← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 218

Sashe 68

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ammi da ke ta gane ma'anar kallon sai tayi saurin fa'din" Kayi ha'kuri nace..da kaina fa na baka ha'kuri Muhammad".
Sake lumshe idanu yayi ita kuma sai ta mi'ke tsaye.
" Allah ya yi maka albarka ya kuma hutar min da zuciyar Baba na...yanzun zan turo a gyara maka wurin ka daina tashin hankalin nan ka kaji".
Kai kawai ya 'daga mata a hankali la66an sa suka motsa ya furta" Thanks Ammi".

Salmerh😘
[29/9/2022, 4:19 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...42*

Kamar yadda Ammi ta fa'da wata ta tura ta gyara masa inda yake kunfar baki akai 'din tamkar dama can shi ke aikin da kansa.

Amra duk bata san me ake ba sai bayan da aka gyara wajen dan 'karshe ma bacci ne me nauyi yayi gaba da ita ta batare da ta shirya masa ba.

Ko da ta fito bata tarar da kowa ba Rayyan ya riga yayi ficewar sa..haushi sosai Amra taji da ganin baya gidan, acewar ta taya zai hana ta fita shi kuma yayi ficewar sa batare ma da ta sani ba.
Ta mance cewar fushi tayi ta shige dakin ta ta barshi shi.

Jin wani jiri jiri yasa ta koma ta zauna tana sakin numfashi 'kasa- 'kasa.
Ammi bata tankawa Zaitun kan maganar ba har sai washegari, nan Zaitun tai mata bayanin komai da ya faru, Ammi bata ga laifin ta ba, sai ma laifin Rayyan da ta gani dan shi ya mayar da abin babba, ta kuma san ba wai laifin Zaitun 'din ne asali damuwar sa ba da alamu dama da 6acin ransa yake tafe Zaitun ta taka sahun 6arawo ne, laifin ta 'daya ta gani martani da zagin da tai masa, ta kuma yi mata fada sosai kan hakan domin tamkar 'diya take ganin ta fadan da zata yiwa su Marwa shi zata yiwa Zaitun, kuma ko ba komai Rayyan ya girme mata bai dace ace ta zage shi ta wannan sigar ba.
Itama Zaitun sai a lokacin da ga kuskuren ta, nan tayi nadamar zagin ta kuma bawa Ammi hakuri da alkawarin Insha Allahu bazata sake maimaita irin hakan ba.

Sosai Ammi taji dadi dan haka nasiha ta 'kara yi mata gami da sake bata damar cigaba da komawa bakin aikin ta.

Duk da Zaitun bata so komawa can 6angaren ba amma Ammin ta wuce haka awajen ta...ta koma amma da takatsantsan fin wanda take yi abaya...duk wata hanyar da zata hda ta da Rayyan a gidan bata binta, aikin ta kuma tana yi yadda yakamata amma tafi sakewa tayi aikin idan ta tabbatar ya fita, hatta 'dakin sa ita ke gyarawa ta sharo ada amma daga baya ya hana yace baya so dole ya tilasta Amra take yi masa iya nashi 'dakin ta sharo kullum wataran ma bata yi sai ya kusa dawowa.

A wannan karon an samu sauye- sauye sosai daga Amra, musamman wajen abinci, Zaitun ta rasa dalili, sam bata san mugunta ke sata yi mata hakan ko kuwa menene ba, amma sai ta hada musu abinci Amra zata ce sam ba shi take so ga wanda take so, wani sa'in ma ko tayi wanin kuma ba kula shi zata yi ba.

Ba 'karamin haushi ke kama Zaitun ba, ta kuma rasa yadda zata 6ullo mata.

Ranar kawai ta yanke shawarar yi musu abincin gargajiya, duk da Raleeya ta ta6a bata labarin yadda suka kwashe da ta ta6a yi musu, mai gidan kadai yaci amma Amra bala'i ta ringa surfa mata kuma bata ci abincin ba.
Amma ganin tsirfar da Amra ta tsiro da shi cikin kwanaki yasa ta yanke shawarar gwada sa'ar ta.

Cikin sauki ta ha'de komai ta kammala ta jera musu kan dinning tana dariyar mugunta ta koma 6angaren Ammi.

Cikin ranta take ayyana ita da su ganta sai kuma gobe, in sun so suci in sun so su kwan da yunwa amma ita babu ma mai ganin idanun ta balle tasha kananun surutai.

Ko lokacin da suka zo cin nasu abincin da dare data tuna da su Amra daria taji na shirin 'kwace mata, bata ta6a sanin ita muguwa bace sai yau.

Tuwon semo ta tu'ka musu da miyar kuka, kukan ma da 'kyar ta samu sai da ta zo kitchen 'din Ammi ta 'dauka.

