← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 218

Sashe 105

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta girgizawa Ammin ba tare da ta dube ta ba...da alamun a a.
" Duk da yake ba yau na fara tambayar ki ko nuna miki manufata ba ta son sanin ainihin labarin ki ba amma bazan gaji da tambayar ki ba har gobe har kullum ma har sai zuwa lokacin da zanyi dacen samun amsar 'daya daga cikin tambayoyi na, Allah ya sani ban ta6a nufin ki da sharri ba balle diyarki zama nake da ke da zuciya ta daya, amma na lura ke har yanzu kin kasa fahimtar hakan balle ki iya bambance wanda ya dace da wanda bai dace yasan wace ke ba, duk da hakan zan baki shawara ko dan gaba, ba wai nufina in miki titsiye ba Zaitoon ba kuma dan zan iya tilasta ki ba, but matakin 'kaunar da kk nunawa Mufeedah ya kai matsayin da dole ne adasa ayar tambaya akai, na haifa Zaitun 'yan uwana sun haifa, 'ya 'yan ciki na sun haifa 'kawaye na, ma'kwabtana da kuma sauran mutane, amma ban ta6a ganin zahirin 'kauna da sha'kuwa kamar yanda na fuskanta game da ke da Mufeeda ba, hakan yasa bazan iya ha'kurin ri'ke wannan a zuciya ta ba domin ba tun yau na shiga tsananin kokonta da tunanin sanadin hakan ba, abaya hasashe na yana bani ne akan cewa..mahaifin Mufeedah mutuwa yy ya barki da ita shiyasa kk ha'da 'kaunar da kk yiwa mahaifin ta da nata duk kk nin ka mata su..amma kin ce ba haka ba ne, ni kaina wani sa'in kuma na kanga kamar ba hakan ka'dai ne zai saki yiwa Mufeeda irin wannan 'kauna da sadaukarwar ba..shin Zaitun bakya tunanin akwai mutuwa da zata iya raba ku watarana ne? Bakya tunanin akwai wata kaddarar ta daban da zata iya raba ki da ita..?
ban miki fata Zaitun amma kiyi tunanin irin halin da 'dayan ku zai iya shiga idan mutuwa ta gitta tsakanin ku..."
" Kuka sosai Zaitun ta fashe da shi a fili ta furta " " Ammi...!"
Sai kuma tayi shiru illa kukan daya ci 'karfin ta, ji tayi gaba daya zuciyar ta ta cunkushe.
" Idan na 6ata miki kiyi hakuri, but u need to no this bcuz ke yarinya ce 'karama, baki san me duniya take ciki ba baki san manyan 'kalubale da ke cikin rayuwa ba, matukar kika kasamce uwa dole ne ki koyi hakuri, juriya kawar da kai da kuma natsuwa...akoda yaushe ki rika ji aranki cewar wanda ya baki 'da ko 'yar zai iya raba ku duk lokacin da yaso, kuma ba lallai ne dama ku taso atare ba, baki duba marayun yaran da iyayen su ke barin su tun basu san kansu ba amma cikin ikon sa sai kiga sun taso cikin kulawa da gatan da ko iyaten su albarka, har kullum kisa aranki cewar dake ko ba ke dole ne watarana Mufeeda zata yi kuka, zata yi rashin lafiya, zata rayu inda babu ke tunda dole ne ki kaita makaranta, karshe dole ne 'dayan ku zai iya mutuwa ya bar 'daya a lokacin ya zaki ji bayan kin gama sawa aranki cewar kina tare da ita, kin manta cewar mutuwa zata iya giftawa ko kuma itama kin gama dasa mata hakan aranta ki 'kiyasta kiji yadda zaku tsinta zu'katan ku..."
