Sashe 95
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyan zucia ta sau'ke sannan ta 'dora da" Hakane Rayyan, Allah ya kare min ku, ya tsare min ku, ya dawwamar da farin ciki cikin rayuwar ku ya kuma wadata ku da imani da tsoron sa...".
" Ameen Ammi...muma Allah ya kare mana ke ya 'kara miki nisan kwana mai albarka ya kuma bamu ikon kyautata miki har 'karshen rayuwar mu..."
Murmushi tayi kawai tana kawar da idanun ta shima haka murmushin yayi.
Tun yana office 'yan sanda suke ta 'ko'karin takura masa kan bincike bisa 'konewar motar amma sam ya 'ki basu wata dama domin yasan wahalar da shi kawai zasu yi ta yi da zirga zirga, kuma shi bayi da wata hujja da makama bayaga zancen da Zaitun tai masa da safia wannan ma bai tabbatar ba duk da babu wasa tsakanin su balle yace wadsa take yi masa ya kuma san mawuyaci ne ta shirya 'karya haka nan kawai ta fa'da masa.
Kuma matu'kar ya kuskura ya furta wannan kalmar ga 'yan sanda bazasu ta6a barin yarinyar ba an ringa bincike kenan hakan kuma bazai ta6a bari Ammin sa ta nutsu waje guda ba itama ayadda ya fahimce ta, matukar aka fara binciken batun yarinyar itama Ammi bazata nutsu ba kuma shima baya 'kaunar yaga Ammin sa cikin tashin hankali.
Ai indai kere na yawo zabo na yawo dole wataran za'a ha'du...kuma ya riga yasan babu wanda ya isa ya yi musu abinda ba shine 'kaddarar su ba duk da hakan ya kanyi imagining duk ranar da Allah ya bashi ikon 'dam'ke makashin ahalin sa irin hukuncin da zai masa..fatan sa kawai shine Allah ya bashi tsawon rai ya kuma nufe shi da nasara a lokacin da ya fi dacewa, hatta su Huzaifan bazai dakatar da ko guda daga cikin su ba sai zai 'kara sanya idanuwa ga dukkan su...ya kuma sawa aransa dole sai ya kafa warning wa yarinyar can gudun kar tayi azar6a6in sanar da Ammi abinda ta gani ta bari kawai tsakanin su shi da kanshi zai 'dauki mataki akan koma wanene.
Da wannan tunanin ya koma 6angaren sa dai- dai lokacin da Amrah tazo ta mamayi tunanin sa.
Dagaske fa yayi kewar ta shi kansa yasan hakan, amma hauka da rashin hankalin ta yake so yaga iyakar su kawai shiyasa bai ta6a nuna damuwar sa ga kowa ba.
Bai samu lokaci ya yayiwa Zaitoon warning akan fitar da batun ba kwatsam bayan kwana biyu Sultan ya kira yake jajanta masa abinda ya faru nan yake maimaita masa batun kamar yadda Zaitoon ta sanar da shi, ya so yayi mamakin inda Sultan ya samu labarin sai dai cikin sau'ki Sultan ya warware masa komai cewa shima wlh Marwa ke bashi labari inda ya jajanta masa sosai ya kuma nuna alhinin sa gami da tabbatarwa Rayyan 'din cewa dole cikin kwanakin nan zai dawo a san abinyi kan lamarin.
Rayyan yayi saurin dakatar da shi da fa'din kar ya damu kuma da Allah ko yayi waya da Ammi kar ya kuskura ya sanar da ita gudun kar hankalin ta ya tashi inda ya tabbatar masa da cewa bazai fa'da mata ba kuma itama Marwa zai ja kunnen ta.
Da haka suka yi sallama kowa abinda ke zuciyar sa daban..shi Sultan dama ba so yake ayi ta ririta maganar ba gudun tonuwar asiri, yayin da Rayyan yaso yayi mamakin yadda akayi Marwa tasan labarin sai dai tuna kusancin da ke tsakanin ta da Zaitoon ya sa mamakin sa yin nasa waje..haushi ya maye gurbin sa.
