Sashe 149
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muna cikin gudun ne nayi tuntu6e da wani abu da ban san ko menene shi ba, ai kafin nayi wani yunkuri ko dabara tuni na fa'di da ciki na cikin rashin sa'a kuma sai na fa'di akan wani gurbin karan dawar da ake yanke amma ba'a gama cire shi gaba 'daya ba, kuma ta sai tin ciki na....
Sau 'daya nayi ihu mai cike da azaba daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bu'de ido nayi na ganni kwance a wani babban asbiti dake cikin garin Maiduguri, wanda kusan zan iya cewa wannan shine shiga na cikin garin na farko.
Ashe Ummaru ne yaje gida da gudu arikice ya sanar da su wai Zaituna ta mutu da jini a jini .."
Jin hakan yasa mutane suka yi saurin kawo min 'dauki nan aka tarar da ni sume na kuma zubda jini ba 'dan ka'dan ba.
Yaah Bukar shine ya 'dauki nawin komai da akayi min a asbitin har suka dawo gida, kama daga kudin jinya 'karin jini da akai min har zuwa 'dinkin da akai min a wurin nan 'kasan cibiya ta ka'dan, kafin ya warke kuwa ba 'karamin wuya na ci ba sbd rashin samun cikakken kulawa.
A wannan kwanciyar tawa ma sake tabbatar da cewa ni din marar galihu ce, mutun 'daya ke tausayi na kuma shine ke min dukkan 'dawainiya sai 'kawa ta Dije da muke kusan yini tare da ita.
A lokacin na sake tabbatar da cewa babu 'kauna ta ciki kuwa hadda mahaifiya ta.
Domin har nayi ciwon na gama na cigaba da harkoki na ko da sau 'daya mahaifiya ta bata ta6a shigowa gidan mu da sunan duba ni ba...sosai abin ya bani haushi amma bani da matakin 'dauka...domin bani da ikon yin komai face illar da hakan ke sake yi min a zucia ta.
Ga gurbin ciwon nan har yau idan na ta6o shi na kan ji abin na dawo min sabo dal cikin raina.
Ashe ita ma Abban mu cewa yayi da ita ko da a cikin mafarki ta yadda ta taka 'kafar ta wuri na sai yaji dalili balle a zahiri sai ya daure ta, ni kuma idan ni naje wajen ta bai yafe min ba...ni sam ban san wace iriyar 'kiyayya bace wannan, a yanzun kuwa da nake fama da wannan ciwon sosai nake bu'katar mahaifiyar ta a kusa da ni, ina matu'kar bu'katan kasancewa tare da ita, ada har fushi nayi amma daga baya sai na fahimci ba laifin ta bane kawai tana jiye min mummunan bakin mahaifi na a gare ni ne, amma so da burin samun mace makusanciya abokiyar shawara kusa da ni wacce zata kula da ni ina ji araina tamkar da wannan burin rayuwa ta zata 'kare, ba 'karamin ka'daici ke 'dawainiya da rayuwa ta ba.
Bana son yawan fa'dan da Iyami ke yiwa Yayana saboda ni, abin na min ciwo sosai, ni kaina ina so ya huta haka nan, baya ga haka ma yau da gobe ya wuce ya wuce wasa, bana so watarana bakin Iyami yayi tasiri akansa tunda mahaifiya ce ita agare shi dolen sa yi mata biyayya ya kuma guji 6acin ranta, Yaah Bukar yana matukar kiyaye komai da 6ata mata amma a kaina hakan baya tasiri sam.
Ba kuma na so akai bigiren da hakurin Iyami zai kai ma'kura har ta furta wata kalmar da zata iya zame masa dafi mummuna cikin rayuwar sa, a koda yaushe alkhairi nake wa Yayana buri ba sharri ba.
Ba tun yau na fahimci cewa shima 'din iyami so take ta raba mu ba, na fahimci bata 'kaunar wannan shakuwar ta mu sam Iyami bata so ta ganni da kowa ma balle 'dan ta na cikin ta...hatta Dije ma dan kawai Allah ya hada jinin mu ne, kuma mahaifiyar ta ba mai jin ziga bace, amma Iyami ta so shiga tsakanin mu ta hanyar gayawa mahaifiyar Dijen matsalar da ke damuna na mafarki a tunanin ta hakan zai sa su gaje ni ne sai taga sa6anin haka.
Afa'dar Iyami wai idan mahaifiyar Dije bata raba Dije da ni ba to kuwa itama watarana sai ta kwaso musu abinda yafi 'karfin su domin mutanen 6oye ne dani kuma kullum lalu6a ta suke yi cikin dare..."
Ita kam bata wani bawa zancen muhimmanci ba shiyasa maganar bata je ko'ina ba, kuma ma ai tasan a da na kan sanar da Dijen abinda ke faruwa da ni wani sa'in ma itama Dijen na sanar da ita idan abin.ya damu zciyar ta shiyasa bata ji shi matsayin bakon lamari ba balle har ta kai ga daukan kalan matakin da Iyami ke fata.
Bayan wannan Iyami ta 'kara da wasu 'karairayin amma duk basu yi wani tasiri ba hakan ne yasa ta ha'kura ta fita hanyar su.
Juyi na sake yi ina jin tausayin kaina sosai yana 'kara kamani.
Tuno wancan maganin da Yayana ya kawo min ne ya sani ta shi nayi kamar yadda yace nayi duk na shafe jiki na da shi bayan na ji'ka da ruwa.
