← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 218

Sashe 51

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga me fahimta zai iya fahimtar inda tunanin ta ya tafi da abinda take son ji sa6anin Raleeya da itama alhini ya cikata bata lura da hakan ba, sai ma cigaba da tayi da bawa Zaitun iya abinda ta sani game da Jihar ta Borno.

Zaitun banda salati cikin ranta babu abinda take yi, wai duk tana ina hakan ya faru..? Meyasa bata da labari sai yanzu?.

Tashi tayi tana toshe bakin ta da hannu dan yadda take ji kuka na shirin kwace mata.
Raleeya da idanu ta bita cike da tausayi da kuma jinjina halin tausayi irin na Zaitun 'din, not knowing that kanta take wa kukan, mahaifan ta, 'yan uwan ta, dangin ta, da kowa nata take tunawa.
Da sassarfa ta isa 'dakin ta, tana shiga ta maida 'kofan ta rufe, jingina tayi da jikin 'kofan ta sulale 'kasa tana sakin kuka, kuka mai tattare da ma'anoni da dama.

Ita kanta bata san tsawon wani lokaci ta 'dauka yashe a wajen take kuka ba, Mufeeda zuba mata idanu tai itama duk jikin ta yayi laushi tamkar tasan abinda ke faruwa.

Ashe rabon taji mummunan labari yasa ta fita ayau 'din, ashe dama kuka bai kare mata ba kwarin gwiwar da take tunanin ta bawa zuciyar ta duk ba nisa zasuyi ba ashe.

Tayi kukan da tun barowar ta gida bata ta6a yin irin sa ba, tsoro da fargabar ta cikin kowani seconds hauhawa yake da'da yi, dama can Zaitun muguwar matsoraciya ce, da jin wannan labari kuma tsoron nata sai ya 'kara tsananta, tasani ba sai an bata labari ba itq 'din shaida ce game da illar da 'yan ta'addan ke yiwa yankin su.

Gashi in tayi duba da labarin da Raleeya ta bata sai taji tsoron tunkaran hanyar, tana so taje taga ahalin ta amma in ba ta sama zata bi ta ina zata iya riskar su?
Idan itama taje aka yanka wuyan ta fa?
Kuka sosai ta 'karasa yinin ranar da shi har sai da taji kanta ya fara sara mata kafin ta sarara.

Bata 'kara iya fita cikin 'dakin ba har washegari, hatta abinci bata iya taci ba ta dai bawa Mufeeda gudun shiga hakkin ta.

Sosai taji jikin ta yayi sanyi, dukkan wani 6oyayyen raunin ta ya fito fili, shirun ta ya ninka na baya.
Kasa ma yanke takamamman shawarar da ya dace ta yi, shin taje ne ko kuwa ta dakata tukunna.
Idan taje aka kashe ta a hanya fa?
Ko kuma sai ta isa garin itama su 'dauke ta tamkar yadda Raleeya tai mata bayanin yadda suka 'dauke 'yan mata da matasan yara da dama a 'kauyen nasu.
Wannan wace iriyar musiba ce haka, sai yaushe ne zasu samu zaman lafia da kwanciyar hankali.

Gaba 'daya ta rasa mafitar 6illewa, 'karshe dole ta yanke shawarar bada tazara kafin zuwan ta, amma dole zata koma gida...ta tabbatarwa zuciyar ta.

Tun daga lokacin Zaitun bata sake walwalar kirki ba, in ma anga tayi walwalar to da Mufeeda ne, sosai ta shiga wani yanayi na tsananin tashin hankali da damuwa, ta ya ma zata ji farin ciki ne bayan jin labarin abinda ya faru.

Bata sake tattauna maganar da kowa ba, sai dai a kullum addu'ah take ubangiji Allah ya kare mata ahalin ta ya kuma kawo musu saukin lamarin.
Wa'danda aka tafi da su kuma tana nema musu sassauci wajen ubangiji ya kare su ya kuma ku6utar da su izuwa ga iyayen su lami lafia...bata yi 'kasa a gwiwa ba kuma wajen rokon Allah in har zuwan ta shine mafi alkhairi Allah ya bata yadda zata yi ya kuma bata daman zuwa nan kusa.
Tun daga wancan ranar bata 'kara fitowa koda wajen corridor bane balle har ta 'karasa can main Palor.

Cikin 'daki take zama tana kuma mamakin yadda har yau 'din da take 'ko'karin cike kwanaki hu'du cikin gidan bata sake ji ko ganin Hajiyar gidan ba...bata ma sake jin 'duriyar kowa da ya dangance ta ba, mamaki take dama wai haka Hajiyar ke rayuwa ita ka'dai bata da kowa.
Koda yake ita da take 'daki koda ace akwai wani na Hajiyan ai ba lallai ta gansu ba tunda ba fita take ba.

Zaitun akaran kanta 'karshe taga cewa zama gidan nan bazai yi mata ba, dan tun zuwan ta babu wanda ya bi ta kanta, babu wanda ya damu da lamuran ta, babu wanda ya damu da sanin halin da ta take ciki, hatta abinci tana ji ba dan albarkacin Raleeya ba ba lallai ne ta ringa samu yadda ya kamata ba.

Tsoron ta 'daya ma kar a kuma maimaita 'yar gidan jiya, bata da 'karfin zuciyar da zata sake jure irin wancan badakala da wahalwalun rayuwar da har abada bata jin zata iya mancewa da su.
Ha'duwar ta da Dr Rasheed ya kansance 'daya daga mummunan babi cikin rayuwar ta wanda ya tsaya mata a zuciya.

