← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 218

Sashe 60

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baiyi mamaki ba dan shima yafi kyautata zaton malerian ne kuma treatment 'din sa yake mata.

Haka yake yini 'kiran wayar ta dan tabbatar da lafiyar ta da kuma shan maganin ta akan lokaci.

Yayin da duk amsa wayar da Amrah ke yi bata a gidan, tana can tare da Sultan a wani tsadadden hotel.

Shiri sosai tayi kafin ta fita, harda socks da ni'kabi ga dogon hijabi da ta sanya, in ba dai wanda yai mata farin sani ba ba lallai ne a gane ta ba.

Kwanaki kusan shida kenan tana yiwa Rayyan 'karyar ciwo yayin da gefe guda babu ranar da bata ha'duwa da Sultan kuma duk abinda yake so yake yi da ita...gajiyar ha'duwar ta da Sultan take bayyanawa ga Rayyan matsayin bata da lafia, hatta Ammi sai da tazo duba ta har side 'din ta, haka ma Marwa musamman tazo gaida ta.

Bata samu lokacin Rayyan ba har sai da Sultan ya sarara mata akaran kansa bisa shiryawar ta, dan tasan yanayin ta ita, jikin ta irin jikin nan dake son gyara akai- akai a koda yaushe yakan bu'kaci gyara, matu'kar ta 'dan 'dauki lokaci bata yi amfani da kayan gyaran jiki ba ita kanta ta kan fahimci wasu canze- canze, ganin yadda Sultan ya ri'ke mata wuta kuma ya sanya ta'ki yarda tayi amfani da komai dan matukar tayi toh bazai fasa neman ta ko na rana guda ba, tana.shan azaba kam amma haka take jurewa har sai da ya 'kure da kansa...ai kuwa shirin ta yayi aiki dan Sultan da kansa ya sarara ya kyale ta yana sake jaddada mata cewar ta tambayi Rayyan ku'di tayi gyaran jikin ta.

Baki ta tura tana kukkuni 'kasa- 'kasa da ta tabbatar zai ji ta.
" Shi ina ruwan sa, ba cin duk kaine ka lalata komai shi yaushe ma ya bani ku'din, kuma idan ya bani ku'din bakai ke amshewa ba.
" Kar ki damu wannan karan wlh bazan amsa ba, ai dani za'a kwashi garar, dole in bari kiyi dan kina bukatar hakan sosai, Matata ba haka take ba kuma ban ta6a bata ku'din gyaran jiki ba...".

Fa'dan hakan da yayi ne ya sanya suka yi rabuwar baran baran, tana masifar yana ha'da ta da matar sa bacin shi ne yafi nace mata.
Yana mata daria yace " Kema ai kinaso kinga sabon jini kin li'ke min shiyasa da nace hy kike cewa Yesss..."
Fuu ta tashi ta nufi bayi cike da haushin maganar sa tace " Zan kuwa baka mamaki.
" Babu yadda kika iya dani 'yan mata..".
Ya 'karashe yana dariyan mugunta.

Abinda ya faru kenan tsakanin Amrah da Sultan aranar ha'duwar su ta 'karshe da shi.

Tasan gaskia ya fa'da mata tana bukatar gyaran ita kanta ta sani amma ko giyar wake tashe bata isa taje ga Rayyan da wannan batun a yanzu ba sai dai ta nema tayi da kanta, shi kuma Sultan tasan bazai ta6a bata ku'di ba, dole ta yanke shawarar neman ku'di wajen mahaifiyar ta.

Cikin rashin sa'a kuma a daren ranar Rayyan ya nemi hakkin sa wajen ta ta sigar da yasan bata ta6a iya bijirewa bukatar sa.

Ba 'karamin mamaki yayi ba da jin Amrahn tasa ba kamar yadda ya tsammata ba, bayan duk ku'da'den da ya ajiye mata kwanaki tara baya, kuma yana da tabbacin tun ranar bai sake kusanta kansa gareta ba sai yau 'din, kenan bata yi komai ba, amma ai Anty Madeena ta sanar da shi cewa ta ha'da mata komai ya akayi haka.
Ko dai bata yi amfani da su bane.

