← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 218

Sashe 170

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasbihi ta fara yiwa Ubangiji sannan ta 'dora da dukkan kalaman da tasani na godia..sosai ta nuna farin cikin ta a fili, tace wai yau gani ga jinin Rayyan tare da ni, ban san da abinda zan saka mk ba Zaitoon a duniyar nan, abu guda da nasani kuma shine bazan ta6a gajia da yi mk fatan alkhairi ba har 'karshen rayuwa ta, sannan zan mk alkawari guda, Insha Allahu kwana kusa zan sada ki da mahaifan ki domin su kansu sun cancanci yabo da haifa 'diya irin ki da suka yi...zan miki jagora kamar yadda nayi alkawari ba tun yau ba, zaki koma ga iyayen ki ki nemi afuwar su bisa ga abinda ya faru, domin ina da yakinin duk halin tsananin rayuwa da kk fuskanta abaya bakomai bane face ka'dan daga cikin 'kuncin da kk barsu a ciki, kk za6i Mufeeda akan zama da su, iyaye ba wasa bane Zaitoon, duk lalacewar su da kaucewar su matsayin su baya canzawa kuma yin biyayya agare su dole matukar abin sa6awa ubangiji ba..."
" Nagode sosai da 'kaunar da kk nunawa Mufeeda wanda nake da tabbacin ko da ace mahaifiyar ta ne iyake abinda zata yi mata kenan, sannan mu ma ki yafe mana bisa ga munana zaton da muka so yi mk a farko, duk da har ga Allah ni daga baya da kaina na fara kokonton kece kk haife ta amma dai still bani da hujjar da zata wanke min wannan zargin cikin raina..hkn yasa dole dai akan tunani na farkon duk muka tsaya, da ni Rayyan da duk sauran ahali na da suka aikata miki ba dai-dai ba...kiyi mana afuwa ki yafe mana kinji 'diya ta..? Bana jin wannan kyauta da kk yi min a yau akwai abinda zai kai min shi farin ciki har 'karshen rayuwa ta, bb mmk badan ke ba da har na bar dunia bazan samu rabon ganin jinin Rayyan da Nadia ba...nagode sosai Zaitoon Ubagiji Allah yy miki albarka ya raba ki da dunia da mahaifan ki lafia...Allah ya sa..."

" Ammi shi wannan 'din hala mantawa da shi kika yi da har kike fa'din haka...ko...?"
Cewar Amrah cike da raini da yatsina.
Dagaske Ammi ta mance da shi ba 'karyar Amrah bace, hkn yasa tayi saurin dafe kanta wani murmushi na 'kwace mata da zai sanyatar da zuciyar Amrah.

Anty Madeena ce ta banka mata uwar harara dama kufule take da ita tun farko da ta yiwa Zaitoon masifa, ga kuma sanin sirrin da ita kanta Amran bata san ta sani ba.
" Ko kunya baki ji ba..?"
Anty Madeena ta tambaye ta idanun ta cikin nata fuskar ta bb alamun fara'a sam.

Sosai Anty Madeena tayi nasarar rissinar da ita, domin kawar da kai Amrah tayi nan take tana mai jin zuciyar ta na harbawa da 'karfi, har wani 'daci take ji na taso mata sbd tsananin takaici.

Taso tarwatsa maganar Anty Madeenan dan fahimtar inda ta dosa amma ta kasa aikata hkn, illa tsoro da fargabar tonuwar sirrin ta da ya cika ta.

Salmerh😘
[27/4/2023, 9:30 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...95*

........" Abin kunya dan'kare cikin rayuwar ki amma har kina da guts fin tsomawa mutane baki cikin maganar su...?"

Ko zancen Anty Madeena na farko bai kai wannan soya zuciyar Amrah ba.

Sosai taji babu da'di ta kuma ji 6acin rai gami da fargaba matsananci ya kamata.

