← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 218

Sashe 186

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rikice take gaba 'daya tsoron ta 'daya kar Sultan ya tona sirrin ta awajen su musamman da ta san hadda Rayyan aka je.

Wannan wace iriyar masifa ce, inba nacin tsiya ba an riga an kulle mutum miye na sake ziyarta sa..?

Gani kawai take tamkar zuwan ta ne shine mafita inyaso duk ma mene zai faru ta kwammaci ya faru akan idanun ta...'kila hkn ya hana Sultan furta wani abu daya dangance ta, hakan yasa batare da sauraran shawarar da 'daya 6arin zuciyar ta ke bata ba kawai ta 'dauki hanya tabi bayan su.

Duk yadda tayi ta zuba uban gudu bata ha'du da su suba har ta isa bakin gate 'din Prison 'din.

Da 'kyar ta samu aka barta ta shiga sai da aka kai ruwa rana, a hakan ma sai da ta dangana da cewar ita matar Rayyan Sa'ad ce kafin ta samu alfarmar shiga.

Rayyan rungume da 'diyar sa a kafa'da Marwa na bin bayan sa suka shiga, su ma 'din sun 6ata lkc sosai kafin aka fito da shi...dan dole sai anyi wasu bincike bincike da cike - cike.

Rayyan na ganin an fito da shi ya tashi ya bar wajen zuwa wani wuri can daban ya bar Marwa...cikin ransa yk kissima iya lkcn da ya yanke musu su zanta.

Ita kam baki ta rufe ganin sa da uniform din Prisoners da babban numbern sa a gaba da bayan riga...ga wasu karfafa biyu masu gadin sa abayan sa.

Kuka ta saka sosai shima hawayen ya fara da ganin ta, dan bai ta6a zato ba..da gudu taje ta rungume shi amma Sultan bai iya yy kamar yadda tayi masa ba.

Marwa sai ma ta kasa fa'din komai sai kuka har sautin kukan na bayyana a sarari...
Sultan ne yy 'ko'karin raba ta jikin sa yana me saukar da idanun sa kass.
Baya ka'dan Marwa ta ja ta zauna a kujerar da ta tashi dafe da kanta domin jiri take ji na shirin 'diban ta...

" Allah ya sani tana son Sultan da dukkan zuciyar ta shiyasa duk abinda taji akace ya aikata bb 'daya da yy tasiri a zuciyar ta, ta kasa yadda akan shine ya aikata sbd ta yadda dashi 'dari bisa 'dari.

Abinda ya fara zuwa bakin ta bayan ta zauna 'din .." Yah Sultan shine ka biyewa yaya kace mishi wai ka sake ni ko..?"
" Ba cewa nayi ba Marwa...rubutawa nayi da hannu na..."!
Idanu ta waro akan sa..amma sam Sultan ya kasa ha'de idanu da ita.
" Yah Sul..tan"
Ta kira sunan shi cike da rauni jin abinda yake cewa.
" Kiyi hakuri Marwa, babu yadda zanyi, sakin ki a wancan lkcn ya zame min dole ne ki fahimce ni...".
Kuka ta sanya mai ban tausayi, cikin kukan take fa'din" Ba dole bane Yah Sultan, ni ai bance maka ka rabu da ni ba, bance maka na gaji da zama da kai ba, bance maka bazan iya rayuwa da kai cikin ko wani irin hali ba, meyasa zaka biye musu? Meyasa zaka yanke hukunci batare da kayi shawara da ni ba..? Yah Sultan ko tsawon wani lokaci zasu ri'ke anan ai zan zauna ina jira ka har ka fito mu cigaba da rayuwar mu tare meyasa kayi saurin rabuwa da ni Yayah...?"
Ta karashe cikin kuka sosai mai ban tausayi.

Murmyshi Sultan yy 'yar ta'kaitacciya yana mai kawar da kansa gefe ga inda Rayyan ke tsaye..amma bashi yake gani baba, bayan sa yake ka'dai yake iya gani sakamakon baya da ya juya musu.

" Ba lallai ba Marwa, ba lallai ki iya jira na ba..ni fa nan yanzu shine gida na, bani da ranar fitowa Marwa, jama'ar gidan nan sune 'yan uwa da dangi na...bani da ikon sake rayuwa a waje kamar yadda nayi abaya, nan zan cigaba da zama har 'karshen rayuwa ta...kinga kuwa idan ban yanke igiyar auren mu bama ai nna shiga hakkin ki...."
Kuka sosai Marwa ke yi, tace" Ka daina fa'din haka Yah Sultan kana sawa inji na karaya baki 'daya.. ni bazan iya barin ka ba, bazan iya barin ka cikin wannan halin ba, zan ro'ki Yayah ya san yadda zai yi a fito da kai...".
Wani murmushin ya kuma yi da kana gani kasan na nadama ne. yace" Ke yarinya ce Marwa...bazaki ta6a fahimtar wasu abubuwan ba...Yaya Rayyan ai jarumi ne nasan zai iya fiye da yadda kk so ma, amma a halin yanzu ni kaina bana bu'katar rayuwa a waje kamar rayuwa ta baya, na fi so na girbe hali na, na cutar da ku Marwa sosai, na cutar da ahalin ki ta yadda baki ta6a zato ba, nasan bazaki rasa jin wasu daga cikin abubuwan da na aikata ba, ina kuma tabbatar mk hakan 'din ne na aikata Marwa ba sharri akayi min ba..."
A hankali ya tako gaban ta ya durkushe bisa gwiwoyin sa sannan ya cigaba..." buri na dama in ha'da idanu dake ko da sau 'daya ne kuma Alhamdulillah kin zo da kanki waje na..hakan ka'dai da kk yi min bazan ta6a mantawa da shi a rayuwa ta ba... ngd sosai Marwa, abu na biyu da zaki yi min ki yafe min dan Allah, ki ro'kar min Ammi, Yayah Rayyan da Raihana duk su yafe min sbd Allah...ban yi muku adalci ba, na cutar da ku ina kuma jin takaici da ba'kin cikin hali na a halin yanzu, na ci amanar ki ta yadda baki ta6a zato ba Marwa, na zauna zaman auren ha'inci dake batare da ke kinsani ba, na nuna mk kauna ta 'karya, duk da ban samu yadda nk so ba..naso na haihu dake sbd in gaji dukkan dukiyar ku amma hkn bai samu ba...yanzu ne na fahimci cewa lallai idan Allah ya kare mutum bb wanda ya isa ya cutar da shi face da Allah ya da'da kare shi...dan Allah Marwa ki yafe min... laifuka na sun girmi tunanin ki Marwa, kwakwalwarki bazata iya 'daukan nawin laifuka na ba ko nace zan sanar dake baki 'daya...."

