← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 218

Sashe 146

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin hakan yasa Iyami bina da kallo tana dubana da sakakken baki tace" Wai yau ma 'din da hijabin gadon naki zakiyi 'diban ruwan?"

" Iyami zan tattare fa kuma ma ai bai takura ni ba....."
Nayi maganar ina mai 'dan tura baki gami da sunkuyar da kaina dan cigaba da abinda ke gaba na.

Juyawa Iyami tayi tana fifita wuta da mafici tace" Ke kika sani ai...kullum 'kunsun-'kunsun cikin hijabi kamar wata limamiya, ko matan wan ubanki da suke Matan limaman ma ba haka naga suke yi ba sai ke..."

Ni dai ban 'kara fa'din komai ba kawai na cigaba da abinda ke gaba na.

Jajayen randunan ruwa dake tsakar gidan wanda duk suka koma wasu kala sun kokko'de saboda jimawa, 'dayan ma bakin sa a 6algace ko wani irin marfi baya iya rufe shi a hakan duk sai da na cika su da ruwa dake yauvdin ba wani karfi nake jina sosai aciki ba ya sa duk aikin da sanyi nake yin sa.

Bokitin na cika na ajiye a gefe inda naga an tara kwanikan wanke-wanke na fara wanke su har a lokacin kuma idanuna hawaye suke yi basu tsaya ba.

Iyami kam ko kallo ban ishe ta ba balle in samu arzi'kin nuna tausayi ko kulawa.

Sai da na kammala wanke- wanken kafin na wuce 'daki na taso su Khausar da Ummariri dake bacci cikin 'dakin Iyami.

Nan na kama Ummariri na wanke masa idanu yana ta muzurai da alamu baccin bai gama barin idanun sa ba..sai da na wanke masa idanun da kyau sannan nace yy alwala.

Khausar kam buta ta 'dauka ta wuce bayi tun Ina tsayuwar Kiran fitowar ta har na gani na kama wani aikin inayi Amma duk da hakan ta 'dan 'dauki lokaci kafin ta fito tana 'kwa'kule hancin ta.

Ganin hakan yasa nayi kwafa gami da fara yi mata magana da fa'din" Ke Khausar baki ganin hasken rana ne kike yin abu kamar ba sallah zaki yi ba...?"

Kafin Khausar tayi magana Iyami ta riga da fa'din" Kar ki ta kura ta da Allah, nawa ma take da zaki ringa matsa mata akan sallah...koda wani lokaci tayi abinta ai duk sallah sunan ta ba canza suna zata yi ba...ke wannan da Liman 'din ne da kansa ya haife ki ma da bansan me zaki maida kanki ba wallahi...kinbibin masifa haba....!ta 'karashe da jan guntuwar tsaki.
Ni kam 'daki na na koma in mai girgiza kaina, sosai nake mamakin hali irin na Iyami tun ba yau ba...

Gata ne zaka yi wa amma har sai ya zarce 'ka'idan da ya dace ka nuna masa, miye laifi na dan nayi mata fa'da akan daidaita lokutan sallah.

Sai da na gama shan kokon da Iyami ta dama da ko wadattacen damu bai samu ba balle akai ga batun sugar duk na san Yah Bukar ya kawo Sugar jiya jiyan nan amma ni da Baba bamu ko ji alamun ta cikin namu abin 'karin ba, sai da na kammala kaf kafin na fito ma sake 'diban ruwa, shirin wanka nayi kaina sanye da hijabia na sai zani da ke 'daure daga saman 'kirji na..ina sanya takalma najiyo sallama daga hanyar shigowa.

Baki na washe ina kallon wurin duk ban ga mai sallamar ba amma na riga nasan wacecec, cike da fara'ata nace" Dijeh kamar wacce ki kayi kwanan mafarki na?"
Turus taja ta tsaya tana banko min harara tana fadin" da yake ni bana yin abin arzikin da za'a yaba min ko".

Baki na nayi saurin kamawa ina girgiza kai nace" Haba tawan, wace ni da fa'din haka kawai fa nayi mmkin ganin ki ne.."

" Barka na biyo mk mu wuce shiyasa nazo da wuri kafin in zo ban same ki ba"
Ta fa'da tana mai 'karasowa ciki.

Ga Iyami ta juya dake zaune bakin 'dakin ta tana sakace ha'kora..Khausar kuma ce kwance gefen ta ita kuma tana zane akan 'kasa.

" Ina kwana Iyami.."
Ta fada tana mai rusunawa cike da girmamawa.
Iyamin ma ba yabo ba fallasa ta amsa da
" Lafiya Dijeh...Ya Umman ki?"
" Lafiyan 'kalau Iyami".
" Naji kina cewa barka zaku ku da bakwa rasawa, wacece kuma ta haihu da zaku yi wannan sammakon?"
'dan murmushi Dije tayi sannan tace da Iyami" Marwa ce fa matar Bah Shehun mu..Jiya ta haihu da dare shine nace bari in biyawa Zaituna muje muga jinjiri.."
" Aikin kenan..."
Cewar Iyami tana mai kawar da kanta gefe...can kuma tace" Allah ya raya mata...ku ma 'din zuciya zaku yi kuyi auren ku haihu yafiye maku da wannan bibiye- bibiyen gidajen masu jego da kuke faman yi".
Murmushi kawai dukkan su suka yi, yayin da nayi saurin kamo hannun Dijeh muka shige 'daki jna washe baki nake sake tambayar ta da gaske Marwanatu ta haihu Dijeh..me ta samu kuma?"
" Yarinya ce aka samu, ni dai kiyi sauri muje..Ummata fa ta hanani wai sai de anjima muje da su Innani ni kuma zuciya ta ta kasa ha'kurin haka wallahi, ki hanzarta mu je mu 'dauki jinjira..."
" To zauna ki jira ni da Allah...yanzu ma 'dauraye jiki na zani sai kawai mu wuce ko..."
Nayi maganar ina mai nufan hanyar fita jikina har na rawa zabar zumudin da nake ciki, har na kusa fita sai kuma na juyo nace " amma fa ni ce zan fara 'daukan yarinyar idan munje ki Dije..."
" Wallahi ban yarda ba ke idan kin 'dauka bakya bawa mutun da wuri yau ni zan fara 'daukar ta.. haka ma fa Jinjirin Azeeman Yah Bukar ma hanani 'daukan sa kike yi kullum sai de ke..ranar sai da na san'di hanya baki sani ba naje ni ka'dai kafin na samu na 'dauki jinjirin"

