Sashe 49
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Hala da kafa ta kika shigo gidan..?"
Shiru Zaitun tayi tana kallon fuskar ta, mamakin yadda Hajja Ladin ke mata kallon da ta tabbatar ba na arziki bane take da kuma take mata magana wani iri, hakan yasa bata iya bama Hajja Ladin amsar maganar ta ba sai ma wara idanuwa da tayi kan fuskar ta.
"...'daddaure ki aka yi ne aka shigo dake dole?"
Tsayuwar ta daidai ta da kyau sannan ta cigaba da fa'din " Ga hanya zaki iya tafiya ai tunda ke shashasha ce...mthew"
Ta karashe da jan tsaki.
Har ta fara tafia sai ta kuma ta waigo.
" Ki sani ba'a ganganci a gidan nan gara in fada miki, Ammi tace in nuna miki 'dakin da zaki zauna kafin ta dawo sauri nake ina da ayyuka a gabana kar ki 6ata min lokaci..."
Ta 'karashe da juyawa da nufin tafia inda zata nunawa Zaitun 'din.
Ko alama bata yi na nuna cewa tana da niyyan bin Hajja Ladin ba, saima tsayuwa da ta sake gyarawa tana juya maganganun ta, ta kasa fahimtar manufar ta na cewa ba'a ganganci a gidan nan, menene manufar Hajja Ladin ta kasa fahimta.
Hajja ladi da taga bata da alamun bin ta tsaki kawai tayi ta koma kitchen ta cigaba da ayyukan ta, ranta na sake suya da bakantuwa bata sake bi takan Zaitun ba.
Tana nan tsaye har Matar da ta kawo ta gidan ta kuma saukowa cikin sabuwar kamilalliyar shiga hannun ta rike da hand bag 'dinta fuskar ta 'dauke da yalwatacciyar murmushi banda sassanyan kamshi da ke mata rakiya.
" Ah ah Zaitun ya haka? Har yanzun baki zauna ba? Ina Hajja Ladin bana ce ta nuna miki 'dakin ki ba...?".
'Dan cunno baki tayi gaba gami da kawar da kai tana fadin
" Hajiya ni gaskiya bana so dan Allah ki mayar dani ko kisa a maida ni.."
Ta 'karashe hawaye na sakko mata.
'Yar dariya Hajiyan tayi marar sauti tana me 'karasowa gaban Zaitun tace, " ki dube ni matsayin uwa Zaitun bazan cutar da ke ba kinji, zanje Abuja yanzu idan na dawo zamu yi magana, amma ki kwantar da hankalin ki dan Allah bana so in dawo in samo ki cikin damuwar nan, ki saki jikin ki babu abinda zai same ku kinji...?"
Shiru Zaitun tayi tana duban ta bata iya tace komai ba illa hawayen dai.
Hajja Ladi Hajiyan ta sake kwalawa 'kira da sauri ta fito ta iso inda suke tsayen.
" Kinji abinda na gaya miki ko Hajja Ladi, dan Allah a kula da ita kafin na dawo, dauki kayan ki taya ta ku je 'dakin ki nuna mata komai, ni na tafi..."
Kai ta jinjina hankalin ta duk na kan Zaitun tana binta da wani kallo tace.
" Toh Ammi a dawo lafiya...".
Jakar ta 'dauka ta nufi wani hanya.
Ita kuma Hajiyan tana kokarin fita da hanzari ga dukkan alamu dai saurin dagaske take kamar yadda ta fadi, 'kila tafiyar gaggawa ce ta same ta.
A hankali ta 'daga 'kafa ta bi bayan Hajja Ladin bayan ta tabbatar da cewa wacce ake kira da Ammin ta fita..da alamu kuma su ka'dai suka rage cikin gidan dan shiru yk sosai bb alamun kowa.
Cikin wani makeken 'daki da yaji komai na more rayuwa aka sauke ta, komai da yake 'dakin mai kyau ne me kuma bala'in birgewa.
Kasa motsi Zaitun tayi saboda tsoro.
" Anan zan zauna...?"
Ta tambayi Hajja Ladin maganar ta na har'dewa tana sake bin 'dakin da kallo.
" Haka Ammi tace!"
"...Hmm..kema kinga abinda na gani kenan?"
Tayi maganar ne tana duban Zaitun sannan ta cigaba.
" Ni kaina naga rashin dacewar ki da wannan muhallin saboda sosai yafi 'karfin mutun irin ki...".
Shiru Zaitun tayi tana mata kallon mamaki, bata zaci wannan kalmar ne zai fito daga bakin ta ba.
Wai wannan matar me take nufi ne..?
Har ta juya zata fita sai kuma ta waigo"..Ya sunan ki?"
" Zaituna!".
Ta bata amsa kai tsaye idanun su sarke cikin na juna kowa abinda ke cikin ransa daban.
" Toh Malama Zaituna zaki cigaba da zama anan kafin masu gidan su dawo.."
Ta 'karashe maganar da bankawa Zaitun muguwar harara sannan tayi gaba.
Jikin ta sanyi qalau yayi haka ta cigaba da tsayuwa tana sake rungume Mufee da kyau, hakika ita kanta taga rashin dacewar ta da 'dakin, bama gidan Hajjaju ba, ko lokacin da take gidan Dr Rasheed 'dakin ta bai ko taka 'kafar wannan a kyau ba.
Sai ma ta kasa ko da 'daga kafafuwan ta balle ta kai ga neman wajen zama illa sake karewa 'dakin kallo da take daga nan inda take tsayen, sai ta da ta ji 'karfin ta na 'ko'karin 'karewa ne sannan ta nemi wajen zama kan sofa ta zauna daidai da tashin mufee a bacci.
