Sashe 135
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko dare sai da ya shigo duba ta kafin ya kwanta bacci, anan sai yag kamar ya bayyana damuwar sa akanta da yawa kar taga kamar wani abin ne daban.
Harcya juya zai fita sai kuma ya waigo, bai yi mamakin kama ta da yayi tana kallon sa ba, yasan dole sai anyi hakan..." Kallo na kike..?"
Yi tayi kamar bata jisa ba, me kuma yake so ta fada masa bayan ya ganta ta tana kallon nasa... Kar fa kiyi tunanin wani damuwa nayi dake kema kice zaki kwatanta musamman dan kinga ina ta zuwa duba ki, badan komai bane face dan naga baki da lafia ne, sannan ni ba mugu bane, na kuma san hakkin na kusa da ni, bayaga haka ma rama taimakon da kikai ta min nk mk ba komai ba...kin fahimta...?"
Shiru tayi tana juya kanta gefe gami da kwantar da kan jikin gado.
'Kasa kasa tace.." Toh dama ni yaushe nace mk bani da lafia..."
Sarai ya jita amma bai ce komai ba, baya son jan maganar ne, dan haka sai kawai yayi murmushi ya juya yana mata fatan samun lafia.
Bata ce da shi uffan ba har ya fita ya ja mata 'kofar.
Tunani take ta inda ta gaza, shin addu'o'in ta ne suka rauna ta ko kuwa ta kuskure ne..tasan bata wasa da yin addu'o'in ta tun bayan da Yayan ta ya koya mata su, bata ta6a yin sake akansu ba dai- dai da rana guda kuma Alhamdulillah ta ga fa'idar su...
Kasa yin wani baccin tayi kawai tayi tsam da ranta tana tunani, rayuwar ta na can can baya ke dawo mata, tun da da jimawa irin wannan abun ke faruwa da ita ta sani, amma bata san meyasa na yau 'din yafi tsaya mata arai sosai ba, bata san meyasa yafi ba'kanta mata rai fiye da baya ba, shin ko dan ta jima ne, ko kuwa dan ta 'kara wayo fiye da baya ne, sosai taji zafin wannan lamarin musamman da yake ciwon da take ji a jikin ta ya matu'kar bambanta da na baya...har bata san tuna kalar mafarkan nata na baya, ada idan ta farka tana iya tuna komai da ya faru da ita, sa6anin yau da sam ta kasa tuna komai.
Duk yadda ta zurfafa tunani ta kasa tuna daidai da 'kwayar zarra cikin mafarkin nata.
Sanin da tayi cewar bata da mafita, bata da me zama ya fahimci matsala ko damuwar ta ya sa ta watsar da komai, ta cire komai a ranta ta cigaba da hul'do'din ta aganin ta hakan shine kawai mata mafita musamman da yake bayau ne ka'dai ya fara faruwa ba, inda ta sabo ta riga ta saba.
Kawai shawarar da ta bawa kanta shine zata sake tsananta addu'a ta kuma barwa Allah komai, domin tasan duniyan Allahn shine gatan ta ta ko wani fanni.
Ba'a da'de ba Marwa ta shigo gaishe ta nan ta tatar da ita tana aiki..tayi mamaki 'kwarai da gaske.
" Wai mara lafiyar kenan...?"
'Yar murmushi tayi kawai ta fara gaida Marwa.
" Na fa warke kawai dai karfin jiki ne bana da shi sosai..."
" Toh...banda abinki Zaitoon ba sai ki samu ki huta ba, shi Yayan yace kiyi aiki...?"
Da sauri ta girgiza kanta.
" Allah ya ke de Allah ya shirya ki...sai kace dole...da lafiyar kinyi babu lafiyan ma bazaki huta ba, dan Allah muje waje..Fa'iza zata zo ta karasar da aikin..."
Da haka Marwa ta jata suka koma 'daki...sun dade tare kafin Marwa ta tafi dan har Mufeeda ta dawo ma kafin tafiyar ta.
Ammi ma da kanta ta shiga ta duba su ita har Rayyan din.
Zaitoon duk sai take jin kanta a takure sosai, bata sake bari an yi mata kallon marar lafiya ba sbd san rufe sirrin rayuwar ta washe gari ta tashi tsab da ita, dan tayi magana da Marwa akan ciwon da jikin ta ke mata Marwa tace ki gasa jikin ki da ruwa me 'dumi zai rage mk zazza6i kuma zaki fi jin 'karfin jikin ki...
Marwan ce ta 'kara da fa'din" ai ruwan zafi yayi yana da matukar amfani sosai..."
Da kanta ta tsinta wani abu cikin kalaman Marwa kawai tayi ta amfani da ruwan zafi ta kuwa ji dama dama..da yamma ma Rayyan ya bata magani yace mata na zazza6i ne tasha so washe garin rass ta tashi kamar ba ita ba.
Nan ta 'daura rayuwar ta ta mance komai duk da yana nan aranta amma bata yadda ta bashi wani 6angaren cikin lokutan rayuwar ta ba.
_Bayan kwanaki biyar...._
Tana 'daki tana tunanin sai yaushe ne za'a tsinke igiyar auren da aka 'ka'kaba mata tunda kam ya samu sau'ki ba laifi, tasan shi da kansa ma a karin kanshi ba barin auren zai yi akan sa ba dile zai tsinke shi in dai Rayyan da ta sani ne, amma wace rana? yaushe ? Da kuma wani lokaci duk bata sani ba...
Tana zaunen taji 'karar landline dake 'dakin..a hankali ta kai hannu ta duba babu abinda take fahimta, dan haka sai ta sada shi da kunnen ta kamar yadda taga ahalin gudan ke yi, da sanyin murya tace" Hello".
