← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 218

Sashe 117

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakin 'kofar ta take tsaye tana ihun, wutan ne ya hanata wucewa tuni kuma haya'kin ya gama ratsata duk ta fara yin sanyi...cikin sa'a sai yaga daga waje ana faman 6alle windown nata ma da yake suma awajen suna jiyo ihun nata.
Ana gama 6allewa ya taimaka mata ta fita 'yan waje suka kar6e ta cikin sauri yayin da hankalin wasu ya koma kansa cike da hanzari ya fara yun'kurin fita shima amma kafin ya kaiga hakan window ya 6antaro ya fa'do masa kan hannun sa, cike da tsananin wahala ya wani saki ihun aza6a ya zube kasa numfashin sa na 'kokarin 'daukewa.

Hankalin masu taimakon tashi yayi sosai, dayake ma kuma unguwar ta manya ce tuni sun yi magana da 'yan kwana kwana hakan ma basu tsaya jiran su ba ruwa suke 'debowa suna watsawa a kokarin su na ganin 'karfin wutar batai tasirin da zata iya illata wa'danda ke cikin ba cikin sa'a ma da fa'duwar Rayyan sai yan kwana kwanan suka iso har motoci biyu.

Su Anty Madeena ma Neighbours din su sun 'kira su sun dawo, fahimtar cewar da Rayyan acikin gidan ya sa Anty Madeena fara kuka sosai tana fa'din ataimaka mata...yaron ta na ciki.

Ganin abinda ya faru da shi kuwa ya sake 'dugunzuma hankalin ta..ta tashi hankalin ta ta kuma tada na sauram mutanen da ke wajen.

Hakan ne yasa da isowar 'yan kwana kwanan aka fara kashe wutar daga inda Rayyan ya fa'di,....da mutuwar wutan kuwa wasu matasa suka fito da shi kawai aka wuce da shi hospital batare da wani.6ata lokaci ba...daga shi har Nuwaira da tuni take a sume.

Babu wanda yasan mafarin wutan balle asan makasudin ta...babu wanda yasan dalilin ta.

Amma ba 'karamin tada hankalin ahalin Sa'ad Auta wutar nan tayi ba.

Daga Rayyan har Nuwaira jikin su bai kone ba but dole suna bu'katar kulawar likititoci...Musamman Rayyan da ya sha'ki hayakin sosai fiye da Nuwaira, an daiyi nasarar zu'ke haya'kin da ka'dan ya rage yayi masa illa ma dan tuni hayakin yayi masauki cikin zuciyar sa dalilin kenan da yasanya duk da an cire hayakin amma sai da sai da ya fa'da doguwar suma, domin kansa ya bugu sosai ga muguwar karayar da yayi a hannun sa na dama ga kuma zafin wuta da hayakin da ya sha'ka.

Ammi kuka da hawaye take haka ma Marwa da Amrah hatta Zaitoon sai da zubda masa 'kwalla dan ita ta fara kuka ne ma tun daga lokacin da labarin 'konewar gidan Anty Madeenan ya riske ta sanin cewar 'diyar ta na gidan...har Ammi na bata bakin cewa tayi hakuri..ita kanta Ammi a lkcn bata san cewa da gudan jinin ta a ciki ba...hasalima dan shi aka tada wutar gaba 'daya batare da sun san da hakan ba.

Sai da da suka je suka tarar da Mufee na nan zam a hannun Badi'a babau.abinda ya same ta sai dai Rayyan, anan zuciyar su ta karye gaba 'daya..Kukan da Zaitoon ke yi zaka rantse da Allah cewar Mufeedan ta ce aka ce ta rasu, ba 'karamin tausayi Rayyan ya bata da ganin yadda 'kasusuwan hannun sa suka sauka ba.

Ammi kam ai ba labari ma, yah Ilahi tamkar zata shi'de idan ka ganta duk ta fice hankalin ta haka ma sauran, Sultan ne dai babu shi a wajen ba kuma dalilin sa.

