Sashe 161
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iyami kam tun kan Hamma ya dasa aya tayi saurin mi'kewa tsaye tana shewa tace" Zancen banza, ni za'a rainawa hankali? Abubakar ni fa na haife ka, itama 'din gabana akayi rainon cikin ta zuwa na'kudar ta, har kun isa, a tunanin ku kun girma kenan..? Kunyi girman da zaku shirya munafurcin da 'karamin kwakwalwar ku ta sanar da ku cewa ni Hajara zan yadda da ita....?
Yarinya taje tayi cikin ta haife sannan ku wani zo min da wani batu, ita matar jakar ina ce da zata 'dauki 'yata sukutum tace ta bawa Zaituna, bata da dangi ne kome?"
" Haba..Haba Iyami, maganar nan fa gaba 'dayan ta bata tashin hankali bace...magana ce da za'a yi ta ta fahimta ba komai ba, ta ya ma zaki ce Zaituna ta haifa bayan kullum yarinyar nan gaban ki take sabgogin rayuwar ta?
" Kayi min shiru Habu, kayi min shiru banason munafunci..da alamu kaima an koya maka yadda zaka juya ni ne ko...to 'karya kuke?
An gaya ma na manta halin da take ciki ne?
yarinya ce amma kullum safiya sai ta yi wankan buta agidan nan in banda shashanci miye hakan ke nufi?"
Sosai ran Hamma Bukar ya fara 6aci, amma da yake yasan da wacce yake maganar dole ya danne fushin sa...yace
" Iyami wannan ai tsohon zance ne tun yaushe rabon ta da hakan kuma ai kinsan lalurar da take 'dauke da shi da yasa ta ke wankan...".
Da hannu tayi saurin dakatar da shi...
" Raba ni da gaibu, raba ni da shaidar da ban san farkon ta ba, ni babu abinda na sani ni..bansan komai ba, kuma da zakace tun yaushe rabon ta da wankan to ta riga tayi abinda ranta ke so tasan tana da ciki ba dole ta daina bin mazan da take gi din ba..abin nema ne ya samu shiyasa ta daina..kuma da yake tasan gab take da haifo nata ca nake ba'a da'de ba da Dija tazo su je barka ta 'kiya.. ."
" Innalillahi...haba Iyami, meyasa kike furta irin wannan kalamin fisabilillahi...ke fa tamkar mahifiya kike a wurin ta ...".
" Allah sittira, Allah ya tsari gatari na da saran shuka, wallahi ban haifi irin mayu dangin karuwai ba, dan haka baza'a lika min na kale ba, kaima kar ka yi hankali kaga ni, watan watarana muna nan da kai sai an ce kaine uban 'diyar ai.."
" Ya ilahi..."
Ya fa'di yana dafe goshin sa.
Duk wannan tijarar da Iyami ke yi Abban mu na zaune ko uhum bai ce ba, balle yy yunkurin tankawa, Salale ma sai yanzun yayi magana inda ya ce" Haba Iyami sai kace baki san wace Zaituna ba, muma fa da ba gidan muke rayuwa ba zamu iya shaidar halin ta balle kuma ke da kullum kuke tare, wallahi ni har a zuciya ta banji cewa 'karya Zaituna tayi min ba, bata yi kama da mai karya ba balle wannan gagarumin abinda kk tunanin ta aikata, baya ga ma ni a gabana aka kwashi gawar matar da 'dayan jinjirin nata..dan Allah ki sassauta mata iyami, yarinyar nan taimako tayi abin kuma sai ya juye haka nan..."
Kanta ta kawar gefe tana girgiza 'kafafu...Nasiha Salale yayi mata kafin ya bar gidan amma babu 'daya da ya shiga zuciyar ta, sai dai abu guda da ya sa danji kwanciyar hankali shine duk cikin su babu wanda yayi zancen zai raba ni da Yarinyar, babban abinda ya wanki zuciya ta kenan har yasa fa'dan Iyami sam bai wani dame ni ba.
Duk da kuwa hayaniyan da tayi 'dazun ya sanya ma'kwabtan mu na kusa le'kowa hadda masu le'kowa ta saman katanga, matar Hamma Bukar da ke can gidan ta ma tuni labari ya isa mata, haka ta zaro mayafi ta taho cikin gidan, kusan komai gaban idanun ta aka yishi.
Kowa kallon mara gaskiya yake min, kowa na min kallon mai fuska biyu...musamman bayan fitan Salele da Iyami ta cigaba da sababi tana fa'din" Wannan jarabar hijabin dama ai kowa yasan ba zai kasance na alkhairi ba, yarinya ace kullum sai dai ta tashi ta kuma kwanta da hijabi kamar haihuwar cikin limamai? ashe duk na munafurci ne ciki kike 6oyewa a ciki, an dai yi hasara wallahi tallahi, mu kam abin arziki muka gada ba na sharri ba, dama ina za'a irin kirki wajen gantalallu, ace mutane basu da takamamman wajen zama sai cin arziki a zauna a tashi, mu dai gidan nan bamu da makwancin shege sai ki nemi inda dare yai miki tun da wuri ki san yadda zaki yi da kazantar 'diyar ki..."
Wannan maganar ya 'kona min zucia sosai, ban kuma sha wani wahalar fahimtar zagin da take min, zagin asalin mahaifiya ta take, duk da masan kusan abinda ta fada gaskia ne amma hakan ba shine yake nuni da cewar asalin ta ba mai kyau ba ne, mahaifan ta fulani ne kuma na tashi...dalilin rabuwar ta da su kenan bayan auren ta Abban mu har kuma yau din nan bata san inda suke ba suma basu zo gare ta ba dayake suna jin haushin ta na auren barebari da ta za6i yi ta 'ki bafulatani 'dan uwan ta.