" Ki sameni yanzu".
Taji muryar sa yace hakan sai dai kafin tayi wata magana ya kashe wayar.
Doguwar rigar ta sanya ta na'de mayafin rigar akanta sannan ta nufi 6angaren sa, zaune ta ganshi gaban mirror yana shafa mai a hankali kamar baya son yi, cikin ranta tace wannan fa dama da alamu mugun son jiki ne da shi, sai ya ringa wani lalla6a jikin sa tamkar mace...cikin ranta ra furta hakan tana daga inda take tsaye dan ko sallamar da tayi bata ji ya amsa ba.
Tana nan tsaye har ya gama da mai 'din ya taso..bai ko kalli inda take ba ita kam ganin ya taso ya sata saurin fa'din" Ina kwana..".
kallo 'daya yy mata kawai ya 'dauke kansa.
Kayan da zai saka ya warware yana dubawa, su ma 'din da 'kyar ya waro su sbd yau hannun nasa ya matsa sosai, dama ita ke za6ar masa kayan kuma kusan sati kenan rabon ta da zuwa yi masa wani abin, Da can Amrah ke masa komai kuma yanzu bata nan.
Ganin zai saka kaya ya sanya ta saurin 'dauke kanta tayi 'kasa da shi.
Sai da ya sa dogon wandon sannan ya 'dau rigar ma ya sanya gaban mirror ya tafi ya ya zauna duk wannan batare da yace da ita uffan ba.
Ta cikin madubin ya gama 'kare mata kallon da ya kwana biyu bai yi mata irin sa ba, sosai yaga ta canza masa shirun ta ya 'karu, 'yar sha'kuwar da ta shiga tsakanin su ma yanzu duk babu ita.
Ta cikin madubin suka ha'da idanu sai yayi mata alamun tazo, a hankali ta 'karasa ta tsaya daga bayan sa.
Comb ya mi'ka mata yana shafo kansa, ko bata tambaya ba tasan me yake nufi dan haka sai ta matsa a hankali ta fara taje masa gashin har ta gama tajewa bai yi motsin kirki ba, mayukan da yake shafawa akan nasa ya 'dauka ya mi'ka mata ta kar6a ta shafe masa a hankali cikin natsuwa kamar yadda taga yake yin abubuwan sa tun ba yau ba.
Bata zaci har a yanzun hidimar sa bata 'kare ba sai da taga ya juyo mata gaban rigar sa da alamu botiran yake so ta sanya masa.
Idanun sa ta kalla sai ya 'dan 'kan'kance nasa bashi kuma da niyyar furta kalma ko guda.
Hannu ta kai ta 6alle masa botiran daga 'kasa zuwa sama, Turarunkan sa ta 'dauka tun ma kafin ya bata umarni dan tasan itan ce zata yi, bata ga alamun yau 'din yana da niyyar yiwa kansa komai ba.
Haja ta ringa feshe shi da su kamar zasu 'kare ko zai ce wani abu amma bai yi magana ba illa ido da ya zubawa fuskar ta ita kuma ta'ki yadda ta ha'de ido da shi.
Da kanta ta gaji da fesawan ta ajiye tana girgiza kai gami da jinjina al'amarin sa cikin ranta, mugun son 'kamshi ne da shi na masifa, shiyasa ko da yaushe idan ka ha'du da shi 'kamshin sa ke fara ziyartar hancin ka kafin kayi tozali da shi....
Bai 'kara komai daga shirin da tayi masa ba kawai ya sake duba jikin sa cikin madubi sai ya saki murmushin da bata san na menene ba..sai dai a zahiri yayi mata kama da na jin da'di.
Kanta a 'kasa bata sake duban shi ba, ganin hakan yasa shi ha'de yatsan sa ya murza suka bada sautin 'kara.
Da sauri ta 'dago ta dube shi, dama manufar sa kenan, so yake ya ja hankalin ta ta dube shi.
Da hannun sa 'dayan ya yabi jikin sa...sannan a karo na farko tun shigowar ta ya bu'di baki ya tambaye ta..." How do i look..?"
Murmushi ne ya kwace mata ganin yadda yayi 'din hadda gyara tsayuwa yayi.
Babban yatsanta ta ha'da da na kusa da shi ta 'dago masa alamun Superb...ya kuwa ji da'di sosai hadda blowing mata kiss.
Hakan sai ya sata
...Shirgin sa kawai ya 'diba yy waje abinsa ya bar ta da kwalbar turare a hannu.
Mamakin sa sosai ya kamata, dama dalilin 'kiran kenan? Kuma ma ba sannu bare na gode kamar ya samu wata baiwar sa.
Dan rage takaici itama sai fesa turaren sannan ta kama hanyar barin 'dakin sai kuma taga rashin kyautawar hakan, tunda dama can tasan aikin ta ne kafin ta 'dan janye da aikin, ta kuwa san Ammi bazata ta6a tanka ta kan hakan ba, ko da ace daina yin aikin tayi kwata- kwata, dan haka gara ta gyara tun bata 6ata gurbin daraja da 'dan mutuncin ta da ake gani ba.
Baya ta dawo ta fara gyara masa gado dan a hargitse yake ko bakomai kuma aikin ta ne dama ta saba, balle yanzu da ya tasan cewa hadda guzurin lada zata samu ai ba laifi bane idan tayi hakan daga yanzu har zuwa lkcn da zai sallame ta.
Sai da ta gyare 'dakin tsab ta tsabtace shi sannan ta fita bayan ta ja 'kofar.
Cikin ranta take ayyana sai yau aka ga daman zuwa ganin likitan kenan...