← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 218

Sashe 89

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zauna ne tare da su Ammi acikin gida.
Ita ta maye gurbin Rayyan a asbitin da yake aiki ta 'dan fita saboda Ammi tace zama waje 'dayan babu da'di sam.

Bayan auren sa da Nadia da shekara biyu mahaifin Amrah ya fara yiwa Alhaji Rufa'i zancen auren Rayyan da Nadia, dayake duk sun san da zancen dan anyi sane tun Alhaji Sa'ad Auta na raye wato mahaifin Rayyan.

Shima Alhaji Rufa'i bai yi 'kasa a gwiwa ba yace tabbas shima ya fara tunanin hakan, domin zama da al'kawari aka babu da'di gwamma a sau'ke shi.

Musamman a yanzu da ya tabbatar Ammi sun damu da rashin haihuwar sa duk da sun san Allah ke badawa amma suma yun'kurin su ba laifi bane acewar sa.

Ko da aka sanar da Rayyan sam bai wani damu, cikin ransa ya ce su suka sani, komai ma suyi shi yanzu bashi da bakin tankawa, ya riga yasan ba kowacce mace bace zata iya zama da shi in bama irin Nadian ba, yasan ba 'karamin ha'kurin zama take yi da shi ba, tana son shi shiyasa take jure duk wani rashin kirki na sa, yasan ana aure ne saboda kiyaye iyakokin ubangiji amma gundarin zaman auren ba shine gaban sa ba a yanzu.
Itama Nadian ba samun kansa take ba balle kuma wata Amra da ko sanin ya kamannin ta yake ma bai yi ba.
Menene amfanin tara mata bayan ba iya kulawa dasu yake ba sai dai yasan ko kwana zai yi yana fa'da babu wanda zai saurare shi.
Bayaga haka ma shi da kansa zai so a saukewa Abban sa nauyin al'kawarin da ya 'dauka tun yana raye.

Baya ga haka da sam bazai amince ba, ba iya damuwa yake da sau'ke hakkokin dake kansa yake ba, sbd sam shi mace bata gaban sa a yanzu a, ba 'karamin dauriya yake yi yake bata lokacin sa ba idan ta bu'kaci hakan, duk da yasan ada can baya ba haka yake ba, 'kuncin zuciya ce da damuwa duk suka canza shi.

Sai yaga kamar ta fara shiga damuwa kafin yake bata lokacin sa, a hakan ma sau da dama kwanciyar sa yake yi yace ya gaji, bata nuna ta damu sai dai yaga tana ta sallah tana addu'o'i atimes har sai yaga tana kuka...zata 'daga hannu ta jima tana addu'oi kuma yasan hadda cikin addu'o'in nata tana matu'kar bashi tausayi amma ya kasa canzawa.

Ya jima da sanin halin Nadia, ba 'karamin ri'ko tayiwa addinin ta ba, gata kamilalliya natsuwa da ilimin ta take komai.
Ganin yawan damuwar da ta keyi yasa shi ya 'dan sassauta mata yana 'dan bata lokacin sa babu laifi.

Ada idan ta shine zai 'dauki a'kalla watanni biyu ma bai waiwaye ta ba amma yanzu yakan bata hakkin ta babu laifi.
Hakan ma dan ita ne saboda yasan tana 'kaunar shi sosai kuma tana da natsuwa.

Amma tun bayan da aka aura masa Amrah da akayi sai ya koma halin sa na baya, bai damu da ita ba balle ya damu da hakkin da Allah ya 'dora masa.

Sai ya shafe tsawon wata ko fiye da hakan ma batare da ya kusance ta ba, hakan shiya jefa Amrah cikin wani hali, gashi bazai ta6a zama suyi hira ba balle ya fahimci damuwar ta.

Cikin rashin sa'a shai'dan ya rinjaye ta ta fa'da harkar maza, dama can ta saba abinta kuma tun tarayyar sa da ita na farko ya fahimta amma bai tanka mata ba, me ma zai ce da ita toh.
Duk abinda yayi tamkar ya bayyana sirrin auren sa ne,

Auren ta ne ya sa ta sarara wancan halayyar har ma tayi alwashin dainawa, but rashin samun kula daga gareshi yasa ta komawa ruwa.

Tun lokacin da za'ayi auren sa da Amrah dole Nadia ta bar gidan Ammi ya ha'da su a can wani gidan sa da yake babba wadattace, tare suke a gida 'daya amma babu wanda zaman 'dan uwan zai takurasa.

Ko da ya tashi komawa bai yadda ya koma da ko 'dayan su ba, haka yayi bankwana da gida bayan ya barwa Sultan babban garga'di kan kulawa da kuma takatsan-tsan da komai nasu.
Haka kuma bai tafi ba sai da ya tabbatar ya zuba securites wadattu cikin gidan nasu saboda Ammin sa da sistern shi ya kuma zuba a nashi gidan a lokacin ma already Sultan ya bar aikin sojan da aka sanya ku'di wajen sama masa dan acewar bazai iya ba akwai wahala.

Haka rayuwa ta cigaba da gurgurawa, yau da'di gobe akasin haka tun Ammi na saka ran dawowar sa har ta ha'kura sai dai kawai suyi waya da shi suyi video call yana kuma tambayar wani matsala idan akwai...

Cikin hakan Ammi ta sanar da shi Sultan zai koma running ma'aikatar su ta Lagos dan tun rasuwar mahaifin su Kabeer ne kan 'dan kulawa da su yanzu kuma babu kowa da ke kula da su.