Rayyan ya sha ba'kar wahala wajen 'daure hannun nan inda aka yi sa'a ma yana cikin yanayin suma ne shiyasa sukayi at risk domin ta iya yiyuwa idan ya dawo hayyacin sa su tarar basu yi 'daurin bisa tsari ba sai sun sake amma dai basa fatan kasancewar hakan da iznin ubangiji.

Rayyan ya kai kimanin kwanaki shida kwance a asbitin batare da ya san inda kansa yake ba duk wani kokari daya kamata suyi sun jarraba dan ganin ya dawo hayyacin sa amma abin ya faskara har su Ammi sun fara tunanin fita waje da shi amma Fawwaz yace a a, yace a barshi tukunna bama sai an fita ba, dan dole can 'din ma ko an je duk abinda suka yi anan shi din za'a maimaita acan, abinda kawai ake bukata yanzu farfa'dowar sa ne...da dole sai an yi hakurin hakan.

Yace inda hali ma abinda yafi kawai a maida shi gida zai fi natsuwa, shi zai na zuwa duba shi inyaso duk ranar da aka samu nasarar farkowar sa sai a dawo asbitin a'karasa abinda ya kamata.

Anty Madeena ta so tace a a amma Ammi tace ta bari ai aikin su ne shi yasan abinda yafi dacewa ai..ko ba komai tasan Fawwaz aminin Rayyan ne ba zai ta6a yin abinda yasan zai cutar da shi ba.

Da wannan shawarar aka dawo da Rayyan gida sai dai kuma wani 'karin tashin hankali da suka fuskanta sine...kwanan sa 'daya agidan kwatsam sai mahaifiyar Amrah tazo gaida shi itama, dan tun faruwar lamarin sau 'daya tazo bayan nan suka yi wata 'yar tafia sai jiya ta dawo shine yau tace bari tazo duba shi.

Lokacin da tazo 6angaren Ammi.ta fara zuwa bayan gaisuwa suka dan sake jajantawa sai suka tattaro izuwa ga sashen Rayyan 'din bisa rakiyar Ammi.

Wannan karan dole sai da aka 'karawa Amrah masu tayata hidima sbd lalurar mijin ta, duk su Zaitoon sun dawo 6angaren ta, mai raino ma daban, ga su Anty Madeena da ta hana kanta sakat sai da ta dawo gidan itama sbd ciwon Rayyan din Raihana ma tazo tun washegarin faruwar lamarin kuma suna kokarin hudimtawa Rayyan da be masan inda yake ba, wani abin ne dai dole sai matar sa ko Sultan ya kamata suyi masa, hakan yasa suke barin wasu abubuwan ga Amrah.

Shigowar Mummyn ta yayi dai- dai da lkcn da Amrah ke gogewa Rayyan jikin sa ga kuma Arfan ma nata kuka, duk sai Amrah ta rikice.

Sauri take ta kammala hidimar Rayyan sannan ta dawo ga Arfan, cikin hakan aka sanar da ita Mummyn ta tazo.

Zaman jiran Amrah tayi na kimanin mintinan da basu haura sha biyar ba yayin da Raihana ke ta lallashin Arfan da 'kyar yayi shiru, kafin cikar mintina sha biyar din tuni 6acin rai ya gauraye zuciyar Mummyn Amrah.

Har ta shiga ta duba jikin Rayyan ranta bai saki ba, ta kuma riga ta kudurtawa ranta hukuncin da yai mata taga yafi dacewa.