Kuka sosai take da hawaye
"...Wallahi Ammi ban ta6a mantawa da mutuwa ba, taya ma zan iya mancewa da ita? ta yaya? mutuwar ce fa Ammi, mutuwar ce sanadin komai...."
Ta fa'da ne tana me 'kara sakin kuka tare da du'kar da kanta ga dukkan alamu abubuwa take tunawa, abubuwa masu zafi masu tsayawa a zuciya.."
Kai Ammi ta girgiza cike da alhini ta ce" na sani, dama nasan bazai wuce hakan ba Zaitun, da kaina na fahimci ciwo da zogin mutuwa ma'kare cikin zuciyar ki da yake saki zafafa abubuwa harma ya hana ki ganin wasu abubuwa ba'a daidai da yadda suke ba..sai dai yanayi da 6angaren mutuwar ne ban san daga wani kusurwa bane, duk da hakan zan ro'ke ki ki sassauta Zaitun ki sassautawa zuciyar ki abinda yake damun ta..ba ina nufin kar ki 'kaunaci 'diyar ki ba ne amma ki sassauta hakan kar watarana ya muku illah, mutuwa tana kan kowa kuma kowa zai 'dan'dane ta, kin ganni nan badan tawakkali da na sanyawa raina ba da yanzu ba wannan zancen ake mk ba Zaitun da sai dai abaki tarihina, domin ni.m naga mutuwa ganin idona, naga mutuwa daki daki da ba kowa Allah ke jarrabta da irin hakan ba amma dana fawwalawa Allah na mika masa kukana ba gashi yanzu nima ina rayuwa ta cikin farin ciki ba, ba abinda ya rage tsakanin mu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya illah addu'a.
ki sassautawa ranki kema ki kuma sassauta kaunar da kk yiwa yarinyar nan ki daina nuna ta a zahiri ba dan komai ba sai dan irin hakan, wani ma da wannan damar zai yi amfani ya cutar da dayan ku, yayin da wani haka siddan babu gaira babu dalili zai iya jin tsanar ki ko 'diyar kin cikin ransa, akwai masimu mu mgun baki, akwai masu kambun baka duk suna daga cikin mutane masu sharrin da a kullum muke neman tsari da su, sannan dole ne mu kiyaye faruwar wasu abubuwan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo".
...Kuka sosai Zaitun ta ke yi mai ta6a zuciya, hakika ita ka'dai tasan inda kukan ta ya dosa, ta fahimci babu wanda zai iya fahimtar asalin zuciyar ta ko inda rayuwar ta ta dosa sai ita kadai, kamar dai Ammi, ta fahimci tunanin ta daban ne..tunanin kukan mutuwa take yi na mahaifin Mufeeda ko wani abu daban..." Ammi ni kam mutuwa kyauta tai min, kyauta mafi soyuwa a zucia, domin mutuwa ta bani yarinya, ta kuma bani ita ne a gabar da ni kaina ban tsammaci hakan ba, hakika ina jin ciwon mutuwarm har cikin zuciya ta ina kuma godewa Allah kullum bisa kyautar Mufeedah da ya bani wanda hakan shi ya rinjayi komai a zuciya ta cikin duniyan nan...."

