Sashe 44
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kicin- kicin Adam yayi da fuska, taya ma zai yi saurin ha'da shi da Allah kan wani shirmen sa can, da can bai san da girman Allahn bane yake sheke ayar sa batare da tsoron sa ko sanin girman sa ba, ko ko bai ta6a tunanin akwai ranar da Allah da kansa zai yi ram da shi ba bane, shin jira yake a sanar dashi cewa ya girmi irin wannan abubuwan ko ko jira yake sai shekarun nasa da kansu sun sanar da shi?
" In yi hakuri kace...? Laifin me kayi min ni kuma?"
Adam ya tambaya cike da 'karfin hali, baya jin idan ya cigaba da tsayawa gaban mutumin nan da wani lokaci za'a iya samun numfashi tattare da shi a yadda yk jin 'kirjin sa....
" ba hurumi na bane ban kuma cancanci hakuri daga gareka ba ni ko kadan ma ni bani da alaka da hakan, meyasa kake bani hakuri...?".
Adam ya 'karashe da fitar da huci mai zafi yana jin kansa na 'ko'karin juyawa.
" Ni dai nace kayi hakuri.."
Shima 'Dan maliki yayi saurin taran sa da fa'din hakan, bai kuma sarara ba yaci gaba da fa'din" nasha yi maka bayani abaya ba sai na sake maimaitawa yanzun ba Adam, dan hk akan abinda ya riga ya wuce nake baka ha'kuri ka yafe min, abinda idanun ka suka gani yau kuma shima zan iya cewa kayi hakuri, nasan bai kamata in budi baki in furta kalmar hakuri agare ka ba kamar yadda nasan ban cancanci zama uba ga mutun kamili irin ka ba saboda kalmar hakuri tayi ka'dan, amma dan Allah Adam ba dan niba, ba kuma dan halayyata kar ka dubi wannan ka gafarce ni, hakika na matukar jin kunya gami da nadamar abinda ya faru, nasan ban kyauta ba, ban kuma yi amfani da lokaci na ta hanyar da ta dace ba, ban yi ribaci arzikin rai da lafia da Allah ya azurta da su ta hanyoyin da suka dace ba sbd son zuciya ta, na manta da shekaru na, na manta cewa lokaci na nake kararwa a banza, na manta cewa watarana Allah zai iya kunyata ni dan mutuncin da jama'a ke gani na da shi zai iya tafiya, na manta cewa mutuwa na iya riskata a kowani lokaci, hakika nayi nadama Adam ban kuma ji dadin yadda ka tarar da ni ba..."
" Hmm.."
Adam yace yana gyara tsayuwar sa gami da kawar da kai gefe, daga shi har kalaman nasa babu wanda yake jin suna shigan shi bama ya jin cewa nadamar yayi dagaske kamar yadda yake zayyanawa...
" Me kuma yayi saura...?a ganin sa komai ma ya kare ne, babu wani sauran mutuncin da ya rage musu..."
Wani kallo Adam ke yi masa irin kallon nan na ka ma raina wa kanka hankali har ya kai 'karshen maganar sannan cike da bakin rai idanun sa jajir banda huci da yake ji na fito masa daga 'kirjin sa.
"...ni duk ba wannan ne ya kawo ni ba, abinda ya kawo ni gare ka daban ne, tsarin rayuwar ka taka ce, mutunci naka ne...so ka zubda su ko kuma ka basu daraja wannan duk ra'ayin ka ne ba damuwa ta bane ba kuma sune a gabana ba, ka aikata duk son zuciyar ka rayuwar ka ce kai kadai..amma da irin wannan kake so ni in dawo gareka na rayu tare da kai..?"
Kai ya girgiza yana fa'din" har abada! kamar yadda abaya ka horar da ni da rashin zama tare da kai ka koya min rashin shakuwa da kai da ma kowa naka toh akan hakan na ginu kuma har gobe, har jibi, satikai watanni, shekara shekaru ma bana jin hakan zai canza a zuciya ta"
Ya 'karashe da fitar da numfashi me zafi, shikan sa fa'da kawai yake dan ya karasa jagula lissafin Alhajin ba wai dan dagaske abin bai dame sa ba kokari sosai yake wajen dannewa, 'dagowa yayi ya dubi gefen da 'Dan Maliki ke tsaye kallo 'daya yai masa ya 'dauke kansa, duk yadda yk jin kirjin sa na tsanan ta ciwo amma ya kudurta cikin ransa cewa a yau 'din sai ya isar da sakon da ya kawo shi, duk da ba da irin wannan niyyan yazo ba amma yanayi yasa manufar sa dole ya canza dan hk ya cigaba...
" Alhaji bazan iya rayuwa da mutumin da son zuciyar sa ya rufe masa ido ya hana shi ganin dai dai ba, son zuciyar sa bai sa ya iya yakan zuciyar sa wajen ganin ya bar ko guda cikin halayyar sa ba, bayaga haka ma ni miye nawa? miye laifi na aciki? ko laifi ne zamtowa da nayi matsayin 'da awajen ka? Ko kuwa rashin kirkin da baka 'karasar kan mahaifiya ta tun a wancan shekarun bane kake 'kokarin 'karasa shi akaina? Me na maka da kowani lokaci baka da buri illah ka tozarta ni? Me nai maka da bazaka barni inyi rayuwa ta cikin salama irin wacce nayi abaya tun ina yaro ba? naace bana bu'katar tallafin ka bana bu'katar komai daga gareka, bana bukatar duk wani abu daya dangance ka meyasa bazaka barni ba? Meyasa sai ka shiga rayuwa ta a koda yaushe? Ban rayu da sanin inada mahaifi ba tun alokacin da na fi bukatar hakan meyasa sai yanzu?... sunan ka ka'dai da na kasance tare da shi illah ya yiwa rabin zuciya ta a karo na farko..."