Tasan taimakon ta yy, amma daga karshe taimakon juye mata yy izuwa ga wani abu daban abin bakanta ruhi da zuciya, wadda bai tsaya iya nan ba hatta da gangar jikin ta sai da ya bayyana hakan 'karara, illah gagaruma yayi wa rayuwar ta illah kuwa ta har abada.

Kuka take haiqan irin kukan da ke nuna zallar tashin hankali da shiga taskun rayuwa, fuskar ta kife da 'daya daga cikin pillown da ke 'dakin yayin da Mufee ke kwance kan bayan ta tamkar goyo amma babu zani, duk tayi laushi itama ganin Zaitun cikin wani yanayi a kwanakin dole ya affecting nata itama.

A yau'din ji take tamkar ana shirin zare ranta ne gaba 'daya, meyasa tun farko bata tuna hakan ba sai yanzu, meyasa sai yanzu take jin bata da 'karfin gwiwa, ba tun yau tasan irin tashin hankalin dake faruwa a yankin nasu ba, ba tun yau tasan halin da suke yawan tsintan kansu aciki ba, amma meyasa a yanzun abin yafi shigan ta, sosai take hasashen halin da ahalin ta zasu iya fadawa, bata san wani iri bane sannan babu wani tartibin sani game da yanayin da suke a yanzu, taya ma hankalin ta zai kwanta ne...bazata iya ba.

A yanzu da take da burin ganin ta waiwayi gida ko da ba kwana kusan nan ba taya ma zata iya zaman gidan nan ba tare da aikin komai da zai kawo mata ku'di ba, banda bu'katun ta da na Mufee, ya zam mata dole ne ta nemi ku'din motar da zai kaita garin nasu...dan haka bazata iya zaman gidan nan ba da batasan me ke tattare da shi ba, bata san wace kaddarar ke 'kunshe cikin sa ba dole ne ta nemi mafita dan a yanzu tsoro take ji sosai, tsoron ranar da raunin ta zai dur'kusar da ita gaba 'daya.
Kafin faruwar hakan take so ta cimma wani buri nata koda guda ne tal.

*Comment, vote nd Share to other groups* .

Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
_Serlmerh-md_

🅿️ *...32*

.......Washegari misalin 9:13pm.
Kwance take tana maida numfashi 'kasa 'kasa fuskar ta yalwace da murmushin da ya 'kawata ilahirin fuskar ta, lullu6e take da wani babban duvet da ya mamaye dukkanin jikin ta illah kanta dake waje, ba 'karamin gajiya tayi ba, gaba 'daya ta jikkata, bata jin 'karfi cikin jikin ta kona miskala zarratin, hakan yasa ta kasa yin wani kyakkyawan yun'kuri balle ace ta mi'ke tsaye.
Tunani da shau'kin abinda ya wakana tsakanin su bada jimawa ba ya sanya murmushi kasa barin fuskar ta...sosai take so da kaunar sa take kuma girmama lamuran sa.

Tsawon mintina goma sha takwas tana ahakan sannan 'kofan bathroom da take fuskanta ya bu'du.

Tun daga 'kafafun sa ta fara bi da kallo har zuwa saman fuskar sa.
'Kugun sa 'daure yake da towel fari 'kal yayin da hannun sa ke rike da wani 'karamin towel 'din yana tsane ruwan jikin sa da shi.
Gargasar jikin sa ya kwanta luf sakamakon jikuwa da jikin nasa ke da ruwa har kana iya ganin 'digan su tun daga sumar kanshi har izuwa 'kafafuwan sa.

Kallo 'daya zakai masa kasam yana 'daga 'karfe sakamakon irin 'kirar da zaka fuskanta game da shi, ba fari yake can ba skin 'din sa choculate color ne sai idanun sa da suke da 'dan fa'di, sumar kansa kwance take luf gwanin birgewa, murmushi tayi tuno yadda suka sha drama da mahaifiyar sa kwanakin.baya kan ya rage gashin amma ya ki dole ta kyale shi.
Yana da dogon hanci da madaidaicin baki da ya taimaka wajen 'kayatuwar kyan fuskar sa.
Babban abinda yafi birgeta da shi shine jarumtar sa.

Sau 'daya ya dube ta ya 'dauke kansa.
Gaban mirror ya isa ya tsaya, 'kurawa mirrorn idanu yayi yana ganin kansa aciki tamkar wanda akace masa an canza masa kalar fuska ne, idanun sa yake gani da suke ja har yanzun basu washe ba.

Ciki ciki ya saki tsaki sannan ya waiga gami da tahowa cikin wani irin yanayi kamar zai nufi kan gadon sai kuma yayi turus ya tsaya batare da ya 'karasa ba, ko me ya tuno oho.
"...Amrah je ki tsabtace jikin ki kafin kiyi baccin pls..."

Ya fa'di a sanyaye a kuma dake sai dai kana jin muryar sa kasan farinciki bai gama wadatar sa ba.

Mi'ka tayi da ilahirin jikin ta tana daga kwancen..da wata muryar shagwa6a tace.." Baby ban gama hutawa ba fa...".
Ta 'karashe da turo bakin ta gaba.
Ido ya waro yana duban inda take da hannuwan da duk biyu ya kama kugunsa cike da mamakin ta yace " Amrah....."
" Baby Pleeease..".
Ta tare shi da fa'din hakan tana sake narkewa.

Yana shirin sake magana 'karan wayar sa ya dakatar da shi, duban sa ya kai ga wayar dake ajiye kan side drawer yamma da hadadden gadon dake 'dakin.

A hankali ya isa ga wayar... _Mum_ da ya ga ke yawo kan fuskar wayar da alamun hoton zuciya ya sanya shi saurin 'dagawa ya kai kunnen sa.
Chapter 51 · 0% Book details