← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 218

Sashe 209

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin ta tuna ashe ko gaishe shi ma bata yi ba, sai kuma taji kunya ya kamata.

Da sauri ta mi'ke ta nufi bayi, sam ta kuma mance cewa ba wani kayan arziki ke jikin ta ba sai data mi'ke 'din kafin ta ankara, ai kawai sai ta 'karasa bathroom din aguje..abin ya ha'de mata biyu.

Shi kam me zai yi inba daria ba bayan fahimtar manufar gudun nata.

Cikin ransa ya ayyana" Yarinya kenan, mene yy saura kuma yanzu...?"

Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar tayi breakfast kafin ya fita.
Itama daga nan ta mi'ke ta kama aikace aikacen gida dan dama ita ba gwanar son jiki bace.

Bayan sati biyu.....
Har zuwa wannan lokacin Marwa bata ziyarce ta ba.
Haka kuma ba'a kawo Mufee ba, babu ma wanda yazo gidan domin ta ko sau guda sai dai kawai masu kawo sa'ko, hatta daga gidan Ammi an aiko masu aikin gidan sun kawo mata sa'ko madadin Marwa ta kawo sakon da kanta suga juna amma sai aka bawa ma'aikatan gidan.

Haushin rashin zuwan Marwa kadai idan ta tuna wanisau tari sai dai taji kwalla na sauko mata.
Gashi itama Rayyan Bai sake kaita can ba, tamkar wacce aka kawo gidan kaso shiru bb kowa, sai dai tayi zaman ta ita ka'dai indai Rayyan bai nan, tun tana dan jin tsoro har tazo ta fara sabawa da Zaman ka'daici.

Da yake shima ya sani so ko ya fita baya wani 6ata lokaci sosai yake dawowa wai dan kar ka'daici ya dame ta..so in dai ba wani uzuri ya ri'ke shi ba bai fiye da'dewa ba.

In kuwa yana gidan bai barin ta ta huta, ya riqa tsokanan ta kenan, ayi fushi a shirya, wani sa'in in ya kunna ta sai taqi ko kallon fuskan sa ne sbd tasan daria zai sata.

Allah da ikon sa cikin lokaci 'kan'kani sukayi wani mugun sabo da juna, ita kanta atimes inta zauna ta kan Yi mamaki, shin dama haka Rayyan yake ne ko kuwa yanzu ne ya canza.
Sau da dama in Yana wani abin kallon sa baya idan ta Sam.
Tun tana mamaki har tazo ta daina.
Ina fa'da, hantara da kyarar da ada ta sansa da su, duk taga Babu su yanzu.
Ko kuwa dama can tsanar da ya mu su ne yasa yake musu komai da fada, hadn't been bai aure ta ba har zuwa yanzun, that means hakn zai cigaba kenan ko kuwa?
Da kanta tazo ta fahimci ba hakan bane Sam.
Rayyan bayi da bakin Hali Amma akwai zafin Kai Yana Kuma da fushi in aka riski wajen fushin...Amma sanyin halin sa ya rinjayi komai.
Hayaniya ce ta fahimci Bai so har gobe.
Wani lkc takance wata'kila dan yaga ta zama matar sa ne kuma cikin gidan sa shiyasa ya canza amma wata zuciyar takan ce da ita sam ba haka bane ya canza ne sbd akowani lkc yaga dama zai iya neman abu tattare da ke kuma bai 'kaunar a ahana sa..shiyasa ya canza dan gujewa hakan.

Sai dai sam can kasan zuciar ta ta kasa yin na'am da wannan batun, can cikin ranta take ji kamata yai tayi masa adalci..tasan idan hakan ya shiga ranta ya kuma samu waje ya zauna, toh mawuyaci ne ta ri'ka masa kallon daraja Koda Nan gaba.

Bata tsawaita tunanin take dakatar da shi, yawanci dama kuma zaman kadaici ke sata zurfafawa.