Fargabar ta 'daya ce na rashin sanin ainihin abinda Anty Madeena ke nufi da maganar ta, tsoro take ji kar ace tasan ko da guda ne daga cikin sirrin ta.

A zuciye ta tashi rungume da yaron ta mayafin ta na take mata baya tayi waje fuskar ta tamkar ba'kin hadari mai shirin zubda ruwa.

Tsaki Anty Madeena taja bayan ficewar Amran...sai dai tun ma kafin ta gama dawo da kallon ta cikin Parlon Ammi tace" Baki kyauta ba Madeena..ai bazata ji da'di ba ke kanki kin sani...".
"...so what rabu da ita dan Allah Hajia Aseeya, ina cikin yanayin farin ciki bana so takaicin ta ya canza ni...yarinyar bata da kunya ne sam...".
" Amma dai ko ba komai ai 'dan dai da take magana akai 'din ai shi dolen mu ne, sbd jinin 'dan mu ke yawo a jikin sa...ni shaf mancewa nayi da shi ma shiyasa na fa'di waccan maganar....".
" Ai dole ki mance tunda karere ne bb ha'din jini...".

Cewar Anty Madeena a zafafe tana mai kawar da kanta.
Duban hakika Ammi tayi mata tana mai son gano manufar maganan, a hnkl ta kirayi sunan ta sau 'daya tak..Anty Madeena yi tayi tamkar bata san Ammin tana yi ba.

Marwa ce ta mi'ke kawai ta kar6i Mufeeda dake hannun Ammi sannan ta 'dago hannun Zaitoon suka yi waje, ganin hakan yasa Badi'a da Imrana ma suka biyo bayan su aka bar Ammi da Anty Madeena ka'dai.

*****
Tunda ya fita ya bar parlorn yake jin zuciyar sa cikin wani irin yanayi da shi kansa bazai iya pointing takamamme halin da yake jin ta ciki ba, yana jin farin ciki tabbas da bayyanar wannan sirrin, amma ya rasa dalilin da yasa farin cikin nasa ya kasance ragagge.

Ya kwanta a 'dakin sa yaji baya da natsuwa sam, hakan yasa ya fito duk da ciwon hannun sa yk hakan bai sa ya gaza tu'ka kansa da kansa a mota ba.

Can gidan sa ya wuce yana sake tunowasu abubuwa da suka shu'de shekaru ka'dan baya.

_Nadia_ !
Sunan ya gifta masa cikin kwanyar sa.
Sai ya lumshe idanu ya kuma bude su nan take.
Wannan karan lips 'din sa ne ya motsa wajen furta sunan Nadia akaro na biyu.
Kai ya girgiza a hnkl yana jin wani irin cikin ransa.

Ashe tsakanin su bai 'kare ba..!
Ashe zai cigaba da ganin wani abu da ya dangance ta tare da shi...?
Har ya isa gidan tunanin da ke ransa kenan kuma koda ya shiga gidan ma still dai Nadian ne.

Sosai ya 6ata lokaci wajen tunani a wancan gidan, amma abinda yake 'daure masa kai shine rashin sukunin zucia...da 'kyar ya iya gano inda matsalar damuwar tasa take.

Ba'kin ciki 'dacin rai yake ji da kuma tsananin kishin da ya jima bai tsinci kansa a cikin sa ba.

Yanzu da ya tabbatar da cewa erh da gaske Aishatul Mufeeda 'diyar sa ce sai yafi jin haushin abinda Amrah tayi masa fiye da baya.

Sultaan...!
Wannan karan sunan da ya gifta masa cikin 'kwakwalwa kenan.
Sai ya rintse idanu da 'karfin gaske yana jin zuciyar sa na harbawa.

A yadda yake ji a halin yanzu baya ji akwai abinda yafi tsana da 'kin jini irin Sultan...Sultan yayi masa abubuwa masu dama da ya tabbatar daga yanzu har zuwa ranar da ransa zai bar dunia mawuyaci ne ya iya mancewa da su.

