Sashe 140
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rayyan kam shiru yayi yana duban ta gami da fasa maganganun ta dalla dallah ya kuma fahimci me take nufi tsab.....
Shi dama ba gwanin lallashi bane dan haka yayi shiru yana duban ta sai dai tsananin tausayin ita har Mufeedan yake ji.
" Wallahi bazan ta6a yafe muku ba, kuma bazaku ta6a yin 'karshe mai kyau ba Insha Allahu...duk.wanda yake da hannu cikin kisan 'diya ta sai yaga sakayya...."
" Zaitoon...!"....
Yayi saurin dakatar da ita da 'kiran sunan ta, sai dai ga mamakin sa jawabin ta da ya biyo baya kaushi gare shi...".karka kuskura ka 'kira suna na, ka 'kyale ni nayi kukana
tunda haka kuka fi so ku ganni, burin ku ku tozarta ni, burin ku ku ganni cikin kunci shiyasa kuke ha'de bakin ku, macuta kawai maciya amana, marasa tsoron Allah, maha'inta kawai....".
Ta fada batare da ko jin shakkar sa bane.
Shi kam bai san kuma me zai 'kara fa'da mata ba illah ido daya tsura mata yana kallon yanda take kuka...wai dama dagaske haka iyaye suke ji ne akan 'ya'yan su..ko kuwa natan ne na daban hadda iskanci, shi bata ma ga jarumtar sa ba da ya iya sadaukar da ran 'diyar sa ya fanshi nata aranar ba dan son kai take fa'da masa irin wannan ba'ka'ken maganganun akan that same yarinyar...? ya tabbata da sunyi.niyyar kashe ta da gaske da sun kashe masa 'ya aranar amma Allah ya dube shi, amma shine zata sashi gaba da irin wannan tijarar..?
Abinda ya tambayi kansa kenan yana sake waro idanu akanta cike da mamakin ta.
Zaitoon kam ganin irin kallon da yake yi mata ne ya sanya taji fa'duwar gaba sosai, ko shakka bata yi ba balle tsoro ta 'dago hannu ta nuna shi da yatsa, cak kukan ta ya tsaya ta wani 'kan'kance idanu, idanun ta cikin nasa tace
" Kar ka gaya min cewa kun kashe min yarinya ta dagaske ne..?"
Shirun da taga yayi yana duban ta ne ya sanya ta fizge abin hannun ta gaba 'daya ta mi'ke, bata damu da jirin da ke 'diban ta ba ta tashi ta tsaya a tsawace tamkar itace sama da shi tace
" Tambayar ka nake ina 'ya ta, wallahi matukar Mufee na ta rasa ranta ta dalilin ka wallahi kaima kashe ka zanyi da hannu na, dan akanta babu wanda bazan iya 'daukan mataki akan sa ba...."
Sai kuma ta zube 'kasa saman gwiwoyin ta tana me sake rushewa da kuka ganin ko 'kala ya 'ki cewa da ita, kuka sosai ta saki tana bubbuga kanta tace" ita ka'dai fa gare ni, Mufee bata san kowa ba sai ni, babu wanda yake son ta sai ni, kunsa na ci amanar alkawarin da na 'dauka na cewa zan bata kariya, 'karshe kun kashe min ita kuka rabani da ita haka nan kawai batare da tai muku laifin komai ba..mecece ribar ku? wallahi bazan bar duk wanda ke da hannu akan kisan yata ya cigaba da farin ciki ba..."
Tsaye ta mike a harzuke zata yi hanyar waje yy saurin ri'ko hannun ta da hannun hagun sa mai cikakken lfyr, ita ma da 'daya hannun ta take bubbuga na shin tana fa'din
" Ka sake ni, mugu kawai azaalumi, masu 'daukan rayukan yara 'kanana wallahi Allah bazai barku ba sai ya mana sakayya..."
Ganin taki natsuwa ne ya sanya shi bu'de murya ya 'kira near by Nurse.
