← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 218

Sashe 160

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bani da hujjar da zan rika dan kare kaina akan rike yarinyar nan da nayi amma can kasan zuciya ta nake jin ban aikata kuskure ba, ban sani ba ko 'kwarin gwiwar da nake ji daga wani 6angaren dai dai ne ko kuwa son zucia ta ne kawai ba.

Jijjiga kai nayi hawaye na gangaro min...da baya da baya na fara barin wurin wani tunani na 'darsuwa min cikin zuciya..ko ganin gabana da kyau bana yi saboda yadda hawayen ke min turereniya.
" Kowa yanzu da 6arauniyar yarinya zai ganni...zan kai musu ita su ha'da ta da dangin ta indai suna da damar hakan.....".
Tafiya nafara ina jin zuciya ta babu da'di, rabuwa da yarinyar idan na tuno shine ke tunkaro ni sai naji kwata- kwata bani da wani kuzari, kan gwiwoyi na na zube na ringa kuka ina sake rungume yarinyar"...kiyi ha'kuri Hajia wallahi bazan iya ri'ke yarinyar nan ba, bazan iya rike mk wannan amanar mai gagarumin girma ba, sam bazan iya ba, tafi 'karfi na, Iyami, Abban mu, Hamma na, mahaifiya ta da 'yan uwa na duk babu wanda zai goyi bayana.

Kuka nake sosai wanda ya 'dauke ni tswon lokacin da ni kaina ban sani ba...kuma wai duk kukan zan rabu da yarinyar ne.

'Karfin hali nayi na mi'ke na sake bin hanya har na fito bakin titin da niyyan kaiwa jami'an tsaron yarinyar su tafi da ita sai dai kan titi shau na ganshi tamkar an yi ruwa an 'dauke, babu kowa, babu jami'ai babu motocin su, dagaske bangan su ba babu su babu alamar su.
" Innalillahi".
Na furta cike da ka'duwa.

Waige- waige na fara sai ma naga babu kowa ba jami'an tsaro kadai ba hatta wa'danda suka tsaya kallon ma babu su.

Tsakiyan titin na sake hawowa wai na gani da kyau amma abu 'daya idanu na ke gani babu kowa.

Wannan karan ma kan kwaltar na zube na saki wani kukan da tasomin tun daga can kasan zuciya ta yake fita...a fili nake fadin" dan Allah ku dawo, ku dawo zan baku ita wallahi ku tafi da ita...ko bama tare zan yi mata addu'a, zan yi mata fatan alkhairi muddin raina.

Babu wanda ya bi ta kaina balle asan manufata, babu wanda yasan halin da nake ciki balle asan matsala ta ko damuwa ta, babu kowa...hatta cikin garin ma ba mutane ne sosai ba sakamakon rashin natsuwa da aka wayi garin dashi.

Da 'kyar na samu na lalla6a na koma gefen titi na sha kukana son raina kafin na tashi na kama hanyar gidan Inna ta.

Kamar daga sama naji wata murya daga gefe na ta can nesa ka'dan da ni an 'kira suna na.

waigawa nayi na kallo wurin da jajayen idanu na.

Salele ne mai chemist.." Bai da'de ba Bukar ya bar nan duk hankalin sa tashe yake yana neman ki ashe kina nan?".
Yayi maganar yana nufowa inda nake.

Turus yayi kuma yana bi na da kallo sama da 'kasa yace" me ya same ki kuma kike kuka haka Zaituna .?"

Kai nayi saurin kawarwa gefe sannan nace babu komai, kaina kawai ke min ciwo".

Ina shirin yin gaba sai yayi saurin dakatar da ni ta hanyar shan gaba na yace" Haba Zaituna da gani wani abu na damun ki, dan Allah ki sanar dani, ai ni kamar yayan ki ne"

Kuka na rushe masa da shi nayi 'kasa da kaina...yanda nake kukan har yasa babyn dake hannu na motsawa gami da yin mi'ka irin tasu ta yara.

Salele cike da mamaki yake bi na da kallo, idanun sa duk waje yace" Wai me nake gani ne haka kamar mutum a hannun ki Zaitoon?"
Wannan karan da yaren kanuri yayi min wanna tambayar inda ya 'karashe yana mai 'daga hibajin jiki na.

Baya ka'dan yaja da ganin yana kare min kallo sama zuwa 'kasa.

" Subhanallah" yace cike da firgici.
" Zaituna na waye a ina kk samo kuma?"

Cikin kuka nayi masa bayanin komai har niyya ta na basu yarinyar amma na tarar sun tafi.
Kai ya girgiza yace" ikon Allah baya karewa, yanzu ina zaki?"
" Gidan Inna ta".
" To kije insha Allahu anjima zanzo 'kila ma Muzo da Habu yanzu kinga lokacin sallah yayi idan mun fito daga masallaci zaki ganmu, ki kwantar da hankalin ki kinji?"
Kai na na 'daga masa sannan nayi gaba.

Inna ta kam bata ce da ni 'kala ba har na 'karashi kuka na nayi bacci.

Tashin hankalin ta 'daya ne kawai yadda za'ayi da yarinyar na dan tasan halin tsohon mijin ta kamar yadda tasan halin mijin ta na yanzu.

Ita bata san gangancin da ya hana ni 'kin bada yarinyar ba.

Su Hamma na sai la'asar suka shigo shi da Saleh, duk hankalin sa a tashe dan yau yinin nemana yayi amma bai same ni ba...banda wani tashin hankalin da ya same shi ganin idon sa.

Ko da ya ganni ma tsayawa kawai yayi yana kallo na dan duk Salele ya gama sanar da shi komai.

