← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 218

Sashe 38

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Kafa'dar ta taji an dafe daga bayan ta tayi saurin 'daga kai sbd tsoro, nan tai arba da Mufeeda, Mufeedan ta rike a hannun wata babbar mace da bata san ko wace ita ba, murmushi take yi da ganin yarinyar amma idanun ta na zubda 'kwalla, yau ga ta ga Mufeeda suna yiwa juna kallon kallo, bayan tsawon wasu kwanaki wadanda suka kasnce mafi tsananin muni daga cikin rayuwar ta.

Hannu Mufeeda ta mika mata tamkar wacce ta tuno wani abin tana fa'din"..Mammi...".
Da sauri Zaitun ta 'dago nata hannayen ta amshi yarinyar da duka ta taho gare ta tana washe mata baki.

Ita canzawar yarinyar ne ma ya bata mamaki sosai, kokadan bata ga abin da zata ce bai yi ba game da yarinyar.
Garin kar6ar Mufeeda ne idanun ta suka yi arba da Zabba'u da Zaleeha tsaye abayan matar, Zaitun sai ta dan kalle su sannan ta dubi matar.

Dukkan su kuka suke yi kuma tasan kukan bana komai bane face na tausayin 'dan uwan su, aikin shai'dan kenan da kuma sharrin biyewa son zuciya, baya ga haka ga shi da yan uwa masu tsananin kaunar sa, ga mahaifiyar sa mace nagartacciya ga innocent yaran sa masu so da kaunar sa amma ya lalata musu sunan ahali...ya barwa yaran sa tabon da har su mutu bazai goge a garesu ba.

_Yah Ubangiji Allah ka raba mu da son zuciya...kasa mufi karfin zuciyar mu cikin dukkan wani tsanani na rayuwa._

Mahaifiyar Rasheed ta nemi su koma gidan su da Zaitun amma taki amincewa, dan ita yanzu ba wannan bane burin ta, taya ma za ai ta iya ra6ar wani daga cikin ahalin Rasheed, sosai ta yadda da kaddara amma bazata sake kuskuren jefa kanta cikin wata damuwar ba, bazata yadda ta bada gudummawar faruwan kuskure makamancin wanda ta tsallake da 'kyar ba.

Dan hk sai tabawa Hajiyar Rasheed ha'kuri, ta bawa su Zabba'u ma ha'kuri dan tasan sune zasu sa Hajiyan cewa ta roke ta, tana san suna kaunar ta amma bazata iya sake rayuwa tare da duk wani abu daya dangance su ba, bazata iya bin su ba.

Sun so takura mata amma mahaifiyar su ta dakatar da su, acewar ta su barta ba dadi tun bata ra'ayi ba dole bane sai ta zauna da su, ita aganin ta Zaitun din ma tayi tunani, domin zama tare da sun din bazai bar abin ya 6ace mata a zuciya cikin sau'ki ba, gara tayi nesa da su.
Ita Zaitun din ma akaran kanta yanzu bata bu'katar taimakon kowa bata so ta sake ra6ar jikin kowa bata bukatar tallafin kowa cikin rayuwar ta, in kuwa ya kasance dole ne toh gara cikin biyu tayi abu da'ya....

Daga 'karshe kayan ta dake leda tun wanda ranar ta fito da su su ta gani sun mi'ka mata ba da son ran su ba, sosai tayi farin ciki da ganin kayan bayan duk gwagwarmayar da ta sha ashe kayan ta nan nan...daga haka sukai mata sallama suka yi gaba tana kuka suna kuka, kowa abinda ke zuciyar sa daban.

Mufeeda dake hannun ta ta sake rungumewa tamkar wacce za'a 'kwace mata ita, dagaske tana jin kanta wata iri ne yanzu, tana jin kamar she is no more that Zaitun da ta sha gwagwarmaya abaya, dole ta canza musu salon rayuwa dole ne ta za6i abu guda cikin rayuwar ta, a yanzu tana jin zata iya fuskantar koma menene ya tunkaro ta, tana jin cikin ranta tamkar bata shakkar kowa..dan haka dole tabi za6in da zuciyar ta tai mata game da rayiwar su.

Jin kamar tsayuwar na neman garar ta ne yasa ta koma ta zauna tana maida numfashi, tana tuno lkcn da irin wannan abin ya fara riskar ta tun bayan da aka kulle su bata iya doguwar tsayuwa sai ta fara jin jiri bata kuma san dalili ba.

Ta kai tsawon mintina biyar a zaunen banda aikin kuka rungume da Mufeedan babu abinda yake yi, tun bayan tafiyar su Zabba'u bata sake 'dago kanta ba, wanda tana yin kukan cike da tausayin kansu, gida take son komawa, amma bata da ko sisi da zata iya 'daukar nauyin su da shi, bata da ko sisin da zata dauki 'dawainiyar su da shi ko da ta koma gidan, toh kuma idan taje gidan wajen wa ma zata nufa?, wajen Yah Bukar..kai ina tsinuwar Iyami fa da ta riga ta anbata...?
Gaban mahaifiyar ta...?...toh auren ta fa?, bata so tayi sanadin kashewa mahaifiyar ta aure..daga karshe dole dai ta sake yanke wata shawara ta daban.

Tana cikin kukan taji an sake dafa kafa'dar ta akaro na biyu, 'dago kai tayi da sauri tana tunanin yanzun kuma wanene kuma menene, tunda wancan dafawar da akai mata Mufeeda ta gani da ta 'dago yanzun kuma fa.