Duk yadda yaso ya kawar da tunanin cikin ransa kuwa sam ya gagara yin hakan.

Wata zazzafar wuta mai tiriri yake ji take ruruwa masa a zucia game da Sultan, tiririn da gaba 'daya yy nasarar lullu6e duk wani farin cikin da yake ciki.

Da 'kyar ya taushi zuciyar sa har ya iya lali6o wayar sa ya 'kira Fawwaz.

Bayan gaisuwa bai jira wani surutu ba, ko 'yar tsokana da Fawwaz din ke jansa da shi ma bai kula ba.

Bayanin duk abinda ke faruwa yy masa atakaice domin yasan Fawwaz ba abokin 6oyewa matsala ko damuwar sa ba ne balle abu irin wannan da ya riga yasan Fawwaz din ya jima da hasaso komai tun ma kafin shi ya fara tunanin faruwar sa, duk bai ankare ba sai yanzun da komai ya bayyana masa sannan ya tunano maganganun Fawwaz na baya.

Bai yi kuma mamakin yadda Fawwaz ya matukar nuna farin cikin sa a zahiri ba domin kuwa ya kasa 6oye tsananin farin cikin da ya shiga ga Rayyan.

Bayan ya gama da Fawwaz wata number ya kuma 'kira yy 'yar takaitacciyar magana sannan ya kashe wayar bai ajiye ta ba sai da ya sake amsa waya har sau biyu sannan ya ajiye wayar yana sakin zazzafan numfashi.

*****
Amrah kuwa can 6angaren ta ta koma ta fara zarya tama kasa zama waje guda balle tayi tunanin abinda ya dace, takaici da bakin cikin dake zuciyar ta gami da fargaba sune sukayi awun gaba da natsuwar ta gaba 'daya.

Layin mummyn ta ta fara laluba amma cikin rashin sa'a bata same ta ba...hatta na mahaifin ta ta nema shima baya tafia, duk din su kuwa ta gwada fin sau a 'kirga amma duk bb wanda ta samu ya shiga.
Haushi ya sake cika ta tayi saurin dafe goshin ta da hannun ta 'daya hawaye na ziraro mata.

Ji take tamkar ta tarwatsa wayar nan take sai Sultan ya fa'do ranta..domin dole ma ta neme shi kan batun nan, maganganun Anty Madeena karan tsaye sukai mata a zuci tana bu'katar fassarar su da wurwuri.

Tsoro take ji kar ace Anty Madeena tasan komai ne dan hk dole sai ta sako Sultan cikin lamarin dan 'kwa'kwalwar sa tafi tata ja acewar ta.

Sai dai ko da ta 'kira layin san da ta tabbatar dashi yake amfani acan shima baya tafia..har ta gaji da gwadawa cike da haushi kuwa ta ha'da wayar da bango tana zubewa 'kasa cike da takaici da kuma rashin madafa.
Karaya take ji na shirin yin galaba akanta dan haka kawai ta sanya kuka hadda 'daura hannu biyu aka hawaye na sakko mata shar shar.

Tashin farko taji ta tsani Anty Madeena tsana mafi munin bayyanawa.

Tuni wayar Amrah ta tarwatse a wajen, dama Samsung ba jure wahala take ba, ai kuwa lkc guda ta tashi a aiki dan ba 'karamin bugu tasha ba.

Ranar haka tayi kwanan ba'kin ciki a 'dakin ta dan ko shi Arfan ma tare da Nannyn sa yake bata sake bi ta kansa ba.

Notification na yawan neman da Amrah tayi masa da ya gani bayan bu'de wayar tasa washegari ya sa yayi tunanin neman layin ta amma baya tafiya.

Yasan tana can gidan Rayyan a halin yanzu, dan sunyi magana da ita kafin tahowar ta gidan ta kuma bashi tabbacin zata koma shiyasa bai yi tunanin zuwa gidan mahaifin ta ba.
Chapter 170 · 0% Book details