Sashe 216
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari da safe yaja su Jam'i Zaitoon na wani shashshare sa.
Ta gaida shi.
" Toh wannan fushin fa wai duk na menene.
Baki ta tura..." Fisabillilahi mutum na wajen taro a wani tsamo shi ya kwana anan, yanzu da wani idanu zanje in dube su dan Allah...?"
" Da wannan idanun mana..da can da wani idanu kk duban su...?".
" Toh haka ake yi ne..?!
" An ma riga anyi ai madam sai dai in za a sake..".
Ta dan harare sa.
Yayi daria.." toh ai gaskia ne...in kuma kinga bazaki iya komawa ba kina jin kunya shikenan sai kiyi zaman ki anan, nima da naje aka 'daura auren zan dawo in same ki musha hutun mu har su gama bikin su...".
" Ai tafiya zasu yi toh su barni anan.."
" Ina zasu tafi kenan?"
" Can Bauchi mana..".
" Kyale su suje abinsu, dama ai ke babu inda zaki".
Ido ta waro" gidan amaryan..?"
" Sau nawa zamuyi maganar nan ne nikam, nace banda ke a zuwa Bauchin nan..kin ki daina maganar...".
Ya 'karashe da jan dan 'karamin tsaki.
Kawai sai ji tayi wani zufa ya karyo mata, take ta fincike hijabin, tana duban sa, gani take kamar wasa yake, amma yanayin fuskar sa ka'dai ya tabbatar mata da cewa dagasken gaske yake.
Take sai ta fara kuka, kuka fa irin sosai din nan.
Rayyan kuwa tashi yayi ya ma bar mata 'dakin ya koma can nata 'dakin.
Sai dai bai ji ya nutsu ba ya sake dawowa.
Hijab din da ta cire wajen yin kukan ya 'daukan mata ya sanya mata sannan ya kama hannun ta zata yi gardama ya 'daga baiwar Allah sai gaban motar sa.
Direct Youheal ya wuce da ita aka kira Dr. Hauwa yayi mata takaitaccen bayani, both jini da fitsari aka diba, in minutes sai ga sakamako ya riske shi.
Cikin office din Dr Fawwaz ya yi sujudush shukur yana mai yiwa Allah kirari.
Fawwaz kan sa farin ciki yake yana 'karawa..ita kam tana can office din sa baccin ta ma take dan tunda aka diba jinin da yaga ta fara jin bacci ya sa a kaita can.
Yasha tsiya wajen Fawwaz kafin su baro asbitin Zaitoon duk bata san wainar da ake toyawa ba...ita dai taga bakin sa kamar gonar auduga, fara'ar dake saman fuskar sa bama zata iya misalta shi ba.
Lokaci lokaci ta kanji ya saki hamdala sannan yakan yawaita duban ta.
Har suka je gida.
" Kina jin baccin ne har yanzu?"
Ya sake tambayar ta bayan sun isa gidan.
Kai ta girgiza masa alamun a a..dan sosai take son komawa can gidan.
kai ya girgiza shima" a a madam....dole ki kwanta fa ki huta, kafin inje daurin auren nan in dawo ko...?"
" Zata yi magana yace" Please..bana son musu"!
Dole tayi shiru...tayi rau rau da idanu.
Kawar da kai yy tamkar bai gani ba.
Da kansa ya kaita 'dakin sa ta kwanta idanun ta zubda hawayen takaici.. shima kwanciya yayi gefen ta...hannun sa ya 'daura saman marar ta har ya bata tsoro tunanin ta ko wani abun zai sake yi mata amma sai taga daga hakan bai matsa ba.
Goshin ta ya sumbata.." I love u wifey".
Ya fa'da da sauti mai taushi.
Lumshe idanu tayi cikin ranta ta ayyana" nidai wa'dannan abubuwa duk ba birge ni suke ba burina ka barni in je wajen Marwa ta yanzu.
Komawa yayi ya kwanta gefen ta, still hannun sa na saman cikin ta, cikin ya 'dan dago ka'dan amma ba sosai ba, sannan marar tayi 'karfi ba kaman da ba.
" Baki taba jin canjin yanayi tattare da ke ba da zai sa ki zargi wani abu?"
Da sauri ta girgiza masa kanta.
Sai ya danna cikin ta saki 'yar 'kara.
Yace" yanzu fa." Tace" da ciwo".
Sai ya saki ajiyan numfashi yana kallon saman 'dakin yace" Kiyi min addu'a wifey...na taimake ki zaki 'kara samun wata ko wani babyn in Allah ya yadda''.
Shiru tayi bata ce komai ba kawai tana 'ko'karin fasa maganar tasa dalla-dalla.
Take maganar Marwa ya dawo mata.
" Wai dagaske ne?"
Ita kanta bata san tambayar ta fito fili ba sai dai jin amsar da Rayyan ya bata shi ya tabbatar mata da cewa a fili tayi maganar.
Yace
" Yes mana..kina kokonto ne?"
" Yah Rayyan ni ce zan haifi Babyn?"
Ta kara jefa masa tambayar.
Yace" ni nafi son hakan ma kodan in huta da raki ma in anga ana da yara har biyu".
" Yayah wai dagaske nice zan haihu?".
Ta 'kara tambaya a mamakance..domin.sosai maganar tasa ke bata mamaki.
Yace " A a Ni ne"!.
" Ohh..da sauki".
Tace da iya gaskiyar ta.
Kai ya 'dago tamkar zai rufe ta yana duban fuskar ta yace" wai me kk so in baki as in tukuici..?"
" Ni...?"
" Yes..".
" Tukuicin mene?"
" Ke de fadi duk abinda kike so"!
" Ka tabbatar zaka bani?"
" Me zai hana, ai ni abinda kika bani ya sha gaban koma me zan baki.."
