← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 218

Sashe 181

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana gab da shigewa batare da ya dakata da tafiyar ba yace ki ha'da mata tea 'din ta sha.
Ko 'kala bata ce masa ba sai 'dan 'karamin tsaki da taja ta 'karashe da hararar ledan da ya ijiye can nesa da ita.

Cikin ranta ta ayyana ashe ma ya san me yarinyar ke so shine dan mugunta zai wani kulle mu yy tafiyar sa.
Wannan wani irin zalunci ne.

Sai da ta tabbatar ya wuce ciki kafin tabi bayan sa da harara tana mai gyara zaman Mufee a jikin ta hadda yin 'kwafa tamkar wata 'ka'k'karfa.
Ji take ayau da ace ita wata aba ce ko kuma sama take da shi da bb abinda zai hana ta zane shi tass da tsumagiya.
A zuciye ta tashi ta nufi hanyar fita sai dai ga mamakin 'ta still kofan a rufe take zaton ta ya bu'de ne.

Yadda ta zauna cike da jin haushi bayan barowar ta wajen 'kofan har sai da tasa Mufee motsawa, tana motsawa kuwa ta bude idanu ta 'dora akan rigimar da take kafin tayicbaccin.

Dole badan taso ba ta tashi ta shiga kitchen ta 'dauko cup da spoon ta je wajen ledar da ya kawo 'din ta fiffito da shi.

Sosai kayan cikin ledan suka bata mamaki suka kuma 'dauki hankalin ta, domin duk kayan cima ce ta yara, sai manyan kayan tea zuma da sauran su.
Baki ta kya6e irin basu wani birge ta din nan ba amma har cikin ranta taji da'di bayan fahimtar duk sbd Mufeeda ya kawo.

Tea 'din kawai ta ha'da mata sai ta ciro mata wani crackers da ita kanta sai da ya shiga ranta.
Amma ta basar kawai ta sanya Mufeeda a gaba tana bata a baki.
Da shigan sa bai da'de ba yaji wayar Ammin sa, ko da ya 'dauka tambayar sa tayi akan su Zaitoon dan taji shiru kuma Raihana ta sanar da ita akan cewa yayi cikiyar ta 'dazu kuma yana tare da Mufeeda..toh in ba fita suka yi ba ya turo mata su.

" Ammi munje can gidan ne amma anjima ka'dan zamu dawo..."
Ya bata amsa yana mai sakala wayar tsakanin kafa'dar sa da kunnen sa yana kuma kokarin cire safar 'kafar sa a lkc guda.

" Can gidan kamar ya kenan? Su me zasu yi mk mk acan gidan Rayyan?"
Ammi ta tambaya cikin rashin jin dadi.
" Bakomai Ammi"
Ya bata amsa a takaice yana lumshe idanu.
Yanayin Ammi sake zafafa yayi.

" Hk ake yi fisabilillahi...without informing me or ur sisters kawai sai ka 'dauke min yara zuwa can wani wuri daban...".
Da sauri kuma da mmk yace " Haba Ammi!..nine fa!
Kuma gida na nace ba wani waje ba daban ba...."
" Bana so toh...ka dawo min da su right now".
Daga hk ta kashe wayar tana sakin 'karamin tsaki.

Shi kansa mamakin Ammin sai ya kama shi.
Ca yake wa'dannan bayin Allahn dai a halin yanzu bb wanda ya isa ya kaisa iko da su kuma yana da daman fita da su zuwa duk inda yaso batare da an tuhume shi dalili ko ba'asi ba.

Wayar ya ciro ya bita da idanu tamkar zai ga Ammin a ciki.
Nan take Anty Madeena ta fa'do ransa bai bata lkc ba kuwa ya danna 'kiran ta.

Ko gaisawa basuyi ba ya fara isar da abinda yasa yy kiran ransa a'dan 6ace.
" Anty wai me ke damun Ammi ne ?"
" Kamar Yaya meke damun ta, me kuwa zai dame ta banda damuwar halin da gidan ta ke ciki..ko wani abin ya faru ne?"
" Kusan haka Anty.. shikenan ni ta ko ina ban isa nayi iko da 'diya ta ko matata ba sai an nuna min ni ba komai bane akan su...?Ita kanta yarinyar nan ta gama raina ni Anty kuma duk Ammi ce ke goye mata baya..."
" Wace matar kk nufi ne na kasa ganewa..ca nake Amra dai na gidan su, me ze ha'da Ammin ka da lamarin ta a halin yanzu...?
A kufule yace
" Anty yarinyar nan fa...!..wai..wai..."
sai kuma ya rasa me ze fa'di..." ni dai Anty dan Allah ki sa baki Ammi ta barni in sha iska, yadda take nuna musu shiyasa yarinyar nan duk tabi ta raina ni.."
" Har yanzu bangane wace yarinyar kk magana ba malam..."
" Wancan yarinyar...Mamin Mufeeda..."!
" Toh dan me zata raina ka?..hala dai wani abin kayi mata".

Shiru kawai yy yama rasa meze ce da Antyn.
Shi dai yasan bb abinda yai mata ya kuma kasa gane manufar Ammi, dan tun ba yau ba ya fahimcicta bata so taga ta da'de inda yake.

