← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 218

Sashe 134

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ya akayi kasan...kasan..."
Sai kuma ta rasa kalmar da zata 'daura bayan hakan.
Shine ya kar6e zancen da fa'din..." ...ya akayi nasan damuwar ki ko...? Ko ba shine abinda kike son tambaya ba.
Sai tayi shiru...still zuciyar ta na sake cika da mamaki.
Yana gyara zaman sa yace
" Ai ni 'dan baiwa ne, ke baki ta6a sani ba? tambayi Ammi na zata fa'da mk ai...".

Shiru Zaitoon tayi tana mai kissima kalar baiwar tasa sosai ta auna ta a mizani ko dagaske yake ko kuma wasa...tunanin ta ya kasa bata, amma bata ta6a ji ko ganin baiwar tasa ba meyasa sai a kanta.

'Dagowa tayi ta dubi fuskar shi da tunanin ko zata samu amsar tambayar ta saman fuskar amma ta gaza.

Shi kam 'yar murmushi yayi da ganin hakan.
" Wasa nake mk sarkin bin 'kwakwaf...kece da bakin ki kk ban labari fa idan kin nutsu zaki tuna lkcn da kanki..kuma kar ki damu Insha Allahu za'a 'dauki mataki akai bada jimawa ba"

Yanzu kam rai ta ha'de sosai tana me kawar da kanta gefe... 'kasan ranta tace" Ni kuma? da yaushe toh..?"
Sabon kuka ta fashe da shi na takaici da bakin ciki ta kuma jinjina wautar ta cikin ranta.

Me ma yasa tayi hakan, meyasa zata sanar da shi, da yaushe tayi hakan ta kasa tunawa...a wani ma dalilin zata sanar da shi, ina hankalin ta ya tafi da har tayi hakan.?
Tambayoyi ne birjik cikin ranta amma bata da me amsa mata su...hakan kuwa shi yasake tsawaita kukan tata kuma kasa rarrashin zuciyar ta balle tayi shiru.

Rayyan ma bai ce da ita komai ba, dan be san me ze ce 'din ba dama...amma tsananin tausayin ta da haushin kansa yake ji na cikasa.
Sai da tayi kukan me isan ta tayi shiru tana sakin ajiyar zuciya.." kiyi hakuri.."
Itace kalmar da ya iya furta mata sau 'daya tak kuma be sake ba har tayi shirun.

Takaici goma da ashirin ne suka yi mata yawa a zuciya.
Jin tayi shiru ya sa shi sakin 6oyayyar ajiyan zuciya.

Mufeeda ya 'dago yana gyara mata zama ajikin sa yace..." Kin yi wankan ki amma baki yiwa mama na ba...".
Shiru tayi bata tanka shi ba sai jan numfashi da tayi.
Tuno cewa yarinyar zata skull ne ya sanya ta bashi amsa da fa'din" Zan mata yanzu...".
Tace tana mai 'kokarin yin dauriyar tashi.
Hadda cije baki banda wani 'dan zazza6i da take ji ka'dan- ka'dan yana taso mata.

A fakaice yake duban ta, yasan dauriya kawai take, shi kansa kuma yana so ta huta sosai a yau 'din.

Kawar da kansa yayi yana yiwa Mufeeda data wani narke a jikin sa wasa, tamkar itama tasan waye shi agare ta yanzu, bata gudun sa kamar baya.

Batare da ya dube ta ba... Yace" in tayaki...?"
Sai ta waigo da sauri ta dube shi.

Rayyan sai ya 'dan daburce da tunanin kar fa ya za'ke da yawa kuma..." I mean in taya ki yi mata wankan...?"

Tana ninke daddumar da ta tashi akai da sanyin murya gami da mamakin jin furucin sa tace..." a a..ai bazaka iya ba..."!
" Kina kokonto ne...?"
" a a tabbacu nake da shi, kai da komai ma sai an tayaka yin sa shine har zaka iya yiwa Mufee wanka..."
Tun tashin ta wannan shine doguwar magana da tayi na bai 'daya..ta kuma yi shi ne da sanyin sauti me cike da birgewa.

