Sashe 93
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwata- kwata ma mancewa da cikin da take dauke da shi yayi saboda tashin hankalin rashin ta yafiye masa wannan, sai dai lokacin da cikin ya fa'do ransa ma da wuri ya kawar da tunanin sa domin yasan matu'kar ana raye inda rabon sa Allah zai sake bashi wani amma Nadia fa, baya jin zai iya samun mace a duniyar nan kamar ta, mace mai sau'kin yanayi, fahimta, juriya, hakuri da da'din zama.
Mace ce da ya san indai har da gaske damar shiga aljannar ta a hannun sa take toh indai ya kasa bata wannan damar toh bai yiwa kansa da ita kanta adalci ba, babu ta inda ta rage shi sai dai abinda ba'a rasa na daga ajizanci irin na Adam.
Tun ba yau ba ya jima da mata la'kabi da suna mar'atussaliha.
Ko da ya isa Maidugurin babu abinda ya canza sai 'karin tashin hankali daya riska, ayadda yaga yanayin su Umma da su Auwal sosai shima ya 'kara shiga cikin ru'dani, bai tsinke da lamarin bama sai da suka yi masa cikakken bayanin abinda ke faruwa.
Shikansa salati kawai.ya fara yasa hannuwa duk biyu yana shafo kansa.
Baya so tun yanzu ya nuna karayar sa amma sosai yake jin tsoro.
Sai dai babban tsoron nasa ya zarta wannan.
Yana shakkan yadda da abinda zuciyar sa ke raya masa...baya fatan ace hakan ne ya kasance, bazai iya jure wannan lamarin ba sam.
Idan akace 'yan ta'ddan nan ha'duwa suka yi da Nadia suka 'dauke maasa mata da ke dauke da cikin sa, kuma kashe masa mata suka yi...baya fatan cikin duk wa'dannan guda daga cikin su ya kasance gaskia.
Da yake yana hul'da da manya haka ya sa batare da 6ata lokaci ba akayi masa bincike sosai amma Allah da ikon sa babu wani labari da ya shafi Nadia.
Motoci 'konannu da gawarwakin mutane aka samu masu yawan gaske, wasu ma tuni har 'yan uwan su sun 'dauke su dan yi musu sittira yayin da wasun kuma abin sai a hankali sam babu kyan gani suna nan babu ma alamun za'a zo gare su...mutun dai, ran mutum dai haka tamkar ba 'dan Adam da Allah da kansa ya karrama ba...sosai ya ka'du da ganin abubuwan nan, kuma har a lokacin wasun su basu samu kula yadda ya dace ba hakan kuma shi yake sanadin wasu daga cikin victims 'din yayin da wasu ke cikin mawuyacin yanayi.
Shi da kansa ma mancewa da damuwar sa yayi tuni ya sakala handglove ya taimakawa da dama daga cikin victims 'din da iya taimakaon da zai iya na daga ilimin likitanci dayake da shi cikakke.
Zuwan su asbitocin nan soai ya 'kara sanyatar da jikin Rayyan da 'kyar kuma binciken su ya nuna musu motar da Nadia ta taho da shi ya kone 'kurmus, kuma bisa ga bincike jami'ai sun antabbatar da cewa tare da mutane fasinjoji acikin motar ta 'kone kuma tuni an binne su, kuskuren da suka yi shine basu fa'di mutane ko nawa bane aka cire a cikin motar abinda ya sake tada hankalin Rayyan kenan, dan yasan matar sa ba tafiya tayi ta cikin jam'in mutane ba, balle har a dangana ta da fasinjoji.
Sosai abin ya 'daure kansa, sai dai ya kasa yadda da bayan nasu.
Ko da suka nemi cikakken bayanai akan lamarin basu samu komai yadda ya dace ba.
Yadda yake ji kansa ke juyawa ma ji yake ya tsani komai dama garin gaba 'daya, sauran abubuwan Sultan ne ya 'karasar da su da wasu cike ciken file na cikiya hadda photon Nadia suka bari wajen hukumar bincike ko da ko da za'a dace da ganin Nadian sai a sanar da su...dan sam Rayyan bai yadda da waccan bayanan ba, duk kuwa da cewa hukumar transport ta tabbatar musu da cewa lallai motar nan da aka samu konanniya kan hanya daura da wani 'karamin 'kauye akan hanyar Maidugurin lallai itace motar Haruna dirver da yakai Nadia Damaturu, domin kafin tafiyar sa sai da ya sanar da hakan, kuma iyalan sa ma sun tabbatar da cewa motar tasa kenan sakamakon numbern motar da suka iya ganewa, sai dai shima har a lokacin basu samu wani sahihin labarin inda yake ba.
Daga Damaturu har Maidugurin aikin da suka yi kenan kusan kwanaki hu'du suna abu 'daya...da 'kyar suka samu suka dawo gida bayan duk sun fita hayyacin su sbd tsananin rashin. sukuni da tashin hankali.
Ko da suka dawo gida koka'dan Rayyan ya kasa komawa dai- dai, a kullum damuwar sa 'kara yawaita take yi.
Tsoro yake ji kar ace irin rabuwar da zaiyi da Nadiar sa kenan, kuma can 'kasan zuciyar sa yake jin wani abu na tabbatar masa da cewa mayuwaci ne idan Nadia tana raye, in kuwa tana rayen toh tana ina? tana ina ta barshi cikin mayuwacin halin rashin ta.
Sultan kam duk lokacin da ya dubi Rayyan sai dai ya saki makirin murmushi sosai yake jin da'di da faruwar wannan al'amarin domin aganin sa 'yan ta'addan sun sau'ka'ka masa al'amura ne.
