Sashe 4
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Roban da zata rika yiwa yarinyar wanka, abinda zata shimfida mata dan tana matukar son taga tayi mata shinfida itama tayi bacci asake kamar ko wani yaro, kwana biyun nan duk akan cikin ta take kifa ta suyi bacci a hakan, sai kuma take ga tamkar tana takurawa yarinyar ne da hana ta sakewa tamkar batai mata adalci ba, gefe guda kuma ga abincin yarinyar da shi yafi komai daga mata hankali idan yai kasa.
Bata kara fitowa ba har kusan karfe biyar na yamma...tana zaune tana ta sake sake banda sallah babu abinda ke tada ta.
Maman Abdul dince da kanta tazo wajen ta ganin tun dazun bata sake jiyo motsin ta ba, sai tayi tunanin ko aikin shirya kaya ne ya rike ta, tausayin Zaituna tun dazun ya kasa barin zuciyar ta ganin cewa yarinya ce karama da akalla zata iya yin kanwa da ita kusan na hudu amma jibi yadda haihuwa tai mata sammako ya riske ta tun a karancin shekarun ta, raino baya da sauki kokadan musamman ga yara irin su Zaitunan.
Wannan tunanin ne ya sanya ta nufi dakin tan da zummar kama mata wasu ayyukan su kammala da wuri.
Sai dai me ba karamin mamaki tayi ba lokacin da ta riski dakin ba a yanayin da tayi tsammani ba...turus ta tsaya ta karewa dakin kallo.
Da sallama ta shigo Ahmad da bazai haura shekara guda ba tafe abayan ta, fuskar ta cike da alamun mamakin da har yakasa boyuwa mata idanun ta kur akan Zaitun din domin daga ita babu wani 6angare da zaka 6atawa kanka lokaci wajen duban sa a dakin dan tas yake babu komai.
Kakalo murmushi tayi tace " Na jiku shiru ne gashi har yanzu baki kwance yarinyar nan kin huta ba Zaituna.."
" Zan kwance ta am..am"
Sai kuma ta kasa karawasa.
" Da kyar ma idan kin yi mata wanka..." da sauri Zaitun ta girgiza kanta...
" Ai kuwa naga alama bari akwai ruwan wankan su Siyama dana dora musu na dare sai ayi mata wankan da shi inyaso sai in sake sanya musu wani kafin a dauke wutar".
Bata ma jirayi amsar Zaitun din ba ta fice da sauri.
Da yake ma a kettle ne ruwan tana juyewa ta sake sanya wani ta taho da wannan cikin baho hadda sabulu mai kamshi ta dauko.
Da kanta ta karbi Yarinyar dan yi mata wanka yayin da Zaitun ta juya ga kullin kayan su ta ciro riga wanda ya kasance shine karshe cikin kayan sawan yarinyar da bai yi datti ba...dama ba wani yawa gare su ba ga kuma yanayi na rashin matsuguni da ta shiga kwanaki biyun da suka gaba ta hakan sai ya hana ta samun sukunin wanke mata kayan hakan kuma bai hana ta cancanza mata kayan ba..a lokacin jiga dankwalin ta take ta goge mata jiki da kyau sannan ta sa mata kaya.
" Dole sai nayi wanki kenan a yau ko gobe"
Zaitun ta fada cikin zuciyar ta lokacin da take kokarin dauko rigar.
Maman Abdul bata sake tambayar Zaitun komai ba dan ta gama fahimtar ko wani irin taimako ma Zaitunan tana bukatar shi a yanzu.
Kuka sosai Yarinyar tai ta tsanyarawa lokacin da ake gasa mata jikin ta da ruwan dumin da yake ta kwan biyu bata samu hakan ba.
Ai kuwa Maman Abdul na gama wankan ta sata cikin zanin goyon ta mikawa Zaitun ita tare da fadin " wannan me sassanyan muryan ta iya kuka...bata tasha kafin a karasa shiryata."
Zaitun kam da tunanin bai gama bata ma'anar maganan Maman Abdul ba cigaba kawai tayi da lallaba yarinyar dan tayi shiru.
Murmushi Maman Abdul tayi" ai inaga in ba nonon ta kama ba bazata taba yin shiru ba wannan..."
'Dif zuciyar Zaitun ya buga da karfi...bata so ta sake maimaita abinda kunnuwan ta suka jiye mata Maman Abdul ta fada.
Jikin ta har rawa ya fara ta kasa daga idanu ta kalle ta..sam sam bata so ta fallasa asirin zuciyar ta a yanzu...amma meyasa babu wanda ya ta6a cewa ta shayar da yarinyar sai Maman Abdul.
Maman Abdul kam jinjinawa kunya irin na Zaitunan tayi shiyasa ma kuma bata ga laifin ta ba...domin ita Kunya adon mace ce.
Kokarin dauko madarar yarinyar Zaitun tayi da dayan hannun ta...wanda yasa maman Abdul dake kokarin mikewa da niyyar barin dakin dan bata damar sakewa gudun kar ta takura ta bin hannun nata da kallo...
" Wannan za'a bata..."
Zaitun ta fada batare da ta iya daga ido ta dubi Maman Abdul din ba.
Ba karamin mamaki maman Abdul ta shiga ba sai dai bata tsawaita tunanin ba ta karbi gongonin ta ajiye...Zaitun kam idanu ta zuvawa yarinyar sai ma lallashin ya gagare ta..gaba daya rasa abinyi tayi, abu daya da tasani kawau shine tana matukar kaunar yarinyar nan irin kaunar da a kowani irin lokaci hauhawa yake yi baya raguwa.
