← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 218

Sashe 35

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar almara kamar a mafarki abubuwan ke ta faruwa mata daki- daki duk cikin kankanin lokaci.
Cikin kalilan 'din watanni ta tsinci kanta a waurare da kuma yanayi daban- daban wa'danda ko cikin tarihi bata ta6a jin su ba iya tsawon shekarun ta na dunia, bata ta6a tunanin faruwar haka ga rayuwar ta ba, shekara 'daya tak baya in ance mata zata fuskanci wadannan abubuwa bugan kirji zata yi ta karya ta amma abin mamaki sai ga shi karshen ta ma yau ga inda kaddara ta jefo da ita.
Ta kuma rasa shin waye me laifin, iyayen ta ne ko kuma ita? ko kuma Mufeeda.
Shin Iyayen ta da suka kasa rike ta sbd kaddarar data same ta ne ke da laifin ko kuma ita da ta kar6i kaddarar tata ta rungume hannu biyu..?"

Haka suka cigaba da kwana cikin prison 'din, basu da banbanci da dabbobi, domin kowa baya musu kallon arziki, kowa kallon su yake kamar ba 'yan Adam da Allah da kansa ya karrama su ba.

Kafin cikar kwanaki Sha hudun nan Zaitun sun koma sai 'kashi idan ka dube su, banda katon kai babu komai, duhu sosai suka yi suka jeme, ba ma kamar Hameeda da ake 'dan 'kara gyara jikin da lafiyayyan mayuka da supplements tsadaddu, yanzu da ya kasance babu shi komawa tayi kamar wata Hameeda ta daban.

Tuni ta mance da 'kiyayyar da take faman yiwa Zaitun 'din dan yanzu ta koma mata ne kamar 'yar uwa.. lokuta da dama Zaitun din ta fita kwarin zuciya da ma dauriya, domin ita tun asali Zaitun a wahala ta taso...sau kusan uky ana kai Hameeda asbiti ana dawo da ita sbd cutuka da suka tasammata haikan kamar bazasu barta ba, tuni jinin ta ya hau, Ulcer ga zazzafar Maleria sakamakon mummunan cizon sauro da suke sha, yayin da aka kai Zaitun sau daya tak dan itama malerian bai barta ba...dalilin ma kenan da ya kara lalata mata kamanni, in dai ba sanin Zaitun kayi ba bazaka ta6a gane ta ba, sosai ramar ta fito fili.

Tun farko Zaitun yarinya ce kyakykyawa da duban farko idan kayi mata ba sai ka kara ba zaka san cewa ita din kyakykyawa ce.
Wani kyau ne da ita mai sanyi da shiga zuciya, idan kuma kai mata duba na fahimta zaka fahimci cewa komai daya dangance ta me kyau ne, ga tarin nutsuwa da Allah ya bata, in badan muguwar 'kaddara data fa'da mata ba Zaitun mace ce har mace, ta kasance me matsaikacin tsawo, round face mai 'dauke da dara daran idanu, eye lashes mikakku gazar gazar haka suke, fuskar ta na dauke da karamin baki gwanin birgewa...tana da yalwar gashi daidai gwargwado wanda kana iya ganin yanda yake kwance luf saman goshin ta da..sai dai bata cika fari sosai ba.

Yanzu duk ba wannan Zaitun 'din wata ce ta daban zaka gani, wata siririya me tsayi, sbd ramar da tayi fuskar ta dake round ta 'yar koma karama goshin ta ya 'kara fitowa kaitsaye zaka iya kiran ta da me baby face sai hancin ta daya kara fitowa sosai..sai dai ban da ramar a har yanzun ta me kyau ce ita.
Ko a wannan jigila cikin 'yan sanda hare haren masu akuyancin halin da yawa ta tsallake cikin kariyar ubangiji kuma har kawo yau da take Prison 'din basu daina kawo mata hari ba.

*****
Mufeeda kam na can wajen mahaifiyar Rasheed tare da sauran yaran sa, da kyar ta saba zama da su, da fari tasha kuka sosai, da kyar take cin abinci su Zabba'u da su Wildan ne sukai ta kokarin bata kulawa da jan ta a jiki har ta dan saki jiki da su sai dai ba sosai ba, abu guda dake kara ta azzara rashin sakewar ta ya hana ta sukuni shine mage da suke da ita a gidan, Mufeeda bata son mage, jikin ta baya so kuma har zuciyar ta, dan bayan firgici da take shiga idan taga magen, gashin jikin ta ma duk sai ya wani mimmike wani abu rudu- rudu ya fito kan fatar ta kamar gurbin cizon wasu kwari.

Akwai ranar da magen tazo jikin ta Mufeeda ko kuka kasawa tai kawai ta sume a wajen.

Fahimtar abinda ke sata cikin wannan yanayin da Hajiyar Rasheed tayi batare da tunanin komai ba tasa aka dauke magen aka killace ta, dan acewar ta ita ta kar6o yarinyar bai kuma kamata tayi watsi da lafiyar ta ba tunda zama ne na 'dan lokaci zasu yi, ranar da suka rabu sai su fito da abar su ta cigaba da rayuwa kamar da.

Tun da aka killace magen kuwa Mufeeda bata sake shiga wani yanayi ba, sai dai kewar Zaitun da take faman yi duk da kuwa karancin wayo da take da shi hkn bai sa ta mance da ita ba...sau tari ko tana bacci takance" Mammi..!"
Duk sun san wa take nufi dan hk kawai sai dai su tausaya mata, musamman Hajiyar Rasheed da tasan cewa 'dan tane silar koma menene..sosai take tausayawa rayuwar su gaba 'daya.

