Sashe 143
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shafo kanta tayi daga gaba zuwa baya, sai kuma.ta 'daura hannu aka take ta kuma sauke shi...a hankali ta girgiza kanta hakan bai mata, sai ta sake girgizawa da karfi wai ko zata farka daga baccin da take yi abanza,...sake mintsinin saman hannun ta tayi still Rayyan take gani yana kuma duban ta yake yana jiran amsar ta duk cikin yanayi guda, yanayin da ya kasance iri guda da wanda yake mata maganar, idan kuma ba 'karya idanuwa da kunnuwan ta ke mata ba, Rayyan ne! Rayyan ne ke cewa mufeedan ta 'diyar sa ce, mufeedan ta jinin sa ne, Mufeedan ta 'diyar sa ce da matar sa ta haifa masa...."
Kusa da shi ta matso ta shafa fuskar sa nan ta tabbatar shi'din ne dai ba wai gizo ba ba kuma mafarki ba..." Mintsine ni dan Allah ko zan farka..."
Tace da shi with serious tune tana mai mika masa hannun ta.
Maganar ta sai ma ta bashi daria, gefe guda kuma tausayin ta bashi sosai, hakika dole abin yai mata bazata domin baya tunanin ta ta6a kawo faruwar hakan cikin ranta, dama ba yau yasan mashirmaciya bace Zaitoon..amma shirmen yau 'din tausayin ta ya dasa masa a zuciya.
Bai yi yadda tace 'din ba sai ma ziro 'kafafun sa da yayi zuwa 'kasa.
" Baki yadda ba ko..?"
Shiru tayi tana duban sa sosai, ashe tayi wauta sosai, meyasa tun farkon fari bata hasaso faruwar irin ranar nan ba, tunani take yi cikin ranta, ta jima tana ganin kamannin wasu 'dai'daikun halittu tsakanin Mufeeda da shi sannan wannan ba'kin da take gani a gefen cikin sa tasan irin na Mufeeda ne, amma ai babu yadda Allah baya ikon sa, taya kai tsaye zai wani fito yace Mufee 'diyar sa ce batare da wata hujja ba, meyasa tun farko bai fadi hakan ba sai yanzu, sai da yaga 'diyar ta ta zama mutun sannan zai shigo da wani zance na daban, wa ma ya ce masa ba itace ta haifi Mufeeda ba da har zai ce 'diyar sace..?"
Kar dai wayo zai mata ya 'kwace mata yarinya.
Hawaye ne ya sakko mata...shar shar.
Tana shirin share hawayen ya rike hannun ta.
Kai ya girgiza mata idanun sa cikin nata.
" Kiyi kuka kinji, kiyi kuka bazan hana ki ba kema bana so ki na hana kanki, kiyi kuka ki 'koshi har sai kokonto da tararradi ya bar ranki domin zance na babu gyara..magana ta hakikan ce...kuma yanzun nan zan tabbatar miki da hakan.
Hannun ta da ya kama yaja yayi gaba dole ta bishi a baya can 'dakin ta suka koma dake nan 6angaren Ammi.
Da shigar su 'dakin nata ya saki hannun ta.
Wancan drawer da kayan Nadia ke ciki ya lalu6o key ya bu'de ya ciro duk kayan da ke ciki.
Da6as ta zauna gaban tarin kayan sakamakon hango. wani hoton da tayi.
Hannu tasa da rawar jiki ta ciro shi tana mai goge jikin sa ta 'kura masa idanu.
A hankali hawayen ta ya cigaba da sakkowa tana shafa saman hoton...
Rayyan idanu ya 'kura mata yana lura da yanayin ta sosai, akwai rudani rikici gami fargaba gami da tsoro duk tattare da ita a halin yanzu, hakan kuwa shi ke sake alamta masa dakwai wani abu da bata san tunowa da shi, sannan akwai wani abu da bata so kuma bata shirya faruwar sa ba a halin yanzu....
Kai Zaitoon ta fara girgizawa tana kuka take kallon sa.
" Ya akayi...?"
Rayyan ya tambaye ta yana mai matsowa kusa da ita.
Kai tayi saurin girgizawa tana fa'din" ba Komai..."
" Kukan fa...?"
Baya ta 'kara ja da sauri tana fa'din..." Wannan matar..! Na santa fa...wallahi nasan matar jikin wannan hoton...?"
Wani sanyi yaji har zuciyar sa.
A fili ya saji ajiyar zuciya.
Dad'in yarinta kenan babu 'karya a lamarin su.
Yana duban fuskar ta yace
" Mata tace ita..I mean itace matata ta farko....".
Baki Zaitoon ta toshe da hannun ta 'daya tana duban fuskar sa sosai.
Gani yayi tamkar bata yadda da zancen sa ba duk da kuwa ya fahimci ru'dani ta shiga.
Hakan yasa ya lalu6o hotunan Nadia da yawa ya zube a gaban ta.
Zaitoon kam banda hawaye babu abinda take yi tana ''da'd'daga hotunan a ru'de.
Gani take tamkar cikin mafarki take ganin hoton Hajia a fa'dar ta.
Ko da ya sake yin hakan ma gani yayi still bata yadda cewar matar sa ce ba, hoton sa dana matar ya sake nuna mata na lkcn auren su da bayan auren da kuma wanda suka yi su uku hadda Amrah, duk yaga alamun bata yadda ba har a lkcn, photunan su wanda tun suna makaranta yata nuna mata dake cikin wayar sa harda ma wanda yy ta mata lokacin da take da tsohon cikin ta kafin ta rasu, wasu pic din tare suka yi da shi, wani kuma a bedroom 'din sa ne bata gane kayan cikin dakin ba dan ba wannan gidan bane..
