← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 218

Sashe 83

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kabeer yayi auren sa na fari a lokacin da suke Jss3 ita da Safaa...tun farkon auren sa ya so ya 'dauki 'daya daga cikin su amma Ammi bata amince masa ba, sai dai daga baya Safaa da suka sha'ku da matar sa sai take yawan zuwa musu, watarana ma har kwana take acan, 'karshe ma taso tarewa gidan na sa gaba 'daya saboda ita Allah ya zuba mata tsananin ma'kon 'yan uwan ta sosai tai wa Marwa zarra ta wannan 6angaren.

Sai da Ammi ta tsaya tsayin daka kafin ta samu daidaituwar zaman Safaa waje guda a hakan ma duk weekend can take yini abinta.

A wancan lokacin Rayyan na karatu a wajen 'kasar nan wanda Ammi ta tura shi badan yana so ba.

Da safaa ya tattauna batun tun kafin tafiyar sa har itama Marwa ta samu labari daga bakin Safaa anan nema tasan ra'ayin sa sun kuma tausaya masa, domin duk cikin su babu wacce yafi sha'kuwa da ita irin Safaa sosai yake zama yayi hira da ita ba kamar Marwa ba da tun asali gaisuwa ka'dai ke ha'da su amma duk da haka ba 'karamin 'kauna ke tsakanin su ba.

Salmerh😘

[16/10/2022, 9:06 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...51*

.......Shekara biyu da auren Yah Kabeer Allah ya azurta shi da samun 'karuwar yarinya 'diya mace 'kyakkyawa da ita.

Ranar suna yarinya taci sunan Ammi Wato Aseeya amma muna 'kiran ta da _Zamrud_ ...

Tun haihuwar Zamrud duk wata 'kauna da soyayyar mu muka tattara muka 'daura akanta, hatta Rayyan da ba 'kasar yake ba ba'a barshi abaya ba, ya kan kira Kabeer lokacin da ya tabbatar yana gida suyi videocall kawai yai ta surutu da Zamrud tana sashi daria.

A lokacin ka'dan ya rage mana mu kammala secondary ni da Safaa domin Yah Kabeer cewa yayi baza muyi SS3 ba har ma mun yi registration na Jamb saura mu rubuta..tun wajen cike Jamb 'din kuma muka samu bambamcin ra'ayi...ni na kasance babban burina shine na karanci accounting yayin da ita kuma Safaa take son karantar fannin journalist.

Duk cikin mu babu wanda aka tauyewa ra'ayin sa...duk din mu ra'ayoyin mu muka bi sai dai still an samu bambamcin samun makaranta.

Safaa nan Kano ta samu BUK yayin da ni kuma nasamu admission a jami'ar ABU dake Zaria.

Ammi taso hana mu rabuwa da juna amma Abban mu yace a a ta bari ai kowa da nashi kaddarar yake tafe, kasancewar mu 'yan biyu bashi zai sa komai na rayuwar mu ya zam iri 'daya ba.

Shi in a ra'ayin sa ne ma aure zai mana kamar yadda ya yiwa Anty Raihana da gama secondary ya aurar da ita acan gidan ta ta yi karatun ta ta gama kamar dai yadda ya kasance da Ammi kuma ba gashi tana aikin ta cikin kwanciyan hankali ba, sai dai ganin zamani ke 'kara bu'dewa ya sa mu 'din ya bamu dama.

Da wannan kalma ta mahaifin mu suka samu damar tafiya makaranta amma zuciyoyin mu cike da alhinin rabuwa da juna.

A lokacin Sultan ma na 'ko'karin ha'de degree 'din sa fannin Computer engineering shima anan BUK yake...dan ko da Abban yai masa tayin fita 'kasar waje kamar dai Rayyan amma Sultan 'kin amincewa yayi, acewar sa gwara ya zauna yana ringa sanin halin da ahalin sa ke ciki.