Maman Abdul komawa tayi 6anagren ta dawo da ruwan dumi a kofi ta dama madarar ta karbi yarinyar da kanta ta bata ga mamakin ta kuwa sai taga yarinyar bata nuna alamun kin sha ko wani abu ba ga dukkan alamu ma ta riga ta saba da shan abinta...ai kuwa shikenan kuka ya kare sai bacci.
Rigar maman Abdul ta dauka tana sanyawa yarinyar a fakaice take duban Zaitun din abubuwa da yawa na mata yawo aka.
Cike da kulawa fa fara fadin
"...amma Zaitun me yasa kuka yi shawaran bata madara tun a yanzun ta ai tayi karama sosai ina ma laifun abari tadan kara watanni kafin, ko mahaifin ta ne ya bada umarnin ayi hakan..?"
Shiru Zaitun tayi tana duban Maman Abdul ido cikin ido bama tasan tayi hakan ba kuma...kalmar mahaifi da Maman Abdul ta ambata shi ke yawo tsakanin kwakwalwa da zuciyar Zaitun.
"mahaifin ta...Mahaifin ta...toh ma shi din waye kenan mahaifin nata...?"
Ta tambayi kanta.
Tsinkayan muryar maman Abdul ta yi tana sake tausan ta duk dai akan maganar madaran nan wanda hakan shi ya sata dawowa daga tunanin da ta lula.
Kai ta girgiza tare da yin kasa da kanta tace " Kaddara ce kawai ta za6a mana hakan daga ni har ita,
Maman Siyama ba nice nayi ra'ayin hakan ba haka kuma babu wanda ya tilasta ni...".
"Amma ai da ba tun yanzu ba Zaitun yarinyar tayi karama Nonon mahaifiyar ta shi tafi bukata a wannan lokacin ba wai madara ba".
Bata sake cewa komai ba illah siraran hawaye da ya gangaro mata ta kuma kasa tsaida su, kamar yadda bakin ta ya kasa buduwa ya ce wani abu, kasa kawai tayi da kanta bata sake dagowa ba.
Ganin hakan da Maman Abdul tayi ya sanya jikin ta yin sanyi..sai kuma taji matsanan cin tausayin ta ya kara shigan ta.
" kiyi hakuri idan magana ta ta 6ata miki rai ne Zaitun ba nufi na kenan ba"
Daga hakan taja bakin ta tayi shiru sai dai ta gaza hana zuciya ta yin sake sake kan lamarin.
Da kanta ta sake zuwa ta hado wani ruwan zafin ta kawo wa Zaituna tace itama taje ta yi wankan bari ta goye mata yarinyar kafin ta fito.
Sosai karamci da mutuncin matar ya tsayawa Zaitun aranta...hakan yasa ko musu batayi mata ba ta dauki ruwan ta shiga wankan duk da cewa kuwa kaf din hankalin ta naga 'yar yarinta dake bayan matar ne..amma haka kawai sai taji tana jin nawin matar nan...kauna ta zahiri ta nuna musu ita da 'yar ta a haduwar su ta yau kadai...rana guda daya tal...dole ta jinjinawa karamcin wannan baiwar Allah.
Fitowar ta daga wankan kuwa ta sake ta tarar da wani abin mamakin domin tabarma ta tadda shimfide a dakin hadda wani bargo akai mai kauri an shinfida shima sai kuma bargon yara daga gefe ajiye ga dukkan alamu dan 'yar yarinyar ta aka ajiye sa.
Bata tadda Maman Abdul cikin dakin ba dan haka sosai farin cikin ta ya kasa 6oyuwa haka ma hawayen ta.
Ayau taga karin mutun cikin wadanda suka nuna kauna ta hakika ga Yarinyar ta..wadanda daidai da rana guda basu taba nuna kyama ga yarinyar ba.
Wannan wankan da tayin ba karamin dadin sa taji ba haka ta shirya cikin wata atampan ta daban duk da yake itan ma ba wata mai kyau ba ce amma dai baza a kira ta kai tsaye da kazantacce ba.
Maman Abdul ce ta sake dawowa goye da yarinyar bayan ta su Siyama ne da Abdul sai Ahmad, " 'yan Islamiya ashe andawo.."
Ta fada tana duban su Siyama fuskar ta wadace da murmushi.
Bata jira yi amsar yaran ba ta maida duban ta izuwa ga Maman sun...da niyyar mika mata tsantsan godiyar ta.
Sai dai kafin ma tayi magana Maman Abdul ta kunto yarinyar daga bayan ta tana fadin..." simintin akwai sanyi sosai shiyasa na sanya muku tabarmar zai dan rage koda kadan ne ma".
" Nagode sosai Maman Abdul, Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, dama inaso in tambaye ki inda zan samu bargon yaran in siya mata sai kuma...."
" ai bama sai kin siya ba Zaitun wannan ta Ahmad ce dayake yanzu ya girme shi kawai ai mata amfani da shi...akwai kayan sanyi ma da Net din sa zuwa gobe Insha Allahu duk zan duba muku tunda mun daina amfani da shi..."
Bata bari Zaitunan ta kara ko kalma guda ba ta tisa keyar yaran ta suka bar dakin suna mata sai da safe domin da kyar ne sake haduwar su a yau din kofar gidan ma tuni sun garkame shi tunda basake fita wani cikin su zai yi ba.
Duk da yake Maman Abdul taki bata daman nuna godiyar ta amma dole ne ko da bayan idanun ta ne ta gode ta kuma yi mata fatan alkhairi da ita da zuri'ar ta gaba daya.
Dan ko kafin Mmn Adul ta rufe kofan gidan sai da ta tambayi bakin Zaitun saboda hakkin zaman tare...Zaitun din ce tace mata ai babu inda zata kuma fita ayau din Maman Abdul ai kin gama wadata mu da komai.
_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( ' Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️...3