" Toh ni ban son komai, kawai ka barni inje Bauchi tare da Marwa..".
" Wannan kawai?"
Da kai ta amsa shi idanun ta cikin nashi.
Cikin idanun ta ya kalla na 'yan da'kiku sannan ya kawar da kansa yana mai sakin 'karamin numfashi.
Tashi ki shirya in sau'ke ki.
Zaitoon na jin haka ta yun'kura da sauri yace" kiyi a hankali mana, kina so in fasa ne ko?".
'Dakin ta ta wuce ta yi wanka cikin 'kankanin lokaci ta shirya cikin wata ubansun atampa da yake duk kayan hidimar bikin na can gidan.
Har ta shirya ta fito Rayyan bai shirya ba 'karshe ita ta taimaka masa ya 'karasa shirin sa.
sannan suka fito.
Allah yasani sosai take jin kunya ta kuwa san hatta Marwa ba barinta zatayi ba sai ta mata tsiya ayau 'din nan..dan haka sai ta hade rai sosai tabi ta 'kofar baya ta shiga zuwa 6angaren Marwa.
Cunkus ta same shi da mutane.
Allah ya taimake ta bayan gaisuwa babu wanda ya tanka ta cikin su illa Marwa dake mata dariyar mugunta 'kasa- 'kasa.
Dayake tasan hali, dama tasan dole Marwa sai ta tanka, hakan yasa bata nuna tama fahimci dariyar me take ba.
Da abin ya ishe ta cewa tayi yarinya yi ki gama dariyar naki lokacin na nan zuwa zan rama ne...".
Ko su Ammi bata iya taje gaida su ba, haka ta hau shirin ta ta gama ana ta hada hada, sai dai in hanya ta hada ta da mutun bkawai su gaisa ta cigaba da harkar gaban ta.
Rayyan kuwa duk sai dayaje ya gaida su a lokacin ma ana shirin tafia 'daurin aure...so bai dade ba ya fito Ammi na tambayar sa Zaitoon fa yace tana cikin gida.
Daf da zai fita yaga Mufee hannun wata mata yace" 'yan mata..".
Muryar sa kawai taji ta fara waigen sa ai kuwa tana hango sa ta nemi a sau'ke ta ta nufe shi tana fa'din" Abbah..".
Yace" Na'am maman Abbah...I missed u..".
Ta wani sar'ke shi a wuya..." Mufeeda cikin taro fa zanje zaki hautsina min kayana kuma...".
Wata yarinya ya yafito a gefen sa, ya mi'ka mata Mufee ta kuwa ki zuwa, yace bari inje allura in dawo kinji mamana, mai kike so in kawo mk...ta cuna baki ta girgiza kai alamun bakomai.
" Zanzo muje Yawo anjima..ko?"
Da sauri ta washe baki..." sarkin son yawo kawai"
Yarinyar ya mikawa ita yana fadin" Kaita wajen Ammi na direct kar ki bada ta ga kowa".
Yace da yarinyar sannan ya shiga mota ya fita.
Dubbanin jama'ah ne suka shaida 'daurin auren...Adam Shaheed Jibrin 'Dan maliki tare da amaryar sa Marwah Sa'ad Auta bisa sadaki mai matukar daraja.
Marwa kam da jin an 'daura aure ta fara kuka, duk wani uban make-up da akai mata sai da ta goge sa tass.
Sai yanzu tunanin barin gida yazo mata.
Zaitoon ma kukan take haka nan kawai bata san dalili ba.
A haka aka 'karasa yinin nan har zuwa la'asar basu da walwala.
Lokacin da za'a tafi da amarya Mufeeda na can dakin Ammi tana Bacci...Rayyan yaso tabi Zaitoon sbd kar tayi rigima idan taga babu su duka amma Ammi tace sam..damun Zaitoon kawai zatayi acan ta takura mata, abar mata ita agida kawai.
Da kansa ya 'dauki amarya da Anty Madeena sai Matar sa Zaitoon da wata yar uwar Ammi sai ragowan motocin kuma suka dauki ragowan yan rakiyan amarya zuwa garin Bauchi.
Memories da yawa Zaitoon ta bari cikin garin nan, akwai abubuwan da har abada bazata ta6a iya mancewa da su ba.
Kawai sai kukan ta ya dawo sabo.. a hankali hawayen ta ya fara sauka....
Sau daya Rayyan ya dube ta ya dauke kansa.
Ba sai ya kaiga tambayar ta ba yasan me take tunawa, sbd dama yasan dole ne ta tuna 'din...daya daga cikin dalilan da ya sa tun farko yace bazata zo ba.
Wani abin tamkar ciwo yake kasancewa a zuciya wanda abu 'kalilan ke iya fame sa.
Serlmerh😍
[23/01, 4:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...108*
........Da kukan nata ya ishe sa ne...a zuciye yaja wani uban birki tsakiyan titi..." Rayyan lafia?...Ya akayi?"
Anty Madina ta jefa masa tambaya cike da mamaki tana mai waigen baya.
Bai bi takan maganar ta ba..sai ma duban Zaitoon da yayi.
" I swear idan na sake ganin digon hawayen ki bazaki 'karasa shiga cikin garin nan ba zamu koma...haba da Allah"!
ya 'karashe maganar a zafafe.
Sai a lokacin ne ma duk suka ankara da cewan tana kuka.
Anty Madina da 'yar uwan Ammi ne suka fara yi mata nasiha cikin natsuwa, ita Anty Madeena dayake duk tasan meke faruwa, ita kuma 'yar uwan Ammi tunanin ta ko kukan rabuwa da Marwa ne.
Nasiha duk suka hadu sukai mata bayan yaja motar a fizge, shiru kawai tayi ta sunkuyar da kanta.