Sashe 189
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hafiz zama ya gyara yana me bu'de gaban motar yace" Alhamdulillahi".
'Kafafun sa ya diro 'kasa sannan ya fito da duk jikin sa waje ya sha'ki ni'imtacciyar iska yana me gyara zaman rigar jikin sa yace.
" Ina fatan ya kasance gaskia Bello, dan har ga Allah na gaji da wannan zaryar nan...kuma kasan mutumin nawa 'dan anace ne idan yy niyyan abu toh bb sassauci..."
Murmushi Bello yy yana kan tafiyar ya amsa shi da fa'din" Kasan dangi gar'di gare su, kuma ba'a raina wanzuwar su, balle shi da ya rayu ya girma babu su dole nashi ya bambamta...dan ma mai zumuncin ne shi ba kamar wasu can baya da suka yi sanadin watsa zumunchin ba..."
" Toh sarkin magana ni dai dakata a wajen ka jirani...nima shiga zanyi ai in ganewa idanuna na tunda an dace..."
Cewar Hafiz yana mai 'kara hanzari domin taro shi.
" Toh wai da sauri nk yace ruwa yk son sha..."
"...kiyi hkr Goggo, dan Allah ki bar kukan nan, ban san ko zuwa ne ya janyo hkn ba, duk da nidai ba niyyata kenan ba..amma kiyi hakuri Goggo, ni na biyo bayan zumunchi ne na kuma biyo bayan 'yan uwan mahaifi na kamar yadda na sanar dake abaya, Alhaji Jibrin Adam 'dan Maliki shine asalin mahaifi na, kuma ni 'din nan nine 'da guda 'daya tilo a wajen sa..."
Abinda ya sau'ka kunnuwan su Hafiz dake 'karasowa cikin gidan kenan bayan sunyi sallama.
Yadda suka zuba mishi idanu suna kallon la66an sa da son jin abinda Goggon nashi zata fa'di yasa Adam 'dan murmusawa.
Hk kuma itama goggon ke duban sa hawaye na bin kuncin ta.
Bugu zuciyar ta keyi a duk lkcn da taji ya zayyano wannan sunan, bugu bibbiyu zuciyar ta ke yi a lkc guda, suna ne mai matukar daraja da 'kima awajen ta, sunan 'dan uwan ta abin alfaharin ta, 'dan uwan ta da ada yafi kowa son ta, 'dan uwan ta da tun kafin auren ta yy musu 6atan dabo...a yanzu shi da 'diyar da tayi irin 6atan sa take tunowa shiyasa ta kasa tsaida kukan ta...abin ya zame mata bibbiyu ne.
Da 'kyar Hafiz ya bata baki ta rage kukan da take duk da besan dalilin kukan ba kusan ma dukkan su basu san dalilin ba amma shi'din dayake Allah ya bashi baiwar iya magana sosai kalaman sa sukai mata tasiri.
Sun yi gaisuwa sosai sun yi hira sun tuna bayan rabuwa, ta kuma wadata su da duk wani abu da ta sani na tarbar ba'ko a 'kauye da zai matu'kar faranta zukatan su, dama ita gidan ta akwai yalwar 'dakuna, hkn yasa bata sha wani wahalar samar masu masau'ki ba.
Ko da taji cewa Bello ma daga cikin 'yan uwan ta ya 'dauko shi farin cikin sai yy mata yawa...ta jima da cire rai akan ganin wani nata ashe indai da rai da rabo...'kaddarace kawai ta raba su ta kuma tabbatar da cewa bawa baya ta6a wuce 'kaddarar sa....
Duk wa'dannan sun biyo bayan kukan da ta yi tasha ne akan rasa mahaifiyar ta da ma wasu 'yan uwan ta da taji lbr daga bakin su ciki kuwa hadda Babban 'dan siyasan nan da yy 'kaurin suna a yankin dake makwabtaka da su wato Alhaji Jibrin 'Dan Maliki da bata san cewa 'dan uwan ta bane sai yau.
