Sashe 148
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sallama ya shigo wanda yasa ni waigawa da sauri na dube sa, tsaye na mi'ke ina fa'din" Yaah Bukar kaine da wannan lokacin?"
Murmushi yayi yace nine 'kanwata 'dazu nazo ai akace wai kunje gidan Babaji kallon Jinjiri..."
Murmushi nayi nima gami da fa'din" Yaah ai ma bamu da'de ba fa muka dawo gida..."
" Da alamu fa kin ma fi mai jegon farin ciki ko 'kanwata ..?"
'Yar dariya nayi sai yace" eeh mana ai na fahimta, yadda naga wannan fara'ar saman fuskar ki nasan duk ta ganin sabon jinjirin ne, jiya ma fa Ummaru yace min kunje da shi, sai gashi yauma kun koma..."
" Ni dai ina son yaran ne kawai Yaah amma ai gobe bazan je ba..wata'kila ma sai ranar suna..."
Nayi maganar ina murmushi shima yana murmushin yayi" anya kuwa! banga alamar zaki iya ba, munyi sa'a ma da baki tare gidan ba gaba 'daya ai..."
Wannan karon kam dukkan mu dariya muka yi sannan ya zauna daga bakin 'dan gado na na kwangwala dake 'dakin.
Sosai ya dube ni ya kuma.mayar da hankalin.sa kacokam akaina.
Ganin hakan ya sa nayi kasa da idanu na ina wasa da yatsun hannu na.
" Magana fa nazo muyi 'kanwata..."
Ya fa'da yana mai gyara zaman sa.
A hankali na 'dago na dube shi " Toh Yaah ina jin ka..."
Daga haka na kuma mayar da kaina 'kasa.
" Kinga duk yinin yau 'dina ke kadai na barwa shi kamwa ta..har Yerwa na shiga sbd ke kadai, ba dan komai ba kuma sai dan kawai domin neman maki magani..."
Sallayan dake hannu na na ajiye gefe da inda yake zaune daga 'kasa na zauna ina duban sa cikin sanyin yanayin da ya riske ni lkc guda.
Maganin ya fara mi'ka min sannan ya 'daura da fa'din" na samo miki magani da wasu addu'o'i kuma ina da yakinin insha Allahu zaki daina mafarkin nan da kike yi kinji..?"
Kai na 'daga masa da sauri alamar naji ina mai sunkuyar da kaina, dan ni kaina na gaji da wannan mafarkin, sosai na gaji da yinsa.
Bai fito fili ya bayyana min asalin abinda malamin ya sanar da shi ba amma yace da ni...malamin yace duk lokacin da na farka na kuma ga sauyi a jikina ko kuma ba'kon abu kawai nayi wanka saboda gudun kokonto...ai kin iya wankan tsarki ko 'kanwa ta?"
Kai na 'dage masa alamar erh ina mai yin 'kasa da idanu na.
Sai yace" yauwa kanwa ta, to zaki yi amma da niyya daban, niyyan janaba zakiyi ba irin wanda kk saba ba kinji, da iznin Allah komai zai daidaita ki daina ganin kowa a mafarki...akwai wasu addu'o'in da ya bani kuma suma duk zan koya miki su amma kafin nan, ai kin iya su kulhuwallahu ko?"
Kai na 'dage masa alamar erh" karanto min dai inji ko kin iya da gasken babu kuskure".
Yayi maganar yana 'dan murmushi, nima murmushin nayi sannan na fara karanta masa.
Bai ci karo da gyara na ko guda ba, dan haka yace na karanto masa Ayatul kursiyyu..jinjina min yayi fuskar sa yalwace da annuri bayan na karanto yace " addu'an bacci shima kin iya ko?"
Da kai na bashi amsa domin dama gwanace ni wurin 'dinke baki ta zanta da mutum da sassan jiki na.
Bai damu ba sai cewa da yayi" Karanta shima inji..."
" Masha Allah ashe 'kanwar tawa hafiza ce bansani ba"
Haka ya rinka min tambayoyi ina amsa shi wanda ban iya ba kuma ince masa ban iya ba, haka wanda nayi kuskure sai ya gyara min shi, ya kuma ringa maimaita min har kusan sau bakwai kafin idan yaji baki na ya iya ras sai muyi gaba.
'Karshe jinjina min yayi yana mai cika da tsantsan farin ciki yace
" Yauwa 'yar kanwata...daga yanzu ki daina damun kanki kinji, matukar mutum ya ri'ke addu'o'i to insha Allahu babu abinda zai sha masa kai a rayuwa, ya kuma ya dingi ganin dai dai kenan cikin rayuwar sa har illa masha Allah.
Wannan 'din ma ina fatan daga wannan lokacin ya 'kare kenan har g.."
Bai kaiga rufe baki ba muka ga an 'dage 'dan yamutsatatten labilen dake bakin 'kofar 'dakin.
A tare muka kai duban mu wajen nan muka yi arba da Iyami...ranta a ha'de sosai tace" tun 'dazu naji sallamar ka Buba amma shine baka san ka zo ni ka fara gaida ni kaga ya nake ba ka wani zo ka rashe anan ko? Wace uwar take tsinana mk banda shirmen banza da na wofi, kar ka fita hanyar yarinyar nan kaga, wallahi duk mutuncin ku zanci daga kai har ita, uwar ta ma da ya na 'kare da ita anan gidan da 'kyar wallahi na yakice ta ajiki na gashi kaima an 'dauko hanyar hk...ka fito yanzun nan ka wuce gida..."
