← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 218

Sashe 102

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lissafin time yayi yaga bashi da isashshsen lokaci, ga azahar ya riga ya gabato ba'a abin ya 'kira Huzaifa yazo ya kaita gidan ba amma zaman jiran sa ma ai aiki ne, toh ko office din zai wuce da ita yaga sam ina, itama ai yanzu haka tan bu'katar wanka, abinci, natsuwa or may be bacci da sauran su, da kulawa da ita zai ji ma ko da ayyukan sa... shawarar zuciyar sa yabi kawai ya mi'kata gidan Anty Madeena in yaso bayan tashin sa a aiki sai ya biya ya 'kara sa da ita gida ko kuma ya kuma tura kawai akaita can gidan.

Karshe dai gidan Anty Madeenan ya kaita yace " Anty dan Allah ina da ayyukane, anjima da yamma ko gobe zan dawo in 'dauke ta amma kar a gayawa Ammi tana nan kar ma a sanar da kowa cewa Babyn ta nan..."
Kai Antyn ta jinjina masa, shi kuwa ya fadi hkane badan komai ba sai dan kar Ammi taga kamar da gangan yayi hakan dan ya 'kuntatawa Zaitoon alhali ba haka bane.

Fita yayi bayan kamar mintina ashirin har yayi salla kafin ya dawo da kayan ciye ciye da su pampers da komai da yasan Feefy zata bu'kata ya ajiye mata, hatta tarkacen skul 'din ta duk sai da ya shigo da su ya kuma ce idan ta fara kuka su 'diga mata maganin bacci.
shima drop 'din da kanshi ya kai siyo shi.

Wannan ne kadai Anty tayi magana akai inda tace
" A a fa Rayyan kar ya cutar da ita..miye abin sai an bata drop an sata baccin dole..."
" Babu abinda zai mata Anty bacci kawai zatayi banaso ta dame ku da kuka ne..."
" Amma ai da shiga hakki...?"
Cewar Anty.
Kai ya girgiza yana shirin mi'kewa yace " Anty sai.kacr baki san yarinyar nan ba, Allah kuka zata tai muku abanza.."
" Babu ruwan ka idan ma tayi kukan kai ina.kake...?"
" Ai shikenan Anty nikam na wuce..."
" Adawo lafia...".

Daga haka ya bar gidan ya koma office.

Kusan hauka Zaitoon tayi ganin har yamma babu su babu labarin su, hatta abinci yinin ranar kaf bata sa a bakin ba tun breakfast din safe, Sallah ka'dai ne take iyawa batare da jin bata da kwarin gwiwar yin ta ba, ko aiki ma ranar bata wani yi na kirki ba, da ace a hannun wani yarinyar take misali Ammi, Marwa ko Sultan da sam bazata damu ba kamar yanzu da ya kasance tare take da Rayyan, bata manta ba kwana biyu kacal da ya gabata shi yayi sanadin fitan jini a bakin yarinyar wanda har yanzun ma gurbin ciwon bai gama barin bakin ta ba, idan ta tuna hakan sai taji ta rasa natsuwar ta gaba 'daya yayin da haushin sa ke kara ninkuwa mata.

Wankan jikin ta ma sai da Marwa ta shigo ta tilasta ta yinsa tana zolayar ta da fadin" Raguwar uwa maras dauriya...tace since from her day one in skul kin wani gigice haka kamar wacce akan ta aka fara, tace makarantar da an fara ta kenan har zuwa nan da shekaru masu yawa Allah ne kadai yasan iyakar yaushe karatun nata zai tsaya, ba mamaki daga nan har Phd...tace kuma ma Yah Rayyan 'din ne baki sani ba kome, ko kina tunanin zai 6atar miki da yarinyar ne...shi 'din fa kaf Kano ba 6oyayyen mutum ba ne miye abin tada hankali Zaitoon..ji yadda duk kika takura kanki....?