Sosai yaji haushin Zaitoon da fa'dan ma Marwa maganar da tayi.
*****
Kwanci tashi rayuwa nata mi'kawa, Sultan ya dawo ya kuma matsawa Rayyan da batun dawo da matar sa gida inda ya nuna masa cewa ba mutunci ne zaman sa haka nan 'din ba a matsayin sa na babba gare su kuma madadin uba, duk abinda tayi masa ha'kuri zai yi ya mance da shi dama da ha'kuri aka san babba balle matsayin sa na namiji bai kamata ace yana biyewa shirmen mata ba.
Kallon sa Rayyan kawai ya tsaya yi yana murmushi da jin da'din kalaman dan uwan nasa, badan komai ba, bawai dan yana marmarin dawo da Amrah ba sai dan kawai ganin girma da mutuntaka da suka bayyana daga Sultan din.
Yayin da Sultan ya 'dora da" Kuma ma Yayah ai ko bakomai sai ka duba babyn mu dake tare da ita, ko dan shima ya kamata ace ta dawo kusa damu 'kar'kashin kulawar mu..ni bama sai kaje ba inka amince kawai zanje in dawo da ita..."
Duk da yaji da'din maganar Sultan din amma hakan bai hana shi fa'dan nashi ra'ayin ba.
" Ban amince ba Sultan ka rabu da ita, duk lokacin da tayi ra'ayi sai ta dawo da kanta ai ba nine nace ta tafi ba, ra'syin da ya sata tafita shi zai sake sawa ta dawo"
Ido Sultan ya 'kwalalo yana duban sa.
" Haba Yah Rayyan, sai kace bamu san darajar Babyn mu ba, ai in muka yi hakan a fili muka nuna bamu damu da cikin dake jikin ta ba...."
Karya wuya Sultan yayi ya cigaba" ni fa wallahi ba itan ce damuwa ta ba Yayah Unborn din mu ne, wai duk 'kauna da mura'din da muke yi akan haihuwa sai mu bar Amrah ta tafi can wata uwa dunia da ciki bacin muna nan araye da lafiyar mu kuma ba rasa abin da zamu kula da su muka yi ba...Ni nama yi mamaki wallahi yadda kayi biris ka share lamarin har tsawon lokacin nan...".
"
" Sannu sarkin surutu..".
Rayyan ya fa'da yana mikewa tsaye batare da ya bashi amsa 'kwa'k'kwara ba.
Sultan ya 'dauki kimanin yini biyu yana ro'ko da ban baki ga Rayyan game da dawowar Amrah amma ya'ki amincewa 'karshe sai da ya ha'da da Ammi cikin maganar kafin Rayyan ya amince masa zuwa dawo da itan ko za'a dace amma shi kam yace baya da lokacin zuwa.
Sosai Sultan yaji da'di, badan komai ya damu ya dawo da Amrah ba sai dan abubuwa biyu, na farko saboda cika burin sa da ya jima da shiryawa akan cikin nata, na biyu kuma saboda kansa ne, dan sosai yayi missing dinta.
Batun yau yasan cewa Amrah bata Kano ba tana can Kaduna, tunda kusan kullum sai sunyi waya da shi, ita kanta ma takan 'kira shi koda shi bai 'kira ta ba, kuma sosai take nuna masa irin kewar sa da tayi har ma hakan ya ta6a tunzura shi 'daura niyyar zuwa Kaduna wajen ta sai dai bai samu lokaci ba dan a dawowar san nan Rayyan ya ri'ke masa wuta da ayyukan office sosai.
Kuma duk da takan tura masa hoton ta harma da na cikin ta amma sosai ya matsu yaga cikin a zahiri kafin ya aikata shirin sa.