Iyami zata sake magana Yaah Bukar yy saurin dakatar da ita.
" Haba dan Allah Iyami, gaskiya baki kyautawa yarinyar nan, saka hijabin nata laifi ya zama dan yau ta gamu da 'kaddara? dan Allah kar kiyi amfani da wasu abubuwa na rayuwar ta ki 6ata mata suna dan Allah Iyami, yanzun aka gama yi miki bayani amma kina sake 'kwakulo wata maganar daban saboda menene dan Allah...?"
" Saboda Ubanka ne Modu Kyari..nace sbd uban ka ne kaji Habu...wallahi bana son shashanci idan ka ishe ni zan zazzabga maka mari yanzun nan babu ruwa na ka kiyaye ni..."
" To kiyi ha'kuri ni dai Iyami, indai dan yarinyar nan ne insha Allahu zuwa gobe za'a san yadda za'ayi da ita ki iwantar da hankalin ki".
Ya fada yana mai sunkuyar da kansa cikin tsananin damuwa.
Ni kam dama tuni kuka nake, rabon da idanuwa na su bushe har na manta lkcn.
Jira nake Abban mu ya furta wata kalma ko.zan samu sassauci daga wajen sa amma babu alamun hakan.
Iyami ce ta kawar da kai tace" Da yafi muku dan wallahi, dan ni babu wanda ya isa ya zauna min agida da shegen iri".
Hamma na kai ya girgiza kawai ya tashi ya nufi 'kofa...haka ma Goni da tun zaman sa bai furta ko da kalma guda bane shima 'dakin sa ya wuce.
Azeemah kuwa tsaye take hannun ta ri'ke da yaron ta tana bina da wani shegen kallon da na tabbatar na tsana ne.
Har Hamma ya fita sai kuma sai ya dawo daga bakin 'kofa ya tsaya yace" Ke Azeemah zo ki wuce gida".
Inda yayi maganar babu wasa balle fara'a saman fuskar sa.
Sum-sum naga tabi bayan sa ta fita itama tana 'kara hade ranta.
Ni kam banda kuka babu abinda nake yi har a lkcn.
Iyami ma 'dakin ta ta shige Khausar bata nan haka ma Ummaru suna gidan Hamma Bukar tun 'dazun.
Ganin kowa ya barni ne ya sani kallon inda Abban mu yake zaune, wani uban harara ya banka min da muka hada idanu wanda yasa take na mi'ke na shige 'daki na ina sake rusa kukan rashin madafa.
Shikenan fa kafin ace sallar maghrib maganar Iyami tayi tasiri ta kuma yi nisan zango, inda tayi tafiyar da ni kaina bansan iayakr ta ba, tafia ce da zata bawa kowa mamaki.
Kowa cewa yake ashe dama Zaituna 'yar iska ce, gashi ta haifi 'yar da ba'asan waye ubanta ba....ashe.. ashe...ashe..ashe dai maganganu dai kala- kala.
Dayawan mutane fa sun san me yafaru yau agarin, an kuma san cewa an zo an kwashi gawawwakin mutane, sannan ko cikin garin namu akwai wa'danda abin ya ritsa da su ya kuma yi sanadin rayukan su, kuma sunga lokacin da aka tafi da gawar matar da 'dayan jinjirin amma saboda son zuciya kowa 'karyatani yake, wai sharri kawai nayi mata dan naga itama ta haihu...kuma dan naga bata raye ne shiyasa, amma ai tare take da jinjirin ta..babu wanda ya yadda cewar matar ce ta haifi 'yan biyun ta kuma ban 'daya a hannu na illa Salele mai Chemist da Hamma Bukar.
Iyami kam kafin dare yayi duk ta cire abinda ke 'kunshe a ranta game da ni, ciki hadda zaryar shiga bayi da nata yi da safiyar ranar, kwana da nayi da ciwon ciki da tafiyar dur'kuso da nayi sbd ciwo wai duk ashe na'kuda nake bata kula ba...ni kuma na 6oye sbd munafurci.
Sai bayan maghrib Hamma ya dawo, lokacin kuwa yarinyar na ta kuka nima ina taya ta dan na rasa yadda zanyi da ita...da kansa ya 'dauki yarinyar ya bata zam- zam da ya shigo da shi ya kuma tauna dabino mai yawa ya bata Allah cikin ikon sa kuwa sai tayi bacci.
kwantar da ita yayi sannan ya kalle ni" Kukan ya isa haka nan to".
Ya fa'di yana kallo na.
Hawayen fuska ta na fara sharewa yayin da Hamma ya cigaba da fa'din" Kin dai ji abinda Iyami tace ko? nasan abu ne me wahala ta bari ki zauna da yarinyar nan cikin gidan nan, kin kuwa sani ba sai na maimaita mk akan Abbah ma ba zai ta6a tankawa ba..Baffah Liman kam na tabbatar har gwamma kowa akan sa dan 'dazu na same da shi da batun sai ya nuna min cewa ai tun 'dazu ma yaji labari yace kuma shi babu ruwan sa be ce kije ki kwashi ciki ba balle a rataya masa wani nawi, duk yadda naso fahimtar da shi abin ya faskara sai ma wasu hujjoji da yake bani kwatankwacin na Iyami, dole na hakura na baro wajen sa...koma fa ya tsaya ya saurareni bai yi ba, shima yayi amfani da zancen mutane na cewa kece kika haifi Yarinyar".