Sashe 82
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai ta shiga tashin hankali.
Abinda ya 'kara 'daga hankalin nata kuwa shine rashin samun Rayyan da bata yi ba, wayoyin sa duk na cikin motar lokacin da ya fita ga wannan dattijon shiyasa ta kasa samun sa.
Sau'kin ta 'daya a ranar ta yi niyyan dawowa gida dama, ai kuwa batare da 6ata lokaci ba ta tattara ta nufi filin tashi da saukan jiragen sama.
Ita ka'dai tasan halin da zuciyar ta ke ciki a wannan lokacin.
'Bangaren su Zaitoon kuwa..'karar wayar Marwa akaro na biyu shi ya sake 'daukan hankalin su gaba 'daya.
Har ila yau 'din dai Sultan ne.
Sai dai wannan karan batare da 6ata lokaci ba ta 'daga 'kiran...kawai sai ta sanya mishi kuka.
Kukan da tun 'dazun take faman dannewa.
Da kyar Sultan ya lallasheta tayi shiru, ita kanta Zaitoon dake Zaune gefe sai da taji 'kwalla ya zubo mata, duk da bata san dalili ba amma haka kawai sai taji rauni gaba 'daya ya mamaye ta.
Ko da Sultan ya tambayi Marwa abinda ya sata kukan bata 6oye masa ba, a zahiri hankalin Sultan ma ba 'karamin tashi yayi ba har Marwa sai data fahimta 'karshe kwantar mata da hankali yayi yace bari ya nemi Rayyan din yaji meke faruwa.
Haka Marwa ta share hawaye kamar yadda ya bu'kata ta kuma sawa ranta ruwan sanyi, dan sosai taji ta gamsu da kalaman Sultan 'din.
Yayin da 6angaren Sultan murmushi yayi, 'dayan wayar sa dake hannun sa ya 'dago yana sake kallo akaro na babu adadi, abin mamaki Rayyan ne, da motar sa lokacin da take 'konewa, an 'dauki takaitaccen video ne na abinda ya faru har zuwa lokacin da Rayyan ya bar wajen cikin motar Fawwaz.
Da sauri Sultan ya kife wayar yana lumshe idanu gami da 'daga kansa sama ya fitar da wani zazzafan huci a fili ya furta" Shegen ya tsallake...wannan karan ma bai fa'da ba...sam na gaji, na gaji da ganin ka kana shawagi agabana, na gaji da ganin ka kana tauye ni da hana ni fantamawa...."!
'Dayan wayar sa ya 'dago yy 'kiran wata number yana mi'kewa tsaye.
Bakomai ya sanar ba face " zan shigo, dole a yau zan dawo ko zuwa gobe...ka shirya sabon shiri zamu 'dauko...".
Haka ya furta cikin wayar sannan ya rabata da kunnen sa.
Gaba 'daya kamannin Sultan ya canza ba kamar yadda yake ba.
Marwa na ajiye wayar tata kafin ta sake wata magana wani 'kiran ya sake shigowa.
Wannan karan Anty Raihana ce ta 'kira, itama ba komai ta sanar da Marwan ba face ta nemi wayar Ammi bai tafi ba.
Marwa tace ai kuwa da safen nan munyi magana da ita amma da yake yau zata dawo ba mamaki sun taso ne shiyasa wayar ta daina tafiya.
" Toh Allah ya iso da ita lafiya..."
Cewar Raihana cike da gamsuwa.
Inda ta 'kara da fa'din" Sai naji muryar ki wani iri Marwa ina fatan dai lafiya..?"
Gyaran murya Marwa tayi da sauri tana fa'din" babu komai fa Anty Raihana kawai dai 'yar mura ke damuna kuma already ma nasha magani..."
" Allah ya 'kara afuwa toh nima zuwa nextweek zamu dawo north 'din hutun karshen shekara na matsu in dawo wallahi, I so much missed u guys..."
Wani ihu da Marwa tayi na farin ciki har saida Anty Raihana ta cire wayar a kunnen ta tana dariya da shirmen Marwa 'karshe ma tsinke wayar tayi gaba 'daya.
Wannan albishir 'din na Anty Raihana shi ya faranta ran Marwa har ya sa ta saki ranta murmushi ya wadaci fuskar ta.
" Na kasa 6oye farin ciki na, kinsan rabo na da Anty Raihana, tun bayan bikin mu da tazo ban kara ganin ta ba".
Tayi maganar tana duban Zaitoon.
Kai Zaitoon ta jinjina tana fadin " Lallai, dole kiyi murna, itama 'diyar Ammi ce ko...?"
" erh mana ita ke bin Yah Rayyan fa..."
" Na kasa ganewa, shi kuma mijin ki fa, ina nufin Yah Sultan..?"
" Ohh..shi..?"
Marwa ta tambayi Zaitoon tana 'yar daria.
" Wannan ma 'dan Ammi ne amma ba ita haife shi ba shiyasa ma kika ga har munyi aure da shi..a yadda muka samu labari wai Abbah ya fito sallar asuba ya tsince sa a 'kofar gida tun yana jinjiri, muma bamu san wannan labarin ba har sai lokacin da ya nuna yana son aure na kafin maganar ta fito dan har girman mahaifan mu basu bari munsan da wannan batun ba duk da kuwa akwai bambamcin kamanni ta zahiri tsakanin mu da shi...tausayi da kuma kaunar da bansan ina masa ta sa na amince da auren sa duk da yake da farko ba ni ya fara so ba 'yar uwata Safaa ya fara nunawa 'kauna kafin rasuwar ta...."