Ya fa'di hakan yana me 'daura hannun sa bisa kirjin sa saitin zuciyar sa, yana sake tuno yadda Hajiyar sa tayi amfani da sunan 'dan Maliki ta tarwatsa masa tsaftatacciyar soyayyar sa ta rushe duk wani burin sa kan Zaitun.
" Kasantuwar ka tare da ni a kullun sake illata ni yake Alhaji so kake in bar maka duniyar ne ko gani na a duniyar gaba 'daya ne baka bukata?...in haka ne dan Allah kawai ka kashe ni Alhaji! kasa hannun ka ka rabani da numfashi na lokaci guda ba ka ringa kashe ni kowacce rana ba Alhaji, ka 'dauko makami ka kashe ni nima in huta a duniyar nan baki 'daya....."
Ya karashe maganar a 'dan zafafe yana jin zafin zuciyar sa na karuwa dai-dai da sau'kar tagwayen mari da ya ziyarci gefe da gefen fuskar sa a lokaci guda.
Bai damu yasan waye 'dayan da ya mare shin ba illah hannu 'daya da ya kai ya dafe gefen kuncin da ya tabbatar hannun 'Dan Maliki ne ya sau'ka a wajen, hawaye yaji ya cika masa idanu lokacin daya tsinkayi sautin muryar Hafeez yana fa'din" baka da hankali ne Adam..haba!..Haba dan Allah Shaheed ina ilimin ka da sanin yakamatan ka ya tafi? mahaifin ka ne fa kake furta masa irin wannan kalaman...?"
Kan gwiwowin sa ya sulale ya sau'ka a hankali cike da raunin da dole idan ka dube shi sai ka tausaya masa, dai- dai lokacin da hawayen da suka cika masa idanu suka gangaro, sarai yaji abinda Hafeez ya fa'da amma bai bi takan zancen ba kamar yadda bai damu yasan iya tsawon lkcn da Hafeez ya 'dauka tare da su a Palorn ba, yana shafa gefen fuskar tasa hawaye masu zafi na sau'ko masa idanun sa kan 'kafafun 'dan Maliki yake fa'din.
"....Ka mareni..?
da hannun ka ka mari fuska ta yau Alhaji..? abinda na da'de ina mura'din gani? abinda na jima ina son ganin ya faru dani, abu guda da nake tsananin so nima inga mahaifina ya min watarana amma ban ta6a samu ba, ban ta6a yin arzikin samun hukunci daga mahaifi na bisa wani laifi ba ko daidai da rana guda ba...Hafeez yau Alhaji mari na yayi da hannun sa saman fuska ta...".
Hawaye Hafeez ya share da sauri yana jin tausayin abokin nasa na sake cika shi, batun yau yake jin tausayin abokin nasa cikin ransa ba, batun yau yasan babbar damuwar sa ba a rayuwa dan kusan duk wata damuwar Shaheed da Hafeez yake tattauna ta, shiyasa shima yake matukar kaunar sa har cikin ransa yake kuma biye da duk wasu lamuran sa na rayuwa, yasan bai ta6a samun yadda yake so daga mahaifin sa ba, ya rayu cikin tsananin kewar abubuwa da dama cikin rayuwar sa, duk kuwa yadda yake 'kaunar ganin ya kasance tare da mahaifin nasa amma bai ta6a nuna hakan a fili ba.
Yasha kama shi yana share 'kwalla a duk lokacin da ya ziyarci gidan su ya kuma ga yadda mahaifan sa ke nuna kulawa da yin nan nan da shi, sau tari idan mahaifin Hafeez ya zaunar da su yana musu fa'da kan wani abin ko kuma nasiha kawai game da halin rayuwa Adam da hawaye yake tashi a wajen dan shi bai ta6a samun irin haka daga nasa mahaifin ba, ko da fa'da mahaifin sa ya masa har ta kai ga hukunci hakan ba karamin birge Adam Shaheed yake ba har wani sa'in ba ya iya yin shiru ya kance " Hafeez kai kam kaji da'di..a kullun mahaifin ka burin sa shine gyara goben ka sa6anin ni da neman dukiya kadai ce agaban nawa mahaifin ba shi da damuwa da ni, irin 'dan hukuncin nan da ake samu wajen mahaifi ban ta6a samu ba, ba wai dan bana yin laifin ba kuma kawai dai bani da wannan gatan ne..."
Sosai Hafeez ke tausaya masa duk da yake bashi da matsala wajen kulawar uwa dan Hajiya Talatu ta toshe duk wata kafa da zai iya sawa yaji cewa shi 'din maraya ne, amma ai dole ya ringa jin ba dadi idan ya tuna mahaifin sa na raye amma ba shi da damuwa da shi sam ba shine gaban sa ba yana nan ne yana rayuwa tamkar wanda mahaifiya da mahaifin sa suka bar duniya gaba 'daya, shi bai ma ta6a jin me irin makamanciyar tasa rayuwar ba.
Duk da hakan a matsayin sa na aboki kuma me son ganin farin cikin sa yakan taushi zuciyar sa da furta masa kalaman kwantar da hankali sosai yake kokarin ganin ya nuna masa muhimmanci da kuma kaunar da mahaifin sa ke masa duk da bashi da tabbaci kan hakan amma mawuyaci ne ace mutun da 'dansa kuma ce babu kaunar dan nasa tattare da shi.