Ko da suka ke6e da Amrah abinda da ta fara furtawa shine" Daughter jaka kk maida kanki a gidan nan wai ko me Allah ya nuna min..?"
Cike da mamaki Amrah ta dubi Mummyn ta.
" Jaka kuma Mummy kamar yaya...?".
Tayi maganar tana gyaran Arfan dake kan cinyar ta tana shayar da shi.
" Ke baki ganin yadda duk kika 'kare ne Amrah..?
ke ce kk haifa musu 'dan ne da zasu barki da jinyar sa ke ka'dai ga kuma 'dansa ma da kike fama da shi da wanne zaki ji..?"
'Yar murmushi Amrah tayi tana fadin..." Kai Mummy na sha wani abin ne ma wlh, bafa ni ke jinyar sa ba, Allah duk su ke yin komai ni nawa hidimar ka'dance, wannan da suke ji tamkar ya tashi 'dayan su ya kwanta a madadin nasa ne zasu barni da jinyar sa ni ka'dai...shi kuwa wannan 'dan banzan kuka dama gare shi da ni da Nannyn.nasa duk isar mu yake yi..."
Ta 'karashe maganar da jan hancin Arfan tana duban fuskar sa...
With serious tune Mummy Amrah cike da bakin rai tace.
" Ni dai wallahi bazan barki zama jinyar wani 'kato can ba maza tattaro kayan ki mu wuce gida..".
'Dan 6ata rai Amrayi tana karkace wuya tace.
" Haba Mummy...mijina ne fa kk ce wani 'kato bayan na fada mk ba wata hidima da nake ni dai babu inda zani wallahi..."
" Wallahi Allah sai mun tafi Amrah ta ya ma hankali na zai kwanta bayan na tafi na barki alhali idona ya riga ya gane min? dole ma mu tafi in kinga ban tafi dake ba 'kaddara wata uwar kk canza bani ba..amma matsawar ina nan a matsayin mahaifiyar ki to bazan ta6a barin ki cikin wannan 'kuncin ba..yaso idan Allah ya tashi kafa'dun sa kya dawo ki cigaba da zama...amma irin wannan wahala haka ina zaki iya juran sa na tabbata kafin a ce ya samu sau'ki ke kuma duk kin 'kare nima jinyar ki za'a barni dashi..."

Haka ta koma Parlor ta bar Amrah nata zum6ura baki tana ha'da kaya.

Ko da suka fita babban Palor su Anty Madeena ne zaune da Raihana sai kuma Sultan da shigowar sa kenan.

Cike da mamaki suke duban Amrah ganin ta da lullu6i da handbag tama kasa duban idanun su sbd nawin abinda Mummyn ta ta tsefe idanu take shirin aikatawa.
" A ah lafia na ganku cikin shiri haka, hala unguwa zaku..?"
Mummyn Amrah ta.bada amsa da fadin.." Ba wata unguwa, tafia zanyi da ita sbd ba ma'aikaciyar jinya na haifa ba..."
Cike da mamaki duk suka dube ta hatta da Sultan kuwa.

" Hajia Hafsat ban fahimta ba..me kk son fa'da ne...?"
Anty Madeena tayi 'karfin halin tambayar ta.

" Erh ina nufin bazan barta zaman jinya ba...tafia zanyi da 'diya ta...ku samu wanda zai muku jinyar 'danku amma ba Amrah ta ba..."

Amrah ji tayi tamkar ta saki ihu sbd takaici.

Taya ma Mummyn ta zata ce haka, a ganin ta ai hakan ma butulci ne, itafa tana 'kaunar mijin ta kuma bata ga wani abu da tayi masa da har za'a ce ya shiga layin 'kunci ko wahala ba..duk ma yawan mutanen gidan nan amma duk da haka ta wani ce sai sun tafi..abinda ma yafi tsaye mata arai shine cewar da Mummyn tayi wai da wanne zata ji a cikin su yanzu, da 'danta ko kuma da kulawa da majinyacin da babu ma tabbas 'din zai rayu...?"
Kuma ta fa'di maganar ne fa ga Anty Madeena da Raihana ga kuma Sultan ma zaune..sannan ta tabbata wasu ma'akatan gidan ma sunji salon su rainata ta ko menene.
Amrah ji tayi da tana da ikon bijirewa mahaifiyar tata da babu abinda zai hana ta bijirewa ta'ki binta.

Amma tasan halin mahaifiyar ta da zafin rai sosai akan duk abinda ranta bai 'dauka ba.
Chapter 117 · 0% Book details