Shiru tayi kawai bata tanka Marwa ba amma tunanin wancan ranar kawai take, babu mamaki ita Marwa ta mance ne da batun saboda ba'a idanun ta komai ya faru ba, amma ai ita bazata iya mancewa ba har abada, wancan ma gaban idanun kowa ne balle kuma baya tare da kowa sai ita sai shi ai Allah ne kadai yasan muguntar da zai mata.

Marwa kamar ta shiga zuciyar ta sai cewa tayi" Ko abinda ya faru shekaran jiya ne kike tunani har kika ri'ke a ranki...?"
Shiru Zaitoon tayi cikin zuciyar ta tace..." Ashe kin ma sani..."
Yayin da Marwa ta cigaba da fa'din" wannan ma nasan bisa kuksure ne, amma Yah Rayyan din shi bayi da abinyi ne da zai tsaya mugunta wa Mufeeda? kema kinsan ba hka bane...duk tunanin da zaki yi akan sa Allah ba haka bane kawai dai jinin ku ne bai ha'du da shi ba shiyasa..amma ki kwantar da hankalin ki na tabbata ur daughter would surely come back home safely nd healthy Insha Allah I assure u this...".

Bayan fitar sa ne Anty Madeena ta fara ragewa Mufeeda kayan jikin ta 'karshe da pant kawai ta barta tana 'kiran Nuwairah take harha'da kayayyakin da ta cire mata..." Nuwair....cak maganan nata ya tsaya sakamakon wani gani da idanun ta suka yi..fat fat fat...zuciyar ta ya fara ya fara harbawa ta tsura mata idanu.

A hankali ta kai hannu jikin Mufeeda tana kama yatsun hannun ta, hannun Mufeedah tayi saurin sakewa tana mayar da nata hannun saman cikin Mufeeda, wani ba'kin abu tamkar tabo, ba'ki ne sosai tamkar an shafa ba'kin Paint, kwatankwacin girman sa kamar coin yana nan daga gefen cikin Mufeeda 6angaren dama, shine ya 'dauki hankalin Anty Madeena har Nuwaira da ta ke ta kwala 'kira tazo bata ma sani ba.

Hakika wannan al'ajabi da yawa yake..toh me ya kawo hakan? menene sila, ta jima tana kallon kamannin yarinyar da ahalin wanta marigayi Sa'ad Auta a fizge, haka nan kuma bata ta6a bawa abin muhimmanci ba, but after seeing this bata jin zata iya yin shiru har sai ta ji me yake faruwa? Menene yake 6oye da bata sani ba? me su Ammi Aseeya ke 6oye mata tsawon lokacin nan..?

Koka'dan ko da wasa bata manta da nasa ba lkcn yana 'karami kuma tana da ya'kinin har girman sa abin yana nan bai goge ba, ta tsinci zuciyar ta cikin tsananin mamaki da al'ajabin da bata jin zata iya 6ata tsawon lokaci batare da tayi binciken da ya kamata ba.

Da gaske akwai ayar tambaya, tun a farkon fari meyasa suka zo gidan...?
Amsa Ammi Aseeya ta sanar da ita komai cewa yawon bara suke har suka taka sahun 6arawo zance har kotu sai dai bincike ya nuna bata da laifi kotu ta wanke ta shine ita kuma ta taho da ita..."
Ta yadda da wannan but on what Purpose?
Ammi Aseeyah ta sanar mata da cewa zata na mata aiki ta biya ta saboda tafi san irin su wa'danda basu san ku'di ba balle su dasawa ransu ha'inci duba da yanayin rayuwar gidan su....
Tabbas ta yadda da wannan 'dari bisa 'dari.

Amma a wani dalili Ammi Aseeyah ta basu masau'ki daban da na sauran ma'aikatan ta...?
Babu amsa.

Meyasa aka sau'ke ta a 'dakin Safaa...?"
Bata sani ba.

