan Rayyan tamkar shi da hannun sa ya 'kone mayafin.
Aikin ta ta cigaba da yi tana jin 'kwalla na ganagaro mata amma bata iya ta share sa ba.
Har sai yaushe mutane zasu fahimci wace Moopy ne, har su tausayawa maraicin ta, su tausaya wa rayuwar ta su daina yi mata mugunta....
Wani sabuwar tsanar Rayyan take ji na taso mata, meyasa ya za6e su ne, meyasa ya za6i ya maida su abokan gaban sa bayan yasan tako ina yayi musu zarra ya musu fintinkau, me suka tsone masa a duniyan nan...ko zaman gidan ne baya kauna suke yi..?
Tambayoyi ne cunkus cikin ranta amma bata da me amsa mata su.
Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya har zuwa lokacin da Amrah ta dawo.
Ita kam gaba 'daya sai a hankali ta ko ina bata da sauki, ita kanta bata san meyasa ta tsani Zaitun ba, balle ita kanta Zaitoon din ta sani, sai da bari aranata cewar kawai rashin jituwa ne.
Komai tayi laifi ne a wajen Amrah, abu ka'dan sai tace Zaitoon ta raina ta ne shiyasa take yi mata rashin kunya, ko kuma tace Ammi ce ta daure mata gindi yasa har ta raina ta.
Salmerh😘
[10/10/2022, 10:12 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...46*