An doshi sati har biyu kenan yanzu da rashin Nadia sosai zu'katan ahalin biyu ke cikin tsananin tashin hankali, kar ma Anty Yakura taji labari domin in ka 'dauke Umman Nadia da Rayyan toh Anty yakura tafi kowa shiga damuwa sbd tasan sanadin ta ne komai ya faru, ita ne tazo ita ta zo dubawa, duk da kuwa tasan girma da dajarar kaddara ga duk wani muslumi amma damuwar rashin Nadia da rashin samun cikakken bayani game da ita sai ya hana Anty Yakura samun sukuni kwata kwata.
Dole suka sake bu'de wani babin binciken da taimakon mai gidan ta suke nasu daban domin ko ba komai zata so ace kowa yasan takamamman halin da Nadia take ciki, inma bata raye zata zo su san cewa erh bata rayen dagaske da kwakkwaran shaida da kuma Hujja tanadaddiya...sbd hankula zasu fi kwantawa.
*****
Zaune yake gaban Ammi bayan ya shigo gidan gaishe ta da safia, amma yadda Ammi ta ganshi sai taji duk hankalin ta ya tashi sosai itama, kusan kowacce rana Rayyan sake zabgewa yake yi, yayin da Amrah kanta bata samun hankali da natsuwar sa cikin kwanakin kwata- kwata.
Ita kanta Amrah rashin Nadia ya ta6a ta sosai amma da yake tana tare da shai'dani sai ya 'ki bawa hakan damar bayyanuwa a zahiri.
Dai- dai da 'kwayar zarra Sultan bai canza daga yayayin sa ba sai dai na ganin ido wanda yake yin sa na 'dan lokaci, sai dai ko in yana tare da Ammi, Rayyan ko Marwa yake nuna cewa shima fa yana cikin damuwa da rashin Nadia, amma sa6anin wa'dannan rayuwar sa yake cike da walwala da jin da'din nasara da kesake tunkaro sa a ko wani lokaci.
" Rayyan har sai yaushe zaka gane cewa mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke ka daina damun kanka, kaga kuwa yadda ka dawo? so kake kace min ja da ikon Allah kake ko me Rayyan...?"
" Ammi ba ja nake da ikon Allah ba, ni waye da zan ce ban yadda Allah ke kashewa da rayawa ba, kawai dai Ammi ni kaina bansan meke damuna ba, na kasa cire lamarin araina.."
" Ammi..Nadia nada wata daraja ne a idanu na wanda zai yi wahala na iya mancewa da shi cikin lokaci 'kan'kani haka balle ace mancewa na har abada, damuwa ta a kullum bai wuce na in san inda take bane a yanzu, shin tana raye ne ko kuwa ta barni, wallahi a kullum jin zuciya ta nake tamkar zata fashe saboda ra'da'din rashin ta Ammi.."
" Ha'kuri zaka yi mu kuma cigaba da Addu'ah, ni kaina wannan abin na tsananin 'daure min kai, gashi abin damuwar ma shine tsohon cikin da take tare da shi..fatan mu a kullum shine ubangiji Allah ya bata kariya ya bayyanar mana da ita a duk inda take cikin koshin lafia..".
Sunkuyar da kansa kawai yayi yana jin wani 'kuna cikin zuciyar sa...a duk lokacin da ya tuno cikin da take tare da shi ji yake tamkar ransa zai bar jikin sa ne, sosai yake tsananin tausayin halin da Nadia zata shiga da tsohon ciki jikin ta...Yah Allah ka bayyana min iyalaina ka kare min su a duk inda suke".
Wannan shine addu'ar da yake yi kusan kowa ni lokaci fili da zuciyar sa.
Ya jima yana 'kaunar haihuwa ya jima yana son ganin gudan jinin sa a dunia amma Allah bai bashi wannan damar ba sai a wannan lokacin sai gashi kuma bayan ya gama saka rai da samun haihuwar sai Allah 6oye masa su cikin 'kudurar sa.
Dalilin yawan damuwar Rayyan akan Nadia da har Amrah ta fara kawo mata 'korafi ya sanya Ammi zuwa gidan da kanta ta ciccire duk wasu photuna da duk abinda daya danganci Nadia cikin gidan tayi musu ajiya mai zurfin gaske ta inda kwata-kwata tunanin sa ba zai kai ba..hkn yasa ko wani irin bincike zaka yi cikin gidan bazaka ta6a cin karo da photon Nadia ba, tayi tayi da shi ya saki ransa amma abin ya gagara hkn yasa kawai take yi masa nasiha kullum gami da Addu'ar samun sassauci wurin mahalicci.
Aganin ta zuwa yanzun kam ya kamata ace sun yadda cewa Nadia ta barsu kenan bari na har abada, kamar yadda aka bayyana musu tun farko ta 'kone cikin mota kamar kuma yadda mahaifan ta suka yadda suka kuma 'dauki dangana suka mi'kawa Allah sauran lamuran, to kuma su wenene da bazasu fawwalawa Allah ba, tunda sun riga da sun san haka..a ganin ta Addu'ah ce kawai yanzun zasu cigaba da yi mata bakomai ba.
Ko jiya sai da suka yi waya da mahaifan Nadia su ka zanta da mahaifiyar ta ta kuma fahimce ta sosai domin mutanene su masu dattako gami da tawakkali, 'karshe ma ita Ammi daya kamata tai musu jaje ita Umman Nadia ke 'kara bawa ha'kuri gami da 'karfafa mata zuciya.