Meyasa Ammi Aseeya ta bata yaddan da har yasa ta sake mata ragamar komai na gidan batare da wani shamaki ba..?"
wannan ma bata da amsa.

Meyasa har aka sa ta aiki 6angaren Rayyan...?
No answer...

Meyasa Ammi Aseeya ta bata daraja fin sauran duk masu aiki da take yi...?
Cikin maganganun Ammi Aseeya ta sanar mata da cewa haka nan kawai take jin tausayin ta tana kuma jin ta tamkar 'ya take a wurin ta da bazata iya mata rikon househelp kawai ba face 'yantacciyar 'ya a wajen ta.

Tambayoyi ba ka'dan ba sun jima suna trending a brain din ta, meyasa sha'kuwar su da Marwa kullum 'karuwa take...hakika dole akwai wani abu da ita bata sani ba.

Sai dai bata fatan ji ko ganin mummunan lamari game da ahalin wan nata, amma tana tsoron sakamakon da zata binciko game da wannan batu dan tabbas wannan daga jinin Sa'ad Auta ta fito bata tantamar haka.

Salmerh😘
[25/10/2022, 1:09 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...60*

......Wayar ta tasa a akawo mata ta k'ira shi sai dai bai samu zuwa akan lokaci ba sai bayan ya tashi a aiki.
Anty Madeena cike da 6acin rai take duban sa har abin yaso bashi tsoro.
Sai dai wannan kallon da take masa shafan mai akan tambayar da ta jefa masa wacce ya jita tamkar saukan ruwan zafi saman fatan jikin sa.
erh mana ruwan zafi dan shine zafi da radain.sa ke rasawa direct izuwa ga zuciyar ka...amsa kuwa maganar tata ta fara yi masa har bai san lokacin da ya mike tsaye ba a firgice..." Wai Rayyan dama wannan yarinyar 'diyar kace shine kk 6oye mana ko kuwa ni ka'dai kake 6oyewa.....?"
Da 'kyar ya iya sau'ke idanun sa kanta la66an sa na rawa ya furta"...Anty wace yarinyar kike magana akai...?"

Harara ta buga masa " Wace kuwa banda Mufeeda..kar ka raina min hankali Rayyan...".

Ido yazaro cike da firgici yace " Anty Mufeedah kuma...? Ni 'din...?"

Kai ya girgiza yana sau'ke ajiyar zuciya yace" wlh kin bani tsoro Anty, ni har na isa in 6oye mk abinda na jima ina nema ne Anty?"

" Maganar fahimta nk so muyi Rayyan kar ka 6oye min komai...wato dama munafurtar mu kayi ganin ta haifa ma yarinya shine ka shirya kawo ta gida ta hanyar Ammi Aseeya da sunan taimako mata ko...?"

"...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..Haba Anty mana, haba dan Allah..sai kace baki sanni ba, Anty manta waye Muhammad Rayyan kika yi ne...ban san inda maganar ki ta nufa ba sam how I wish mafarki nake...".

Ya 'akarsa da dafe kansa da duk hannuwan sa biyu, sosai yake jin babu da'di da kalaman Antyn tasa.

Wani gatsau- gatsau yake jin suke sukar sa hatta kansa juya masa yake yi.

Bata ce da shi komai ba sai ta fara kiran mai aikin ta..." Nuwairah!...Nuwairah!!... Nuwairah!!!.."
" Na'am Hajia.."
" Kawo min yarinyar nan".

Rungume a jikin Nuwaira suka fito an sake mata wanka sai dai babu kayan da zata saka hakan yasa aka maida mata da nata bayan an wanke shi har ya bushe.

Moopu kuwa na ganin sa sai ta 'kura masa idanu duk da bata shiri da shi sosai amma kunsan yaro wanda ya saba gani shine nasa sau da dama zaki ga yaro na 'kin mutum agida amma dazarar kun ke6e inda bb kowa da ya sani sai kaga ya za6e ka akan sauran....
Chapter 102 · 0% Book details