← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 213 OF 218

Sashe 213

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Bakomai fa".
" Murya ta ne baki son ji ko?"
Da sauri ta girgiza kanta tamkar yana gaban ta, sai kuma tace" Ba haka bane fa, Mufee ce ta kai wayan can wajen Ammi..shiyasa".
" Meaning?"
" wayan bata yini tare da ni ba.".
Shiru ya dan yi na 'dan sakanni.
Ita kanta sai take jin bugun zuciyar ta na 'kara hauhawa, sake manne wayan tayi da kunnen ta lokacin da ya sake 'kiran sunan ta.
" Ki min alkawari Marwa bazaki sake kuka sbd wani namiji ba?"
Shiru tayi.
" Please Marwa, ki yi min alkawarin bazaki sake tunawa da past din ki har ki zubda precious hawayen ki sbd hkn ba..."
" Hakan abu ne mai wahala Yah Adam..."
" So promise me zaki rage..."
" Insha Allahu.."
" Good girl".

" Ya batun tafiyar ki?...kin fasa din?"
" No!"
" Zan tafi..Yayah ya barni inje..."!
Ta fa'da with full of excitment.
Shima kansa murmushin jin dadi yayi..for once ya fahimci tana farin ciki.. a hankali yace " haba dai?..yaushe ya barki".
" Yanzun nan...".
" Kai dear".
" Dagaske Yayah Adam...yanzun haka ma yana gidan nan.."
" Masha Allah...congratulation my dear, i mean for both of us, nima zan sami sukuni yanzu, amma shine ko a kira a fada min wannan kyakykyawan albishir din..?"

" Ba gashi na 'kira yanzu ba..."
Yar daria yayi
" hakane but wannan kiran ai nasan manufar sa dabanne..."
Tace
" Manufa kuma?...ba komai fa"
" Fadi gaskia madam, nasan kin kira ne sbd kinga tarin missedcall dina, tunanin ki ko wani abin ne ya samu masoyin ki...".
" Wayyo Allah, ni Allah ba haka bane..".
" Toh menene?"
" Kin 'kira ne kiji ya nake, ko na yini lpy ko kuma a a?..ni dama nasan wannan 'kiran 'kauna ce...?"
" Kit ta kashe wayar tana murmushi rungume da wayar a kirjin ta.

Shima murmushin yayi, yana mai sake jin tausayi da kaunar ta na ratsa masa zucia.

Bai ajiye wayar ba sai da ya rubuta sako ya tura mata kafin nan.
Tana cikin murmushin taji karan shigowar sako, ko da ta dago wayar sai taga daga Adam ne.
Da sauri ta bude sakon.
Haka nan kawai sai take jin ta kage da son karantashi.

_If ur love nd emotions get ignored.... do urself a favor nd walk away._

_You're worth so much more than what people have unfortunately made u to believe my Marwa, u ar very special, rare and precious_ .

_Wait to be with someone who cherishes u nd is proud to have u with every day that passes._

_Someone who actually knows ur worth...Someone who is there for u nd genuinely wants to know ur heart's needs nd desires. This is what your life needs Marwa ta._
Marwa ta karantacsakon nan fin sau bakomai amma har a lkcn bata gaji da karantawa ba..haka nan kawai sai ta ji sakon yai mata dadi ya kuma tsaya mata a zucia.

Tun lokacin da Adam ya ga Marwa ya fahimci cewa she is depressed, but bai san meyasa ya kasa tsananta bincika kan hakan ba, ya dai riga yasan Zaitoon bazata ta6a cutar da shi ba kamar yadda yasan bazata bari wani yayi hakan ba, inda wani abu 6oyayye da ya kamata ya sani zata sanar masa.

Hakan yasa bai wani damu sosai ba sai dazun da ya kira waya yana zaton ba a san an 'daga wayar ba ma Allah dai ya nufe shi da jin ka'dan daga cikin abinda ya ke damun ta sannan ya gaskata zargin sa.

Ya dai san Marwa ta ta6a Aure, kuma wanda ta aura din tamkar dan uwanta yake, a yadda labari ya riske shi, kuma sun rabu ne sakamakon shigan sa gidan yari bisa wani gagarumin laifi da yayi.
Toh shi bai damu da sanin laifin ba tunda ba Marwa ce tayi sa ba, kuma bai isa yace ya 'kita sbd hakan ba bai ma da hujjan nuna mata 'kiyayya musamman da ya ke shima mahaifin sa a gidan yari Allah ya 'dauki ransa, in muguwar tarihi ce yasan nashi yafi na kowa.
After all zuciyar sa ta riga tayi na'am da yarinyar dari bisa dari, baya jin zai iya barinta sbd wani dan kalilan din dalili.

Kuma bai 6oye musu batun mahaifin sa ba, duk da Ammi ta riga tasan da batun tun can baya, amma duk da hakan basu 'kyamace sa ba, suka dubi kyawawan halayen sa, suka dubi nagarta da kamalar sa, suka dauki auren 'diyar su da suke ji da ita suka bashi.

Ita kanta hajiyar sa bata yi zaton zasu bashi cikin sauki haka nan ba duba da cewa manyan mutane ne ba na wasa ba, 'korafin da taso yi ma shine wai sbd Marwa bazawara ce amma itama bata ja maganar har na tashin hankali ba.
Ya kuwa ce shi sam ba wannan ne gaban sa ba, ai sunnar ma aiki ce ma dan ya fara da auren bazawara, abin dubi kawai shine hankali da natsuwar yarinya, kuma ya tabbatar Marwa capital A ce ta wannan fannin.

