Sashe 90
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dawowar Rayyan da kusan watanni biyar aka wayi gari Nadia na da juna.
Misalta muku irin farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu ciki musamman ma Rayyan 6ata lokaci ne.
Rayyan ji yake tamkar ya goya ta saboda da'di, ji yayi kamar babu wani sauran bakin ciki da ya rage masa...tunani yake ashe shima yana da rabon ganin 'kwansa a duniya...duk da yake dama ba wai ya cire rai da samu bane a kullum yana kyautatawa Allah zato saboda yasan shi ke badawa ga duk wanda yaso, amma atimes idan ya tuna Anty Madeena da har yau Allah bai nufe ta da haihuwan ba ga Kawu Sufyan har ya bar dunia bashi da magaji sai jikin sa yayi sanyi.
Amma tuna cewa Raihana ma ta haihu hakan yakan yakan bashi 'kwarin gwiwa da tunanin shima zai haihu da iznin Ubangiji sai gashi Allah ya cika masa burin sa.
Yayin da 6angaren Sultan sam abin ba haka yake ba, kwata-kwata bai tsara hakan cikin jadawalin sa ba, haihuwa daga Rayyan babban nakasu zai kawo ga cikar burin sa, ya jima da 'daukan mataki daga 6angaren Amrah domin da kansa yake 'dirka mata magungunan hana 'daukan ciki har ma ba bisa ka'ida ba.
Amrah bata ta6a taka masa birki ba dan sosai kaoaman sa suka yi tasiri cikin zuciyar ta, acewar sa na hana 'daukan cikin sa kawai yake mata a wautar ta kuma sai ta amince da batun sa bata ta6a musun sha ba kamar yadda bata ta6a nuna damuwa ga rashin haihuwar ta ba.
Sultan ya jima yana kitsa mata illolin haihuwa agareta, zakayi mamaki idan kaji irin kalaman da Sultan ke sanar da ita tamkar shi har itan ba haifan su aka yi ba, inda ya tabbatar mata da cewar haihuwa jirkita mata halitta zai yi kawai kuma ahakan ta tafi kowacce mace a duniya kyau da tsari, kar ta yadda ta haihu tun yanzu batare da ta mori 'kuruciyar ta ba.
*****
Akwana a tashi babu wuya a wajen Allah, sai gashi cikin Nadia nada watanni takwas cif sosai ya gama fitowa, da yake itama ma'akaciyar lafia ce tuni tayi scanning kusan sau uku ana tabbatar mata da cewa cikin 'yan biyu take 'dauke da shi.
Ranar da aka 'kara tabbatar mata da hakan kusan kwana tayi tana yiwa Allah godia duk da nawin da cikin ke da shi amma hakan bai sa tayi kasalar yin nafililin nuna godiyar ta ga ubangiji ba.
Kuma bata labarta wa Rayyan ba dan tafi so wannan ya kasance suprise mafi soyuwa cikin zuciyar sa da za'ai masa a rayuwar sa.
Tafi kowa sanin halin sa da irin tsananin farin cikin da zai shiga idan yaji labarin amma tafi so ya gani kawai da idanun sa ba wai jin labari kawai da kunnuwan sa ba.
Da ace Rayyan ma'abocin tambaya ne da sai ya tuhume ta akan kwana sallar da tayi amma da yake shi ba gwani bane wayen shiga rayuwar mutum ya sanya tunda ya lura ta tashin nata shima kawai ya tashi ya jonata, haka ya ringa tayata raya daren dan yasan dama ita ma'abociyar tsayuwar dare ne...sai dai ga mamakin sa har ya kammala yayi addu'o'in sa ya kwanta Nadia bata kammala nata ba, sam sai bacci ya kasa 'daukan sa ma, haka ya ringa juye- juye yana lura da ita har kusan sallar asubah, nan ma bata yi bacci ba har sai da ta dangana da sallar asubah kafin ta koma ta kwanta.
Bai yadda tayi bacci ba sai da ya tabbatar ya ha'da mata tea mai zafi tasha kafin a hankali ya ringa matsa mata 'kafar ta yana tsokanar ta.
Inda yace " Allah yasa dai nima an nema min gafara da albarkar dan nasan duk wannan dogon daren saboda abin cikin ki ne ka'dai ba ni ba..."
Murmushi tayi tana gyara kwanciya tace" Wa yace maka idan ana sallah ana mancewa da alwala...?".
" Babu wanda yace...wama ya isa..."
Ya bata amsa cike da 'kauna.
" Toh kaga, dole shine tushen ibada, taya za'a yi a manta da shi...".
Ta 'karashe maganar da hasaso irin farin cikin da zai shiga duk ranar da Allah ya bata ikon sau'ke masa 'ya'yan sa har guda biyu da bai san da zaman cewa su biyu bane acikin ta.....
" Ke de fadi gaskia nasan siyasa za'ai min kawai anan...".
" Haba yalla6ai...wace ni da yi maka siyasa sai dai in ta maka biyayya har 'karshen rayuwa ta...yauwa ma dan Allah inje Maiduguri mana in duba Umma ta, ni ko kwana 'daya ne ma idan ka amince bazan 'kara ba dan Allah...."
Ta fa'di maganar tana mai 'ko'karin sake mi'kewa zaune domin fuskantar sa.
" Ai ma bazan amince 'din ba madam balle har ki samu damar 'karawa...".
" Haba yalla6ai...dan Allah fa, ni haka kawai kwanan nan nake so in ganta tana yawan zuwa mafarki na...".
" Ki bari sai kin haihu..."
Ido ta zaro sosai tace
" Haihuwa kuma...wannan dogon zangon ai na me nisan kwana ne dan Allah fa kayi ha'kuri..."
" Sleep my dear ba wani tafiya da zakiyi ina.tabbatar miki...."
