← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 218

Sashe 166

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kewa guda ta ke damuna a hlin yanzu shine kewar gidan mahaifi na, su 'din dole na ne, bani da tamkar su, ko da su basu nemi inda nk ba tunda ni ina nan da lafia ta dole zan neme su.

Hakan yasa na yanke shawarar ziyartar gidan mahaifi na da wata safia sbd kawai in hadu da Abbahn mu yasa na fita da sassafe.

Da sallama ta na shiga..Iyami ce 'tsakar gidan " Wa alaik..."
Sai kuma tayi shiru ta ha'de rai ba'ki'kirin tana bina da wani mugun kallo.

" Lafia ..?"
Ta jefa min tambaya.
" Nazo gaishe ku ne Iyami"
Na bata amsa ina 'daga 'kafata zuwa ciki.
" Wa yace miki yana bukatan gaisuwar ki anan gidan...? Gayyar 'kasantar..gantalallu mabiya lunguna...?"

Sam zagin Iyami na yau 'din bai shiga zucia ta balle ya dame ni, burina kawai in ida nufi na inyi gaba.

Kujera da na gani gefe nayi 'kokarin zaunawa ina mai bin cikin gidan namu da kallo yadda duk 'kazance...ko irin gyaran shirye- shiryen sallah da ake yi din nan banga alamun ana da niyyar yi cikin gidan ba.

" Iyami Abban mu na nan kuwa..?"
" Kin bada ajiyar sa ne..ko kuwa dan kin tmraina ni kk tambaya ta shi, ai naga alamun yanzu raini ke 'dawainiya dake tunda kin riga kinsan waye 'da namiji ba dole ki fitsare idanun ki ba..."

Ban bi ta kan maganar tata ba kawai na mike na nfi inda tsintsiya yake na 'dauko domin tsaftace gidan kamar yadda na saba kafin barina gidan.

Da sauri Iyani ta hayyako min tana masifa ta kwace tsintsiyar ta.." ai da in bari ki share min ki zazzaga min burbudin karuwanci na kwammaci datti ya hadiye mu ni da yara na, maza kama hanya ki bar gidan nan, bukatar ganin ki ma babu mai yi balle marmarin aikin ki..."

Wannan hayagaga ta Iyami ita ta fito da Khausar da ke 'daki ita da Ummaru hk ma Abban mu.
A hnkli nace
" Haba Iyami...wai dan Allah mance matsayi na cikin gidan kk yi ne...ni 'din fa 'diyar ku ce kuma a tunani na ba'a ta6a canzawa tuwo suna..."
Da gudu naji an rungume min 'kafafu..ko da na kalla sai naga Ummaru ne..." Yaa Zaituna..."
Ya furta cike da farin cikin sa.
Ina kakalo murmushi na dube shi.
" Yah Zaituna Iyami tace wai bazaki sake dawowa ba sbd kin zama karuwa nayi ta neman ki banganki ba...ashe zaki dawo, Yah Zaituna kar ki koma kinji...?"
Kai na 'daga masa ina mai shafa kansa daidai lkcn da wani zazzafan hawaye ya sakko min.

Sam ba aimin adalci ba, kokadan ba'a kyauta min ba a gidan nan..indai har za'a zauna a tsarawa yaro 'karami irin Umar wannan maganar toh me ne kuma za'a aikata da zan bani mmk.

Iyami na kalla sai ta kya6e baki ta kawar da kanta...bani da wata kalma da zan fadiwa Ummaru domin wanke kaina amma nasan watan wataran zai fahimta.

Khausar na duba ta banko min wata uwar harara dai dai lkcn da sautin muryar Abban mu ta doki kunnuwa na.
" Sakar min yaro da Allah...me ma ya kawo gidan nan...?"
" Abbah"
Na furta ina zubewa bisa gwiwoyina na rushe da kuka.
" Abban mu nice fa Zaituna...!"
" Sai akayi yaya...bani da wata ala'ka da mutun irin ki balle mai irin sunan ki, na riga na cire ki cikin yaran gidan nan tun daga ranar da kk kwasowa kanki abin kunya, kuma daga yau 'din nan ko a hanya kk ha'du da jinina kk yadda magana ta hada ku wlh ban yafe mk ba, kije can da 'diyar ki..kije ta zame mk dangi amma ba ahali na ba...kin zame mana abin kyamata domin haihuwar irin ku bata da wani riba..."
" _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...haba Abbah! Dan Allah ka sassauta min Abban mu, wlh bani da alaka da yarinyar nan indai kuma akan ta ne kk kokarin cire ni daga cikin yaranka Abbah na hakura da yarinyar a mayar da ita gidan marayun na amince amma Abbah kar kai min mugun baki akanta, wlh bani ce na haife ta ba kaddara ce kawai ta hada mu..Abba tausayin ta nk ji sosai agabana aka harbi mahaifiyar ta..._!..

Dakatar da ni yayi da hannun sa.
" Wannan duk damuwar ki ce Zaituna...kin haifa baki haifa ba sam bai dame ni ba, amma kasantuwar kin hada jiki da yarinyar kin kuma 'kaunace ta aranki hakn kadai bazai sa in barki cikin zuri'a ta ba...mun riga mun haramta gareki, kije ki rayu da 'diyar ki..inkin ga dama ji zama uwar karuwan duk dunia ma bai dame ni ba Zaituna...tashi ki bar min gida na, kuma daga yau ban yafe ba idan kk sake ko kallon 'kofar gidan nan...".