Rayyan kansa jin da'din maganar ta yake dan haka sai yayi 'dan murmushi.
" Zan baki mamaki kuwa..just wait nd see.."
Tace.." Allah ka bari zan mata ma fa yanzu..."

Tsaye ya mi'ke da Mufeedan ya nufi bathroom yana fa'din " ke de ki jira mu...."

Zaitoon saroro tayi da mamakin sa tama kasa ta6uka komai har suka yi wankan suka fito.

Bata san me yace da Mufeeda ba kawai taga sun fito duk suna dariya.

Mamakin ta ya 'kara 'karuwa.
Gaban ta yazo ya mi'ka mata Mufeeda domin iya abinda zai iya yi mata kenan.
Bakin gadon ya koma ya zauna yana duba agogo yace" yau dai kinsa yarinya latti a banza".

Shap shap ta shirya ta cikin uniform 'din ta, tuno ko breakfast bata shirya mata ba balle na lunch 'din ta...a ranta kuma tana tunanin dan bai san meke damun ta bane da har zai ce haka...amma ita kadai tasan ciwon da jikin ke yi mata.

Duk abinda take Rayyan na lura da ita, ya kuma fahimci kawai dauriya take domin motsin kirki bata yadda tayi da jikin ta sai dai in ya kama na dole ne.

Kawai ji tayi ana magana awaya...ya kuma saka wayar a speaker...
" Na 'kira Ammi bata 'daga ba..."
Muryar Marwa taji daga 'dayan 6angaren tace..
" May be tana 'kasa ne bari in duba ta..."
Cewar Marwa tana mai ziraro 'kafafun ta daga saman gado.

" No barta, breakfast nake so a shirya min yanzu da lunch 'din Mufeeda plz..maman ta bata jin da'di ne yau......"
" Ok "
Tace tana ajiye wayar.
Zaitoon yau mamakin sa kasa barin ta yayi, wai dagaske Rayyan ne yau 'din ko kuwa wani daban ne aka canza shi.

Yana cire wayar idanun sa akanta ganin yadda take masa kallon mamaki yasa shi 'dan ha'de rai yace..." What...?"
Kawar da kai tayi bata ce da shi komai ba.

Duk yadda ya fa'da 'din hakan akai masa, a cikin mintinan da basu haura ashirin ba aka gabatar da masa da komai da ya bu'kata.

Gaba yasa Mufeeda da Zaitoon akan suyi breakfast Zaitoon sam ji tayi bata bukatar komai tea kawai ta sha yayin da yasa Mufee ta 'dan ci soyayyar irish da aka kawo da Tea 'din sannan ya 'dauki lunch box 'din ta gami da kama hannun ta suka yi waje.

Ga James yaje ya dam'ka ta yace akaita skul, in time 'din tashin su yayi kuma a 'dauko masa ita.
" Oya..Mamana bye bye...ayi karatu so kinji..?"
Ya fa'di hakan yana sakin hannun ta gami da 'daga mata hannu sannan ya koma 'dakin sa.

Bai sake dubo Zaitoon ba sai bayan kusan 2hrs kafin ya koma 'dakin nata dan duba jikin ta.

Du'kun'kune ya same ta cikin bargo da alamu sanyi take ji sosai.

Hannu yasa cikin abin rufan ya ta6o wuyan ta yaji yaji babu zafi, saman goshin ta ya sake shimfi'da tafin hannun sa sai dai jin yanayin zafin jikin nata yasa ya kasa 'dage hannun nasa har ta bu'de idanu ta sau'ke akan fuskar sa.

Salmerh😘
[30/11/2022, 2:22 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...77*

........" Sannu".
yace mata yana shirin zama gefen ta.
Da sauri ta matsar da jikin ta gefen ta tana kuma 'ko'karin cire hannun sa da ke kan goshin ta amma ta kasa 'dagewa, ya kuma 'ki bata damar da zata 'daga 'din.

