← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 218

Sashe 145

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata ajiyar zuciya 'kakkarfa Rayyan ya sau'ke yana mai lumshe idanu tun 'dazun abinda yake jiran ji kenan baya ga haka mai zai zaunar da shi cikin hayaniyar nan tasu da tuni ya cikawa tayar sa iska yayi gaba, amma sam ji yayi bazai iya ba, ji yake idan ya tafi tamkar ya 6antari wani 6ari ne daga cikin abinda yake son ji daga bakin ta, yafi so da bukatar ayi komai kan idanun sa..da kunnuwan sa yake son jin komai ba maimaici ba, ba kuma a bashi labari ba.

Kunnuwa ya baza yana fatan yaji kyakkyawa, yana fatan yaji komai kamar yadda yake tsammani, yana fatan abinda Zaitoon zata fa'da ya kasance masa tabbaci ne akan cewa Mufeeda 'diyar sa ce babu wani kokonto.

Shiru 'dakin ya 'dauka jin abinda Ammi ta fa'da, idan ka 'dauke Marwa, Rayyan da Ammin babu wanda yasan kan maganar Ammin amma da jin sunan wanda ta ambata yasa duk hankalin su ya dawo gare ta.

Zaitoon kam duban Mufeeda tayi dake kan cinyar Marwa ta tsura mata idanu tunanin can can baya na dawo mata daki daki, tamkar yau ne abin ya faru, tamkar yanzu ne yake ya faruwa...hakika badan da idabuwan ta taga hotunan Nadia tarecda su ba babu abinda zai sata fasa wannan sirimrin gare su, amma a yanzu bata da wani hujjar 6oyewa, bata da wani hujjar hana su jin abinda ya faru tunda ta sani sun kuma san ta sani 'din.. abinda kawai ta kasa raba ranta da shi shine tsananin mamaki, idan akace abinda ta fara sanar da Ammi 'dazun ya kasance hakan ne meyasa tun farko bata gane ba, meyasa duk cikin su babu wanda ya gane sai yanzu..?

Tausayin kanta ne taji ya kamata, tausayin halin da zata iya shiga tun ma kafin ya riske ta, domin tasan ayau 'din nan wani abu babba, gagarumi na tunkaro ta ne, wani abu da bata san ta sigar da zai iya zuwa ba, ta iya yiyuwa bakin ta ya furta abinda zai zam mata hujja wajen hukunta ta kan abinda tayi, kan son zuciyar da ta yi abaya...sai dai sam bazata fasa ba, ayau ta riga ta 'dauri aniya, ta 'dauri aniyar bayyana musu sirrin dake tsakanin ta da Mufeeda domin tasan 'kage suke suji, tasan ayanzu basu da wata bukata sama da hakan.

Idanu ta lumshe wani zazzafan hawaye ya gangaro mata..batare da ta bude idanun ba ta 'daura da fa'din.....

Salmerh😘
[24/12/2022, 11:00 am] Zee Ingawa: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...82*

......" Asalin suna na shine Zaitoon Ahmad Kyari, 'yar asalin jahar Borno ce ni cikin 'kabilar Barebari, mahaifi na kanuri ne na asali dake zaune a wani 'kauye ne dake 'kar'kashin wata 'karamar hukuma acan jahar ta Borno, yayin da mahaifiya ta ta kasance bafulatana ce usul sai dai bazan iya fa'din asalin 'yar wani yanki bace ita.

Tun tasowa ta na budi ido da ganin mata biyu a gidan mu wato matan mahaifi na, Iyami itace babba sai mahaifiya ta da ta kasance biyu.

Mu biyar ne a wajen mahaifin mu, Yah Bukar shine babba sai mai bi masa Yaagana ( Zahra) sai Muhammad ( Goni) sai ni Zaitoon, autar mu itace Khausar..Duk 'yan uwana guda hu'dun nan sun kasance 'ya'yan da Iyami ta haifa ne, ni kuwa tilo mahaifiya ta ta haife ni a gidan daka kaina Allah bai sake bata wani haihuwar ba.