A halin yanzu ita Goggon ka'dai ta rage masa dama ya sani cikin dangin sa, kuma Alhamdulillah burin sa ya cika yanzu, alwashin da ya 'daukan ma duk wani dake cikin ahalin mahaifin nasa ya samu cikawa...sai dai ita Goggon ce ya rage ya sada ta da 'yan uwan sun bayan tsawon shekarun da suka 'dauka basu ga junan su ba....su kansu suna matu'kar so su san inda take..amma sun kasa zurfafa bincike dan gano ta.
Sun sha hira sosai, Goggo ta ri'ka bashi labarin yadda tayi kewar 'yan uwan ta anan ya 'daukan mata al'kawarin ai komai ya zo 'karshe Insha Allahu da kansa zai kaita wajen mahaifi da dangin ta duk da yake yanzun mahaifin nata tsufa ya kama shi sosai, shima yasha ba'kar wahala kafin ya samo ainahin inda suke...amma yanzu Alhamdllh complete yake jin sa a halin yanzu ta fannin dangi...saura abu guda tak ya rage masa...kuma bai ta6a cire rai da samun ta ba haka yake ji aran sa.
Shiyasa ya'ki aure ya'ki 'yan mata ya'ki kowa, kowace mace ma bata birge shi haka suke yin hidimar bikin abokan su su gama batare da kowace mace ta burge shi ba, dama yan mata kam sai dai Hafiz shine gwani ta wannan fannin.
Sam bai yadda sun kwana gidan Goggon ba amma yy mata al'kawarin dawowa da sassafe Insha Allahu kafin su wuce, breakfast ma yace a gidan ta zasu yi Insha Allahu kuma baza su da'de ba zai dawo dan sada ta da sauran ahalin ta.
Haka suka 'dauki hanya zuciyoyin su cike da zulumi da jin da'di, sai dai suna ji tamkar baza su sake ganin juna bane.
Tun ma kafin su bar 'kauyen yayi wa hajiyar sa albishir 'din wannan gagarumin nasarar da ya samo bata kuma 6oye farin cikin ta ba ita kanta, dan bata da son kai akan sa, duk 'kaunar da take yi masa da wahala da dawainiyar da tasha akansa zuwa daular da take ciki ayanzu ta sanadin sa, hakan bai sa dai- dai da rana guda tayi 'kyashin taya shi addu'ar ha'duwa da dangin mahaifin sa ba.
Hafiz dake tu'ki ya juya ya kalle shi sau 'daya ya 'dauke kai.
" Kasan mene...?"
" Sai ka fa'da Hafiz..".
Ya fa'da yana kashe wayar.
" Da alamu kana cikin tsananin farin ciki..."
" Ba 'dan ka'dan ba Hafiz!"
" Nake gaya ma ji nake tamkar Alhaji ya dawo yaga wannan 'yar uwar tasa da idanun sa, da kansa ya ban labarin irin kewar ta da yake, aure ne sanadin rabuwar su kasan tunda sukai mata aure shikenan, toh shi kuma ko a lkcn ya jima ma bai zo inda suke ba shima sai daga baya ya neme su kuma ya samo inda suke amma bb ita".
" Allah sarki...Allah ya ji'kan Alhaji ya gafarta masa...".
" Ameen Yah Allah" suka ha'de baki wajen furtawa.
Yayin da Hafiz ya cigaba da fa'din
" Amma mutumi na kana fa da sauran aiki agaban ka....."
" Name kenan.."?
" Wannan Goggon mana...duba 'daya zakai mata fa ka tabbatar tafe take da damuwa gagaruma amma na jira na jira har yanzu ban ji ka furta komai akai ba...".
Idanu ya zaro akan sa..." Hafiz ashe ba ni ka'dai na lura da hakan ba...wallahi tun 'dazun abin na raina na so in tambaye ta fa amma sai nayi tunanin ko duk rashin 'yan uwan ta ne, shiyasa ma na yanke shawarar dawowa ba da jimawa ba dan tafia da ita..naso tun yanzu nayi hakan amma kasan komai dole sai da iznin mijinta...".