Daga hk ta saki labilen tana mai cigaba da mitar" Mutane munafukai, dangin azzalumai, wama yasan tushen su wani iri ne, duk ta bi ta mallake min gida yanzu kuma an dawo kan dan ciki na, ni kuwa bazan lamunta ba dan naga abin yana neman yafara zarce iyaka, ina gidan nan amma Bukar ya fara mancewa da ni sai wata banza can dangin mayu..."
Ni dai 'kasa nayi da kaina ban 'kara kallon ta ba, fa'dan Iyami ai inda sabo ya kamata ace na saba shi, dan duk ranar da fa'dan ta ya cika ta sosai take sau'ke min buhunan bala'i akaina har sai ta gaji dan kanta take kyale ni...mahaifiyar tawa ma da a lkcn ba gidan take ba amma bata tsira ba.
Tsaye Buba ya mi'ke da sauri ya bi bayan Iyami yace"..na zata fa kina sallah ne dana shigo shine kawai nayo nan 'din kuma addu'ah ma nake karanta mata saboda matsalar mafarkin da take fama da shi ba komai ba Iyami dan Allah kiyi hakuri...."
" Kai da Allah rufa min baki...wani addu'ah kai 'din ka iya da har zaka koya mata...in kayi wasa ma karshe sai sun zo sun ce kaine mai danne ta cikin daren ai..."
Da sauri ya 'dage kansa ya kalle ta ransa duk babu da'di yace " Haba Iyami, Zaituna ce fa, dan Allah ki ringa gyara kalaman ki kafin ki furta su, ki daina fa'din abu irin wannan ba da haka aka san babba ba..."
" Sai ka koya min ai tunda ni bansan me nake ba, banza shanyayye kawai, ana nuna maka gaskiya kana bau'dewa ni dai wallahi bansan wani iri na haifa ba, ga Khausar nan 'yar yarinya da ita amma tasan ta faranta min tayi min biyayya amma banda kai..ka fice min anan ne ko sai na make ka...".
Ta kai 'karshen maganar da kauce masa ta bashi hanyar barin 'dakin.
Kai ya girgiza sannan ya fara tafiya da sanyin murya yace" Sai da safe 'kanwata kuma kar ki manta sau uku- uku duk zaki karanta kafin ki kwanta kuma ki ringa yin alwala..sauran addu'o'in a hankali zan koya mk daga baya.".
Shiru nayi ban ce masa komai ba illa kaina da na sake du'karwa...
Sai da Iymai taga fitar sa kafin ta dawo kaina tace" Aikin banza..wama yasan ko da kanki kike gayyato abinki kina ta wahal min da yaro abanza...mthhew"
Ta 'karashe da jan tsaki tayi gaba.
Ina cikin wata matsala 'yan uwa, dan girman Allah ku sani cikin addu'o'in ku ko da sau 'daya ne tak.😭
UBANGIJI ALLAH YA KAWO MIN MAFITA CIKIN AL 'AMURA NA, YA YAYE MIN DAMUWA TA🙏
Salmerh😘
[25/12/2022, 11:19 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...84*
.......Ban iya na sake motsawa a wurin ba har akayi sallar isha'i sannan na tashi na kunna 'yar tocilar da Yaah Bukar ya siya min kwanaki ganin 'dakin nawa babu wadataccen haske...to ma gashi batirin duk yy sanyi..yau kuwa ban yini a gida ba balle na tuna na sa su arana su 'dan farfa'do.
A haka na lalla6a na gabatar da sallan ta hasken tocilar na kara sau'ka, 'karshe ma 'daukewa yayi gaba 'daya.
Idanu na lumshe ina ta sake maimaita karatun da ya yi min 'dazun dan kar in manta, a haka na gama dukkan addu'o'in da zan yi na shafa daga haka na hau kan gadon kwangwala ta da babu komai akai face wata 'yar tsohuwar tabarma.
Da hannu na nayi pillow idanu na tsam a wuri guda ina tunanin rayuwa ta gaba 'daya, kwata- kwata bana jin da'din zaman gidan namu a halin yanzu, domin bana samun walwala da sakewa yadda ya kamata, idan an ganni da fara'a cikin gidan nan toh ni da Ummaru me ko Yayana, amma ni da damun sakewa sai dai in bana cikin gidan amma matukar ina gida komai a takure nake yin sa, a hakan ma abin da 'dan sau'ki domin kwana biyu Iyami bata tura ni jeji ba.
Ajiyar zuciya na sau'ke tuno abinda ya faru da ni watanni 'kalilan baya da suka wuce.
Hannu na na kai cikin riga ta kan saman ciki na nake shafawa, bazan ta6a mantawa da 'dan karen wahalar da nasha ba a lokacin da naji ciwon nan..wannan ma Iyamj ce ta tura ni 'debo mata kara a jeji wai na hura wuta, ranar sai na taki sa'a Ummaru yace zai rakani, haka muka tafi muna 'yar hirar mu ni da shi sama...tare muka harha'da karan na 'daura ina shirin 'dagawa sama kafin na 'daga har na kai hannu kenan sai naji Ummaru ya kwalla min 'kara da iya 'karfin sa a lokaci guda kuma yake 'dan jan baya idanuwan sa warwaje yace" Yaah Zaituna maciji...maciji ki matsa..."
Yayi maganar yana mai yi min nuni da inda ya hango macijin.
Da sauri na saki karan na mi'ke tsaye ina mai kai dubana wajen da yake nuna min 'din... ido hudu nayi da macijin nima nan na tabbatar da gaske yake, take nayi baya jiki na na daukan rawa..hannun Ummaru na kama muka fara gudu gudu sosai tamkar ance min bayan mu macijin ke bi, ko ganin inda nake sanya 'kafata ban yi, bamu kuma bi ta kan karan da muka daura 'din ba.