Yah Bukar yana da mata 'daya mai Azeema da yaran sa biyu Ummaru da Haneefa ( Aisha)..sai Yaaganan mu dake aure a nan cikin garin itama tana da yaran ta uku.

Duk da yake ni kadaice gaban mahaifiya ta amma hakan bai sa na taso cikin kula da gata yadda ya dace ba sakamakon tsangwama, rashin sukuni da kwanciyar hankali da Innata ke fuskan ta a gidan har nima ya shafe ni.

*****
Shesh- she'kan kukan da kunnuwan sa suka fara cin karo da shine ya 'dauki hankalin sa da shigowar sa gidan kenan, mahaifiyar sa yake gaidawa amma hankalin sa da idanuwan sa na ga 'kofar 'dakin da yake jiyo kukan duk ya 'kagu ya shiga yaji abinda ya sani kuka yau kuma da wannan farar safiyar.

Tsaye ya mi'ke fuskar sa cike da alamun tsantsan damuwa yake fa'din" Iyami yau kuma me ya samu Zaituna da sassafen nan take kuka?"
Baki Iyami ta kya6e gami da komawa tana fiffita wutan da take hurawa a tsakar gidan na abin karin safe...'kasa- 'kasa cike da jin haushi tace " Wannan kuma sai ka isa gare ta kunnan ka ya jiye maka ai...tunda ni banyi darajar a zo a sanar da ni abinda ke faruwa ba dan munafurci sai dai a zauna a kukan 'karya..."

Bai damu da kalaman Iyamin ba sbd ba yau yasan halin ta ba, da hanzari ya juya ya nufi 'kofar dan duk hankalin sa tashe yake jin sa dan ma na tsagaita kukan tun lokacin da na tsinkayo muryar sa...

Tsaye yake daga bakin 'kofan 'dakin ri'ke da labile yake duba na cike da tausayi da alamun tambaya saman fuskar sa.

Ganin hakan yasa nayi 'kasa da kaina ina mai share hawayen dake bin kunci na suka kuma kasa tsayawa.
" Hamma Bukar barka da safiya.."
Bai amsa ba sai ma tambaya da ya jefe ni da shi" 'Kanwa ta me ya saki kuka kuma da safiyan nan haka..ko yunwa ce..?"
Madadin in bashi amsar tambayar sa, a a sai ma wani kukan da ya kufce min mai karya zuciya.

Sosai jikin sa yayi sanyi a hankali ya saki labilen gami da 'karasowa ciki bayan ya zame takalman 'kafafun sa.

Gaba na ya 'karaso ya dur'kusa da sanyin murya mai tafe da kulawa cikin yaran kanuri yace dani" Baki da lafiya ne...?"
Ina kukan na girgiza masa kaina alamar a a batare da na dubi idanun sa ba.
" To menene?"
Ya sake tambaya ta da kulawa sai de har yanzun ban iya na bashi amsar tamabayar sa ba kuka na kawai nake yi mai sanyin sauti gwanin ban tausayi...da Hijabin da ke kaina na rufe fuska ta nake kuma share hawayen da shi.

Shiru yayi yana sauraron kukan nawa tsawon da'ki'ku sai yama rasa kalmar 'daurawa, har cikin zuciyar sa yake jin kukan nan domin na kasance mafi soyuwa a zuciyar sa duk cikin 'kannan sa gaba 'daya.

Shakuwar ta daban ne, kamar yadda Yah Bukar ya kasance na daban cikin dukkan yayye na.

Sam baya so ya sako sunan mahaifiyar sa cikin maganar duk da yana iya zargin makadmsudin kukan daga wajen ta ne, amma yana iya raba zargin nasa zuwa gida biyu musamman da yasan cewa da wannan safiyar mawuyaci ne ace wani abu ya ha'da mu domin rayuwar gidan kaf cikin tafin hannun sa yake...sanin hakan da yayi yasa shi tafiyar da zargin sa izuwa 6angaren zargin sa na biyu.