'Kin fitowa yayi yama yi kwanciyar sa dan a har yanzun hutu bai ishe sa ba ga 'karin takaicin da ya kwasa daga dukkan 6angarorin uku.

Marwa kuwa da 'kyar ta lallashi zuciyar ta tayi shiru amma ta kasa ji aranta cewa Sultan mai laifi ne dagaske kamar yadda ake fa'da.

Sosai kuma ta ke so ta ganshi, tana matu'kar bu'katan ha'duwa da shi kuma aranta take ji dole sai tayi hakan kafin zata samu natsuwa.. 'karshe 'dakin ta ta koma ta kwanta tana tunanin abubuwa da dama da suka shu'de.
Can 'kasan zuciyar ta take mamakin ina Zaitoon ta shige, dan tunda aka fara maganan bata go gilmawan ta ba..ba ita bb Mufee.

Bayan kamar sa'a 'daya Ammi sai ta sake 'kiran sa a waya, har bacci ma ya fara 'daukan sa dan haka cike da jin haushi ya fito jikin sa ko kayan kirki babu kuma ko ta kan hakan bai bi ba sbd haushi.

Zaitoon dake nan kan Dinning da Mufeeda har a lkcn da sauri ta rintse idanu tana ha'de gira...tacwani yamutse fuska.

" Kai Subhanallahi...wannan wani irin rashin kunya ne haka...?"
Ta fa'da a zuciyar ta not knowing that a fili tayi maganar...

Cak ya tsaya sannan ya waigo ya 'kare mata kallon da tashi daya ya fahimci manufar rufe idanun da tayi, this girl is always trying me...amma wallahi zan koya mata hankali...bata san waye Rayyan bane...

Jikin sa ya sake bi da kallo yaga dai bb laifi kayan wandon sa three quarter sai rigar sa armless bai ga wani aibu ga hakan ba.

'Kofan ya bu'de sannan ya dawo kusa da ita ya tsaya, facing her gaba 'daya amma bai ce komai ba.

Jin shiru ya sa ta ta 'dan bu'de idanun da ganin sa kusa da ita sai ta sake rintsewa da karfi...har tana fa'din wayyo Allah..a'uzu billahi minash shaidanirrajeem.....".

" Ji!...kin raina ni ko...?"
Yace a dake.
Da sauri ta girgiza kanta.
" Nine shi'dan ni ne maras kunya ko?"
Da sauri ta girgiza kanta.
" To ke kunyar gareki?...ko ko sai yau ne kk san da cewa idan kk ganni a haka rasar kunya ce?
" Sake rintse idanu tayi da 'karfi dan ji take tamkar akwai kafa da ta rage bata rufe sa ba.
" Waiyo Allah..".tace a ranta dan ta gama fahimtar manufar sa.

" Sa'an ki ne ni ko..?..shiyasa kk raina ni.. "
Sake girgiza kai tayi tana mai toshe fuskar da hannun ta duk biyu.

Da rawar murya tace
" Ni..wlh ba raina..ka nayi ba, gani nayi bb kyau mutum ya rinka yawo bb kayan kirki a jikin sa gaban mutane....."

" Zan yi maganin ki...zaki ga rashin kyau kuwa ganin idanun ki yarinya..."
Ya fa'da a zuciyar sa.
A fili kuwa cewa yayi"  Ammi na neman ku.."
Da sauri ta bu'de idanu da jin hk...da ganin bai matsa ba kuma sai ta sake rufewa nan take.

Har daria take bashi yarinyar nan ta 'kware a pretending a cewar sa, lkcn da yake kwance bayi da lfy meyasa bata ji kunyar ganin sa ba sai yanzun dan rainin hankali.

'Yar 'karamin tsaki ya saki yana mai wucewa dakin sa, 'kasa yayi da idanun sa zuwa jikin sa, in ba iyayi da raina shi da tayi ba, menene abin jin kunya cikin shigar sa? wando three quarter ne zata ce ba kayan kirki ba ko kuwa rigar? a hakan yaso ko sallah zai iya yi batare da fargaban komai ba... toh in kuwa har zai iya yin sallah da wannan shigar why not ya iya fitowa cikin iyalan sa a hakan.

Jin Ammi ke neman su ya sa da rawan jiki ta mi'ke bayan shigewar sa, 'diyar ta 'dauka sannan ta nufi 'kofa a sukwane gudun kar ya sake hana su fita.
Bayan fitar su da kamar mintina sha biyar sannan ya sake fitowa.

Madadin three quarter trouser din yanzu long trouser ne jikin sa sai dai bai canza rigar ba...nan kuwa yaci karo da ledan kayan da ya kawo wa Mufeeda Zaitoon bata 'dauka ba.

A zuciye ya fizgi ledan ya fice da shi.
Nan ya sami Ammi a parlon 'kasa, ita ka'dai tana shan fruits hankali kwance.

Yasan dama ba lallai ne yaga Marwa ba, Raihana ma tun asali yasan halin ta da son ke6ancewa ba'a fiye zaman hira da ita ba balle wani abu ya gifta kuma ai sai a hnkl.
Chapter 181 · 0% Book details