Gefe ya koma dafe da kansa yana sakin numfashi mai zafi.
Cikin muryar da yasan ita ka'dai zata jishi yace" Amrah baki son farin ciki na ko..?"

Baki ta 'dan tura gaba ta riga tasan laifin ta amma hakan bai hana ta basarwa ba tana yatsine fuska tace " Baby ni me nayi kuma..., bayan duk kokarin da nayi?"

'Karamin tsaki yaja" Sau nawa zance miki ki daina wasa da amfani da abubuwan da Anty Madeena ke ha'da miki..?"
" Ai nayi..".
Ta fa'da tana turo baki.
" Shut up da Allah.."
Ya dakatar da ita a tsawace yana 'dan waigo wa.
" Ni kike cewa kinyi Amrah? karya zan mk kenan ko me?"
Shiru tayi ta kawar da kai tana jinjina hali irin na Rayyan, sam baya 'daga 'kafa indai akan abinda ya shafi shimfi'dar sa ne baya wasa da lamarin.

" Sau nawa ni da kaina ma nake kawo mk abubuwan da nasan zasu miki amfani Amrah amma banga alamun kina kusantar su ba, duk wani abinda zan shigo miki dashi gidan nan sai na tabbatar da cewa zai anfane ki nake shigo da shi, amma dan ki nuna min baki son farin ciki na shiyasa kika za6i yin watsi da komai ko...."
Tashi tayi daga kwancen tana jan mayafi dan sitirce cikin ta ta zauna da kyau kan gadon tana kara turo baki gaba.
" Wait ma kafin tafiya ta ban baki ku'di ba da kika ce zaki gyara jikin ki meyasa kika fi son 6atan rai ne Amrah.."
" Toh Baby ba bani da lafiya bane kuma ma fa nayi kawai dai wlh dan ka kwan biyu ne shiyasa kaji kamar ban yi ba.."

Tsaki yaja kawai ya tashi ya wuce bathroom ya sakarwa kansa ruwa.

Sosai taji tausayin sa tasan yana matukar kokari wajen kulawa da ita, baya shayin kashe mata kudi ko nawa ta bukata indai wajen ganin ta gyara jikin ta ne musamman boobs din ta, ko da 'karya tai masa kan gyaran jiki baya shayin tura mata kudi, wataran tana yi kamar yadda yake so but wataran Sultan ke hana ta ya amshe ku'din.

Wani lokaci kuma da gayya zai bari har sai tayi gyaran jikin ya rike mata wuta har sai ya lalata komai.
Tana so da 'kaunar Rayyan sosai but tana jin dadin mu'amala da Sultan bata kuma son rabuwa da shi bata san me yasa ba.

Amma yadda ayau 'din taga yadda Rayyan ya 'dau fushi ya sanya ta yanke shawarar neman mafita sai dai bazata tunkari Anty Madeena kai tsaye ba, dan a ganin ta ai ma sai ta raina ta ganin koda yaushe sai ta nemi kayan gyara zata iya gano lagon ta.

Ko bayan ya fito bai ko dubi inda take ba ya gama shirin baccin sa itama ta fa'da bathroom 'din ta watso ruwa ta fito.

Rigar baccinta ta maida ta feshe jikin ta da turare mai sanyin 'kamshi sannan ta 'dauki wayar ta da niyyar barin 'dakin ganin Rayyan ya'ki ko duban inda take ne da alamu fushi yy da ita...gaba 'daya ji tayi itama tayi sanyi.

Fahimtar hakan da yayi ya sashi cafko hannun ta ya janyo ta ta fa'da jikin sa, kamar jira take kuma kawai sai ta saki kuka.