Gashi ko waya babu hannun ta balle ko Innar tane ta 'kira taji 'duriyar su.
sosai tayi kewar gida, yan uwa da danginta.

Sau da dama kuka kawai take sanyawa in ta tuna yadda 'kaddara ke walagigi da ita da rayuwar ta.

Musamman wannan da take ciki a halin yanzun, 'kaddarar aure tasa ta yi nesa da gida gashi ko wanda zai zo ya le'ka yaji ya take ma babu shi.
Ko ayau ma tunanin da take kenan.
Tana cikin wannan kukan Rayyan ya samo ta.
Da kyar ya samu tayi shiru sannan ya nemi jin dalilin kukan.
Bata yi 'kauran baki ba ta sanar masa kewar gida take da su Innar ta.
Ido ya 'dan zaro" Shine abin kuka har haka?"
Ta dube shi.
Shi kam ya cigaba da magana" naga ko jiya nace dake suna gaidaki, hatta Yah Abubakar ma munyi waya, kusan kullum ma muna gaisawa da shi toh menene abin damuwan hadda kuka irin hk.. ?"

Harara ta doka masa 'kasa'kasa, cikin ranta ta ayyana lalle ma wannan mutumin.
Afili kuwa cewa tayi" Kai ai kana tare da Ammi koda yaushe bazaka gane ba ?"
Tana fa'din haka ta kawar da kai.
Ya fahimci magana ta fa'da masa.
Sai kuma yaji jikin sa yy sanyi.
Shi kansa yasan bai kyauta ba sam.
Domin bai ta6a ha'da ta da 'yan uwanta awaya ko na rana guda bane.
Yana Kuma da yakini hatta 'yan uwan nada muradin jin muryar ta amma ya fuske kuma yasan ita batada waya a hannun ta balle suji juna.

Jikin ta ya janyoshi ya rungumo ta ta baya, da hannun sa 'daya ya 'dago kuncin ta, sai dai ya dubi fuskar ta sosai ya karanci yanayin da take jin zuciyar ta kafin ya sau'ke mata kiss saman goshin ta then saman la66an ta a hankali...suna ha'de idanu ya furta" I'm so sorry wifey".
Idanu ta lumshe bata ce komai ba.

" Me kk so ayi yanzu, tell me..karki 6oye min..kinji?"
Yy maganar a rarrabe.
Da jin hakan tayi saurin bu'de idanu sai dai bata motsa ba..lips din ta ka'dai ta motsa wajen furta" Mu koma can gidan kawai kusa da Ammi yafi...".
" are u sure?"
Ta 'dage masa kai slowly.
" Wasa kike yarinya.."
Ya fa'da yana murmushin da tasan bana nasarar ta bane.

Raba jikin ta tayi da nashi..ta gyara zaman ta sosai ta fuskance shi.
" Dan Allah fa Yayah! "
Ya dube ta sosai suka hade ido.
Sai ta toshe baki" Aww abban Mufee.."
" Hmm" kawai yace.
" Pls mana, ba Kaine kace in Fadi yadda nk so ayi ba...?"
" Yess...but ki canza wani ba wannan ba. ".
" ni dai mu koma can dan Allah, nafi so in riqa kallon mutane amma nan shiru kullum sai ni kadai.."
" Bagani ba".
" Ni a Ina nake ganin ka?"
Duban ta kawai yy cikin idanu.
Sai tayi shiru.
" Bakya gani na kk ce?"
Zata sake magana ya tare ta" Yarinya better keep quite wooo, bb wani inda zaki koma apart from this house, banda abinki ma nan fa gidan mijin ki ne, mallakin ki, kiyi iko da gidan ki, kiyi da mijin ki, kiyi da yaranki, kiyi da ma'aikatan ki toh me zai dameki.."
" Ni wlh duk ban so, Allah gidan yy girma sosai".
" Haba dai?"
Yace yana 'yar daria.
Tayi saurin 'dage kai alaman erh.
" Ai shikenan, dama wani abokin aikina ya bani kyautar 'diyar sa na aura, sai nace Masa ai Ni matata amarya ce ba yanzu Zan Mata abokiyar Zama ba, Amma yanzu tunda kince hk kawai zan aurota sai ku zauna ku biyu abinku. No more ka'daici or Girman gida... shikenan ko?"
" Oyah say thank u to me"!

