Sashe 176
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amra bata san wainar da ake toyawa ba dan ita ba gwanar kallon talabijin bace, har sai da 'kawar ta Ameera ta 'kira take tambayar ta abinda ya faru, dan acewar ta taji ana sanarwa da sunan mijin ta da kuma maganar kotu a gidan talabijin..?"
Cike da rashin damuwa Amra tace" wannan gayen! 'Kyaleshi ai fiye da haka ma zakiji indai Rayyan ne tunda ya saba dama..can aikin sane ya jingine ta..."!
" Aikin sa!"
Cewar Amira ta tambaya da mamaki.
" Yes...ke da can kina nufin baki san shi Lauya bane..?"
Da sauri Ameera ta tare ta da fa'din
" ke wannan fa daban ne wlh 'kawata, ni kaina abin ya 'dauki hankalina da zan samu dama sai na halacci kotun nan wallahi tallahi, fata na ma ace bai ga sanarwar mahaifiyar tasa ba ayi zaman, 'kage nake da son sanin irin shari'ar da za'ayi, mahaifiyar sa ce fa da kanta ta bada kashedin..kinga kuwa babban al'amari ne ai".
" Kai Ameerah kina nufin Ammi da kanta?"
" Ita dai.. ko ke baki ga rahoton ba ne...?"
" Ban ma bude Tv yau ba sam".
" tab an kuwa yi bb ke madam..wlh kallo ya barki, ki tuntu6i mijin naki kiji labari toh, nayi mmk ma da har sai da Ammin ta kawo nan, shi da take da damar da zata han fita ko'ina daga gidan ma, taki ka'dan fa zatayi ta cimmasa a 6angaren sa amma har sai da ta kawo nan? ko de bakwa gari ne ke da shi..inji...?"
" Muna nan.."!
Ta bata amsa a takaice da 'dan sanyin sauti.
" Ikon Allah, rabon dai muma muji labarin ne...".
" Ai kuwa! Ku kuma 'yan jiran kota kwana ko? 'yan fa'di ku 'kara"
Dariya Ameera tayi Amra kuwa tace" Wai me tace ne Ammin? Ameera dan Allah sanar da ni, kin sani a duhu fa wlh..ni kinsan ba lallai in sani ba ai..?"
" Inajin shari'a ce tsakanin shi da wasu 'yaran nata daban a yadda dai bayanan suka fito, ko kuma cikin dangi haka da alamu kuma ita bata so hakan ba, ina jin bada son ranta aka shigar da 'karan ba..."
" Yaranta kika ce Ameera..?
" Erh"!
" Anya kuwa?..Kinsan hadin.kan yaran.Ammi kuwa...bana tunanin hakan gaskia sai dai ko a dangi din..amma sunan wa kk ji ta ambata?"
Amra ta tambaya wannan karan cike da ru'dani.
Yayin da Ameera ta cigaba da fa'din" Sunan Rayyan ka'dai nima naji...ni kaina nayi mamaki, gasu sanannu a gari mafi yawa kowa ya sansu, shiyasa kowa ke 'daukin zuwa ganin tataburzar..."
" Yah Subhanallahi...!"
Amra tace tana dafe goshi, take ta nemi nutsuwar ta ta rasa, tsoron ta 'daya kar ace da Sultan za'ayi wannan zaman shari'ar, indai hakane kuwa itama ai zama bai ganta ba domin tasan kashin ta gab yake da bushewa.
Bama tasan lokacin da ta raba wayar da kunnen ta ba sbd tashin hankali.
Kalma guda kuwa ta innalillahi ta kasa zuwa mata kan harshen ta.
Safa da Marwa ta fara cike da tashin hankali har wani zufa ke karyo mata banda jiri da take gani.
Wani 'karan 'kira sake ji a firgice ta 'dago wayar abin mamaki wata tsohuwar kawarta da har ta mance ma da ita bama tasan har a lkcn tana ajiye d number din ta ba sbd rushewar da zumunchin tsakanin su yy da jimawa wai ita ke kiran ta.
Ta riga tasan duk dai batun bazai wuce wanda ke gaban ta a yanzu ba..hakan yasa bata daga ba,.ko da wani kiran ya sake shigiwa a karo na biyu rejecting kawai tayi ta na mai jan tsaki cike da haushi biyu.
Bayan nan ta sake samun kira daban daban har guda biyu da sabbin lambobin da bata ma san ko su waye ba amma duk bata koyi alamar zata daga ba har suka katse.
Nombobin wayar Rayyan da na Sultan kaf sai da ta gwada amma bata samu ko guda 'daya tayi ringing bama balle ta samu arzikin 'dagawa.
Hakan shi ya sake tayar mata da hankali ya kuma hargitsa mata lissafi baki 'daya.
Ammi ka'dai ta samu, kuma itan ma bata 'daga wayar ba, haka ma Marwa da dama hankalin ta ba jikin ta yake ba a wancan lkcn.
Hankalin Amra dai hankalin ta inyayi dubu to ya tashi..dama hausawa sukace..aikata alkhairi sai kaga alkhairi...in sharri ka aikata nutsuwar bata dawwama har abada.
*****
_Washegari 8:22am_
.......Tsaye yake gaban madubi ya 'kure madubin da shanyayyun idanun sa da duk suka rine suka koma jajaye sbd stress, rashin bacci da kuma damuwar da ya sanyawa zuciyar sa..sai dai duk da wadannan 'kalilan din karaya ko sassauci babu tare da shi.