Shigowa tayi tana mai rusunawa.
Yi min magana da doctor".
Fita Fa'izan tayi tana mai jinjina kanta.
Cikin sakanni 'kalilan likitan ya shigo.
Da turanci yy masa magana wanda hakan ya sa Zaitoon banka masa uwar harara.
Fita likitan ya sake bai da'de ba ya dawo shi da wata nurse abayan sa..Zaitoon nata fama da kokuwar 'kwace jikin ta amma ta kasa, kuka take amma da ganin likita na gyara Allura ya sanya ta zabura tana 'kara sautin kukan ta, ba wai dan tana tsoron alluran bane a a, sai dai dan takaicin rashin 'diyar ta a ganin ta bb wani ciwo dake damun ta illah ciwon rashin Mufee kuma allura ba zai mata maganin wannan ba, dan hk babu wanda ya isa ya sa ai mata allura....
Hannun ta take shirin fisgewa daga cikin nashi yay saurin gyara rikon yana duban fuskar ta.
Matso da ita yy kusa da shi ya sar'ke ta da 'kafafun sa ganin hakan yasa ta fara fizga tana fa'din" Bana so.."
" Ka kyale ni, mugaye kawai, azzalumai...wallahi sai nakai 'karar ku wajen hukuma dukkan ku...masu zuciyar fir'auna kawai, masu halakar da kananan yara, in ba zalunchi ba me yarinya tai muku....".
Sam bai damu da zagin da take jerowa ba, da hannun sa 'daya mai cikakken lafiyr ya matse ta cikin jikin sa amma ko motsi kasa yi tayi dan sosai ya dabaibaye ta da 'kafafun sa.
Hannun daman ta dake cikin nashi ya mi'kar wa likitan yana bashi umarnin yi mata allurar.
Nurse din ce ta taimaka masa suka kwantar da ita..yana gyara mata mazaunin kanta bisa pillow tana 'dan lumshe idanu tace" Kai..ma mugu ne ashe...."
Murmushi yy ta'kaitacciya, dan shi ka'dai yaji abinda tace dan lokacin bacci ya fara cin 'karfin ta.
Sai da ya shafi fuskar ta kafin ya nufi hanyar fita yana amsa 'kiran da Ammi tayi masa.
Tsawon time 'din da Zaitoon ya kamata ta 'dauka a baccin ko rabin sa bata yi ba ta farka, su kansu sun yi matu'kar mamaki, ta kuwa 'daga musu hankali, ga shi Rayyan bayanan, sai Marwa ka'dai, duk yadda taso kwantar mata da hankali sam Zaitoon ta 'kiya, dole sai da Marwa ta 'kira Rayyan a waya yazo, yana can yana kan 'karasa binciken abinda ya faru ya tsinkayi wayar Marwa hankalin sa ya tashi, sosai ransa kuma ya 6aci.
Yarinyar na can gidan Anty Madeena mancewa ma yayi bai taho mata da ita ba da safen, dama niyyar sa sai ya tashi komawa ne zai tafi da ita.
Jin tashin hankalin da take yi musu kuma ya sanya ransa 6aci yama fasa 'dauko yarinyar, haka ya nufi asbitin cike da zafin rai.
Yana zuwa ya tarar ta birkita ko'ina tamkar mahaukaciya ta kasa sauraran kowa duk ta jiwa kanta ciwo banda kuka da take yi duk wai akan Mufeeda.
Marwa kanta ma kukan take tana fa'din haba Zaitoon! Haba dan Allah, wai kina hauka ne?...ance miki Mufeeda na nan a raye bb abinda ya same ta meyasa bazaki kwantar da hankalin ki, ki bi komai a sannu ba...?"
Idanu ta waro akan Marwa tana duban ta da mmk...
" Marwa in kwantar da hankali na kika ce, bayan sun kashe min yarinya...?"