Dole tayi shiru amma ba wai dan ta ha'kura ba, ta 'dauki a'kalla tsawon kwanaki uku tana lalla6a shi kafin ta samu ya amince bayan ankai ruwa rana...ya kuma ce ma bisa shara'di ne kwana biyu rak ya bata ta dawo...kuma dole tafiyar jirgi zata yi tace ta amince.
Tunda Sultan ya samu labarin wannan tafia ta Amrah ya fara Jin da'di da tunanin babbar dama ta sake zuwa masa bayan tsawon lokacin da ya 'dauka Yana dakon zuwan irin ranan nan.
Duk da 'karancin shekarun Sultan amma yawan sharrukan da ke cikin zuciyar sa sun zarta yawan kwanakin sa a dunia.
Sultan bashi da burin da ya wuce ace yau shi ne shi ka'dai ke da mallakin INFINITY GLOBAL COMPANY Kano da kuma ( IGC Ikeja.) da wannan burin ya girma aran sa tun Alhaji Sa'ad na raye kuma har yau wannan burin ke sake ginuwa bai ta6a rushewa aransa ba.
Burin Sultan ace duk wasu ba'ki ko masu san ha'din gwiwa da companyn Infinity ace da shi suke zama ba da Rayyan ba, babban dalilin da ya sanya ba ya iya zama a Kano sosai ya 'kwammaci yayi ta tafiye- tafiyen izuea 'kasashen 'ketare kenan ko kuma idan ana bu'katar kaya ya tafi shi ya jagoranci tafiyar acewar sa hakan yafi masa da ya zauna yana ganin kayan takaici, kuma ma ai hakan duk 'karuwan sa ne domin zai 'kara samun experience ne sosai kan harkar kasuwancin 'kasashe har lokacin da komai ya dawo hannun sa bashi da fargaba.
Saboda Companyn Infinity ya 'kwammaci ya karanci computer engineering badan komai ba sai dan son cika kwantattun burikan da suke ransa.
Sultan yakan yi duk shirin sa cike tsari da iyawa, zai yi wahala tashin farko a zarge shi, ko Kabeer ma ya fara zargin Sultan ne sbd zurfafa bincike da yayi, sai dai bai kai ga tabbatar da zargin sa ba Sultan yayi sanadin mutuwar sa.
Ko cikin mafarki, ko kusa ko alama Sultan baya 'kaunar yaga ahalin Alhaji Sa'ad na kara hayayyafa a duniya balle har suyi yawan da zasu fi 'karfin shirin sa, domin ba burin sa yayi ta rayuwa 'kar'kashin su ba, burin sa ya kafa kansa ne shima ta yadda dunia zata san da zaman sa, dunia ta dama da shi...duk damuwa da suke da rashin haihuwar su Sultan kawai taya su yake abaki bawai dan yana jimantawa ko 'kaunar haihuwar ta su da gaske bane, musamman Rayyan ya tsani yaji Rayyan ya haihu.
Samun cikin Nadia kowa yayi farin ciki da shi illah Sultan da cikin ya kusan zame masa babbar barazana ga shirin sa da 'kyar ya saita kanshi, abu guda daya 'kara masa 'kwarin gwiwa shine tabbatarwa kansa da yayi ko ta halin 'ka'ka ne, ko bayan an haife cikin sai ya halaka abinda aka haifa ya kuma tabbatar wa ransa hakan shiyasa ya watsar da batun kawai ya cigaba da rayuwar sa kamar kowa.
Ba dan komai Sultan ya nuna 'kauna ga Marwa har ya aure ta ba sai dan kawai ya ga ya haihu da ita ta yadda kota halin 'ka'ka ne shima ya kasance yana da share acikin Infinity Company.
Infinity Global Service babban company ne da ake sarrafa 'karafuna, kuma suke sau'ke motoci manya da 'kanana..kuma Alhamdulillah ya samu kar6uwa, gefe guda kuma ana kasuwancin any kind of computer, typewriting machine, photocopier, scanner, wayoyi da sauran su, duk dai nau'i kan elctronics da ake amfani dashi a 'kasar nan sukan sau'ke shi babban waje ne sosai, kuma Alhamdulillah ba 'karamin samun 'karuwa da Ma'aikatar suke ba kuma.
Sannan sukan sau'ke Spare parts na motoci a Infinity dake Lagos dama motocin kansu, Rayyan sun zauna da Ammi akan irin ribar da companyn ke kawowa kwanaki abin har na basu tsoro amma a sirrince suka yi shawarar suka.kuma yanke shawarar bayan zakka da suke cirewa zasu ringa tura wasu ku'da'den cikin asusun kungiyar tallafi ta su Ammi batare da ansan su ke aikawa da ku'din ba, kamar yadda suka saba saka kudi cikin asusun Gidan Marayu batare da ansan su ke turawa ba.
Sai dai Rayyan ya ro'ki Ammi akan ta bar aikin ta wakilta wasu Ammi tace sam zata yi abinta da kanta...dole Rayyan ya ha'kura ya 'kyale ta sai dai har gobe baya 'kaunar tafiyen tafiyen Ammi kawai babu yadda ya iya da ita ne ya sashi ha'kuri.
Shirye- shiryen tafia Nadia ta fara kamar wacce zata je Saudia, abin har sai ma ya fara bawa Rayyan haushi, ita ma Marwa shige da ficen Nadian sai ya fara 'kona ranta amma bata tanka ba.
Rayyan kasa ha'kuri yayi yana tsaye kanta tana zuge zip 'din akwati ya wani 'daure hannayen sa duk biyu a 'kirji yana duban ta har ta kammala sannan yace" Wai duk wannan na menene haka...?"
'Yar daria tayi tana matsar da akwatin tace" tafiya mana..."