Sashe 18
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" a a har tafiyar kenan...?"
Hajja tace da Zaitun bayan ta leko babu ko kunya balle nuna alhini.
Zaitun bata ce da Hajjan komai ba baya ga juyawa da tayi, kallon ido cikin ido tai wa Hajjan batare da tayi niyyar furta komai ba.
Tana shirin dauke idanun ta Hajjan tayi saurin fadin. " abu bai yi dadi ba, sai naji babu dadi kin san sabo.."
Tayi maganr tana kya6e baki wanda duba 'daya idan kai mata kasan iya fuska maganar ta tsaya.
" amma ni kam 'yar nan.. me ze hana ki koma ga iyayen ki ki nemi gafarar su ba fi miki wannan gantalin ba...?"
Kallon Hajja tayi da farko bata yi niyyan tanka ta ba amma jin cewa shawara yau din Hajjan take bata amma me kama da cin mutunci data tabbatar kuma gaskiya Hajjan ta fa'da yasa ta bude baki da kyar muryar ta duk bata fita tace" Ni ba gantali nake ba Hajja meyasa kowa bazai fahimce ni ba?, ko can gidan na koma babu wanda zai karbe ni matukar ina tare da yarinyar nan...".
" Toh ke meyasa bazaki yi irin yadda 'ya'yan zamanin keyi ba, ki jefar da ita kiyi tafiyar ki mana ko kuma ki maishe da rikon ta gidan marayu..."
" Bazan iya ba..bazan iya rabuwa da ita ba.."
Ta bawa Hajja amsa cike da tabbatarwa. Da yasa Hajjan bude idanu akanta sosai " aw toh...Allah shi kyauta.."
Cewat Hajja kenan tana me gyara daurin zanin ta.
Zaitun sake duban ta tayi daidai tana gyar rikon da ta yiwa jakar kayan su..." ni na wuce Hajja, idan Mmn Siyama ta dawo kice mata injini dan Allah ta yafe min..."
Tana gama fadin hakan ta tunkari kofa bata sake waiwayar gidan ba hatta dakin da ta zauna ciki wanda ragowar kayan ta ke ciki ma bata waiwaya ba balle Hajja dake mata Allah ya bada sa'ar tafiya.
Tayi tafiya me nisan gaske da ita kanta bata san inda take nufa ba, dan a har yanzun bawai sanin garin tayi gaba daya ba, mafi yawan unguwanni da wurare duk bata san su ba.
Ba ita ta dakata da tafiyar ba har sai da taji tamkar kafafun ta zasu tsinke sbd gajiya, banda numfashin ta dake fita sama sama yana kokarin ankarar da ita cewar bata ci wani abin ba tun ruwan lipton da ta sha da safe, 'dan guntun madarar data rage musu Mufee ta hadawa tasha dashi ita tasha ba'kin lipton din ba ko isashshen Sugar balle mahadi makamancin bread.
Bakin wani makaranta ta zauna tana dan ajiyan numfashin gajiya gashi ko sallar la'asar bata yi ba ga maghrib nan ta gabato.
Gani tayi zaman nata baya da wani amfani dan haka tashi tayi ta dauki jakan kayan nasu ta cigaba da tafiyar ta, duk da bata san inda zata ba, bata san inda ta nufa ba amma gwara tayi ta tafiyar kamar yadda Hajiya ta bukaci cewa tayi nesa da shi...ita kanta a yanzu zuciyar ta tafi bukatar yin nesa da su din ko hankalin ta zai kwanta.
Tun farkon alakar tasu da kanta ta ji aranta kamar Adam din ba sa'an yin ta bane amma shine duk ya kawar mata da wannan tunanin ganin yadda a kullun yake kokarin nuna musu zallar kauna yake nuna mata cewar ita din mutun ce mai daraja ashe hasashen Adam ne kawai, har yanzu darajar ta bai kai ko bakin farce ba wanda bata farga da hakan da kanta ba har sai da lamarin ta dangana da Hajiya ta tunatar da ita.
Wani gida da Zaitun ta gani kawai tayi shawaran shiga inda ta roke yarinyar da ta gani akan tana so ta yi fitsari, sallah take so tayi amma tafi son ta fara yin fitsarin sannan.
Batare da ko 'dar ba yarinyar ta bata buta gami da nuna mata bayin.
Jaka kawai Zaitun ta ajiye ta ansa butan gami da godiya.
" Da goyon zaki shiga kuma? ai da kin kawo ma na rike miki..."
Yarinyar ta fada cike da kulawa..Zaitun da ke kokarin shiga sai cewa tayi.
" a a bakomai nagode ."
Sai daga baya ma Zaitun ta fahimci ashe yarinyar itace matar gidan, yarinya da abu mai wahala ne in zata wuce sa'ar ta, da alamu ma amarya ce duba da ganin komai na gidan sabo ne..tunani take yi itama da zuwa wannan lokacin tana nata gidan a dakin mijin ta.
Alwala tayi ta fito tana shirin shimfida dan kwalin ta matar tace a a haba bari mana abaki abin sallah.
Godiya tayi wa matar bayan ta ansa abin sallar.
Addu'a tayi sosai takai kukan ta wajen Ubnagiji wanda har bata ankara tana yi da kwalla ba sai da taje shafa addu'ar kafin taji kwalla a idanun ta..bata tashi ba ko da ta sallame sallar la'asar din data tsaya mata tun dazun tana nan kan abin sallar ta tajiyo kiran maghrib bata yi kasa a gwiwa ba shima ta gabatar da shi, kuma duk tana yin komai ne da yarinyar ta daure dam abayan ta, dan akan yarinyar sam bata yadda da kowa.