Sai da yaga ta matsa ne sannan yace.." What..."!
Tayi shiru.
" Ashe babu da'di...ni da kullum kike ta6a min jiki na fa...?"
Yatsina fuska tayi tana kawar da kai gefe.
Rayyan sai yayi 'yar murmushi...a hankali yace..." Ya jikin fa.."
Da sar'kewar murya ta amsa shi..." Alhamdulillah...lafiya ta ma kalau....".
" Kin tabbatar...?"
Ta 'dage kanta.
" Toh zafin jikin fa...?"
" Haka nan kawai....".
Yana shirin sake magana yaji 'karan wayar sa dake aljihun gaban rigar sa.

Duban sa ya kai ga wayar kafin a hankali ya 'dauke hannun sa dake saman goshin ta ya ciro wayar Ammi ya gani...

Yaje gaishe ta ya tarar bata nan sassafe yau ta fita.

Gaishe ta yayi ta amsa sannan ta 'dora da fa'din" Ina 'diya ta?"
" Wace...?"
" Gidan ku Rayyan...".
'Yar dariya yayi" Toh Ammi ai Marwa na can part 'din yau bata zo nan ba...".
" Aww toh...Zaitoon nake nufi, Marwa tace min wai bata ji da'di ba in jika...?".
'Dan kallan inda take yayi sannan ya amsata da fadin.." erh wlh Ammi, tana bacci ne amma da sauki dai Alhamdulillah...".

" Dama me ya same ta?"
'Dan jim yy sai kuma yace" Bata da lafiya ne Ammi?"

" Subhanallah, toh Rayyan a duba ta, in kuma bazaka iya ba, a 'kira Doctor ko kuma a kaita can a duba ta zaifi ko?"

" Toh Ammi.."
" Wanne za'ayi ?"
Ta sake tambayar sa dan tabbatarwa sbd tasan halin.sa da 'kyar ne idan zai bawa maganar muhimmanci.

" Ammi fa na duba ta kuma naga jikin ne da sauki yanzu sai dai zafin zazza6i"
" Baka da hankali Rayyan, ai ba a raina ciwo, plz ka duba ta ko kuma kasa a duba ta, shi ciwo ba'a raina wanzuwar sa..."

'Kayataccen murmushi kawai yy bai ce komai ba, sai da ta sake magana sannan yace" Insha Allah Ammi za'a yi kamar yadda kika ce..".

Ga Zaitoon ya maida duban sa yana fa'din har baccin ya ishe ki..?
Shiru tayi masa bata bashi amsa ba.
Shima bai damu da rashin masawar tata ba dan in da sabo ya riga ya saba da halin ta batun yau ba.
Juyawa tayi 'daya 6angaren tana gyara kwanciyar ta.
" Ba kiji ba...?"
Sai ta 'dan waigo tana 'kan'kance idanu..ina ke miki ciwo yanzu?"
da kai ta bashi amsa alamar bako ina ta hanyar girgiza masa kanta.

" Ammi ta 'kira tace wai akaiki clinic a duba ki, kuma ai naga jikin da sau'ki ko?"
kai ta sake 'daga masa tana 'ko'karin tashi zaune...

" Ke ya kika gani, ko kema kin fiso aje can 'din...?"
Har cikin ranta bata so 'din amma sbd kar Ammi taji babu da'di idan taji cewar ta 'kiya yasa ta fa'din
Bai kai ga rufe baki ba tace" ai ma naji sau'ki, bana jin komai yanzu...."

" Toh...kawai idan ta nemi magana da ke kice da ita anje kinji?"

Shiru tayi bata bashi amsa ba...dan haka ya mi'ke ya fita a 'dakin Zaitoon bata ko sake kallon inda yake ba...damuwar da ke cin zuciyar ta yafi damun ta a yanzun.
Chapter 134 · 0% Book details