Ba 'karamin mamaki Zaitoon tayi da jin wannan labarin ba, domin in ba sani kayi ba abu ne mawuyaci ka iya fahimtar cewa babu wata ala'ka ta jini tsakanin Sultan da Ammi sbd yadda ta ha'de kansu duk da juye mata izuwa sirki amma in ba fa'da maka akai ba bazaka ta6a kawo wa cikin ranka cewar Sultan 'dan tsintuwa ne agidan ba.
******
Asalin Sunan Mahaifin mu Alhaji Sa'ad Auta, 'dan asalin nan garin Kano ne....sun ha'du da Ammi Aseeya ne wajen wani taron musaba'ka da akayi na jahohi su Ammi ne aka turo daga jihar Borno inda akayi musaba'kar a Kano, nan Abbah yaga Ammi daga baya ya bibiye ta ya nemi mahaifin ta suka gana 'karshe har suka yi aure bisa ga umarnin iyayen ta kuma Alhamdulillah lafiya lau suke zaune agidan sa ta cigaba da karatun ta dan sunyi aure ne tun tana cikin shekarun 'kuruciya shi kuma ya girme mata sosai amma hakan bai sa yayi amfani da shekarun sa ya tauye ta ta kowani fanni ba.
Kannen Abbahn mu ne Kawu Sufyan sai 'karama Anty Madeena, kuma tuni tayi aure ma sai dai Allah bai bata rabon haihuwa ba, haka ma Kawu Sufyan bashi da 'da ko guda amma duk sun mika lamuran su ga mahallici dan sun san shike badawa kuma shike hanawa.
Yayin da Ammi take ita 'kwara 'daya tal a gaban mahaifan ta daga sai 'yar mage da ta kasance mata abokiyar hira.
Tun tasowar ta ta tarar da mahaifiyar ta na kiwon mage kuma ko wani abu ya samu wacce take dashi din ta kan dauko wata amma bata ajiye fiye da 'daya.
Hakan yasa Ammi sha'kuwa da mage sosai ko lokacin da tayi aure taso ta 'dauko a gidan ta sbd kaunar ta da su amma Abbah yace sam baya so, ta 'dauki abin wasa inda ta nemo wata 'yar kyakyawa 'karama ta kawo da tunanin ai idan yazo ya ga ta riga ta kawo zai hakura ya barta da abinta.
Bata ta6a sanin cewa jinin sa ne baya son abin ba har sai da ya dawo gida taga halin da ya shiga abin ya ru'da ta sosai fatan jikin sa yayi rudu rudu idanun sa suka firfito da gaba 'daya ta rude ta fara kuka da 'kyar yayi mata bayanin abinda ya kawo hakan, tun daga ranar da ta cire a gidan ta bata 'kara kawo ta gidan ta har yau 'karshe itama sai taji ta daina birgeta dan ko wajen mahaifiyar ta taje da tuni sunan ta ya juye izuwa maman Mage bata sakewa da abin sai taji ta takura ta sai ta baro gidan tukunna.
Daga baya ta fahimci ba Abbah kadai bane, hatta su Kawu Sufyan da Anty Madeena ma hakan ke faruwa dasu matukar suka hada muhalli daya da mage kuma haka yaranta ma dan Kabeer da Rayyan sun tama fuskantar irin matsalan nan. Sai kuma Su Safaa suma a gidan Dada dake daura da su...
Da farko Anty Madeena can Gombe take zama farkon auren ta, sun kuma zauna a Bauchi daga baya suka dawo nan Kano da zama gaba daya, ganin basu samu rabon haihuwa bane ya sanya maigidan ta sake wani aure bisa ga amincewar Anty Madeenan cikin sa'a kuma sai Allah ya azurta shi da samun 'diya mace shekara guda bayan auren nasa, yarinya ta ci suna Badi'a shekara hudu bayanta aka sake haifan Imran...yadda Anty Madeena ke nuna 'kauna ga yaran ya sanya a hankali rikon Badi'a ya dawo hannun ta duk da yake gidan su ba 'daya ne da abokiyar zaman tata ba kuma akwai fahimta sosai a tsakanin su.
Sa6anin Anty Madeena kuwa 'dan uwan ta sosai ya samu yalwar 'ya'ya dan yaran sa biyar ya haifa, Muhammad Kabeer shine babba sai Muhammad Rayyan, Muhammad Sultan da aka tsince sa lokacin da Ammi ke da 'karamin cikin Raihana, tsintar sa da watanni bakwai kafin Ammi ta haifi Raihana sai Marwa da Safaa da ta rigamu gidan gaskiya.
Dalili kenan da ya sanya yaran sa suka kasance shida sa6anin biyar da ya haifa.
Su Marwa sun kasance sune auta a wajen mahaifan su, kamar yadda suka kasance 'yan biyu ka'dai da Ammin su ta haifa.
Wani aiki ne ya kai Abban su 'kasar saudiya tsawon watanni takwas wanda tafiyar ta ha'da hadda Ammi a lkcn tace bata san ma tana da cikin su ba har sai da suka isa can...kafin hakan ta jima da cire rai da samun wani haihuwa arayuwar ta dan Raihana har na da shekaru bakwai da haihuwa tuni an barta zaman autar Ammi kwatsam sai ciki ya sake bayyana mata.
Sun yi ma'tukar farin ciki da kyautar da Allah ya basu haka aka cigaba da rainon cikin su acan Saudia cikin kwanciyar hankali, Ammi ta haife su ne washegarin da aka fara aikin hajji a wancan shekarar dalili kenan da ya sanya suka yanke shawarar sanya musu suna Safaa da Marwa.
Sun taso cikin gata da 'kaunar yayye da mahaifan su, wanda Allah cikin ikon sa daga kansu Ammi bata sake haihuwa ba.