Sashe 29
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanya Hameeda ke sake tambayar sa amma ba da'dewa zatayi anan din ba ko?
Yace" Ni kaina ban sani ba, ma mmk su dade 'din.
Turus tayi cike da takaici batayi kasa a gwaiwa ba ta sake jefa masa wata tambayar.. zata na fitowa tayata aiki yace sam ita ba me aiki bace majinyaciya ce.
Wannan karon sosai ya hassala ta duk wani zafin da ke zuciyar sai da ya bayyana kan fuskar ta ta kasa danne shi.
" Amma Abban Naina sai nk ganin kamar ka zake da yawa akan yarinyar nan...taya za'ai ka kawo min gantsamemiyar yarinya irin wannan hk kawai kuma kace in Zauna da ita ba muharramar ka ba ba tawa ba ba komai ba..."
" Thought gidan nawa ne..?"
Ya tare ta da tsawa yana waigowa gareta muryar sa da alamun fushi, ji yy ya gaji da maganar gaba 'daya, tun daren jiya yk kokarin fahimtar da ita amma ta kasa fahimtar sa.
Hameeda saroro tayi tana duban sa cike da mamakin sa.
" Anya Abban Naina cikin hnkalin ka kk kuwa...?"
Ta tambaya cikin wani sanyi da raunin tsoron yadda ya buga mata tsawa sbd waccan yarinyar.
" What ever..abinda na sani kawai shine ke da duk wani abinda ke cikin gidan nan mai rai ko sa6anin hkn mallaki na ne, kuma karkashin iko na, dan hk ba lalle sai nayi tarayya da wani wajen zartas da hukunci cikin gidan nan ba...Zaitun zata zauna tare da mu daga yanzu har zuwa lkcn da nayi ra'ayi nd that's final...."!
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️ *...20*
Yana gama fa'din hakan yy gaba abin sa batare da sake jiran wata kalma tata ba, da kallo kawai Hameeda ta bishi cike da tsananin mamakin sa..." is this real...?"
Ta tambayi zuciyar ta.
Dr Rasheed ne ke mata irin wannan surutan akanta..me kenan hkn ke nufi?..kenan...kenan laifi ne dan ta nuna bazata iya zama da yarinyar ba?
Kasa ko 'daga kafafun ta tayi a wajen tana jin wata karaya na tsirga mata cikin dukkan ga6o6in ta.
Ji take tamkar ta sanya hannu aka tayi ihu ko zata ji saukin zuciyar ta.
Gaba 'daya ji tayi ya 'karawa zuciyar ta zafi..sosai taji tsanar Zaitoon har can kasan zuciyar ta fiye ma da farko, akanta ne Rasheed ke buga mata irin wannan tsawar da rabon da ta ji yamata irin sa baza ma ta iya tunawa ba?
Da gudu ta koma dakin ta hawaye na zuba mata babu kakkautawa.
Waya ta lalu6o ta dannawa mahaifiyar sa kira nan ta zayyano mata komai har ma da kari, ga mamakin ta hakuri kawai ta bata tare da kalaman da zasu kwantar mata da hnkl.
Inda ta kara da fadin in kuma taga zuciyar ta bazai kwanta da zaman yarinyar acan ba zatai masa magana ya kawo ta nan wajen ta.
Godiya kawai Hameeda tayi mata ta kashe wayar, tana nufin itama tasan da batun kenan? Kenan kalaman ta ta fahimci tamkar lbrn ba sabo yk agare ba, baki suka hada ko kuma mene...tun yaushe Rasheed ya shirya wannan lamarin bata da masaniya.
In kuwa har mahaifiyar sa ma tasan da batun dole itama ta nuna nata ikon in ba hk ba zasu kaita kasa.
Dole akwai wani boyayyen abu da ita bata sanshi ba..zata bincika za kuma ta 'dauki mataki.
Ta jima tana tunanin yadda abubuwan zasu iya wakana, ita zama da yarinyar tare da su din bata bukatar sa sam sam kuma shi tafi tsana sannan abinda zai iya biyo bayan zaman, ko da tace akai ta can gidan ta din ma Hameeda sai taji bata aminta da hakan ba, da aje can ana hada kullin da bata sani ba gwamma ayi agaban idanun ta yafi, koba komai zata san shirin su.
Kai anya ba baki aka jada za'a mata sakiyar da ba ruwa ba..tunanin ta ya kasa tsayawa waje guda.
Wannan yarinyar in ta wanku ai ko bakin farcen ta ba ta isa ta kama a kyauba, in kuwa akace yau ta zama kishiyar ta ta gama kadewa har ganyen ta.
Kuma in dai bb wata akasa me yasa shi aminta da ita yarinyar har da kawo ta gidan sa.
me yasa Rasheed dagewa akan ta, shi da ko 'yan aiki bai yadda da ko guda cikin gidan sa ba, duk girman gidan ita kadai ke kula da abinta..ita kadai ke shawagi cikin sa sai 'ya'yan ta, sai kuma me sharar haraban gidan sai duk bayan kwana biyu shima yake zuwa yayi sharan sa ya kama gaban sa..gateman kadai ne yk nan.
Karshe dai dole ta yanke shawarar zaman Zaitun din tare da su a gidan taga gudun ruwan su kafin kuma ta 'dau nata matakin.
Dr Rasheed bai sake bi takan Hameeda ba har ya gama shirin office ya fice abinsa shi da Wildan ya ajiye sa a schl.