Shi kansa yasan bai kyauta ba masifar da yayi mata, tunda yasan ba ita ta halicci kanta ba Allah yayi ta haka, amma ai ba laifin sa bane itama ta sani, out of anger yayi wa'dancan maganganun, bai tashi sanin bai kyauta ba kuma har sai da ya samu natsuwa bayan ya gama wankan sa tukunna.

Shafa bayan ta yake a hankali yana 'ko'karin cusa kansa tsakankanin wuyan ta.
" I'm so sorry Babyn Baby...I didn't mean to...".

Sau 'daya ya fa'di hakan bai sake magana ba illah shafa bayan ta da yake faman yi alamar lallashi.
Tasan dama ba hana ta kuka yake ba, in dai abin kuka ya same ta fili yake bata tayi kukan ta son ran ta batare da ya hana ta ba sai ta gama kukan kafin yake lallashin ta.

Kamar yanzun ma dai, sai da ta gama kukan kafin ya bata ha'kuri ya kuma yi al'kawarin sake tura mata ku'di ta sake gyaran jikin domin dagaske yaji ta canza sosai irin canjin da ya gaza samun natsuwa da ita...dan yafi so koda wani lokaci yajita zam- zam.

Haka suka kwana tana rungume cikin jikin sa tana sakin ajiyar zuciyan kukan da tayi.

Washe gari bayan ta tabbatar ya tafi office sannan ta fara lalubo mafita, dan ta gama yanke bazata tunkari Anty Madeena ba ai da kunya.

Ameera ta yanke shawarar tambaya sai ta tuna ai Ameerar da 'kyar ne ma ta sani balle ta fahimce ta musamman da yake ba aure ne da ita ba.

Cikin wani group 'din su na whatsapp mai suna matan Aljannah ta tura tambayar tata kan cewa _urgent please a bani list 'din kayan gyaran jiki ni'ima dana Boobs._

Take kuwa aka watso mata su kala- Kala har sai da ta gaji da dubawa.
Da 'kyar ta ware wasu da suka fi kwanta mata kamar haka.

HA'DIN KAYAN ITATUWA
Yana 'kara ni'ima sosai ga mace.
Kankana
Cucumber
Tumatir
Mazar'kwaila
Dabino
Madara peak.

Gani tayi duk abubuwan nan babu wanda Rayyan bai yawan kawo mata acikin su amma bai ta6a fa'da mata amfanin shansu ba itama bata basu muhimmanci sam, Anty Madeena ce dai ta ta6a fa'da mata amfanin wasu daga ciki...dan haka su ta yanke shawarar nema.

Sai da tabi procedures 'din duk da aka fa'da ta sake duba wani ha'din Hulba wanda ake yin sa shima da abubuwa kamar haka.
Gya'da
Aya
Mazarkwaila
Hulba
Nono ko madara.

Akwai kuma
HADIN 'BAWON RUMAN
Wanda ake yin sa da Zuma da 'Bawon Ruman wanda akace Larabawan Dubai suka fi amfani da shi domin sanin muhimmancin sa, wannan ha'din yana matsi sosai.

Wa'dannan suka fi kwanta mata arai, dan haka Raleeya ta nemo ta tura kasuwa dan siyo mata abubuwan da ta tabbatar babu cikin gidan.

Da kanta ta ha'da komai da taimakon Raleeya ta kuma fara amfani da shi tun a lokacin dan ya kasance ne shan safiya da yammaci.

Kwanaki biyu bayan hakan Sultan ya 'kirata yake tambayar ta ko Rayyan ya bata ku'din, tace masa ya ki bata yace ne wai sai ya samu ku'di.
" Ji munafuki, ku'din da zai bakin ne har zai ce sai ya samu?"
" Haka yace amma Insha Allahu idan ya dawo yau 'din zan sake mai maganar".
" Ya dai kamata kam dan kina da bukatan canji gaskia."
cewar Sultan yana kashe wayar sa.
Haushi sosai na cika sa.
Chapter 60 · 0% Book details