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauqe ganin tashin yarinyar, kaso guda daga cikin damuwar ta tuni taji yayi nasa waje..zaka yi mamakin ganin murmushi saman fuskar ta tana 'dago yarinyar suka fuskanci juna.
"..'yan mata na an tashi a baccin ?".
Shiru Mufeeda tayi tana duban fuskar Zaitun sosai tamkar wacce ke karantar wani abu.
Fa'da'da fara'ar ta Zaitun ta yi tana kamo kumatun Mufee.."...Mamana kina mamakin gani na tare da ke ko..? na dawo gareki yanzu sai dai gamu cikin wata 'kaddarar da muka kuma fa'dawa, ban kuma san ta mecece ba ita...amma koma miye Insha Allah ina nan tare da ke babu wanda zai raba mu, a shirye nake da koma menene a yanzu, tunda muka tsallake shari'ar nan Insha Allahu babu abinda zai sha gaban mu da zai fi 'karfin mu kinjj, Allah na nan tare da mu..."
Kusan za'a ce ita ka'dai ke sumbatun ta dan Mufee ba fahimtar ta take ba, kamar yadda ba magana take ba balle ta amsa ta, amma ga mamaki na a yadda Zaitun 'din ke mata maganar itama sai ta washe baki tana fara'a irin tasu ta yara.
Wanda ya matukar faranta ran Zaitun, sosai ta fahimci Mufeedan tata, tana dariya ne saboda ganin ta da tayi, ba mamaki ta riga ta cire rai da hakan, duk da yake yarinya ce amma farin cikin ta kasa 6oyuwa yayi da ganin Zaitunan shiyasa tayi 'yar dariya.
Can kitchen kuwa Hajja Ladi ce ke faman yanka albasa bisa chopping board da zafi zafi tamkar zata ha'da da yatsun hannun ta ne ta yanke su tare, ranta duk a jagule hatta da saman fuskar ta bai 6oye tsananin 6acin ran da take ciki ba...tun dawowar ta daga kai Zaitun 'daki bata sake yin wani abu cikin natsuwa a kitchen 'din ba...dan ma ba ita ka'dai ke aikin ba da tuni tayi kwa6a wajen girkin.
Raleeya duk na lure da ita, ta kuma riga tasan ainahin matsalar Hajja Ladin, tasan meke saurin ba'kanta mata rai a cikin gidan nan, ta lura Hajja Ladi ta sani taga kowa matukar ba ahalin masu gidan bane ya 'dara ta ta wani fanni.
'Yar murmushi tayi ta gefen baki da ko da ace kallon ta kake bazaka fahimci abinda tayi ba balle baka duban fuskar ta.
Bata kalli Hajja Ladin ba tace " Ni kam Hajja Ladi lafiya...? tun 'dazun naga kamar ranki a 6ace...".
Shiru tayi bata tankawa Raleeya ba, sai da ta sake yi mata tambayar kafin ta saki tsaki sannan tace.."...Ni da ba'kuwar Ammi nan ce wlh, ta fiye taurin kai..."
Ta 'karashe da jan wata guntuwar tsakin kuma.
" Ayyah ai kinsan wasu mutane haka suke sai hakuri ba mamaki halayyarta ce.".
"...Hmmm"
Tace sai kuma tayi shiru.
Bayan wasu 'yan sakanni ta sake fa'din..." Ammi ta wuce Abujan yau da alama tana sauri ne..tace taro zasu yi da yamma a yau 'din"
" Allah ya dawo da ita lafiya, zata da'de ne..?"
Cewar Raleeya.
" Gaskia ban sani ba dan bamu yi maganar da ita ba.."
" Ta ina zaku yi maganar bayan kin 'kunsa ba'kin rai a zuciyar ki ..."
Cewar Raleeya cikin ranta.
Yayin da Hajja Ladi ta cigaba da fadin.
" Wai kuwa kinsan inda Ammi ta sa na sauke bakuwar nan...? abun mamaki.."
Cewar Hajja Ladi da ta tattara hankalin ta gaba 'daya kan Raleeya da alamu ta shirya fidda komai dake ranta ne.
Raleeya kam bin ta tai da idanu kawai tana sauraron jin 'karshen zancen cikin ranta take fa'din.." _Ai dama na sani, tatsuniyar gizo kenan_ ..".
"...'Dakin 'diyar ta da ta rasu fa, kinsan kyan 'dakin kuwa amma a rasa wa za'a bu'dewa 'dakin sai wannan yarinyar...".
" Hajja Ladi su da gidan su, ai su ke da ikon saukar da duk wanda suka ga dama a kuma duk inda suka so, mu miye namu...a hakan ma ai muna samun bakin rabon mu..".
"...Hmmm..."
Hajja ladi tace bata 'kara wata kalma a zahiri ba, cikin ranta take ayyana da alamu Raleeya bata fahimtar inda tunanin ta ya dosa, dan haka bata 'kara maganar da ita ba taja bakin ta tai shiru.
Tunowa da Zaitun tayi bata yi sallah ba yasa ta mi'ke sai da ta tabbatar ta rufe 'kofa da kyau sannan ta shiga, wanka tayi mai kyau da ta jima rabon da tayi irin sa, ruwa mai 'dumi sosai ta ha'da ta tayi wankan da shi ta wanke kanta sannan ta 'dauro alwala ta fito.
Tsab ta shirya cikin kayan ta da ke shirye a leda tun ranar da suka fito da Hameeda aka kama su.
Salmerh 😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
_Wattpad@_
_Serlmerh-md_
🅿️ *...31*
......Koda ta idar da sallar bata tashi a wajen ba, komawa tayi ta kwanta bisa daddumar ta lumshe idanu, tunanin rayuwar ta ne yake dawo mata daki daki, 'kwalla ne suka fara gangaro mata tayi saurin goge su.