Arba idanun ta suka yi da wata hamshakiyar mata, 'yar gayu da birgewa, babbar mace ce sanye cikin wani tsadaddan lace da mayafin da ya bi tsari da zubin lace din ya tafi da shi, duba 'daya Zaitun tai mata taji bugun zuciya sanadiyyan kwarjini da matar tai mata a idanun ta.
A hankali ta bi hannun da ya dafatan da kallo banda jan lalle babu komai a hannun, sake maida idanun ta tayi kan kamilalliyar fuskar matar dake mata tsugunne gaban ta duk da irin tarin shekaru da gayun da Allah ya azirta ta da shi.

Giran ta duk biyu ta 'dan 'dage zuwa sama..tana bin Zaitun 'din da kallo tace..." Kukan nan ya kasa 'karewa har yanzu...?"
Zaitun bata bata amsa ba illa sake duban ta da take yi cike da mamakin ta, tana so tace ina ruwan ki da kuka na amma bakin ta ya kasa furtawa, bai dade ba take jin zuciyar ta tamkar bata tsoron kowa ashe karya take, sai gashi tun ba'aje ko'ina ba ta karyata kanta da kanta bata kuma san dalili ba, ba mamaki shelarun matar ne, ba mamaki kuma gayun ta, a a ba mamaki dai kwarjinin ta ne da ya cika mata idanu.
Ita kadai take tufka da warwarar ta cikin zuciya, tuno a yanayin yanda matar tai maganar tamkar wacce sanayya ke tsakanin su kwakkwara ya saka ta sake dago idanu ta dube ta daidai lokacin da kai hannu ta kar6i Mufeeda take jikin Zaitun a lafe.

Zaitun bata hana ta ba dan sosai matar tai mata tsananin kwarjini shiyasa ma ta kasa tanka ta.
" Tashi mu tafi..."!
Shine abinda kunnuwan Zaitun suka sake tsinkaya daga bakin matar wanda ta sake maimaitawa ne bayan ta amshi Mufeeda tama 'daukan ledan kayan Zaitun dake gaban ta.

Zaro idanu sosai Zaitun tayi ganin matar ta fara tafiya mata da kaya da kuma yarinya dan ko amsar Zaitun bata jirayi ji ba ta fara takawa, dole Zaitun ta mi'ke ta take mata baya da 'dan sassarfa dan har ga Allah bata san wace ita ba, da sauri da 'dan gudu gudu ta sha gaban matar da niyyar kar6ar Mufee dake hannun ta ta kuma Jaddada mata tambayar inda zata kaisu...amma suna ha'da idanu sai ta ji bazata iya ba sosai nawin matar ya saukar mata ga6o6i har ta harshen ta yai mata nauyi.

'Kasa tayi da idanun nata amma bata bata matsa daga gaban ta ba, tsoro taji ya cika mata zuciya, meyasa ta kasa hanata? me yasa ta kasa tanka ta? anya kuwa, shin da wani irin shiri tazo haka?...murmushi matar da ta gama fahimtar Zaitun din tayi, ta fahimci manufar ta bata da ra'ayin binta ko'ina ne, dan haka sai da ta gyara rikon Mufeeda sannan tace " kina tsaida mu, akwai kuma doguwar tafiya agaban mu fa...".
Sai lokacin Zaitun ta iya bu'dan baki tace.." Hajiya kiyi hakuri, mu ba tafiya zamuyi ba...".
"...Na sani kar ki damu, ke de biyo ni muje sauri nake ina da wajen zuwa ayau 'din wannan shari'ar ce ta 'dauki hankalina musamman ma ke.. dole tasa na taho sbd ke ka'dai..."
Tayi wannan maganar ne tana sake tafiyan da ya sake sanya Zaitun dole bin bayan su ba dan taso ba.

Suna fita harabar kotun kuwa dandazon 'yan Jarida sukai mata caa tamkar dama jiran ta suke....kowa na mika mata tasa irin tambayar yayin da da yawa ke jef mata tambayar yanayin da ta tsinci kanta jin cewa kotu ta wanke su...
Hajiyan nan ce ta yi ruwa tayi tsaki ta hana Zaitun furta komai har suka isa gaban motar ta, Drivern ta yyi saurin karbar ledan hannun ta sannan ya bude mata baya ta shiga tana nuna masa Zaitun da itama dole ta shiga ko dan gujewa tarin tambayoyin 'yan jaridar ma uwa uba kuma ga Mufeeda da aka riga aka shiga da ita.

Mufeeda na ganin Zaitun gefen ta tayi saurin komawa jikin ta itama dake nata burin kenan sai ta rungume abarta da ta lafe luf a jikin ta.

Hajiyar nan sai tayi murmushi ganin yadda duk suka rungume juna da sakin ajiyan numfashi lkc guda kamar wadanda suka dauki shekaru basu ga juna ba.

Cikin wasu mintina suka 6acewa ganin kotun nan, 'karshe ma suka yiwa garin na Bauchi bankwana suka tasamma hanyar Kano, sosai Zaitun ta daina hango komai daya danganci kotun nan, ta rabu da duk jama'a da gwagwarmayar rayuwa da ta fuskanta cikin kotun, ta rabu da Dr Rasheed da kuma Hameeda, ta rabu da Hajjaju me son rabata da 'diyar ta, ta rabu da su Zabba'u da Zaleeha masu kaunar ta da zuciya 'daya, fatan ta shine ya kasance ta bar duk wa'dannan kenan bari na har abada barin nata kuma ya kasance shine mafi alkhairi kuma mabu'din alkhairi ga rayuwar su gaba 'daya.
Chapter 38 · 0% Book details