Addu'o'im da ya koya min shi nayi sau uku uku batare da na gaji da maimaita su ba sannan shima na shafe ajiki na... sai sannan na kwanta ban da'de ba kuwa bacci yayi awon gaba da ni.
Juyi mai kyau ban yi ba har garin Allah ya waye bayan anyi sallah an fito daga masallaci sannan na farka, zuciya ta fes na jita ba kamar yadda nake jin ta cunkushe abaya ba...bansan lkcn da na saki murmushi ba, har ga Allah sosai naji da'din baccin yau 'din, sosai naji da'din sabon canjin da na tsinci zucia a ciki wanda nasan ka'dan ne daga cikin falalar addu'an da nayi.
Da yake dama fa ni ba wani tuna nake da yin addu'an bacci ba har sai da na fara fahimtar wannan lalurar da nake fama sannan na fara tunawa da yin adduar duk da ko abayan ma na 'dan iya wasu amma sam baya zuwa kaina idan zan yi bacci, hakan yasa ban wani bashi muhimmanci ba, amma yau ka'dai da nayi addua'ah cikakkiya sai na ji da'din baccin sosai, ko mafarkin wannan uban ruwan ma da nake yi yau sam ban yi shi ba haka kawai sai nake jin kaina tamkar ba ni ba..." Allah yayi maka albarka ya 'karo maka farin ciki daumammiya Yaya na...".
Abinda na furta kenan a fili tare da mi'kewa na nufi hanyar fita dan 'dauri alwala.
Bayan kwana biyu Yah Bukar ya fara koya min adduo'in, amanar rasulu ya fara koya min sannan sauran addu'o'in wa'danda muka 'dan sha wahala kafin na koye su, amma dai Alhamdulillah yanzu duk na iya su sun zama tamkar wa'ka a baki na, kuma tunda na fara addu'oin ma sau 'daya kawai tayi mafarkin mutumin ya danne ni, da safe da na tashi naga sabon abu a jikina sam hakan bai min da'di ba amma ban sanar da Yayana ba gudun kar ya raina 'ko'karin sa akaina.
Haka naje nayi wannan wankan da Yah Bukar yace na ringa yi kafin nayi sallah idan na fuskanci canjin yanayi tattare da ni.
A hankali damuwar abin ya fara barin raina, har nazo na mance da shi ma kwata kwata, domin a 'kalla na 'dauki sama da kusan watanni shida ban sake ganin mutumin cikin bacci na ba, kuma nima ban yi sanya da addu'oi na dai dai da rana guda ba...sosai na dage da akan su kamar yadda Yayana ya koyar da ni...
Haka kuma babu abinda na fasa daga halayya ta na zuwa ganin duk wani sabon jinjiri da aka haifa saima abinda ya 'karu, wannan kam ya riga ya zame min tamkar jinin jiki kusan kowa ya sanni da wannan 'dabi'ar.
*****
Muhammad Babagana...shine wanda akai mana Baiko da shi, duk iyaye kowa ya riga ya san da zancen lokaci kawai ake jira a 'daura mana aure, shi 'din 'dan gidan wan mahaifin mu ne wato Baffa Liman, an mana baiko da shi tun bansan kaina ba, domin shekara ta goma sha 'daya a lokacin aka bada aure na ga Babagana...yanzu kuwa shekaru na goma sha biyar..'yan watanni kawai ya rage ayi auren sai kuma wani dalili na daban da ya kutso kai ya dan yi tsaiko ga taso batun, shiyasa a duk lokacin da muka je ganin jinjiri idan an haifa sai a dinga yi mana tsiya wai ai muma zamu haihun ne mu daina gaggawa tunda lokaci 'kalilan ya rage ayi mana aure su huta....
Tun bana damuwa da maganar har nazo na fara jin kunya a duk lkcn da aka fadi hakan.
Baya ga haka ma ya kan sani jin 'kaguwa da son ganin hakan ya tabbata zahiri.
Ada sam ban wani damu da auren ba, shi kansa Babagana idan ance min na tuna ranar da na gansa ma bazan iya tunawa ba, amma tunda mutanen nan suka ankarar da ni cewa da zarar na yi aure zan haifi mawa 'dan nima shikenan sai nake 'daukin ranar auren nawa yayi, badan komai ba sai dan kawai nima in ga na samu jinjiri kamar yadda wasu ke fada.
Idan a tuna hakan fa ni ka'dai sai na ringa sakin sassanyan murmushi.
Ba 'karamin 'kauna ce tsakani na da 'yan jinjiraye ba...sosai Allah ya jarabce ni da 'kaunar yara.
Kwanaki na tafiya, komai na rayuwa na sauyawa, yanzu bama zam iya tuna rabon da nayi mafarki da wannan mutumin na bacci na ba, da alamu dai nasara ta samu gare mu ni da Yayana....
Bam manta ba lokacin da Baffah Liman ya 'kira mi kan nayi masa 'karin bayani kan maganar da Yah Bukar yaje ya sanar da shi acewar sa, haka na ringa yi masa kuka na kasa fa'din komai...abin ya min wani irin bambara'kawai ne kawai, taya ma zan iya duban idanun sa na gaya masa ga abinda ke faruwa ni, Yayana ka'dai ne ya san komai kuma nasan shi kamar makullin sirrina yake kuma ban damu ba dan yasan hakan game da ni domin shi 'din mutum ne na daban a waje na, zaman mahaifi yake a gare ni da mahaifiya, yaya yake wani sa'in kuma ya kan kasance tamkar 'kawata.