Cikin ranta ta ayyana hakan wanda a fili banda kwalla babu abinda zaka gani saman fuskar ta.
Ammi kam idanu ta zuba mata tsawon wani lokaci.
Sannan ta dafa kafa'dun ta a hankali ta 'kira sunan ta.
Zaitoon..."
'Dagowa tayi ta dubi Ammi sabbin hawaye na sake gangaro mata.
Ammi kai ta girgiza, sosai ta kwa'daitu da son jin labarin Zaitun...sosai ta 'kagu taji wani abu daga cikin labarin ta koda da yanki ka'dan ne...domin burin ta na gaba shine sada ta da mahaifan ta, cikin abinda ya gaza wata guda zuwa biyu take so ta sada Zaitoon da mahaifan ta, sai dai zata ro'ke su alfarma su bar mata ita ta cigaba da zama tare da su bayan ta tabbatar komai ya dai- daita tsakanin su...amma duk hakan bazai faru na har sai ta san menene dun'kule cikin rayuwar ta domin tasan ta inda zata fara tunkarar lamarin dama iyayen ta gaba daya.

"..Shin laifi ne idan kk bu'de min zuciyar ki kk sanar da ni labarin ki Zaitun? zan so jin asalin tarihin rayuwar ki da kuma dalilin rabuwar ki da ahalin ki tsawon lokacin da ni kaina bazan iya 'kiyasta shi ba...nai mk alkawari zan kuma sake tabbatar mk, daga yau daga yanzu na mk alkwari bazan sake tambayar ki ba matukar baki sanar da ni ba..kuma ba zan ji haushin ki ba ko da baki sanar da ni din ba sai dai nasan sam bazan ji dadi bane kawai...

" Shin rabuwa kuka yi da mahaifin Mufeeda...ina nufin saki ne ya shiga tsakanin ku ko mene..?"
A hankali Zaitun ta 'dago idanu ta ta sau'ke su kan fuskar Ammi..idanun ta na cikowa da hawaye tace " Ammi ni fa ban ta6a aure ba kawai Allah ne ya bani ita batare da na tsamman ta ba..".
ta 'karasa maganar tana mai 'kokarin shanye kukan ta dan kar ta tona asirin zuciyar ta.
Shiru Ammi tayi tana duban ta da mamaki domin ta fahimci kamar bata son tunowa da incidence 'din ne..sai dai mamakin ta bai tsaya nan kusa ba can ya tafi wani wuri daban..
a fili ta fahimci manufar maganar tata, babu mamaki wani ne ya yaudare ta kenan ya ra6e ta har yy sanadin samun cikin ko kuma ta hanyar fya'de amma a zahiri da ka ga Zaitun kasan mutunci da kamala sun wadace ta, da wuya ta iya banzatar da rayuwar ta sai dai sanadin da yazam mata dole kamar yadda a kullum take gastata tunanin ta.

Wannan dalilin ya sanya Ammi sake jin tausayin ta cikin ranta..sosai ta 'kudurtawa ranta binciko gaskiyar lamarin wanda take fatan ta jishi daga bakin Zaitun ka'dai domin zata fi yadda sosai ta yadda da ita.

" ...Allah ya rufa asiri toh.."
Shine kawai abinda Ammi ta furta bayan fahimtar Zaitoon bata shirya bata labarin ba.
" tashi 'kira min Marwa ku dubo min Amrah da jikin ta, tun 'dazun tana raina wlh...."

Ammi tayi maganar batare da ta dubi Zaitoon ba illa juya cokali da take cikin fruits salad 'dinta da har sanyin sa ya tafi.

Sai da Zaitoon ta tashi kafin Ammi tabi bayan ta da idanu, bata san meyasa take kaunar Zaitoon 'din ba sam, haka nan kawai take jin ta aranta tamkar 'diyar da ta haifa amma yarinyar har yau ta kasa sake jikin ta da su.

*****
Tsaye ya mi'ke yana cusa hannun sa cikin sumar kansa, gaba 'daya lissafi ma ya 'kwace masa, meyasa Anty Madeena ta matsa har haka ne...?"
Kai kawo yake yana jin kansa na juya masa...
Duban sa ya mayat gareta yace" Anty haka nan kawai sai mu 'dauki 'yar mutane mu kai hospital dan kawai muna zargin wani abu da ba lallai ne ya kasance gaskia ba...?"
" Ka manta me nace ne Rayyan?...zamu yi ne domin tabbatar wa da kuma gudun kokonto, idan muka tabbatar da zargin mu ba gaskia bane ba shikenan hankali ya kwanta ba, amma for now ina tabbatar maka da cewa dole ne fa sai anyi gwajin nan...".
Anty Madeena ta fa'da babu wasa saman fuskar ta.

Kai kawon ya cigaba dayi yana tunanin wata mafitar bayan wannan...tuno wani abu ya sanya shi 'dage giran sa sama duk biyu.
Chapter 105 · 0% Book details