Daga hk ya sa kai yy waje abin sa hnkl kwance.
Anya wannan Abban mu ne kuwa, anya shi ya haife ni?
Babu abinda nk sai salati fili da zucia ta, yau shine rana na farko da nayi dana sanin duk rayuwa ta, nayi danasanin duk wani taimako da na aikata, ji nayi duniyar tai min zafi gaba 'daya, da wanne zanji, kalaman Abba na sun matu'kar yi min nauyi a zucia ta, meyasa zai ce ko da na batare da yarinyar bazai barni da matsayi na na 'diyar shi ba, dama jiran faruwar lamarin ake ko me? meyasa zai yi saurin yanke hukunci?

Riba guda na samu cikin maganganun sa..domin cikin maganar sa na fahimci yaddar da yai min...juya masa kwakwalwa akwai akayi amma da kansa yasan ni ba mazinaci ya bace, sarai yasan ba ni na haifi yarinyar ba amma sbd ya yiwa matar sa biyayya ya sa shi kawar da kai ga hakan.

" Ki tashi ki bar mana gida ko 'kira matasa su fitar min dake da duka....".

Na tsnkayi muryar Iyami ta fadi hakan.

Kai na 'daga na ganta tsaye akaina fuskar ta tamkar ba'kin hadari.

Tsab nasan zata iya amma duk da hakan ban yi yun'kurin mi'kewa ba.

'Kasa nayi da kaina ina jin wata 'kwarin gwiwa cak kuka na ya tsaya.
Tsaye na mi'ke ina goge fuska ta idanu na a cikin nata nace..." Iyami kiji tsoron Allah, ki sani cewa kowa zai mutu..sannan kafin mutuwar akwai jerin kaddarorin da bau wanda ya san iyakar su balle asan 'karshen su..."
" Dan ubanki bazan ji tsoron Allahn ba, idan kinji zafi ki sa Allahn ya 'mayar da abin kaina in kin isa..."
Kai na juya gefe da gefe.
" Bani da damar sawa ki haifi 'dan da za'a muzanta ki sbd shi kamar yadda bani da damar canza 'kaddarar ki..amma kuma ban isa nace bazaki iya cin karo da 'kaddarar da zata iya sha mk kai ki kasa samun mafita ba koda ace baki da ala'ka da abun..misali kamar dai ni...abu guda da bazan iya gajiya da furtawa agare ki ba shine...kiji tsoron Allah Iyami ki guji hakkin 'dan Adam..."

Daga haka na juya na fita na bar Iyami na ta sababi.
Ni kaina naga 'ko'kari na, domin ban ta6a tsayawa na mayrawa Iyami magana irin ta yau 'din ba tun tasowa ta.

Ko ma'kwabta dake bina da kallon mamaki, tuhuma, zargi, da sauran su duk ban nuna alamun na san suna yi ba kawai na wuce gidan Innata.

Tun daga ranar ban sake tako ko hanyar gidan mu ba, na basu lkc nasan da iznin Allah wataran zasu fahimci gaskia.

Har akayi sallah 'karama aka yi bikin Sallah aka gama cikin farin ciki illa ni da har a lkcn ban san inda nawa farin cikin ya shige ba.

Bayan Sallah da sati Yayana ya koma harkar kasuwancin sa gadan- gadan..kafin hakan kuwa kullum yakan bani baki akan inyi hakuri.

Dama ban 6oye masa komai ba, duk na fa'da masa kalaman Abban namu domin sune suka fi yimin zafi, na ce da Hamma Bukar na hakura a mayar da yarinyar tunda Abba ya kasa fahimta ta yace sam baza'a yi haka ba, ai kalaman sa masu reshe ne, nufin da yarinyar ko ba yarinyar basu sake bukatar ki tunda kin riga kin shafe ta, abari kawai ana addua a hankl wataran Abban zai sakko.
Yace kuma mayar da yarinyar a halin yanzu zai iya zame mana matsala dukkan mu, musamman idan aka tsaurara bincike za'a iya kama mu da laifin rashin bayyana ta tun a farkon fari...shi yana tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo tunda mu ba ishashen ilimi ba, ba dukia ba ba karfin mulki gare mu ba..yace abinda ya guda tun farko kenan amma nakiya, amma bakonai ita kaddara dama rubutacciya ce, Allah ya riga ya tsara hakan inyi hakuri mu cigaba da zama da ita shi ya san yadda zai 6ullowa lamarin, amma a halin yanzu abar Abban ya huce tukunna..."

Sosai na gamsu da bayanan sa, na kuma fahimci kuskuren da nayi tun farko da ban san zai iya faruwa ba, tun da gashi komai na neman kwance min, mahaifi na na neman guje min sbd wannan dalilin.

Duk wannan maganar mun yi ta ranar da yazo yi mana sallama zai tafi kudu harkar kasuwanci.

Ranar ma nasha kuka, kawai nake jin tamkar zan yi kewa idan ya tafi.
Duk wannan abinda ke faruwa kuwa daidai ko 'kwayar zarra ban ji yaragu daga cikin 'kaunar da nakewa Aishatu ba sai ma 'karuwa.

Ko cewa da nayi a mayar da ita na fa'da ne kawai dan samun sulhu tsakanin ni da mahaifana ba wai dan na gaji da ita ko na daina 'kaunar ta ba.

Ko da an mayar da itan da kaina nasan sai nayi kuka da rashin ta, zan kuma yi kewar ta sosai...idan na tuna hakan sai in jinjinawa kaina kawai domin nasan Allah ne ya tsara mana komai, ya kuma sanya min 'kaunar ta mai tsanani a zucia ta.. na gama yadda yanzu 'kauna ta da Aishatu daga Allah ne...!

Duk da yadda mutane ke tururuwar zuwa gaida mu a gidan Innani abin bai ta6a damu na ba domin nasan yadda su suka 'daukan ba hakan yake ba kuma ni bani da ikon canza musu tunani akaina.
Chapter 166 · 0% Book details