Shirye yake cikin ba'kin dogon wandon wani ha'd'ddaden silky suit mai 'dan karen kyau da tsada, farar 'yar cikin kawai ya sanya sai Ma'daurin wuya da yake shima ba'ki, hular da kai tsaye take nuni da bayyana ko shi'din wanene rike a hannun sa ya mayar da idanun sa kanta tamkar bai ta6a gani ko amfani da ita ba akafta 'din rayuwar sa..tamkar yau ne farko ji yake tamkar a yau zai fara sakata.
Kuma hakan yake ji har can kasan zuciyar sa, domin shari'ar da yake da burin gabatarwa ayau din tasha bambam, tabbas ta banbamta da kowanne...Bai ta6a tunani ko hasashen amfani da su nan kusa ba tunda ya ajiye su.
Domin rabon sa da sanya su har ya mance, amma hakan bai sa ya mance da dai- dai da 'kwayar zarra daga cikin matsayi ko yanayin aikin sa ba.
Sai ga shi ayau wata matsala ta tunzura shi ya sanya su, matsala ma ta cikin gida, matsalar da ta bambamta da duk wasu matsolin rayuwar sa.
Duk da yake har a lkcn bai janye ba, bai kuma yi nadamar taki guda na abinda ya aikata ba, saima 'kwarin giwa da yake ji, amma can 'kasan ransa yake jin bb da'di, can 'kasan zuciyar sa yake jin kamar bai yiwa Ammin sa adalci ba da be nemi shawarar ta tun farko ba.
Kuma sarai yasan halin ta, akan Sultan sosai zata nuna 6acin ranta idan taji abinda yake shirin aikatawa, amma ko hakan ma zaiyi ne sbd wani dalili, ba wai dan son zuciyar kadai ba.
Dalili kuwa shine sbd _Ammin sa_ , domin matu'kar Ammi ta sani bazata ta6a barin a hukunta Sultan ba ya sani, 'karshe ma cewa zatayi a ' _kyale shi_
Wannan kalami na Ammi ya jima da haddace su, tun yana 'dan 'karami matukar akayi musu zalunci sai tace a kyale mai shi Allah na sane da komai..zata ce a kayle sa da halin sa ne ya riga ya sani..za kuma tace su yafe masa kawai abarshi yy rayuwar sa bayan basu da tabbacin iya gejin da abin zai tsaya, shin zai tsaya ne ko zai cigaba akansu da ma wasu daban, basu da tabbas din Sultan zai rabu da wannan ba'kar zuciyar da ya sanyawa ransa ya fuskanci dai- dai ko a a.
A ganin sa hukunta Sultan shine dai- dai, dole sai ya hukunta yaron nan, dole sai yasa an ladabtar da shi, bawai dan baya so ko 'kaunar sa bane, ko dan ya tsane shi ba, a a zai yi komai ne bisa gaskia da adalcin da yasan Allah ma bazai ta6a kama shi da laifi akan sa ba...duk da yake yayi masa munanan abubuwa amma har a lkcn yana jin 'kaunar sa aran sa..'kauna matsayin dan uwan sa na jini, shi yasa yake jin nawin wa'dannan kayan dake jikin sa sbd Sultan, Marwa da Ammi.
'Dagowa yayi ya sake duban kansa a madubi still yana shafa hular aikin nasa, tamkar wanda aka bashi umarnin hakan lokaci guda ya tsaya cak, sai yaga tamkar mutum ne bayan sa a tsaye ba kuma ya ganin ko wanene sbd fuskar lullu6e take da fararan gashi ko'ina.
Hular da ke hannun sa yaji an ansa.
Kyam yaji ya tsaya tamkar mutum mutumi.hadda idanun sa guri guda suka tsaya suka daina juyawa.
Bazai iya fasalta yanayin da ya shiga a lokacin ba domin ji yayi tamkar kwakwalwar sa ta dan je hutu da aiki na dan lokaci.
Sanya masa hular yaji anyi akan sa, kana ba'kar babbar rigar aikin nasa itama aka warware ta aka rufa masa ita daga bayan sa.
Sosai mamaki da al'ajabi suka kamashi ganin faruwar lamarin yayi tamkar cikin mafarki.
Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su cikin madubin bayan dawowar brain din sa daga aiki..sam ya kasa 'dauke idanun sa daga kan hoton sa da yake gani cikin mirror 'din kamar yadda ya kasa fahimtar abinda ya faru yanzun nan... shin shi 'din ne ya sanya kayan ko kuwa sanya masan akayi..?
Yana kuma iya hango bayan sa babu kowa ba kamar dazu da yaga tamkar da mutum tsaye ba.
Sam baiji tsoro ko firgici ba kasancewar Rayyan asali namiji ne, me dakakkiyar zuciay lamba daya.
Hakan yasa bai ji tsoro ko shakkan waigawa ba gaba 'daya amma baiga kowa bai ga alamun kowa ba kuma illah kafa'dun sa da yake ji tamkar da hannun mutum a kai...Koda yayi niyyar 'dago hannun sa dan ta6a bangaren kafadar dayake jin tamkar an dafa shin kuma sai yaji hannayen sa kuma sun masa nauyi nan take.
Hakan ya faru ne cikin 'yan 'kalilan din dakikai.
Sosai kayan sukayi masa kyau, suka kuma canza masa kamanni daga Dr Rayyan Sa'ad izuwa Barrister Rayyan Auta.
Kallon gefen kafa'dar tasa yy by his right inda yafi jin alamun mutum amma babu hannu akai shidai bai ga komai ba amma yana iya feeling dafa shi da aka yi hakan kuma shi ya haifar masa da tashin tsigar jiki.
Sam bai ji ya tsorata ba, bai ji fargaba ko firgici da jin hakan ba, sai ma wata 'kwarin gwiwa da yake ji na shigan sa.