Bai kula ni ba sai ya tafi ga Innata suka gaishe ta sannan cikin kalami na fahimta yace" Inna naji duk abinda ya faru, kuma naga kuskuren Zaituna sannan sam sam bazan iya barin ta zama tare da yarinyar nan ba mayar da ita za'ayi?"

Salmerh ce😘
[4/1/2023, 12:03 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...90*

......Kuka sosai na sanya daga cikin 'dakin Inna ta..harga Allah ni banaso kowa ya rabani da ita, yini 'daya tak da nayi da yarinyar sai naji ta 'kara shiga raina sosai.

Bansan ya 'karshen tattaunawar tasu ta 'kare ba saboda kukan da nake yi.
Hamma na nagani tsaye daga bakin 'kofa yana fa'din" Tashi mu wuce gida kafin gobe a maida ta inda yafi dacewa da ita".

Simi- simi na tashi na nufo 'kofar batare da na 'dauki yarinyar ba, sai yace" 'dauko ta mana..ai bazaki barwa Inna wahalar ta ba tunda ke ce kika jaji6o ta".

Ni dama hakan yafi min har a zucia ta, nafi so in tafi da itan..hakan yasa naji dadin kalamin sa wani sanyi ya ratsa zucia ta.

'Dauko ta nayi na rungume ta cikin hijabi na kamar 'dazun na bishi abaya har muka je gida.

Yau kam kowa na gida Baffah ma tuni ya dawo saboda tashin hankalin da ake ciki..ga Goni ma da ya auna sa'a duk bani da labari sai yanzu da na dawo gidan.

Garin nemana da kadan ya rage a harbe sa badan suna tare da Yah Bukar da yy saurin ankarar da shi suka zube 'kasa hakan yasa harbin yabi iska ya wuce, basu mike ba kuwa har sai da 'yan ta'addan suka karasa wucewa.

Kaina 'akasa dama na shiga gidan a bayan Hamma Bukar shi da Salele...a hanya naji suke tattauna batun su biyu.

Tsoro ya sake kamani, sbd jin auna sa'ar da 'yan uwana suka suka yi..yau da ace an harbi dayan su ta dalili na da bansan inda zan tsoma rayuwa ta, banda ma Iyami da sai ta kusan yin dambu da namana.

Gefen tabarmar Abban mu suka zauna inda ya tashi daga kihsingidan da yayi yace" Aww Bukar ka samo ta ne?"

Sam banyi mamaki ba, dan na jima da fahimtar irin mahaifin da Allah ya bani, yafa san bana gidan tun safe amma amadadin a fita da shi a duba ni sai ma zama da yyi a gida ya mi'ke 'kafafu ko alamr damuwa babu tattare da shi, na dawo ko kar na dawo ruwa na, in mutu ko in dawo a raye duk ba damuwar sa bace.

Hamma Bukar ka'dai ya damu dani a gidan na kuma shika'dai ne ya damu da rashin ganin nawa sai Goni da shima isowar sa kenan da safiyar ranar.

Shima din na tabbata da bai dade da dawowa bane da ko kallo ban ishe shi ba, shi dama haka yake, babu ruwan sa da duk wata sabgar da ya san bazata kare shi ba, baya shiga sabgar kowa balle kace ga abinda yayi maka na 6acin rai..'kyaliya ce da shi na masifa.

Ban yi mamakin jin furucin mahaifi na ba sai lokacin da Iyami ta fito daga 'dakin ta tana 'ko'karin 'daura zani naga ta bini da wani mugun kallo..." Ashe zaki dawo na 'dauka ai gawar ki za'a kawo min tunda ke hankali bai gama isan ki ba har yanzun, kina ji gari bb lafiya amma dan iya shege bazaki dawo gida ba sai kin bawa mutane wahala...?"
Ta 'karashe da yanayi na tambaya.
" Wato gawa ta?..to gani ai na dawo da 'kafafu na".
Abinda na fa'di cikin zuciya ta kenan..a zahiri kuma gyara ri'kon yarinyar hannu na kawai nayi.
" Wlh da kin kuskura sanadin ki lafiyar 'ya'ya na ya samu gi6i da sai kin sha mamakin abinda zan aikata agare ki...a ina kk tsaya tun safiyar da baki dawo gida ba....?"
Shiru nayi na ma rasa amsar bata...
" Da kika yi shiru kina jin mutane 'din kuma fa, ba dake ake magana ba ne...banza munafu....".
Maganar Iyami tsayawa daidai yy lokacin da taga na gyara ri'kon yarinyar hannu na akaro na biyu.

Baki ta bu'de tana bina da kallo sai a sannan ta lura da yanayi na, a hankali cike da mamaki tace" Zaituna"!.

" Na'am Iyami..."
Na amsa ta cikin sanyi nima batare da na dubi fuskar ta ba.

" Me nake gani haka wai?..menene a hannun ki...?"

Kafin nayi magana..Hamma Bukar ya riga ni da fa'din" Ki 'karaso ki zauna mana Iyami dama maganar da zamuyi kenan..."

Ai kam kujera tayi saurin 'dakkowa ta zauna tana sake bina da kallo me cike da tambayoyi da ma'anonin da ni kaina bansan iyakar su ba.

Gyaran murya Hammah yayi sannan ya kora musu bayanin duk abinda Salele ya sanar masa yana yi yana kallo na, ni kam 'kasa nayi da kaina dan ko ka'dan babu 'karya a cikin maganar salale bai canza komai cikin duk abinda na sanar da shi ba.
Chapter 160 · 0% Book details