Murmushi nayi na juya ina fa'din
" Bari ke de in yi in zo muje yau dai bazan hana ki 'dauka ba Insha Allahu..."

Duk yadda na ke jina cikin damuwa game da mafarkin da nayi yau 'din tuni damuwar ta kau sanadiyan jin labarin haihuwar da nayi, gaba 'daya hankali na ya tafi wajen gaba 'daya domin Allah yayi ni mai masifar son gani da 'daukar jinjiri, haka cikin hanzari na watso ruwan na fito na shirya cikin zani da riga na sake rufa hijabi na da ko gwiwa ba kai min yake ba amma dai nafi jin da'din sa akan sauran, sa6anin Dijeh da ke 'damare da 'dan gyalen ta yellow kanta 'daure da 'dan kwalin zanin jikin ta sai tshirt fara mara nauyi mai hoton keke a gaba.

Kamar yadda na saba duk ranar da nayi mafarkin sai na bawa Dijeh labari, haka kawai sai na 'dauri aniyar sanar da ita..amma yau din haka nan kawai sai naji bana da ra'ayi kuma, duk wata niyya ta ta son bawa Dije labarin ya kau naja kamar yadda nayiwa Yah Bukar al'kawarin bazan sanar da kowa ba.

_Shin wai wani irin mafarki ne wannan tayi ko kuma ince take yi ma?_

*Ku biyo ni dan jin me ke 'kunshe cikin labarin ZAITOON...taku ce mai 'kaunar ku da burin faranta ranku.....* 👇🏻

Salmerh ce😘
[24/12/2022, 11:00 am] Zee Ingawa: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...83*

......Zaune yake gaban wani dattijon mutumi da ke lullu6e cikin babbar riga, fuskar sa cike take da kamala da kuma annurin ganin 'dan 'dan uwan nasa.

" Allah yayi maka albarka Buba..Allah ya 'kara arziki ya kara rufa asiri, ai kai kam akwai 'ko'kari Buba...jiya ma nake gayawa mahaifin ka cewa wancan satin ka aiko mana da 'kashin miya yace ai bai ma sani ba...shima haka yaji miya daban da ya tambaya ake ce ai Buba ne ya kawo...Allah ya 'kara maka bu'di 'dan nan ai kai kam ba kamar su Muhammadu ba babu abinda suka iya sai shanshanci da rashin hankali.."

Murmushi kawai Bukar yy yana sake sunkuyar da kansa yace" Addu'ah za'a 'kara yi mana Baffah suma 'din Insha Allahu wataran zasu yi fin hakan ma.."
Kai Baffah Liman ya kawar yana fa'din
" Ashsha...ai yaran nan kawai addu'ar dai da kace itan za'a cigaba amma ina wani batu mai da'di kuma wajen su Modu..kwata-kwata bansan yadda zan yi da su ba ni..."
" Sai ha'kuri dai Baffah...Allah ya 'kara rufa asiri..."
" To Amin Buba...Allah kuma ya muku albarka ya 'kara muku zuciya...".

Murmushi yayi yana sake du'kar da kansa yace" Baffah dama Batun Zaituna ne nazo da shi...kwanaki na yiwa Baba magana sai ya nuna min ai bakomai, to abin dai da ya matsa shine na sake yi masa magana yace to zai same ka to kuma bansan yadda kuka yi ba..naga dai bai sake yin maganar ba....".

Hankalin wan mahaifin nasa gaba 'daya kansa ya dawo yana masa kallo mai cike da tambayoyi har sai da ya ji ya dasa aya sannan yace
" Wai wani batu kake nufi sam ban gane ba, Mahaifin ku bai zo min da wani batu kan Zaituna ba sam...ko batun auren dake tsakanin su da Babaji kake magana..?"
Da sauri ya girgiza kansa sannan yace" a a Baffah wani batu ne de na daban.."

" Au to ai kuwa ba muyi magana da shi kan yarinyar nan daban ba baya ga wancan...to ina jin ka Buba...me ne ya faru?"
Yayi maganar yana gyara zaman sa gami da maida hankalin sa kacokam kan Yah Bukar.

Nawi sosai yaji ya kama sa sai kuma ya rasa ta ina ma zai fara bayyana wannan batun, ya tabbata ko ita Zaitunar lokacin da ta fara bayyana masa abinda ke faruwa da ita wayo bai gama isan ta bane shiyasa, yasan da yanzu ne ba zata iya sanar da shi ba duk kuwa da irin kusancin da ke tsakanin su...shiyasa ma yanzu idan tayi mafarkin sai dai tayi ta kuka ga dukkan alamu ta fara fahimtar asalin me ke faruwa da ita ne shiyasa ba ta iya labartawa.

Toh shi kuwa ta ina zai dauko bayanin kenan tun daga farko, da ace Baban su ya fara maganar nr shima zai 'daura nasa amma Abban su bai yi hakan ba.
Chapter 146 · 0% Book details