Kuka ta sanya sosai ta tana mai toshe bakin ta, da gudu ta tashi ta kama hanyar waje sai kuma ta sake dawowa ta kwashi pics 'din da gudu ta nufi wajen Ammi dake can saman ta da su tana kuka ta zube agaban ta, shima da ya biyo bayan ta tsayawa yy hankalin sa a matu'kar tashe domin da farko bai san ina ta nufa ba.
Ita kanta Ammin sun bata tsoro a yanayin da suka shigo mata..." A a laifia nagan ku haka...?"
Tayi maganar tana 'kare musu kallo.
Rayyan bai ce komai ba illah takawa da yayi kusa da Ammi ya zauna yana sakin numfashi.
" Ammi kalli ki gaya min dan Allah wacece wannan?"
tana kuka ta tambayi Ammin tana nuna mata photon dake hannun ta, su biyu ne jikin photon ma enlergement mai kyau da aka yi, gefen ta Rayyan ne suna dariya aka dauki photon.
Ammi kam jikin ta sanyi 'kalau yayi, kallon photon tayi ta 'dago shi sannan ta 'dago ta sau'ke idanun ta akan Rayyan da yake can tsaye.
Jinjina mata kai yy alamun ta sanar da ita...Ammi ita duk zaton ta kishi ne ya sa Zaitoon irin wannan rikicewan...bata 'karasa tunanin ta ba taji muryar Zaitoon na sake fa'din" Ammi dan Allah kar ki 6oye min ki fada min komai..."
Ta 'karashe da shasheqa.
" Ki kwantar da hankalin ki Zaitoon, ki nutsu ki share hawayen ki sai na sanar dake duk abinda kk son ji yanzu".
Kallon Rayyan tayi tace " Babana sam baka jin magana, me yasa zaka tunzura ta har batun Nadia ya shigo bacin kasan bama ta raye...shi kishi bb inda baya ratsawa ..."
" Hannuwan sa duk biyu ya 'dagawa Ammin yace" Ba batun ba kenan fa Ammi ni babu ruwa na...gaskia kawai na fa'da mata, kuma ai ko hauka nk kinsan bazan aikata abinda kike tunani ba Ammi.."
Ga Zaitoon Ammi ta dawo da kallon ta sannan tace" Kinga wannan da kike gani gefen san ko..matar sa ce.. wacce suka yi makaranta tare bayan sun gama sai suka yi aure, ita ta kasance za6in sa ne Amrah kuwa za6in mahaifin sa ne...
Amma Nadia ta da'de da rasuwa kusan shakaru uku kenan yanzu..."
Da sauri Zaitoon ta jefa mata tabayar
" Ammi a ina ta rasu dan Allah..?"
Hawaye Ammi ta share da ya ziraro mata tuno wace Nadia tace" Nadia ta rasu ne acan Jahar Borni can wani 'kauye da ni kaina bazan iya tuna sunan shi ba, ganin iyayen ta taje tsautsayi ya rutsa da ita har ta rasa ranta ita da abinda ta haifa..."
Hawaye sosai Ammi ta share sannan ta cigaba da fa'din" Nadia mutunce harda 'kari Zaitoon, ni kaina na shaidi halin ta wanda sai daga bayan auren su ma naga rashin amfanin sashi ya auri Amrah da muka yi tun farko, domin Nadia ta cike duk wani gurbi da ya kamata ace mace ta gari ta cike shi a gidan mijin ta..Ina da tabbaci ko da ace tana raye ya aure ki Nadia bazata taba 'kalubalantar ki ko kishi da ke ba balle ace ma bata numfashi..."
" hmm Allah sarki, Nadia ta tafi mana da duk wani buri da farin cikin mu, ta tafi da tsohon cikin ta da haihuwar sa zai iya kamawa a koda yaushe amma ajali ya riga ya 'kira ta hakan yasa duk yadda aka so fahimtar da ita abin bai yi tsari ba bata saurare mu ba, muna ji muna gani ta tafi tafiyar kwana 'daya tayi amma 'karshe hotunan gawar ta ne cikin mummunan yanayi ya dawo mana gare mu..."
Kuka sosai Ammi ta sanya hk Zaitun ma da tuni ta ta rarrafo ta rungume 'kafar Ammin tana kuka.
Cikin kukan tace" kiyi ha'kuri, ki bar kukan nan dan Allah ki warware min komai, wacce ta bani amanar Mufeeda sunan ta Nadia Ammi, tace min ita 'yar Kano amma ban san ina take nufi a Kano ba, Ammi kiyi saurin fahimtar dani cewa Feefy na babban matsayi ne da ita ban sani ba, Ammi ki gaya min menene silar mutuwan Nadian ku dan Allah..."
" Harbi Zaitoon...Harbin ta akayi daga ita har yaron da ta haifa...nayi kuka sosai, nayi kuka fili da zucia domin Nadia ta kasance ne abin alfahari, dole ayi kukan rashin ta, bacin haka ma sosai gidan nan muke da kishirwar yara da Allah ya bata kuma sai ya kar6i abinsa nan take batare da mu ya nufe mu da ko da kallon abinda ta haifa ba..."
Dukkan su kuka suke yi...sosai amma Banda Rayyan, sai shi kansa idan ka dube shi zaka fahimci baya cikin yanayi mai da'di, tuno abubuwa da dama yake yi, hawayen ma ji yayi yana shirin zubo masa sai dai bai bar hakan ya faru ba...gaban su ya 'karaso zai yi magana Zaitoon ta riga shi da fa'din.
" Ammi ki kwantar da hankalin ki indai wannan ta jikin hoton ita ce Nadian ku to ina tabbatar miki da cewar har yanzu jinin Nadia na tare da ke Ammi... domin Mufee na 'diyar ta ce, itace ta bani amanar ta...."!