Ga mamakin ta washegari da taje taga dishes 'din bata ga6a ganin sun ci abinci mai yawan na ranar ba.
Shi kansa Rayyan sai da yayi mamakin Amra dan yafi kowa sanin bata son tuwo amma yau ci na musamman tayi masa.
Har sai da yayi mata daria yana tsokanan ta ko de tuwon Zaitun yafi na kowa dadi ne shiyasa take ci hadda 'kari.
'Yar daria tayi masa sannan tace.." Kai Baby bafa wani dadi, kawai danna taimaka mata naci shine yazam wani abu...".
" Ke de fa'di gaskia...".
" Allah ba wani da'di..ji nayi kawai ina son ci..".
" Hmm"
Yace yana mai cigab da cin tuwon sa.
Zaitun data shirya mugunta sai gashi ta kare da mamakin su.
Bata san shi Rayyan dama asali ma'abocin son tuwo bane samu ne da baya yi ya sa shi hakura, in kuwa ya samu baya yi mata da wasa.

Tun daga ranar da an kwana biyu Amra zata ce da Zaitun tuwo, abun har ya fara isan Zaitun kuma, tace dama bata fara na _daga nuna wa mutum hanya shikenan sai yace ya ga wajen zuwa_ .

Kamar wasa tsirfar Amra sai 'kara yawaita suke yi Rayyan kansa sai da yasa ayar tambaya akanta.

Dama yakai 3weeks da zargin wani abu game da ita, gani yake tana 'kara haske ga boobs 'dinta sun cicciko kuma yasan ita kanta bata lura da hakan ba.

Cigaba yayi da nazarin ta batare da ya sawa ransa sosai ba kawai dai yana fatan Allah yasa hasashen sa ya zam gaskia.

Abinda ma ya 'dauke masa hankali shine shirshiryen tafia Lagos da yake yi, wannan abun yazo masa cikin lokaci guda kuma tafiyar ta gaggawa ce kayane da aka kawo musu ba'a sauke ba aka kama shine zai bi sahu amma ya bari a ransa da zaran ya dawo zai yi mai yiyuwa dan tabbatar da hasashen sa.

Tun daren ranar ya tashi zuwa Lagos bai dawo ba kuma sai da yayi kwana biyar.

Cikin kwanaki biyar 'din nan sosai Amra da Sultan suka samu kansu, sheke ayar su suke bada wasa ba, shi da aka matsa ya dawo sbd kula da ma'aikatar su sai gashi ba wannan ne gaban sa ba, dunduniyar Rayyan yake ci batare da shi ya sani ba.

Kamar kullum yau ma wani dan'kareren 'dakin hotel suke kwance bayan sun gama masha'ar su.
Hannun Sultan kan cikin Amra yana yawo da shi yace " Allah yarinyar nan ban yadda dake ba..kinga canzawar da kika yi Amra..anya kuwa..?r
" Anya me...?"
Ta tambaye shi tana ha'de gira...tayi kokarin cire hannun sa a jikin ta ta mike amma yaki bata wannan damar ki tsaya mana in tabbatar tukunna.
" Wai mene Sultan yake damun ka..?"
Bai daina yawo da hannun nasa ba yace" abubuwa da dama Amra...ke bazaki ta6a ganewa ba..".
Dan ya 'dauke hankalin ta yasa shi yin sama da hannun nasa zuwa saman boobs 'dinta yana sake nazartar ta.
" Ke baki ga yadda wannan abin ya canza ba..?"
" Na gani mana, haka ya gadama..."
" A ganin ko Amrah...?"

" Hakan nema ai."
Ta bashi amsa tana sakin nishin gami da ban'karo 'kirjin ta.
Ganin kamar ta fara daukan wani layi yasa shi komawa yayi mata rumfa yayin da ya maye hannun sa dake kan boobs dinta da bakin sa.

Hannun kuma ya cigaba da shafa shi akan ruwan cikin ta har zuwa kan marar ta.
Yana isar da hannun sa wajen ya danna da 'karfin sa nan yaji tauri awajen.

Wani ihu Amra ta saki tana ture sa...bai yi musu ba ya kyaleta dan ya riga ya cika burin sa.

Sai dai tun 'dauke hannun sa kan cikin Amra tamkar tare da farin cikin sa ya 'dauke hannun.
Nan take yanayin sa ya 'dan sauya.
Bai sake 6ata lokaci mai tsayi ba ya watsa ruwa yayi ficewar sa ya barta a 'dakin.

Sai da ta gama hucin numfashin danna mata mara da yayi kafin ta mi'ke tana dafa bango ta shiga bathroom itama, ba 'karamin mamaki ya kamata ba da jin wannan canjin a marar ta.

Koda ta koma gida kwanciya kawai tayi, banda waya da Rayyan babu abinda ta tsinana shima 'din gaisuwa kawai sukayi tace da shi bata jin dadi yace" shikenan Allah ya 'kara afuwa".
Daga can inda yaken murmushi ne ya su6ce masa.
Har ya kashe sai kuma ya sake 'kira Amra da 'kyar ta 'daga dan haushi bacci take son yi.
Rayyan wata tambaya ya jefa mata.." Banda ciwon kai 'din kina jin zazza6i ne?".
Tace
" A ah bakomai".
" Bacci fa..?"
" Ina ji yanzu haka ma sosai.."
" Abinci fa..?".
Chapter 68 · 0% Book details