Tashin farko Sultan daga gida direct ya wuce Kaduna ko neman inda mahaifan Amrah yake kan batun bai yi ba.
Ko da yaje ba 'karamin ka'duwa yayi ba da ganin girman cikin Amrah ba yayin da zuciyar sa ta sake 'dokantuwa izuwa ga salwantar da cikin tun kafin ya dawo, tun yana Kaduna ya fara shirya yadda zai yi da cikin, wasa- wasa sai ga Sultan ya shafe kwanaki uku a Kaduna batare da sun dawo ba, sai da suka gama she'ke ayar su a hotel kafin ya tattaro ta suka dawo Kano.
Amrah sai 'kiran mahaifiyar ta tayi ta sanar da ita cewa Rayyan ya sa an dawo da ita gida.
Haushi ne sosai ya turnu'ke ran MUmmyn Amrah, tace" yasa an dawo dake ko kuma yaje ya dawo dake..."
Shiru Amrah tayi tana ta tunzura baki gaba, tasan dama mummyn ta sai tayi masifa ai, amma ita har yanzun bata san waye Rayyan bane shiyasa take fa'din irin wannan maganar.
Tsaki Mummyn Amrah tayi tana fa'din " Ke kika sani ai, ni gata na nema miki, ta ya zaki zauna da mijin da sam bai san darajar ki ba, tuni ma wannan auren ya fice min aka wallahi badan wannan cikin da ke jikin ki ba Allah sai ya rabu da ke...".
Da hanzari Amrah tace
" Rabuwa kuma Mummy? nifa ina son miji na...".
" Haka zaki ce min Amrah..? shiyasa kika biye yaudarar sa kika koma masa kenan batare da ko mu an tuntu6e mu ba ko? toh kiyi zaman ki tare da mijin ki amma wallahi ki sani..koma menene ya biyo baya kar ki kuskura ki sani aciki...mtheew"
Ta 'karashe da jan tsaki gami da kashe wayar.
Tsakanin mata da miji sai Allah, domin da farko Rayyan yaso share Amrah baiso ya nuna yama san da zaman ta agidan ba, sai dai tun bayan kwana biyu da dawowar ta da Ammi ta tara su tai musu nasiha game da zaman tare ya sa jikin sa yin sanyi, koda dare da Amrah tazo 'dakin nasa cikin kyakkyawar shiga kasa kawar da idanun sa daga kanta yayi, sosai cikin dake jikin ta ya 'kara fito da kyawu da tsarin ta, tun dawowar ta ya ke kaucewa ha'duwa da ita domin baya iya 'dauke idanun sa akan cikin, baya kuma so ta gano lagon sa, sosai ya ke so da muradin jin lafiyar babyn sa amma ya bar hakan cikin ran sa...bai ta6a sanin yana tsananin 'kauna da kewar Amrah da Babyn sa ba sai yanzun da take tsaye gaban idanun sa tana duban sa.
Kallon sakan kusan sha biyar yayi mata sannan ya 'dauke kansa ya cigaba da abinda yake cikin system 'din sa.
Ganin haka yasa da dan gudu gudu Amrah ta taho ta rungume shi daga bayan sa gami da sakin kuka.
Cikin kukan take furta masa kalaman ban ha'kuri da kewa da nadamar abinda ta aikata.
Rayyan bai hanata kukan ba kamar yadda bai tankawa kalamanta ko guda ba, sai dai shima kasa ta6uka komai yayi har zuwa lokacin da ya tabbatar wa ransa cewar kukan nata ya isa hakanan...kuma kalaman tan sosai suka yi tasiri aransa...hannun sa har rawa yake wajen 'ko'karin juyo da ita ta fuskance sa.
Yana juyo da ita at same time kuma yake cusa hannu cikin rigar ta.
Lokacin da yaji hannun sa ya sau'ka kan cikin ta ajiyar zuciyar zuciya ya sau'ke gami da sanya idanun sa cikin nata.