Maganar da yayi da Hajiyar sa cikin natsuwa yasa bata kara jayayya bisa hakan ba, domin ta riga tayi alkawarin bazata 'kara tauye sa ba har karshen rayuwar ta...indai yaso abu toh taya shi son abun zatayi har zuciyar ta...fatan ta kawai shine su kasance alkhairi ga junan su..alkhairi kuma dawwamammiya.

*****
Shirye- shiryen tafia Marwa ta fara yayin da gefe guda kuma ake faman shiryen shiryen biki babu 'kakkautawa.

Kwatsam lokaci guda tafiyar gaggawa ta taso wa Rayyan zuwa Madina batun kasuwancin sa.
Duk yadda yaso akalar tafiyar ta canza abin ya faskara, dole sai shi 'din ne zashi...ko anan ma yayi kewar makusanci ba dan kadan ba.

Shiyasa kwanaki da yayi sha'awan shigo da Bello cikin al'amuran sa bai yi kasa a gwiwa ba ya nemi Bukar awaya kan batun, bai sani ba ashe Adam ya riga yayi masa shigan sauri, bama Bello kadai ba hatta shi Yah Bukar din da kanshi yanzu 'karkashin Adam suke aiki.

Haka ya tarka iyalan sa ya kaisu gidan Ammi, dan bazai iya barin su su ka'dai a gidan nan ba alhalin yana can wata dunia.

Hakan ya matukar yiwa Zaitoon dadi dan tunda aka kawo ta Kano bata ta6a zuwa gidan Ammi ta kwana ba sai dai yini amma wannan karan bama kwana zatayi ba har kwanaki masu yawa..bakin cikin ta daya batare da mutuniyar ta Marwa zatayi wannan zaman ba.

Domin kwanan su biyu da zuwa Marwa ta wuce, tama so tafiya da Mufee amma Ammi tace sam, taje kawai, tunda tare zasu dawo da su Raihanan ai shikenan, kuma ma in ta tafi da Mufee wa zai riqa 'debewa Zaitoon kewa.

Ana gobe zata wuce Adam ya tura mata ku'di 200k tayi tsaraba wa Affan.
Bata so hakan ba dan aganin ta me zata siya masa har na wannan uban kudin.
Shima Adam kawai ya saka wannan kudin ne sbd baya son tayi 'korafin sunyi yawa amma ba abinda yayi niyyan turawa ba kenan, sai dai duk da hakan bai tsira ba.
Kawai sai yayi murmushi...lokacin da tace masa, ai Ammi, da kowa sun siya musu tsaraba ita bata san me zata siya ba kuma.
" Ohh toh kowa yayi nasa sbd ni kuma ban isa ba shiyasa baza'a ansa nawa ba?"
" Ba haka bane".
" toh menene?".
Tayi shiru.
" Hmm" kawai yace ya yanke wayar.
Yasan akwai ciwo a zuciyar Marwa baya so ya rika takura ta kan abu, sbd gudun fama mata miki ko kuma cutar da ita, Marwa na matukar bashi tausayi ba wai dan ta kasance wani abu bu, No, kawai sbd irin abinda kunnuwan sa suka jiye masa, sai daga baya ma da ya matsa sannan Zaitoon ta bashi kaf labarin.
Tausayin kaf ahalin ya zauna masa a zuci, sai da yaji ma ai shi nashi rayuwan bakomai bane compared to nasu.

Wannan tausayin shi ya 'kara habbaka 'kaunar da yake yiwa Marwa, har yake jin tamkar bai ta6a son wani abu a dunia sama da ita ba, shiru shiru ko rashin damuwa da shi din da bata yi sam bai damesa ba, bcuz yasan with time zata yi healing.
Komai dake faruwa ga bawa jarrabawa ce, kuma mukaddari ne, fatan sa kawai shine ya kasance mata haske kuma madogara abin alfahari har karshen rayuwar ta.

Marwa kam cikin tunani ya barta, tasan babu komai da take bu'kata sai dai ta siyan masa tsaraban shi, kamar yadda yace tun farko, haushin kanta ma taji, meyasa lokacin da yace ta tura masa acc din nata bata yi wannan tunanin ba..ko da yake cewa yayi sa'ko zai bata in zata dawo ta siyan masa wani abu da yake so daga can, tayi tayi da shi kuma ya fadi abin kawai basai ya tura kudi ba yace sam, ai fannin kasuwancin sa ne, bai kamata ta siya masa haka nan kawai ba, sbd zai riqa ji tamkar ita yaje wa kasuwanci.

Maganar tasa ta sata daria sosai.
Sun kuwa yi dariyar a tare dukkan su.
Adam ba karamin nishadantuwa yake da irin yanayin ba idan suka tsinci kansu.

Zaman gidan Ammi da ya kama Zaitoon a wannan karan daban take jin sa sosai, a zahiri bazata ce bata jin dadin sa ba, domin babu wani abin arziki da take yi, duk da wani lokacin takan ji sha'awar ta shiga Kitchen wajen masu aikin ta taya su amma Ammi sam ta hana, nan nan take da ita tamkar 'kwai, abin wani lokaci har na bata kunya, ko sau'kowa zatayi a stairs sai tace mata tayi a hankali.
Sam bata bari ta 'dauki Mufee balle ace ta goya ta sai dai tace 'daya cikin masu aikin su goya ta ko wani abin...duk kuma abinda take so taci babu 6ata lokaci ake samar mata shi bisa umarnin Ammi, wani lokacin ma Ammin dakanta zata ce baki bu'katan wani abin ne tace a a Ammi...ita har kunya take ji wasu lokutan.
Chapter 213 · 0% Book details