" Hakane...amma ka de 'kara bincikawa Man..kasan mata da iya 6oye damuwa har sai ta musu illa...".
Shiru kawai yayi yana tunani, shi dai bazai ce ga halayya guda ko 'dabi'un mata ba sbd shi bai zauna da su sosai ba, Hajiyar sa ka'dai ce kuma she is free bata 6oye masa damuwar ta, wajen mace 'daya yasan wannan dabia'r amma ita kuma yanaga kamar 6oye damuwar ta yana da nasaba da irin rayuwar da ta riske ta ne.. ya riga ya zam mata jinin jiki kuma ne...shiyasa bai ta6a kawo shi akan kowa ba sai ita 'din ka'dai.
Ko da suka isa masau'kin su, kusan raba dare yayi yana tunanin abinda zai iya sa Goggon nasa cikin damuwa, a halin yanzu ita ka'dai ce kyautatawar sa bata sau'ka kanta ba amma yafi so duk abinda zai mata duk taimakon da zai yi zai fiso ya kasance bisa tafarkin damuwar ta ya kuma wanke mata shi tass.
Tsawon lkcn nan ya kasa hasaso komai sai ma yafi bawa ko matsalolin rayuwa ne kawai ko kuma ta 'da namiji...
Da 'kyar ya samu yy bacci.
Washe gari kuwa kamar yadda yy al'kawari sassafe ya tisa 'keyar su suka sake komawa Hafiz tamkar zai cinye sa 'danye dan cewa yayi ina ma laifin zuwa sha 'daya amma ace tun 'karfe takwas ya wani tashe su sai kace wacce yaji labarin zata gudu.
Shi dai cewa yayi erh aje 'din dai yafi so ya gansa kusa da ita, kama ta jini dake tsakanin ta da mahaifin sa ya kansa yaji wani 'kauna da sanyi cikin zuciyar sa.
Ita kanta Goggon tasa tayi mamakin ganin su a wannan lkcn amma farin cikin ta ya kasa 6oyuwa nan ta sake wadata su da kayan karyawa irin na karkara, koko da 'kosai ne da yaji yajin 'kuli.
Duk 'din su babu wanda yayiwa zuciyar sa 'kyashi, ci suka yi babu wasa, dan kuwa Goggon nasu ba dai tsabta da iya tsara abu ba, da kansu suka fahimci haka.
Sun 'dan sake ta6a hira inda Hafiz yaso jan Goggon da hira da kuma shan cikin damuwar da suke gani kwance kan fuskar ta duk da yake tana 'kokarin danne shi da farin cikin ganin su.
Amma abin mamaki bb abinda sukayi nasarar ji daga bakin ta sai dai murmushi kawai.
Daga 'karshe tayi dabarar ce da su..bata da wata damuwa da ta wuce ta rashin 'yan uwan ta kuma a halin yanzu tasan ta riga ta hau tsanin da zai sada ta izuwa gare su, a hnklai zata tsinci kanta cikin su tsundum.
Dukkan su sun ji da'din maganar ta dan hk suka cigaba da hirar su amma Adam sam bai yadda hakan ne kadai damuwat Goggon ba...musamman ayau da yafi bada hankali sai ya fahimci cewa dagasken gaske damuwar ce 'karara kwance saman fuskar ta.
'Karge biyu saura suka ce zasu wuce sbd zasu tsaya suyi sallah sannan akwai tafia da kuma kur'da kur'da agaban su.
Sun yi mata sha tara ta arziki amma Goggon sam ta'ki ansan komai nasu tace ita ai sune damuwar ta ba wani ku'di ko wani abin dunia ba.
Burin ta kuma su cika alkawarin da suka 'dauka na dawowa domin ta.
Dama yace Insha Allahu Goggo...bazan jima ba zan dawo.