Sosai Abba yayi na'am ya kuma yi farin ciki da wannan batu na Sultan dan sosai yaga hankali da hangen nesan sa ba wai dan sauran yayyen nasa sun gaza ba a a kawai dai ganin sa na 'karami cikin su amma yasan abinda yafi dacewa...kuma dole dama a matsayin sa na 'dan kasuwa ya nemi matallafi.

Ammi ce ma taso nuna 'kin amincewar ta kan karatun Sultan a BUK 'din amma Abbah ya taka mata birki dan ba laifi Ammi akwai bragging tana so komai nata ya zam first class ne ita a rayuwa.

Koda ya gama Degree 'din nasa a can Sokoto yayi serving 'kasar sa a lokacin dududu shekarun sa ashirin ne da biyu shi da Anty Raihanan mu dake aure a garin Kaduna shekarun su kusan na tafiya dai- dai ne, yayin da Rayyan yake ashirin da biyar zuwa da shida. yah Kabeer kuwa ya kai Talatin.

Safaa da Marwa kuma suna 'yan sha shida ne kacal.
Zaman Safaa a BUK tare da Sultan ya sa suka 'kara shakuwa sosai, kamar yadda zaman ta a gida ya 'kara sha'kuwar ta da sauran yayyen mu fiye da ni da sai nazo hutu.
Hutun kawai ke kawo ni gida, wani sa'i hutun ma ba nan Kano nake dawowa ba kawai sai na wucewa ta Kaduna gidan Anty Raihana nayi hutu na acan.

Muna shekara ta biyu a Jami'ah Yah Rayyan ya gama karatun sa ya dawo gida, yayin da Sultan ya kammala bautar 'kasar sa har ma ya fara aiki da Abban mu 'kar'kashin companyn su kamar Yadda Kabeer yake fama dan shi dama gaba 'daya fannin kasuwanci ya karanta ba dan komai ba saboda tallafawa kasuwancin mahaifin sa acewar sa.

Shekarar da Rayyan yah kammalo karatun sa da 'yan watanni a shekarar Raihanan Mu ta haihu inda ta haifi yaro namiji mai kama da baban sa sak, misalta irin farin cikin da wannan family suka tsinci kan su aciki ma 6ata lokaci ne, ranar suna yaro yaci sunan Muhammad (kakan sa mahaifin Baban sa) amma ana 'kiran sa da Bassam.

Yah Rayyan na dawowa da shedar kammala karatun sa Abbah yace sam bazai cigaba ba sai yayi aure shima tukunna, dan baya so suyi irin nashi ne kasantuwar Abbah bai ajiye iyali da wuri ba har da shekarun sa suka dan jaa kafin, so yafi so 'ya'yan sa su yi aure da wuri kafin shekarun su tasa, yana duba kansa ne dan tuni girma ya gama kamashi ahalin yanzu.

Duk yadda Rayyan yaso zame wa batun abin ya gagara, dan Abbah be zo da wasa ba wannan karan tsaye yake kan batun sa babu ja da baya.

Toh shi a lokacin ma takamammiyar budurwa baya da shi, yarinya 'daya yake kulawa wata course mate 'dinsa kuma itama saboda yabawa da hankalin ta da yayi ne har ya yadda suke abota.
Ta hanyar schoolarship ta samu fita India karatu iyayen ta ba masu 'karfi bane akwai dai rufin asiri na Allah.

Sunan ta Nadia 'yar asalin jahar Borno ce ta kasance daga cikin 'kabilar Barebari...tana da nagartattun halayen da ya tabbatar bazai yi da nasani ba ko da ya za6e ta a matsayin uwa ga 'ya 'yan sa ba.

Ta kasance tamkar 'kawa ce gare shi lokacin suna school amma da jin batun Abban su ya nemi canzawa dangantakar tasu salo duk da yasan dama ita Nadia ta jima tana 'kaunar sa shine kawai bai bata fuskar bayyana masa hakan ba.