Sosai ya rage sautin muryar sa ya 'kira suna na da sautin da ni kaina nasan cewa mai kauna da kulawa agare ka ne kadai yk da lkcn yi mk irin ta.

Kaina na 'dago hawayen na sake gangarowa saman fuskar sa na sauke idanu na da fatan ya fahimci damuwa ta ba sai na kai ga furtawa ba.

Cikin sa'a kuwa da ha'da idanun mu ya jefa min tambayar da ita nafi bukatar jin ya furta fiye da komai.

" Yau ma kinyi mafarkin ne?"
Ya tambaye ni da dukkan kulawa gami da tausayi na.

Wannan karon da sauri na 'dage kaina alamar " Erh".
Kai ya 'dan girgiza alamar damuwa domin sosai hakan ya bayyana kan fuskar sa.

" Kin sanar da Iyami ne?"
Kai na sake girgiza masa alamar a a.
Ajiyar numafshi ya sauke yana mai dauke duban sa daga kaina yace.
" Toh shikenan ki bar kukan nan haka, kuma bana so ki sake gayawa kowa idan kinyi mafarkin kin ji?"
Da kaina na sake bashi amsa alamar to.
Shi kuma ya cigaba
" Abin nima ya fara bani tsoro amma Insha Allahu zan yi magana da Baffa Liman inji ko akwai wani dalilin hakan..in akwai nasan bazai rasa mafitar da zai bamu ba da iznin Allah zaki daina kinji...?"
Kai na sake 'dagawa sama cike da gamsywa da bayanan sa, domin sarai nasan halin 'dan uwa na, afa'da ne a cika bai fiya magana biyu kan abu guda ba musamman kan abinda ya shafe ni baya sanya da shi.
A wancan ga6ar kuma ni kaina na gaji so nake a sama min mafita bata komai ba kuma sai ta yadda zan daina wannan mafarkin mai rikitarwa.
Magamar Yah Bukar ce ta dakatar da tunani na" to maza share hawayen ki fito kiyi abinda ya kamata kuma kar ki fa'dawa kowa kinji...wata'kila wani abin ne daban da bamu sani ba amma Insha Allahu Alkhairi ne zai biyo ba domin shi muke data ko wani lkc ko..'kanwa ta?"
Da sauri na 'dage kaina ina mai jin dadin kalaman sa gami da goge fuska ta kamar yadda ya bukata.
Tsaye ya mike..." Bari naje..zan dawo anjima watakila
Yayi maganar yana mai barin 'dakin nawa.

Mintina 'kalilan bayan fitar sa na 'dauka zaune a 'dakin ganin yawan tunanin ba zai min ba yawa kawai na fito cikin gida.

Iyami dake tsakar gidan baki ta kya6e tana juya kanta tace" Ai na 'dauka jira na kike yi in shigo 'dakin in tuna miki ayyukan da zaki yi...banda shashanci sabon abu ne ko kuwa yau ne farau da zaki wani zauna kina rusawa mutane kuka a 'daki sai kace uwar ki ce akace ta mutu..?"
Haka Iyami ta dinga sababi tana kan ayyukan ta.

Ni dai ban ce komai ba na wuce na 'dauki tsintsiya na fara share tsakar gidan ina hawaye, lokaci- lokaci kuma nake kama bakin hijabi na nake dauke hawayen... Iyami kuwa har lkcn bata bar 'kananun mita ba zaune gaban murhu tana gyara itacen da ke cikin wuta.

Haka na gama sharan na 'dauki bokiti na nufi rijiyan mu dake hanyar fita dan jan ruwa, duk jikina da rauni domin mafarkin nawa na matu'kar tsayawa arai na sosai idan na yishi, kuma yaki barin tunani na sosai yake bani tsoro.
Chapter 145 · 0% Book details