Shiru bata amsa shi ba, Bai San wani tunani take ba but sarai ya fahimci maganan bai wani firgitata ba ita dai zaman nan 'dinne bata so kuma shine gaban ta a halin yanzu.

Mamaki ta bashi matuka, wai kardai ace yarinyar nan har yanzu bata san kishi ba?"
Bai tsinke da lamarin ba sai da yaji tana fa'din...
" Nidai nafi son gidan Ammi gaskia, idan ka auro waccan din kawai sai ka kawo ta gidan nan ita, amma dai kar ka ajiye ta a'daki na can 'dakin ka zaka kaita ko kuma aduba mata wani daban itama...".
" Wai dagaske kk ne?"
" Erh mana".
Ta fa'da da 'kwarin gwiwar ta.
Sai yy murmushin mugunta.
A fili kuwa yace" Shikenan zaki koma can 'din amma ba yanzu ba sai na kusan kawota sannan zaki koma, amma dai ni nafi so mu rayu anan mu biyu da yaran mu ka'dai"
" Sai zuwa yaushe zaka kawota?.
Zaitoon ko ta kan waccen maganar Bata bi ta ta jefa Masa wata sabuwar tambaya.
Yace
" Nan da lokaci ka'dan bi'iznillah"

Bayan kwana biyu
Rayyan ya kawo mata waya wai Marwa nason magana da ita.
" Amarya bata laifi..".
Cewar Marwa tana murmushi .
Itama Zaitoon murmushin tayi bayan fahimtar waye kan wayan.
Tace " bacin kun 'kini...kowa ma mancewa yy dani".
" Ba haka bane wlh Mamin Mufee, Ammi ce ta hana mu zuwa, wai ba yanzu ba tukunna, amma ai ko su Badiyya na son zuwa amma anhana kowa wai sai kin huta...".
" Sai kace wacce tayi gagarumin aiki?"
" Wama ya sani ne?"
Cewar Marwa...tana daria...sannan ta cigaba.
" Kinsan hutun kala kala ne, toh ban dai San wanda Ammi take nufi acikin su ba, amma zuwa yanzun wata guda kam ai nasan dai kin huta ko waya ataimaka abaki ko dan 'yan uwa ma da abokan arziki...Abinda na kira in fa'da mk kenan, wani shekaran jiya ya kir a wai yana neman ki, Inna tasa aka tura masa layina a tunanin ta wai muna tare ne, toh ko jiya ma ya kira nace ban hadu dake ba amma zan fada mk...yace sunan sa Shaheed.
" Laaa...Yah Adam ne!..dan Allah ki gaida min shi..."
" Anqi, ki 'kirasa mana, ai ni kam na gama nawa tunda na cika alkawari.."
" Kai Marwa, kar ki koyi halin mana kema, kin fa san ba waya gare ni ba, wannan mutumin kuma ko aron tasa baya bani toh taya zan 'kira sa...?"
Ta 'karashe da sanyin sauti tamkar zata Yi kuka.
Jikin Marwa sai yayi sanyi..tace" Toh shikenan idan ya sake Kira zan fada masa Insha Allahu..."
" Nagode sosai".
" Kar ki damu bakomai."
Daga nan sukayi sallama.
Taso ta kira Innar ta amma wayar ta riga ta rufu dole ta hakura.
Kawai kuma sai ta saka wayar agaba hawaye na bin kuncin ta.
Gaba daya tunanin gida ya mamaye ta lokaci guda.

Ji tayi da tasani da ma tun farkon fari dama bata amince da wannan auren ba...gashi ya sake nesanta ta da mahaifa da yan uwanta akaro na biyu.
Chapter 209 · 0% Book details