Da yake Mufeen ta tashi already hakan yasa ta sauko da ita guntun abincin su data juyo shi ta bude suka ci ita da Mufee bayan ta yiwa matar gidan tayi duk da tasan ba ci zatayi ba amma hakkin ganin ido, a baki ta ringa bawa Mufeedan har suka kammala..ta bata ruwan da matar ta basu itama tasha sannan ta sake goye 'yar ta matar gidan na murmushi tace" 'yarinyar ki kyakykyawa..."
Itama Zaitun murmushi kawai tayi mata...tana ninke mata abin sallar ta bata gami da mika mata dodiyar ta, cikin ranta take ayyana kila da itama tasan labarin su da bazata karbe su har ta sakan mata fuska ba.
Tafiya ta cigaba da yi yayin da duhun dare ke 'kara shigowa...bata san ina take nufa ba har ta tsinci kanta cikin wata unguwa.
Yawaitar hasken kwan lantarki dake unguwar shi ya hana duhun daren tasirin bayyana kansa, Zaitun gani tayi unguwar sam bata yi kama da tasu da ta baro abaya ba.
Irin Pampo da masu hali ke sawa ta wajen gidajen su saboda bukatun jama'ah da shi Zaitun tayi amfani ta samu ta sallaci Isha'in ta gefen wani gida data ta samu da 'yar lungu kuma anan ta yanke shawaran yada zango kafin gobe ta cigaba da tafiya.
Tausayin kansu ya kamata musamman ma Mufeeda da take 'yar karama sai taji sharr hawaye na zuba mata na tausayin rayuwar data shigar dasu, sake rungume Mufee tayi dake lullu6e kirib cikin hijab din ta, jin yarinyar take daga jini har a zuciyar ta, yanda take kaffa kaffa da yarinyar kuwa abin har zai baka mamaki kamar zata maida ta cikin ta take jin ta...cikin zuciyar ta take fa'din" Kowa ma ya kini zan iya jurewa Mufee na, kowa ya guje ni bazan damu ba amma nayi alqawarin bazan ta6a rabuwa da ke ba har abada..Insha Allahu".
Da yake unguwar ba irin me yawan mutane din nan bace shiyasa babu wanda ya lura da wanzuwar ta a wurin har safiya, itama bata damu ba balle taji tsoro dan a ganin ta ai inda sabo yaci ace ta saba haka nan da kwanan titi.
Washe gari tun asubar fari tayi sallah bata huta ba ta cigaba da tafiyar ta har zuwa bakin titin da take iya hangowa.
Nan ta samu inda ake kunu da kosai ta siya musu suka karya ita da Mufee tafiya kadan tayi ta ganta bakin babban titi sai ta tsaya tsam tana nazartar wurin, gefe can ta hango musakai masu neman sadaka kawai sai ta nufi wajen su tamkar ana ingiza ta.
Kamar wasa sai ga Zaitun ta shiga sahun mabarata...sukan jeru ne kawai wasu na dan wa'ke irin na bara yayin da wasu ke fadin..." Allah ya baku mu samu."
Wasu kuwa shiru kawai suke su tsaya da kwanonin barar su a hannu.
Irin ta da bata san me zata ce ba kawai ta ajiye jakar kayan su ta zauna akai tana bin titi da motocin dake wucewa da kallo, ita kadai ta san me ke addabar zuciyar ta a lokacin, kokari take ta yaki zuciyar ta, so take ta kori dukkan kewa dake san taso mata.
_".....bama wannan ba, ta ya ma ke da shi din 'karamar kwakwalwar ku take muku tunanin ni Talatu zan amince 'da na, yaro irin Adam ya auri mace wulakantacciya irin ki?_ " .......'daya daga cikin maganganun Hajiya ya dawo mata.." Tabbas ni din wulakatacciya ce...amma ba irin wanda ke kike tunani ba Hajiya Talatu...Insha Allah kuma zan tabbatar miki da hakan.
Wannan maganar ne ya kara mata karsashi da kwarin gwiwan sakan jiki a bakin titin ta amsa suna mabaraciya.
*Salmerh😘*
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️ *...11*
'Bangaren Adam Shaheed kuwa sai da ya shafe kwanaki biyu ras idanun sa basu ga hasken rana ba, sai da abokin sa Hafeez ya azazzale shi da mita kafin ya shirya ya fito, sai dai kafin ya je wajen Hafeez 'din ya yanke shawarar fara zuwa wajen Zaitun bfore ya wuce wajen Hafeez 'din dan ba karamin kewar ta yayi ba, gashi ya hana ta fita ya hana ta zuwa aiki yace kar taje ko'ina, kuma yana da tabbacin matu'kar ya hana 'din toh Zaitun bazata je ko'ina din ba kamar yadda ya bukata...in haka ne kuwa yasan jin shiru daga gare shi bai kamata ba sam domin haka na iya haifar mata da wasiwasi akan sa.
Haka ya isa kofar gidan da niyyar 'kara mata 'kwarin gwiwa dan har yanzu bai cire rai da samun ta ba yana ji aransa da iznin Allah Zaitun tashi ce.
Ba yau yasan halin Hajiyar sa ba, lokaci guda take hawa tamkar kumfa in kuwa ta sauka shikenan komai yake wucewa a wurin ta...yana kyautata zaton nan da 'dan wani lokaci Hajiyar zata sauko daga dokin na'kin da ta hau za kuma ta amince da kudurin sa na auren Zaitun, tunda batun aure ne ya 'dauko ba sa6on Allah ba.