_Me kuke tunanin zai faru....?_

Salmerh😘
[2/9/2023, 7:07 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...100*

......." Nasan kowa yaji me na aikata a duniyan nan sai ya tsane ni, kowa yasan mene hali na na 6oye tsana ta zai yi, ngd sosai da baki tsane ni ba Marwa har na samu darajar da kk iya zuwa waje na duk da abubuwan da na aikata mk..ki yafe min dan Allah...ki yafewa wannan bawa mai tsananin son kansa da rashin tausayin wa'danda suka fi kowa 'kaunar sa a dunia, wa'danda suka nuna masa gatan da ko mahaifan sa basu nuna masa ba..wa'danda suka maishe shi mutum a lkcn da akayi watsi dashi...ki yafe min bisa ga cin amanar da nayi mk Marwa...dan Allah ki......"

Amra da ke tahowa a gigice 'karshen maganar Sultan ce ta fa'da kunnuwan ta ai kuwa batare da ta fahimci komai kan maganar ba kawai suka tsinkayi muryar ta da 'karfi tana fa'din" Ka cucue ni Sultan...baka kyauta min ba, ta ya zaka saka Marwa agaba kana tona min sirri?..taya zaka zauna kana fa'da mata cewa kaci amanar ta? taya zaka fa'da mata cewa Arfan ribar cin amana ne Sultan...?"
Sai kawai ta rushe da kuka ta sauka 'kasa bisa gwiwawoyin ta itama.

A yadda tayi maganar da sauti mai 'karfi yasa ilahirin wa'danda ke keway e da wajen bb wanda bai ji me tace ba, ciki kuwa hadda Rayyan.

Hakan kuma shi ya janyo hankula da idanuwan mutanen gaba 'daya kanta.
Ba Sultan da Marwa ka'dai da har sai da ta ha'da da tsayuwa ba hatta Rayyan juyowa yy yana duban ta cike da tsantsan mamaki da takaici gami da jin haushin ta, me ma ya kawo ta kuma a wani dalilin ta tazo..?"
Ya tambayi kansa.

Marwa da yake ta riga tasan zancen bata iya tace komai ba illa kawai ta dubi Amra ta kuma dubi Sultan da cikin yanayin ya 'dage mata kansa alamar tabbatarwa.

Idanun ta ne suka fara cikowa da sabbin ruwa batare da 6ata lkc ba kuma suka fara gangarowa.
Sultan ta nuna da yatsa bakin ta na motsi amma ta kasa furta komai.

Jikin ta rawa yake sosai, ta riga tasan da batun tun a gida a wancan ranar da Anty Raihana ta bayyana mata shi, sam bata ji ta yadda ba, hkn yasa hatta Zaitoon bata iya ta bawa lbrn ba...tazone dama taji gaskiyar lamarin daga gareshi sai gashi Allah ya turo Amra ta bayyana komai...a wancan lkcn sam sam ta kasa jin amincewa ne amma yanzu da kunnen ta ta tabbatar daga bakin da ta san cewa hakan kawae bazata yiwa kanta sharri ba.

Sultan take nunawa tana son fa'din wani abu amma bakin ta ya kasa budewa.
Da gudu ta juya ta fita bata tsaya ko ina ba sai jikin motar da suka zo ta rungume motar tana kuka sosai, irin kukan nan mai matukar ban tausayi a gani da sauraro.

Ji take ko ina yai mata zafi a duniyan nan, taya hakan zai zam gaskia, taya ma ya faru? Wannan wace iriyar kwamacala ce? ace matar 'dan'uwan ta uwa daya uba 'daya sukayi tarayya da mijinta kuma har da haifa masa yaro...innalilallahi wa inna ilaihi raji un...wannan jagwalgwale har ina..?wace iriyar 'kazamar rayuwa ce wannan?

Ji tayi baki daya duniyan tai mata zafi, ji tayi babu wani sauran farin ciki da ya rage mata a duniyan, ada bata yadda Sultan zai iya aikata kwatankwacin hakan ba amma zuwa yanzu tsoro ma take ji sosai kowa tsoro yake bata ba Sultan ka'dai ba.

Rayyan kallon Amra yake yana 'karawa, mamakin ta duk yabi ya cika shi, kuka take amma bakin ta ya kasa yin shiru, da kanta take faman tonawa kanta asiri a bainar jama'a bacin bb wanda ya nemi ko ya tambaye ta jin wani abu.
Shin tsoro ne ko kuwa firgici? ko kuwa tsantsan rashin gaskia ne ya sa tayi hakan.

Takaicin ta bb inda bai ratsa cikin zuciya da jinin sa ba...har wani 'daci 'daci yk ji ke taso masa tsabar bakin ciki da takaici.
Chapter 186 · 0% Book details