Cikin lokaci 'kankani ya samu cikakkiyar kar6uwa, soyayya zazzafa 'kauna da kulawa daga Anty Nadia, sosai ya yaba mata ta wannan 6angaren bai 6ata lokaci ba wajen yi mata batun aure.
Ta kuwa nuna amincewar ta dari bisa dari.

Kafin ya bayyana ta ga mahaifan mu ne, su kuma suka fara yi masa zancen Amrah, dan itama a lokacin tana Jam'i a ne sai dai ita ba nan kusa take karatun nata ba ita a Maleysia take yi..Amrah ta kasance 'diyar abokin Abban mu ne kuma Ammi bata ki batun ba koda Abban ya sanar da ita kan cewa ya nemawa Rayyan auren Amrah farin ciki tayi sosai.

Rayyan bai 'ki batun su Abbah ba kamar yadda bai fasa bayyana musu Nadia ba matsayin wacce ya riga ya za6awa kansa ba har ma ya yi mata batun aure, dan kokadan a rayuwa ba abu 'kalilan ke karya 'kwarin gwiwar Rayyan ba.

Abbah ne yace duk za'a yi, batare kuma da matsala ba da iznin Allah, tunda ya riga yayi mata batun aure haka kuma itama Amrah Abba ya riga yayi magana da Mahaifin ta.
Duk babu wanda za'a karyawa alkawari daga ciki acewar Abbahn mu.

Inda ya shirya komai akan cewa za'a fara auren sa da Nadia kafin na Amrah ya biyo baya tunda ma ita yanzu take karatu mahaifin ta yafi so sai ta gama a yadda Abba ya fahimce shi.

Su Abbah sun kai ku'din gaisuwan Rayyan a Maiduguri, su hu'du Abbah, da 'dan uwan sa Kawu Sufyan sai wani abokin sa Alhaji Rufa'i sai kuma Sultan da ya tu'ka su.

A hanyar su ta dawowa ne 'yan fashi suka tare su anan nan gaba ka'dan da Wudil dan sunyi tafiyar dare ne basu yadda sun kwana acan Maidugurin ba...kuma tafiyar mota ce suka yi.

Harbe Abban mu aka yi a cikin sa yayin da 'kanin sa Kawu Sufyan suka harbeshi saitin zuciya nan take ma yace ga garin ku nan.

Sultan kuwa duka sukai masa sosai yayin da 'daya abokin Abban tun tsaida su da akayi ya suma hakan yasa basu bi takan shi ba sai bayan da komai ya lafa sannan ya farfa'do.

Abban mu da 'kyar yake numfashi cikin azabtuwa da neman agaji...numfashin sa bai tsaya ba har sai da aka dangana shi da asbitin su Yah Rayyan da tun ganin sa da shi yanda ya jikkata ya rikice...duk wata jarumtar sa neman ta yayi ya rasa ta.

Rayyan kasa ri'ke kukan sa yayi, yana kuka yana fa'din sai ya kashe duk wanda yy wa mahaifin sa haka..shi kam Abbahn mu murmushi kawai yake yi masa da haka fuskar sa da murmushi ransa ya bar gangan jikin sa gaba daya.

Kwalla Marwa ta share da dan yatsanta yayin da wani hawayen ke sake biyo bayan yatsun ta.
Ita kanta Zaitoon sai taji babu da'di, daga bakin su ta san cewa mahaifin su rasuwa yayi amma bata ta6a sanin cewa harbe shi aka yi ba.
Bata san me ke damun mutanen mu na yanzu ba da 'daukan rai bai zama abin tsoro a gare su ba.
Cikin ranta ta furta" Allah ya ji'kan Abbah ya gafarta masa.."
Tana 'dauke hawayen idanun ta ta furta hakan itama.

Moopy na kwance abayan Marwa a yadda take zaune bakin bed din ta ta 'dan ran'kwafo ahakan take bawa Zaitoon labarin ita kuma Mufeeda ta kwanta daga bayan ta tana 'yan surutan su na yara har bacci yayi gaba da ita.
Chapter 83 · 0% Book details