Sam Rayyan bai ji da'di ba amma babu yadda zai yi, ko da yy mata maganar ya za'a bar gida ba kowa sai su ka'dai ga Marwa ma idan Sultan ya koma Lagos Ammi taje Abuja ya Marwa zata yi, sai cewa tayi ai Marwan na makaranta dan badan differing da tayi bama da yanzu ba wannan labarin ake ba da tuni ta 'kare, amma a'kalla ta shafe 2 yrs batare da je makarantar saboda rashin lafiya da kuma abubuwan da suka yi ta faruwa abaya.

Dan haka tace da shi bakomai ai zata iya zama tunda aikin ma ba kullum bane kuma akwai Hajja Ladi ma babbar mace ce suna tare a gidan..
" Um-um fa Ammi kinsan mutane..."
" kar ka damu ba komai na yaba sosai da matar ne shiyasa kaga ban damu ba...kuma ma baga can gidan ka ba in tana so zata iya zama acan.."

Shi dai dama sam ba ya son wannan aiki na Ammi tunda da'dewa ya kuma yi iya yin sa akan ta barshi ta 'ki.
Ko Sultan 'din ma Rayyan cewa yayi ina ma laifi yayi aikin a companyn su na nan Kano tunda duk Alhaji Rufa'i aka bari da nawi..amma Ammi tace ya barshi tunda can 'din ya za6a.

Cikin rashin sani basu san cewa Sultan ya hari can 'din bane saboda wancan na Lagos 'din yafi girma da tsari.

Ko da ya koma can 'din kuwa sai da ya tabbatar da cewa ya sa6unta abubuwa masu dama bisa tsarin sa hatta ma'aikatan sai da ya tabbatr ya zuba nashi kafin ya baro ya sake dawowa na nan Kano din..bayan ya tabbatar duk wani share na riba da company zai cire yana da kaso guda daga ciki batare da sun sani ba direct account 'din sa ku'din ke shiga.

Shekarar Rayyan biyar da fara makarantar sa kafin ya kammala inda ya dawo gida matsayin cikakken lawyer mai zaman kansa....Ammi ta sha mamaki sosai ta kuma rasa dalilin wannan canjin nasa...shrmekaru biyar kenan da auren sa da Nadia yayin da auren sa da Amrah yake da shekaru uku...yayin da shi dududu yake da Shekara talatin da 'daya da haihuwa...Sultan kuma ashirin da Bakwai.

Yakan yawan ziyartar matan sa duk bayan watanni shida, duk da nisan waje amma dayake shi ya 'daurawa kansa sam baya gani...sai dai wani abinda Allah ya 'dora masa duk cikin matan sa ko 6atan wata babu wacce tayi acikin su.

Tun fahimtar halayyar Amrha da Sultan yayi shima sai ya saka kansa ya fara bibiyar ta bai sha wani wahala ba kuwa ya amince, dama ya jima yana neman hanyar da zai dur'kusar da Rayyan sai ya gashi ya samu cikin sau'ki...Tun fara harkar su da Sultan sai Amrah ta daina fita da kowa sai shi ka'dai dan ya tare ko'ina ya kuma yi mata kashe din ya sake ganin ta da wani zai tona ta wajen mijin ta ne babu ruwan sa, yace mata shi yasan ko sha'rai za'ayi iyaka ai masa bulala ne tunda ba aure shi ba amma ita hukuncin kisa ne nata, hadda kwatanta mata yadda ake kisan mazinaci abinda ya kara tsorata Amrah kenan yasa take biye masa batare da ta sa6a dokar sa daidai da rana guda ba.

Salmerh😘
[19/10/2022, 6:11 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...54*

.......Amrah bata da wayo sam shiyasa duk umarnin da Sultan ya 'dora akai bi take yi, a hankali ta fara jin tamkar tana son shi kuma tana jin dadin mu'amala da shi, duk da cewa kuwa a wannan daowa ta Rayyan shima ya canza, walwalar sa ta dawo sosai, kula da tattalin da yake basu ya bambanta dana baya...amma duk da haka bazata iya sa6a umarnin Sultan ba ko dan saboda rufin asirin ta ma.

Tun dawowar Rayyan daga Uk ya fara samun offer na aiki a wajeje da dama manya da kananun office, bisa shawarar Ammi ya za6i guda ciki ya fara gwada aiki da su.

Gefe guda kuma yana running business 'din mahaifin sa domin tun dawowar tasa ya tarar Alhaji Rufa'i Diabetes ya kwantar da shi jikin sai a hankali, dole ya 'dauki komai na dukiyar su ya dam'ka a hannun Rayyan dama daowar sa yake jira domin bai ya damka a hannun Sultan ba dan ya lura dan nanaye ne shi natsuwar ka'dan ce.

Shima Rayyan bai yi 'kasa a gwiwa ba ya bada gudunmawa iya iyawar sa wajen kula da lafiyar Alhaji Rufa'in...sau'ki ne dai daga Allah dama yake zuwa kuma sai a hankali.

A ta'kaice yanzu Rayyan Dr ne shi, kuma Barrister ne, CEO ne a companyn mahaifin sa da ya mutu ya bari wato INFINITY GLOBAL COMPANY...kuma duk cikin wa'dannan babu wanda bai 'kware a fannin ba.

Yayin da 6angaren Sultan.wannan abinda Alhaji Rafa'in yayi ya sake 'kon masa zuciya, tsanar Rayyan ta dasu aransa sosai haka ma ta Alh Rufa'i da bai bashi komai kafin dawowar Rayyan ba.

Abinda ma ya 'dan.sanyaya masa zuciya shine gani da yayi Rayyan ya jawo shi ajiki komai da shi ake, koka'dan Rayyan bai bar 'kofar da har wani zai iya zargin shi 'din ba jinin su 'daya bane da juna musamman ma da yake tun tasowar su ba'a nuna musu hakan ba.
Chapter 89 · 0% Book details