Shi kansa yana mamakin kansa, dan bai san dalilin da ya sa yake jin yarinyar ba, yake kuma son su zauna tare da shi, yana ganin dukkan motsin ta, ya san dai tun washe garin ranar da ya taimaka mata yk jin zuciyar sa nayi masa nauyi game da ita ya kuma ji baya son tai masa nisa..amma bai ta6a zaton zai iya tsawatar wa Hameeda akan ta har hakan ba.
Idanu ya lumshe gami da shafo kansa da kansa yasan bai kyauta mata ba amma baiga laifin sa wani cancan ba, batun yau yasan Hameeda da tsananin kishi ba, sarai yasan ta, sai dai abu guda da take birge shi kokadan bata da mummunan zargi akansa sai wanda ta gani da idanun ta, shiyasa duk irin zirga zirgar da yake yi bata ta6a tanka masa ko nuna zargi kan hakan ba.
Kuma sarai yasan ta fisa gaskia akan Zaitun, amma ba yanzu ya shirya barin ta tafiya ba, bai ma yi niyyan kawo ta ba bayaga gudun kar Hajiya ta gano ba'a gidan take ba ta dasa masa wata ayar tambayar da yake tun farko ya riga ya sanar da ita batun Zaitunar.
Kuma jiya kannen sa sun ce masa zasu zo gidan nashi yini kwanan nan...shiyasa ya kawo ta.
Ranar Zaitun taga rayuwa, tun safe bata sake jin motsin kowa ba balle idanun ta suga abinci tun na karyawa da aka basu, damuwar ta ma Mufeedah ce bata ta kanta, da rana ma ragowar bread din su na safe tai ta hankara mata ta kuma yi bacci gashi har yamma babu motsin kowa ita kuma tsoron fita take dan ta lura matar gidan bata yi na'am da su ba tun ganin yanayin fuskar ta safe.
Kafin dare duk sunyi laushi..shi Dr Rasheed ma kwata kwata ya mance da lamarin su sai da yazo ya tarar da Hameeda a 'dime kafin ya tuna sanadin fushin.
Da kansa ya 'diba abinci ya kai musu Hameeda nata binsa da kallo, dan kuwa iya abincin kenan da ya rage nashi ne iya su da ta sabawa yiwa girkin iya su taiwa, dan tuni ita da yaran ta sun ci nasu dan ba karamin fushi take da shi ba akan Zaitunar.
Taya ma za'ayi ace ita zata rika dawainiya da ita bacin itama mace ce kamar ta.
Bata tashi tsinkewa da lamarin na Rasheed ba har sai bayan Isha'i da yasa ta bisa dole sai ta sama masa abinda zai ci.
Bakin ciki kamar zai karta, haka ta nufi kitchen din tana 'kwalla, taya ma za'ayi ta kaunaci yarinyar nan...yini 'daya tak ta birkita mata lissafin miji ta hana ta farin ciki da sukuni ta dauke mata walwala duk ta birkita mata cikin gidan ta.
Bama wannan ba, wacce irin rashin lafiya ce wannan da sai a gidan ta za'a yi jinyar ta? da me tafi sauran marasa lafiyar? kai anya kuwa..?...anya..?.
Karon farko cikin rayuwar ta da ta dasa zargin Dr Rasheed din cikin zuciyar ta.
Ranar kowa 6angaren sa ya kwana, bai neme ta ba haka ita ma bata kusanci ko hanyar nashi 6angaren ba.
Shi kam bai wani damu ba, aransa yake ayyana zaama ta sauko ne, shikenan dan kana da mata a gida baka isa kayi taimako ba, baka isa kayi wani abin alkhairi ba sai ya zam laifi.
Washegari haka banda gaisuwa babu abinda ya ha'da su, shi 'din ma cikin 'daurewar fuska tayi shi, yayi kokarin fahimtar da ita dalilin zaman Zaitun din amma ta gaza fahimtar sa, sai ma sake jaddada masa da tayi cewar bazata zauna tare da ita ba gaskiya, ita bata ma ga alamar jinya ko rashin lafiya tattare da ita ba, dan haka ya tattarata su bar mata gidan ta in dai yana son kwanciyan hankali ya cigaba da gudana cikin gidan sa, in kuma ba so yake ta fara zargin wani abu daban ba.
Wannan bayani da Hameeda tayi shiyasa Dr Rasheed fito mata a mutun shima ya sake kafa nashi dokar inda yace zama da ita yanzu ta fara matukar zata cigaba da zama matsayin mata agare shi bb inda zai kai Zaitunan, in kuma ta gaji da cigaba da amsa sunan matar sa ne bai hanata ba zata iya aikata duk abinda taso.
Wannan dalili ya sake tada hankalin Hameeda sosai ta rikice masa ta hana kanta sukuni.
Bai bi takan ta ba yy ficewar sa office sai dai duk hankalin sa na nan gidan.
Sarai yasan halin Hameeda da kyar ne idan zata sake waiwayar su shiyasa ma tun kafin ya tafi ya mika musu breakfast da kansa, 12 na yi kuwa da kansa yabi ya 'dauko Wildan a shcl ya zarto gidan, da kansa ya tura Wildan yai kiran Zaitun 'din suka ci abinci su duk a dinning zuciyar Hameeda kamar zai fashe sbd bakin ciki, ita har Zaitun din basu wani ci abin kirki ba, kowa abinda ke ransa daban, Zaitun jin ta tayi a takure sosai, Mufeeda tai ta bawa abincin sai da ta tabbatar ta koshi sannan ta mike ta koma inda ta fito.
Dr Rasheed duk na lura da su amma bai cewa kowa kanzil ba, a ganin sa ai duk ba yara bane su.