" Babu wanda ya kashe ta ki kwantar da hankalin ki dan Allah ki nutsu..gaba 'daya kin.kasa saurarn kanki ma balle ki bawa kankin damar sauraran wani, Mufeedan ki tana raye ai kinsan bazan miki 'karya ba ko ba...?"
" Karya ne.."
ta fada da 'dan 'karfin sauti tana mai watsa hannuwa.
" 'Karya ne kawai fada kike Marwa, in dai dagaske tana raye toh in ganta mana, a gabana fa, tana hannu na aka harba mata bindiga Marwa..."
Sai kuma ta rushe da kuka tana mai juya kai side by side.
Rayyan na isa daya 'kare wa 'dakin kallo direct ya nufi inda take idanun sa na kanta...da isar sa ya sa hannu zai kamo hannun ta ta fizge da 'karfi tana matsawa baya kadan.
Juyowar da zai yi kawai ya sau'ke mata mari lafiyayye saman kuncin ta wanda yasa Zaitoon dafe wurin nan take, tana shirin zamewa 'kasa yayi saurin cafko hannun ta hakan ya hana ta zamewa.
Idanun sa cikin nata idanun dake cike taf da ruwan hawaye suna shirin gangarowa yace..." Kina tunanin ke ka'dai ke 'kaunar Mufeeda ne? ko kuwa naki hauka da karamin 'kwa'kwalwan ne ya ninka na kowa..?..ke a tunanin zaki fi kowa jin zafi ne idan akace yau babu Mufeeda, ni kinsan yadda zanji, kinsan 'kuncin da zan fada ne sbd rashin ta, wallahi naki ba komai bane akan yadda ni zanji...?"
Jin furucin sa yasa ta waro idanu sosai akansa ta fara jan baya tana girgiza kanta wani sabon kukan na zuwa mata...gani take kamar kawai ya fa'di son ransa ne, sai taga kamar kokari yake ya kwace mata matsayin da take da shi a wajen Mufeeda baya ga hakan meyasa zai ce haka...?"
Ganin yadda ya sake rikita mata tunani gami da canzawar yanayin ta yasa Rayyan kama hannun ta yaja ta zuwa waje.
Bai tsaya ko'ina ba sai cikin motar sa da wani 'dan banzan gudu yaja motar zuwa gidan Anty Madeena...batare da ya sake furta wata kalma ba ko duban inda take ma bai yi ba.
Marwa kam cike da mamakin furucin sa tabi su da idanu har suka 6acewa ganin ta, jujjuya maganar take cikin ranta ta kuma kasa gano manufar su...a iya sanin ta dai ba hakan bane amma meyasa zai wa furtawa Zaitoon, rashin sanin takamammen dalili yasa tuni tayi watsi da su.
Zaitoon kam kuka take tana jin maganganun nasa nayi mata yawo aka, bata ma san ina suka nufa ba balle tasan lkcn da suka iso sai ji tayi yayi parking.
Koda yayi parking da kansa yazo ya bu'de mata motar ya kuma sake fizgan hannun ta zuwa sabon 6angaren Anty Madeena..abin mamaki da shigan su parlorn sai ganin Mufeeda tayi tana wasan ta cikin kwanciyar hankali.
Zaitoon bata san lkcn da ta zame 'kasa saman gwiwoyin ta ba, gaban yarinyar ta tsaya tana bude mata hannu gami da washe baki, Mufeeda ma na ganin ta ta taho da gudu wajen ta cike da murna tana fa'din " Mammi.."
Zaitoon janyo ta tayi ta rungume ta sosai tana sakin wani sabon kuka na farin cikin ganin Mufeedan ta na raye...yayin da cikin ranta banda hamdala bb abinda take yi.
Mufeeda ma da sauri ta shige jikin ta tana daria ta sake fa'din..." Mammi..."!
Rayyan bai ce da ita 'kala ba kawai ya samu waje ya zauna yana sakin zazaffan huci idanun sa a kansu, a hankali ya 'dage kansa sama yana dafewa da hannun sa 'daya.