*****
Ranar da akai komawa kotu ta biyu a ranar idanun Zaitun suka yi arba da Alhaji Jibrin 'dan Maliki, bata yi mamaki ba duk da yake bata wani tsaya kare masa kallo har na sosai ba, amma iya fuskar sa da ta yiwa kallo daya ta fahimci 'yar kama da suke yi da Adam duk da kamar ba wata sosai bace dan yafi 'daukan kamar mahaifiyar sa ne kamar yadda ya ta6a sanar da ita..amma a hakan ma jini ba wasa bane duk wanda ya san Adam ya kuma ga Alhajin zai ga 'yar kama...kenan dagaske mahaifin nasa ne kamar yadda Hajiya Talatu ta ta6a sanar da ita.

Ranar kam Adam Shaheed bai je kotun ba dan bazai iya juran ganin mace mafi soyuwa aransa da wanda yake matsayin mahaifi agaresa bisa tuhuma iri guda ba...bayan duk wani shirin da yayi na taimakon ta ya rushe toh me zai je kotun kuma yy mata ban da karawa zuciyar sa nauyi.

Haka akai ta fafata shari'ar amma ba'a karashe ta ba aka sake saka wata rana daban da za'a yanke hukunci wanda ya kama nan da kwana ki bakwai masu zuwa cewar alkali.

Da yawan mutane basu so hakn ba, hakama wadanda ake shari'ar da su, in ka dauke 'Dan maliki da shi kam dama bai shirya kar6ar hukuncin sa aranar ba, gani yake kamar akwai mafita akwai yadda za'a yi ya zillewa shari'ar batare da hukunci ya hau kansa ba shiyasa yaji dadi sosai da aka dage shari'ar.

Yayin da 6angaren alkali ya kasance yayi ne sbd wasu 'yan bincike da ya kamata a karasar da kuma tabbatar da kwarrarun shaidu.

Da wannan damar Dr Rasheed yayi amfani ya bayyana wata 'dauka daya yi bada jimawa ba, shi kansa a lokacin bai san dalilin yin daukar ba amma haka kawai yaji zuciyar ta amince masa da yi awata zama da sukayi shi da 'Dan Malikin kwanaki kalilan baya...kuma sun yi zaman ne bisa kokarin fadada harkar tasu izuwa ga babban matsayi wanda zai fi kawo musu ku'di maku'dai yayin da ga al'umma kuma zai kasance ne mafi tsananin tashin hankli sai dai Allah cikin ikon sa basu kai ga ida nufin su ba asirin su ya tonu.

Duk shaidar da Dr Rasheed ya bayar tabbatattu ne masu matukar tasiri, shiyasa ma ba awani sha wahalar bin ba'asi ba, dan hatta da sautin murya wadda yake 'dauka ta waya duk suna nan...sai ma wasu muggan halaye na 'Dan Malikin da suka sake bayyana karara wanda ba kowa ne ya sansu ba.

Bakaramar nadama Rasheed yy ba, sosai yy nadamar mummunan zuciya da halayyar sa wadda suka riga suka bi jinin jikin sa batare da ya ta6a tunanin makomar sa ba, yau gashi wannan banzan halin yy sanadin mutuwar dukkan wani farin ciki nasa na rayuwa, ya kuma yi sanadin kashe duk wani walwala da farin cikin ahalin sa, uwa uba kisan mummuke da ya yiwa wata sabuwar ajiya da ya yiwa zuciyar sa da shikan sa bai gama tantance matsayin da yake kai ba.
Ya ci buri ba 'karama ba kan sabuwar soyayyar da ya tabbatar yake yiwa Zaitun ashe duk zasu tashi ne tamkar tashin tsuntsaye ba tare da komai da ya ci buri sun kammala ba batare da guda cikin burin sa ya kai ga cika ba...gaba 'daya komai ya tsaya matsa cak, duk da yasan abu ne mawuyaci Zaitun din ta kar6e shi cikin sauki, but ya jima yana tsara yanda komai zai tafi masa yadda ya dace ashe saka yake yana warwarewa daga baya batare da ya sani ba.

Kana naka ne Allah na nashi, a yanzu kam gaba 'daya ya saduda, ya kuma tabbatar Allah shike da ikon yin duk abinda yk so duk kuma abinda ya ga dama, sosai ya kara jin tausayin Zaitun bayan duk sun ji abinda Hameeda ta fada, domin bata 6oye duk nata shirin ba ta bayyanawa kotu, ita kanta Zaitun tayi mamaki sosai, ashe da hakan be faru bama wata ukubar akayi niyyan jefata a ciki, hakika Allah maji roko ne baya kuma zalunci sai gashi duk 'din su bau tsallake nasa shirin ba.

Bata ji haushin Hameeda ba kamar yadda Rasheed ma bai ji haushin ta ba, wala Alah faruwar hakan shine mafi dacewa ga Zaotun, da badan faruwar abinda ya faru ba, dabadan shirin Hameeda na 6atar da ita 'din suka fito har aka kama su ba kila da tuni ta 6atar da Zaitunan, da tuni ta shafe babin ta a idanun sa, da tuni ta bar shi da tabon zucin da bai san ranar da zai goge agare shi ba.
Da hakan ya faru kuwa wata dama Allah ya bashi, amma ba zai bi kowa da sharri ba, zai yi amfani da wannan damar da sakawa duk din su da alkhairi gwargwadon iyawar sa bazai yadda ya sake cutar da kowa ba...idan ya wanke laifukan su yasan kotu zata sallame su zaku tafi kowa zai yi hanyar sa ne, Zaitun zata rabu da Hameeda ta yadda babu wanda zai sake tunanin cutar da 'dan uwan sa cikin su, ba mamaki rabuwar su ma ta kasance rabuwa ce ta har abada.
Chapter 35 · 0% Book details